Complete Hausa Novels

Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel

Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 114 of 139

YA ALLAH ALLAH KA JIKAN MAGABATAN MU KA GAFARTA MASU KURAKUREN SU KASA ALJANNAN MAKOMAR MUSULMAI YASA ALJANNA MAKUMAR WANDA YA FURTA KAMAL LA,ILLAH HA,ILLAH MOHAMMADAN RASULULILAH, , , , , , ,

YAN UWA MUSULMAI YA SHAGALGULAN SALLAH DA BANKWANA DA RAMADANA DA FATAN RAMADAN DIN BANA YAZO DA KARA MUNA IMANI A ZUKATAN MU AMIN, , , ,

Ganin da inna tayi na kasa magana sai hawaye ke zuba a fuskana sai kuma ta shiga damuwa lokaci guda ta rude.
Hankalinta ya tashi ta koma fadin ki rufa muna asiri ki rufa min idan da wani abu ki fada min mu san inda zamu bullo ma ko meye matsalan ki da mijin ki yar nan ?
Da kyar na iya budan bakina da yai min nauyi ina fadin inna da matsala a cikin auren mu babba sai dai idan kince na koma mu zauna a hakan zan koma don ke .
Menene matsalan dake akwai tsakanin ki dashi inna ta sake tambaya tana kallona don son jin mezan fada.
Bakina yai nauyi da abinda zan fadawa innan sai kawai naja filo na mayar da kaina tare da sake wani irin kuka lokaci guda mai ban tausayi.
In don matsalan kice da uwar mijin ki wanan ba kanki bane farau ai naji muryan innan na fadi,don da wayau ki kinga irin zaman da mukayi da kakar ku a gidan nan.
Yanzu fa da nayi hakkuri komai ya wuce sai abinda ba,a rasa ba tunda yanzu ta gane gaskiya ita da kanta.
Cikin kukan da nake nayi karfin halin fadi inna matsala ba irin taki bace tawa matsalan daban yake dana ko wace mace inna.
Subbahanallahi wanan maganan babba ke nan ta fada sai kuma tayi shiru na wani dan lokaci can naji ta mike zata bar dakin .
Ta kai kofa ta juyo tana fadin kiyi tunane kafin ki san abinda zaki fadawa mahaifin ku don kin san shi kin san halin sa ta fita.
Ban daina kuka ba sai ma karawa da nayi kan wanda nakeyi da farko don nasan za a rina kan hakan.
Don ba kowane zai yarda da abinda zan fada ba gashi ma ban fada din ba a fahinceni asan akwai matsala akan hakan dana ce.
Haka na kwana ranan tare da dinbin tunane a raina ina nemawa kaina mafita da naga zai dace dani.
Washe gari koda muka tashi inna ta dauki zafi dani sosai ko gaisuwan da nayi mata da kyar ta iya amsa min shi ba cikin dadin rai ba.
Ganin haka yasa nima na nisance ta na koma kuryan daki ban zauna a falo ba yadda muka saba gaba dayan mu.
Kanne na sai shigowa dakin suke suna tambaya ko lafiya nake na zauna a dakin har tsawon kwana biyu muna haka da inna ba wani sakewa a tsakanin mu ni da ita.
Ranan na uku na shirya nake fadin zan je naga maizube tayi min sai mun dawo wanan tafiyan ban yarda na tafi da kowa ba sai karamar kanwa daya dana dauka muka fita tare da ita.
Nayi sa,a na samu malam a gida muka gaisa da matan shi maizube tayi min jegora zuwa wurin malam din.
Ya tareni sosai yana saka min albarka tare da kara ban hakkuri irin na manya kafin maizube tace dashi barin baku wuri ku gana ayi yaushe rabo ko ta fada cikin hikima .
Nace ba sai kin fita ba ai tunda kin san komai tun farko kamar dai yadda kika barmu har yanzu hakan muke dashi.
Ta amsa da fadin eh malam gaskiya kamar yadda dai na fara fada mane zaman nasu ba dadi sai hakkuri.
Ga kuma fannin uwar mijin nata shima dai babu dadi har yanzun din don kiyayyan nata da ita yana nan bai gushe ba.
Nan malam din ya danyi murmushi yana fadin halin ku mata sai ku wallahi mace ko tayi shekaru kamar me bata taba canza halinta na mata.
Ita bata san ke din alheri bace a garesu ke maizube na fada na kara fada maki tun farkon auren yarinyar nan ita din alheri ne a cikin su.
Duk sanda zanyi istihara akan matsalan su ni haske nake gani a lamarin nan banga wani abin aibu ba a cikin auren ta da yaron nan .
Sai dai dan matsala na rayuwa da ba a rasa ba can da ake samu gun ko wasu maurata da suke tare na rayuwa.
Dakin yayi tsit babu mai motsi a tsakanin mu sai can na gyara zama ina sharce zufan dake zubo min a goshina lokaci guda jin abinda malam din ya fada.
A raina ina fadin ta yaya malam zai fadi hakan har in ance malamai suna ganin abinda ke faruwa ga mutum .
Ni tayaya malam zai kira min wani alheri bayan halin da nake ciki muryan malam din ne ya dawo dani daga tunanen dana tafi yana fadin.
Maizube ki bamu wuri in kara ganawa da ita akwai abinda nake son ji a bakin ta don naga akwai nauyi a tare da ita har yanzu.
Take maizube ta mike don bin umurnin mijin nata tana fadin nima dai haka naga yafi don matsalan kawar tawa babba ne don gaskiya malam sai anyi bicike sosai ga matsalan nan.
Ace mace na zaune gidan miji har tsawon wanan shekarun yana kallon ta photo malam ba ko wace mace bace zata iya wanan hakkurin haka.
Hannu malam din ya dagawa mai zube din alaman ya isa tare da fadin ke kuma yanzu zaki zama babban banza ko makin ki yabe ta kan hakan sai kuma ki tunzura ta.
Malam abinne keda daure kai wallahi koma meye Allah na maganin sa ai tana kokari tunda har takai haka dashi yanzu riban ta ya rage ta girba da yarda ubangiji ya fada yana daukan tasbahan dake aje a gefen shi.
Maizube ta sa kai ta fita tana fadin Allah yasa haka malam muma ai hakan muke fata wallahi.
Ki daure kinji malam ya fada bayan fitan maizube dakin yana fadin koma meye matsalan da yarda Allah saukin shi na zuwa.
Kinyi kaifin basiran zama hakan ansani an takura da yawa idan hakan gaskiyane sai na tare shi da fadin.
Malam ba zan mashi kazafi ba ko kadan kalar rayuwan shi shi daban ne dana sauran mutane don da bakin shi yasha fada min shida mace sai zaman mutunci da yan uwan taka a tsakanin su.
Malam ya kada kai nace kuma ko acan da muke ya sha ya fada a gabana da cewa nidin kanwarshi ce ta jini.
Jam malam ya fada da sauri a cikin mamaki kafin yaci gaba da fadin dole akwai abinda ke damun shi a rayuwa daya kawo hakan.
Malam ba wani abu bane illa masifan daya fada rayuwan shi a ciki na bashi amsa daga inda nake zaune a gefen shi.
Ya dago kai tare da tambayana ko kin san duk wani halaiya nasa zuwa yanzu bana son ki boye min komai da kika sani game dashi .
Ki dauka nan kamar yadda zaki sake da iyayyen ki ki bani amsan komai a bayane ta yadda zamu san mafita akan lamarin.
Dan dukar dakai nayi na dan wani lokaci kafin na dago na fara fadawa malam din komai dana sani a game dashi.
Har maganin dana amso mashi a wurin kakan maya da yadda mukayi dashi a lokacin har abinda ya fada min zuwan mu nan ban boyewa malam din komai ba na fada mai.
Sai dai kafin in gama fada mai idanuna sun cika da hawaye a lokacin haka na karasa a cikin kuka da bacin rai.
Shiko malam babu abinda yake fadi sai wa,iyazu billahi har na kai karshe yana girgiza kai cikin mamakin abinda nake fada mai.
Dan shirune ya biyo a dakin kafin inji muryan shi yana fadin Allah kai muna tsari da sherin zamanin nan.
Sai dai ko akwai wanda kika fadawa a cikin yan uwan ki ko iyayyen ki wanan zancen da kika zo ?
Kaina girgiza mai kafin na iya budan bakina da kyat nace dashi a, a malam ko kanwata da muke tare a can bata san da zancen nan ba.
Kin kyauta kwarai da kina karaman na har kika iya rikewa mijin ki siri irin wanan nace to amma malam.
Sai dai yan uwan haihuwan shi da mahaifiyar shi sun sani suma din banice na fada masu ba halin yau da gobe ne yasa suka gane hakan.
Amma mahaifiyar suce nake ganin bata yarda da zancen ba duk da taga makamancin hakan tare dashi amma laifina take gani na ma danta sheri.
Malam ya tare da fadin mata ke nan ga gaskiya sai su baude soboda son zuciya da diya da Allah ya dora masu.
Babu uwar da zata yarda da sherin danta idan bata gani da idon ta ba saidai dan wani haka kuke mata wurin son kai.
Ita yanzu ba abin ta gode maki bane a irin kokarin da kikayiwa rayuwan su da badon Allah ya taimaka kin hadu da wanan kawar data taimaka maki ba wa yasan inda abin zai tsaya mai tunda masiface wanan Allah ya jerabi rayuwan shi dashi.
Nayi shiru shima din dai shirun yayi har na dan wani lokaci kafin na dago kai ina fadin ni yanzu malam so nake kawai a rabani dashi ba zan iya wanan zaman dashi ba.
Da sauri ya dago kai ya tsura min ido kafin ya sake murmushi yana fadin kayya yaro dai yarone ashe ?
Ke abu baki tashi rabuwa dashi ba sai yanzu da tafiya ta kawo ga gangara a tsakanin ku kada ki zoje ladan ki wurin gajin hakkuri irin na dan adam.
Ai tunda kika ji ya fada da bakin shi ya daina haka din ne ya daina sai dai yanzu mu nemo mafita ga zancen kawai.
Yanzu abinda nake so dake ki ban kwana biyu nayi ustihara naga inda bakin zaren yake don mu san daga inda zamu fara aiki a kai.
Ina fatan dai kina da sauran kwanaki kafin ki koma ko ya tambaya yana kallona don jin abinda zan fada.
Sai dana gyara nace dashi malam akwai don kwana goma ya ban nayi a nan yau muna da kwana shidda da zuwa garin nan.
Yace masha Allah kafin sauran kwanakin su cika mun san dan abinda za a gwada a gani ko Allah zaisa mu dace da hakan .
Amma ba zan ce dake komai ba a yanzu sai idan mun duba mun gani duk abinda ya dace sai ayi sai ki matsa da addu,a a naki bangaren don addu,an ki yana da tasiri a gareshi sosai.
Mun dan dade yana min yan nasihohi su na manya kafin in fito in masu sallama na dawo gida.
A gidan kuma bayan barina gida inna da sa,adatu sun tasa sadiya a gaba suna mata tambaya.
Sai fasin take bamu da matsalan komai da yaya din nan take kara basu labarin irin rayuwan da mukeyi a can har zuwa lokacin dana dawo gida .
Gaida inna nayi na shige dakina kai tsaye ban tsaya a falon da suke zaune ba don ban jin dadin yanayina a lokacin.
Sa,adatuce ta dauko abincin ta shigo dashi dakin ta samu na ina rage kayan jikina don zafin daya dameni tunda na faita.
Ga abincin ki anty ta fada na dan kallo ta ina fadin nagode zan kewaya nayi alwala kafin naci don naga lokacin azahar ya gabato.
Kodana idar da sallah ban tsaya bin ta abinci ba na koma saman gado na lafe ina faman tunanen zancen mu da malam da muka fara.
Har inna ta shigo ta sameni a hakan take fadin au abincin ma da aka kawo maki bakici ke nan ko ?
Na dan dago a yadda nake kwance nace zanci anjima inna ta juya tana neman abinda zata dauka a dakin daya shigo da ita.
Zata fita take fadin ya zancen ku na zuwa fambeguwa da kuyi wurin yar inna dake aure a can .
Sai lokacin nadan dago da kyau ina fadin zamu tafi inna akwai abinda nake jira na karba ne zuwa jibi sai mu tafi.
Daga hakan tasa kai ta fice a dakin bata kara magana ba wanan zancen da mukayi da inna ne zuciyar ta ya bata taje wurin malam din koshi yasan irin matsalan da nake fuskanta tunda na kasa fada mata ita.
Da yamma naji tana sallaman mu cewa ta unguwa wanda tun zuwa mu banga ta fita ba sai wanan ranan.
Sai dai duk da hakan ban kawo komai a rai
na ba kan hakan sai ta dawo da mukai mata nan kanne suka sameni a dakin muna hira duk da ba dadin hiran nake ji ba a lokacin.
Taje wurin malam din sun gaisa take fada masa damuwan ta a kaina tare da yadda mukayi da ita din.
Malam din yace koda baki zo ba a yau ni zan aika kizo ai don yarki na cikin gagarumin matsalan rayuwa da ko ke din nan mahaifiyar ta ba lalai bane ki iya daukan hakan.
Sai dai ki godewa Allah da ya baki ya irin wanan a rayuwan ki don ita di abin alfaharine ga kowa idan ya samu yaro irin hakan.
A matsayin ki na uwa a gareta ke ya dace ta fadawa wanan damuwan nata ki san irin matsalan da yarki ke ciki na rayuwa.
Amma sai kika kasa yin hakan gareta kikai aikin jahilci baki tsaya kin san damuwar yar ki a gidan auren ta ba.
Yau da ace ba yarki bane dakeda zurfin ciki da tunane wanan zancen ya fita a garin nan ke kanki da fita waje ya gagareki koda rdarene kuwa.
Gaban inna dake faduwa ya kara bugawa sosai don jin abinda kanin mahaifin nata ya fada a kaina.
Ta dago kai a cikin tsoro tana fadin malam ban san abin yakai girman haka ba na dauka irin shirmen yaran yanzu ne kawai take son ta aikata.
Koma shirmene Asiya ai sai ki saurareta kafin ki balbale ta da fada ki kara tayar mata da hankali haka.
Idan ma baki sani a yanzu yarinyar nan Abu tana bukatan taimakon mu akan rayuwan da takeyi a gidan mijin ta din matsalan ba karami matsala bane a yadda kike tunane.
Na shiga ukku inna ta fada tana kyarma tare da fadin meye matsalan da yai girma haka malam ?
Kin ga ki kwantar da hankalin ki insha Allahu Allah zai muna mafita ga wanan zancen nan inna ta fara kyarma tana magiya ga malam din ya dan fada mata wani abu do hankalin ta ya tashi sosai.
Na fada maki ki kwantar da hankalin ki ya zama dole ai ki san wani abin don ki taya ta da addu,a don ba zamu kyale yarinya ba ta zauna haka har tsawon shekarun nan babu abinda ya taba shiga tsakanin ta da miji na aure.
Innalillahi wa inna alaihim raji,un malan matsalan da yar nan ke ciki ke nan ban sani ba kadan dai kikaji Asiya daga abubuwan dake gudana.
Saidai abinda nike so dake wanan maganan yanzu ya tsaya iyamu don ko mahaifin ta ban son yaji wanan zancen yanzu sai in har abin ya gagare mu.
To ya zama dole ya sani a lokacin don ba zamu yarda yarinya ta koma tana zama haka ba shekaru kurewa shigewa suke ga bawa.
Malam nagode Allah ya bar zumunci inna ta fada dolene muyi maki Asiya don kema baki yarda mu ba ai, ko banza ai dole muyi maki tunda muna raye daku.
Haka inna tayi sallama da malam din cikin tashin hankali ta dawo gida yanayin ta kawai zaka kalla ka san cewa tana cikin tashin hankali.
Kallon juna mukayi nida sa,adatu sai sa,adatu din ta tashi ta bita zuwa cikin dakin sukai kus kus naga itama ta fito a cikin damuwa a fuskanta sai dai ta zauna ta dan wayen ce kawai.
Tun wanan ranan inna ta koma rarashi na tana jana a jiki dama akwai akidar yar farko da takan nuna min wani lokaci don sunfi shakuwa da sa,adatu gaskiya sama da ni.
A cikin hikima da dabara takan sameni a daki mu danyi hira tana dan jefo min zancen zaman mu wani nakan bata amsa wani ko na yi shiru kawai don amsan bai faduwa.
Da haka har inna ta fahinci wani abu take dan ban hakkuri na daure in kara hakkuri don haka zama ya gada wani lokaci mata da hakkuri aka san su dama.
A raina nakance wani hakkuri ba inna nawa kan yafi gaban yin hakkurin da kike nufi nayi.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.