Complete Hausa Novels

Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel

Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 2 of 139

ANCAU

Tun a soron gidan nasu take jiyo muryan Asabe kakar su data haifi mahaufisun tana faman zazzaga bala,i.
Dukda bata shiga gidan ba tasan bada kowa Asabe ke wanan fadan ba haka illa da mahaifiyar su.
Don inda sabo aita saba da wanan hali na Asaben don tun bata da wayo da wanan hali ta bude idanuwanta a gidan.
Kusan kullun fitinan Asabe ne ke tayar dasu daga barci na yau daban na gobe daban.
Yau ma daga inda take take jiyo muryan Asaben tana fada akan iccen girki da innar tasu.
A haka ta karasa ciki rai bace duk da gajiyan ranan data kwaso ga yunwa ga kishin ruwa don tun safe da ta fita bata karya ba .
Hakan kuma ta juyo gida da kafa duk da nisan dake akwai daga makaranta zuwa gidan su.
Shigowan Abu gidan bai hana Asabe fadin abinda take fadawa mahaifiyar tasu ba a lokacin.
A daidai lokacin inna ke fadin adan maraice umma dama ba wani icce mai yawa bane dashi nayi koko da safe yanzu kuma na danyi muna danbun tsakin da akwai don yaran nan idan sun dawo su samu abinci.
Duka bakin wutan baifi guda hudu da guntu indon ruwan dumine barin hada gawayin nan sai ruwan yayi dumi ki samu ki watsa din.
Salman Abune yasa su juyowa gaba dayan su sai dai inna ce tayi karfin halin anwa a lokacin duk da tana cikin rudu da rikecewan bala,in Asaben.
Asabe na fadin to sannu issasa mai diya ke kika san zafin diyan su kin iya kokarin nema masu abinda zasuci.
Niko nawa dan dabai damu dani ba ai haka yasa kafa ya fita bai damu yasan da damuwata ba.
Saukin abindai kema yaya matane a gaban ki, kinkin zuciya duk da gorin da kike sha a gari ki haifa mashi ko da naji dayane da zai taimaka mai idan karfin shi ya kare yasan yana da magaji.
Ke kenan kullun dauksn ciki kina zuba mai diya mata a gida yau ace kitso gobe kumshi sai ko na omo.
Ta yaya zai samu ya aje kullun laluran su yana kara yawa gareshi kullun yana fita nema ba matai maki sai Allah.
Da maza kika haifa ai zai sa ran zasu taimaka mai a wani gurin ga wanan data saka kanta wani karatun boko da baida amfani a gurin ya mace.
Abu dake kallon ta da mamaki tana cire takalmin makarantar dake kafanta wanda duk ya sude a titi saboda rana da yawan bin hanya ga ba kudi balle a saya mata sabo dole haka take maneji dashi.
Saukin abin ma yanzu duk da karancin shekarun ta amma haka ta samu don kokarin ta ba,a taba mayar da ita baya ba har takai aji shida tana neman fitane yanzu.
Duk irin matsin da Asabe kewa mahaifi su akan karatun nasu baida wani rana garesu kasancewar su na yaya mata gareshi.
Don a cewar ta aure zata masu da zaran Abu ta cika shekara goma sha biyar da haihuwa a duniya don ko yanzu wasu daga cikin sa,annin ta sun riga da sunyi aure suna gidajen mazan su zaune daram.
Muryan Asabene ya dawo da ita ciki tunanen da takeyi tana fadin ke kuma munafuka ki kura mi ido kuru kuru kina kallona dasu.
Don rashin kunya rashin tarbiyan da baku samu ba tun farko ga uwar ku babba na magana yara suna kashe shi da ido don rashin kunyan da kuka gada a wurin uwar ku.
Karya nake fada ba gaskiya na fada ba komai ya samo yana gurin ku keda yan uwan ki da makiran uwar ku ku gaku ga bawa na haifar maku ko ?
Ice ma da mutum zai saka ruwan dumi ace an kona shi a gidan nan gaba daya wanan wani irin masifane yaron nan ya haifar min a gidan nan.
Baki na turo gaba don jin irin cin zarafin da kullun Asabe ke muna muda mahaifiyar mu har wata rana takan tsaya sai baba ya saki inna ko kuma ya kara auren macen da zata zo ta dinga haifa mai diya maza a gidan mu.
Da kyat Abba da wasu makwabta sukan iya shawo kan Asabe idan ta fara wanan bambamin nata lokacin.
Inna dai tana duke a bakin murhu tana kokarin hura wuta da gawayi ne data dan kashe dazun sai faman fifita wutan take don ya kama.
Daki na shiga na kwabe tufafin makaranta dake jikina don sanin bamu da clean din da zamu wanke a yau don gobe haka yasa na kwabe su na baza a dan gambun langa langan kwanon dake kofan dakin namu nafito.
Wurin madafin namu na hara ina fadin inna kawo in hura kije ki huta hakana da ranan nasan tun safe baki huta ba.
Barshi inna ta fada tana kokarin boye fuskanta gare ni don kada inga hawayen dake zubo mata a idanun ta a lokacin.
Wanda nasan ba komai inna kewa hawaye ba sai gorin diya matan da Asabe ke mata don indan don fadan barana da Asabe ke fadin tanayi ne ta saba da wanan sai dai wana gorin ne inna bata iya shayewa a ranta sai ta nuna gazawan ta anan.
Da kyar inna ta yarda ta bani maficin tana fadin kije ki huta yar mairo dan inna bata kiran sunana kasancewata yar fari a garesu.
Ina tsugune bakin murhun Abba ya shigo gidan da kayan aikin shi idannun shi ya sauka a kaina yake fadin yar mairo kece har kika shiga girki daga dawowan ki haka?
Dagowa nayi daga inda nake ina fadin Abba sannu da zuwa na nufo shi don amsar ledan dake hannun shi.
Bayan na karba na juya don zuwa dakin su in aje Asabe ta fito tana fadin to to mai zaki tura daki daga kawowa yar nema data gaji kilibibi a gurin uwarta.
Kai haba umma ba komai bane a ciki sai dan garin tuwo da kubewa ko za a samu a dan tuka da dare a samu naci .
Don na fita dazun ban samu bada ko sisi ba a samu ko abin karyawa a gidan nan ina can na damu da tunane tun safe ina faman babu kwasta duk masu zuwa sai cewa suke ai masu bashi idan sun samu zasu kawo kudi.
Kai Amma mutane sun lalace yanzu da son bashi facin ma shi kanshi bashi za ai masu shi kai Allah ya rabamu da fititinun duniyan nan .
Sai lokacin Abba yakai kasa yana fadin barka da wuni umma mun wuni lafiya ya gidan kuma.
Mun wuni lafiya ba lau ba dai tunda ko ruwan da zan dan samu in watsa a gidan nan ban kaiga samu ba har yanzu.
Don kawai nace bazan iya wanka da farar safiya ba sai kawai a hana min ruwan ina kallo wanan matar taka ta hura wuta a gidan nan har ta gama abinda take saida taga icen ya kone ga baki daya .
Amma yarinyar nan ta kasa saka min ruwan dumi in watsa don bakin ciki da rashin sanin muhinmancina a gidan nan.
Daga inda Abba yake tsaye yana jin Asabe takai ayah yace kiyi hakkuri umma .
Kin sa halin da nake ciki yanzu aikin ne nawa babu kasuwa ko ina ya rufe yau kwana uku sai ita saudatune ke dan dabara a cikin aljihun ta muna samu muna dan tabawa.
Asabe tace da mamaki karara a fuskan ta take fadin haka ka koma ban sani ba dan nan ?
Kai bakaji kunyar fadin wai ashe mace ke ciyar damu duk kwanakin nan a gidan nan ba.
Mafarin abin gari ana yadamu da fadin talaucin mu yakai haka har mace ce take ciyar damu a gidan nan kai ka kasa.
Kaga amfanin haihuwan da namijin da nake fadama ke nan da yanzu yarinyar nan namiji ne aida ta fara taimaka maka ta wani gurin.
Inna ta fito dakin ta nufi wurin madafin danbun tsakin masaran data hadane ta shiga rabawa yayin da tsakar gidan namu yayi shiru kowa ya zuba idanu yana kallon inna.
Na Asabe ta fara zubawa ta mike ta nufo ta tana fadin umma akai dakine ko a kawo maki nan aje anan in gani Asabe ta fada a hasale.
Saida Inna ta kai kasa don girmamawa ta aje kwano a gaban ta inda take zaune saman kujera dan tsugunno.
Bude kwanon samiran tayi tare da juya dan danbun dake cikin kwanon a yatsune tana tabe baki kafinta dago kai tana fadin.
Saudatu wanan abincin fa kamar za,aba dan goye shi ta juya wurin Abba tana fadin ka duba dai ka gani da idanuwan ka yanzu dan abinda aka zubamin.
Don kawai kace itace ke ciyar damu a gidan yanzu ai dole wullakanci ya shigo a bani abinda akaga dama don kawai rainin da kaja muna don kasawan ka yanzu da gidan.
Umma ba hakana bane kiyi hakkuri tsakin ne baida yawa iyakarshi ke nan dan gyara don yaran nan dake.
Nasan nida malam ba samu zamuyi bama a karshe tace duk da haka a kara min don wanan dai ba isane zaiyi ba ehhe.
Kallin Asabe nayi lokacin da naji ta fadi hakan ina mamaki hali rashin tausayi irin nata duk da jin zancen inna din da tayi.
Dakuwa ta jefo min da hannun tana hagu tana fadin daina kallo na yan nema mai kama da yanyawa.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.