Complete Hausa Novels

Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel

Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 94 of 139

ZAINAB IDRIS MAKAWALITTAFIN NAN NA KUDINE DON ALLAH KI BIYA MU FITA HAKKIN JUNA DANI DA KE YAR UWA, , , , ,

Gidan shiru kamar ba kowa tun bayan tafiyan su ashe mutum rahamane sosai don duk yadda nake dasu sai gashi na koma ina kewan su.
Ina dakina kwance don tafiyan dare sukayi ranan tunda muka dawo daga rakiyan su na shige daki ban kara lekowa waje ba har dayan rana.
Yunwa ya fitar dani na sauko nan ma babu kowa wurin a lokacin dakin su na nufa na tura na shiga.
Na hangosu saman gado kwance ba barci sukeyi ba sai dai sun kwanta shiru a lokacin ba wai hira sukeyi ba.
Sadiya tana kallo a wayana ita kuma fadila tana kwance ta kurawa rufin dakin ido tana tunane.
Kin tashi Fadila ta fada tana dagowa daga kwancen da take nake fadin eh dama ba barci nakeyi ba ina dai kwance ne.
Abinci fa ta tambayeni nace shina sauko ci zama nayi a dakin ta kawo min abincin na dan ci muna hira.
Itace ta sako zancen su tana tuna yadda hankali ya tashi da ciwon hjy kafin ta koma hiran yadda hankalin mami ya daga akan su koma gida alhalin basu gama kwanakin da zasuyi ba a nan.
Bandai yi magana ba sai murmushin da nakeyi kawai ina jin raina yana matukar baci sosai ga hiran da take min din a lokacin.
Nan dai na zauna a dakin har lokacin sallah yayi na mike na koma dakina bayan na idar da sallah kuma ba sake fitowa ba falon saida dare da zamuci abincin dare.
A takaice dai bamu hadu da yaya ba sai bayan kwana biyu da tafiyan su ranan ya samemu a falo zaune duk suka shiga mai sannu da zuwa.
Yanayin shi kawai na kalla nasan a buge yake yashawo maye don ko wurin hawa sama saida ya dan tsaya kadan kafin ya daure ya hau sama din.
Binshi nayi da kallo zuciyana tana wani irin tafasa kafin in mike zuwa part din na sameshi a yadda ya shigo din kwance shame shame saman kujera yana barci.
Saida na kare mai kallo na duka wurin kafan shi ina cire mai takalman dake kafan shi saye baiko tsaya ciresu ba.
Ya dan bude idanun shi a daidai lokacin dana fara cire mai takalman a kafan shi yana fadin wai meye hakane kin dameni fa yarinyar nan.
Kai na girgiza ina zare mai safan kafafuwan shi na mike dasu zuwa inda yake aje takalman daya saka kafin a goge mai a mayar.
Wanan ba aikina bane yana da mai gyaran dakuna a gidan yasa ban wani damu da inje in masa wani aiki ba a dakin nasa.
Na sake mai gudun AC din falon don yayi saurin farfadowa da wuri sanan na ja masa kofan na fita zuciyana na cike da tsanar sa.
Daki na na shiga ina tunanen zancen hjy a gareni da take fadin yar nan ki taimakawa mijin ki don Allah badon mu ba ko uwarshi dake nuna maki rashin kauna taimako zakiwa addini ki zauna dashi.
Zan samu lokaci mu zauna dashi kan matsalolin ku saidai hakan ba zai samu ba sai kin hada da hakkuri cikin al,amarin.
Hawaye ne yazo min dana tuna da wanan nauyin data dora min wanda ta rantse datun farko tasan da halin sa ba zata taba yarda ya aureni ba.
Yanzun kuma data sani din iya taimakon da zamuyi mai shine addua da saka ido ga wasu abubuwan da yake aikatawa koda yin hakan zai ja mana matsala a tsakanin mu.
Shine dalilin gwada hakan da nayi yanzu bayan na fahinci a buge ya shigo gidan ke nan don baida niyar daina hakan alama ya nuna.
Haka na kwana a cikin bakin ciki washegari inda na idar da sallah nan na kwanta sai barci don ban samu barci da dare ba saboda da tunane.
Haka ya shigo dakin ya sameno kwance kasa ina barci a takure ya dan dade tsaye yana kallona kafin ya juya zai fice daga dakin.
A lokacin na bude idanuna don nauyin mutum danaji a kaina tare da gyara kwanciyana shi nagani zai fita jin motsina yasa shi juyowa.
Baiyi magana ba ya sa kai ya fice dakin da sauri kamar wanda aka kora yayin da ya barni da mamakin abinda ya kawo shi dakin lokacin.
Saida naga fitan shi na mike da sauri na zauna ina dan dube dube a dakin banga komai ba na sauke ajiyan zuciya.
Wayana dake saman gadone ya dauki kara lokaci guda na mike zuwa inda wayan ke ruri na dauka bakon lamba daga Nigeria ake kirana dashi da mamaki nakai wayan a kunne na.
Muryan mami ne ya daki kunuwan nawa tana amsa sallaman da nayi saida na dan daga wayan daga kunne na a cikin mamaki.
Na mayar ina sauraren ta tana fadin mun sauka lafiya zainab nace Alhamdullahi mami ya gajiya ya sauran yan uwa da gajiya ta amsa a sake da lafiya lau zainab.
Ya kowa nan wurin ku kuna dai lafiya ko nace a cikin dan dari dari da ita lafiya muke to ki kara hannkuri don Allah zan kara kiran ki idan mun huta muyi magana a kan mijin naki kiji ko ?
Nace to mami nagode kiyi hakkuri kinji komai yai farko yana da iyaka insha Allahu ta fada a sanyaye na kara fadin na gode mami.
Bayan ta kashe nabi wayan da kallon mamaki ina rayawa a zuciyana yau ni mami kewa magana a tsigar lalashi haka ?
Nan ta barni da tunane barkatai a raina karshe na mike na shiga bandaki na watsa ma jikina ruwa cike da mamakin mami a zuciyana.
Don koda zata wuce wanan kalman ne muka rabu dashi na don Allah na kula na kara daure koma zai zo da sauki insha Allahu.
Ina zaune gaban mirrow nake wanan tunanen sai ga wasu hawaye masu dumi suna gangaro min a fuskana nasa gefen hannu na share a hankali.
Ina ayyanawa a raina cewa ni kuma nawa kaddaran ke nan auren dan luwadi mai bin jinsin shi ya gane me a hakan da yakeyi wai.
A take naji wani itin ysanarshi ya kara mamaye min zuciyana na mike zuwa wurin kayana ina dauka naji an shigo dakin.
Dan juyowa nayi shine ya shigo dakin a cikin shirin shi yayi wanka yasa tufafi a jikin shi yayi wani irin kyau da kamala zakace wani musulmine da tsoron Allah ya gama ratsashi.
Kallo daya nayi mai na kawar da kai daga kallon shi hakan bai hanashi karasowa inda nake tsaye ba.
Saida yazo gab dani ya ja ya tsaya yana fadin zuwa gobe ku shirya zamu bar gidan nan mu koma wani unguwa.
A raina nace at list ai zaka fada min da wuri don mu shirya amma ba haka kwatsam na inji wai gobe zamu bar wanan gidan zuwa wani wurin.
Saidai a fili ce mai nayi Allah ya kaimu kawai ya juya zai tafi sai kuma ya kara juyowa yana fadin uafin ku kawai da kuke so zaku dauka .
Naji na fada yasa kai ya bar min dakin na sauke ajiyan zuciya ina mai godewa Allah dayasa na rage kayana da yawa na tura gida.
Don hjy nabawa ta kai min gun innan mu don ita sakon zaifi saukin kaiwa a wurin don a kaduna take zaune.
Saida na gama shirina na fito falon zama nayi don inci abinci na samu irin girkin mu na yan Africane aka girka don girkin fadila daban yake da nasu idan tayi.
Zama nayi naci abincin sosai na turo ban kai ga dagawa ba fadila ta fito daga daki su tana fadin ashe kin fito yanzun nake zancen ki a raina ai ko kin tashi ?
Na tashi na bata amsa, sai ta dago kai ta dan saci kallon idanuwana da sukasha kuka tun a dare don tana saurin gane hakan idan har nayi kukan .
Zama tayi a gefena tana fadin kuka dai ya zama maki sana,a madam ya kamata zuwa yanzu kin saba da halin mijin na ki ai don shi bai dauki abinda yakeyi yanzu a bakin komai ba tunda yana cikin masu irin wanan dabi,an.
Da ace a gida Nigeria yakw rayuwan shi don dole yabar wani abin daga ciki saidai kash yanzu kan taro shi sai Allah gaskiya don yayi nisa sosai a cikin bata.
Ba yaya yasani kuka ba mamice mukai waya da ita da safen nan da sauri tace ba dai laifi kikai mata ba kuma na girgiza kai kawai tare da fadin hakkuri tabani kawai kanshi.
Anzo wurin ke nan ashe yanzu ta daina ganin laifin ki kan danta tunda ta gane gaskiya dama ai tasan gaskiya tunda ita ta haifi abinta.
Na mike tsaye don barin wajen ban son zancen yayi nisa kafin na juyo ina fadin yace gobe zamu bar gidan nan fa don haka mu shirya kayan mu a yau.
Gobe goben nan dai ta fada da mamaki nace haka ya fada dazun da zai fita tace ikon Allah shidai haka rayuwan shi take daban dana kowa .
Bahagon rayuwa dai ko dan wani abin da sani yakeyin shi don bai dauki mutane da muhinmanci ba a rayuwan.
Sadiya da aka fada mata sai murna da farin cikin komawa sabon wuri takeyi a fili da murrnan ta tacin min daki na rasa meke min dadi a lokacin.
Don Allah ya gani nasan wanan komawa gidan da zamuyi da biyu da uku zai canza wurin don wanan din ma da muke cikinsa ba laifi don in a Nigeria muke cikin sa sai ya zama gidan kwatance a gari.
Yayan mu ashe mu bar gidan nan cikin washe baki take tambayana haka na kallota ina fadin kinji dadin hakan ke nan ke ?
To ai abin murna ne ya samemu baki daya tana kaiwa kwance take wanan maganan nace eh abin murna kan ya samemu sadiya dake da maigidan ko ?
Don zamu koma can yayi bushashan da yake so yanzu idan nan na saka mai ido haka na damun shi.
Sam na manta da sadiya nake wanan maganan sai naji tace dani ba gidan sa bane yaya komai zaiyi yaje yai tayi balle ni banga wani abinda yakeyi ba ma.
Sadiya ki fice min daki tun kan ranki yakai ga baci yanzu na fada a hasale ina shirin sauke haushin daba nata ba a kanta kamar yadda uwa wani lokaci takan sauke haushi kan diyan ta idan ranta ya baci.
Falo ta koma ta zauna tana fushi har ya dawo ya sameta a wurin yanayin ta ya kalla kawai ya gane akwau abinda ke damun ta.
Ciki ciki ta gaidashi tana kawar da kai ya amsa har ya wuce ya dawo yana fadin sadiya yau ya akayine na ganki zaune ke kadai ?
Ba komai ta fada ciki ciki ya tako har inda take ya zauna kusa da ita ya sake fadin fada min mana yar kanwata waya taba min ke a gidan nan kuma ?
Yayan muce ta fada a sanyayye tana son yin kuka mai kikai mata kuma kukai fada ta sake fadan ba komai don kawai naji anty na fadin wai gobe zamu bar gidan nan shine shine ta kasa fada.
Shine me ya riko hannun ta yana tambaya shine tace wai ina murna don kawai zamu bar nan don na taya ka yin bushasha da kake so a can ?
Meye bushasha kuma ya tambaya da mamaki ta dago kai tana fadin nima ban sani ba haka dai ta fada ta koroni wai zata bata min rai.
Mikewa yayi ba tare dayayi magana ba zuwa part dina ya turo kofan ina zaune bakin gado na tsurawa kasa ido ina tunane.
Na rasa meye damuwan ki zainab duk yadda nake son mu rabu lafiya dake naga baki fatan hakan ke ?
Kai na dago ina mamakin dalilin wanan maganan yaci gaba da fadin meye bushasha a canza gida da har zaki zauna kina fadawa yarinya kamar sadiya wanan maganan ?
Ita ta fadama nace hakan nacene don bansan uban da takewa farin cikin don za ka canza gida ba ?
Idan ke baki farin ciki da hakan ki bari ita tayi don naga sadiyan tafiki wayau ma tunda ita yadda aka ajeta haka take bin abu.
Bazan taba bin karya da halaka ba saidai idan kasheni zakayi don ka fada dama zan saka kaina ga halaka idan nace sai nabi su mami ai.
Kai ya girgiza tare da fadin ni ban taba kashe ko dabba ba balle mutum idan ma haka kike tunane gareni.
Rashin inmani ai yana saka bawa yayi komai a rayuwan shi matukar ya fara kaucewa maliccinshi komai ma zai iya yi ai.
Shirme ke gareki zainab ina daukan ki yarinya da tasan kanta ga hakkuri da juriya ashe ba hakan kike ba ke ?
Zan iya jurewa a kan komai amma ba akai laifin da Allah zai tambayeni ba ranan hisabi wanda bani na aikata hakan ba kawai laifin wani ya shafeni.
Wani kallo yayi min na dan kasheshi da idon rashin kunya na dan lokaci kafin in dukar da kaina kasa .
Nasan da ace ba ya jafar bane nakewa wanan rashin kunyar haka da andade da jin mu da mai shi ko.
Amma sai inyi mamaki zan masa abinda bai dace ba saidai ya kalleni ya kyaleni hakana ya fice don a kullun muka hadu sai munyi fitina kan abu daya kuma yaki dainawa shi.
Yanzu kan tunda na kara dab shekaru na fahinci waye jafar din na daina tsoron shi sam a raina duk da ina dan dari darin shi ga wani abu idan bai shafi irin halaiyan rayuwan shi ba wani lokaci.
Yana fita na kuta don sadiya ta kaini iyaka yanzu banda daman yi mata fada sai tayi dalilin daya sani yaji yayi magana a kansa don hakane na shirya mata tsiya kan hakan.
Yan tufafina kawai na hada a cikin jakkunan tafiyana sai takardun karatuna dana dauka baya gasu ban dauki ko cibi ba a gidan kuma ?
Don nasan ko gida zan koma iya abinda zan bukata ke nan a yanzu don haka banba kaina wahala ba .
Sai dai da safe da yace idan akwai wani abinda zamu so zamu iya dauka don duk fitar dasu za,ayi don wani ne zai zauna a gidan na kasa dashi a wurin aikin su.
Nan na fahinci wanan sauyin gidan daga ma,aikatansu ya taso ke nan don haka na yanke shawaran kiran Maya da take kawata don na fahinci itama irin mune masu karamin karfi a kasan.
Kwatance nayi mata tazo gidan ta dauki duk abinda ranta keso tana murna ita kan da farin cikin hakan mota guda ta hada na kayan zuwa kauyen su da baida nisa da cikin garin sosai.
Sai da yamma yazo muka dauki hanya tafiya mai dan nisa da unguwar da muka baro din ya kaimu wani hatsabibin gida na zamani wanda kamar ba hannune ya gina shi ba.
Tsayawa fadin tsarin gidan bata lokacine don kowa yasan yadda chaina suka kwarai a wurin ginan su komai na zamani akwaishi a wanan gidan don ni abin har tsoro ya bani sosai.
Kamar yadda na zarga haka dinne ya faru don part din mu daban nasa daban a wanan gidan don haka zaici kareshi ba babbaka a wanan gidan.
Don ko kattai goma ya kawo ba zamu taba ganin su ba sai idan wani abu yakai mutum ya gani ga filin parking babba ga motoci a je a wurin.
Ga swimming pol mai kyau dashi ga wurin kiwon dabbobi can daga gefen gidan ganin haka sai kawai shima kanshi jafar din ban yarda da rayuwan shi ba gaba daya yanzu.
Har wani aiki yake masu yake samun wanan mahaukatan kudin haka a kasan mutane don ni in an barni zance wanan arzikin gaskiya da biyu.
Ban kara tsorata ba sai da muka shiga part din da yace shine namu ana saka muna kayan mu tsoro ya kara kamani sosai.
Haka muka kwana sabon gidan namu mai cike da abin aljabi a cikin sa wai matashi mai shekarun jafar ne mamalakin wanan katafaren gina irin haka.
Komai na gidan kan sai masha Allah ba a maganan wani bincike don fadan daya fi karfin ka sai ido don haka na raya dare ina kai kukana ga mahakicina Allah don neman tsari ga wanan gidan dashi kanshi mamalakin gidan a yanzu.
Da part din mu da nasa akwai katon falone gidan ne dayaji kayan alatu a tsakiya namu da nasa shima mai hawa biyu ne ginan saidai akwai bambaci sosai a tsakanin mu da wancan da muka baro.
Sannu sannu har muka fara sabawa da wanan gidan mai girma da ban tsoro duk da akwai tsaro sosai ba wani abin daga hankali a gidan.
Mu kanmu in ma cigaba ya samu ko wani daukaka mun sani don daula kan muna cikin sa sosai saidai hakan duk ragage ne a wurina.
Na daya da ace a gida muke cikin yan uwa hakan zai fi muna dadi don ko banza zaka taimakawa wanda ma baka da alaka dashi a can sabanin nan da kowa ta kasa yakeyi ba ruwan wani da wani don makwabtaka duk da unguwar da alama ba mabukata sam.
Sai na biyu wanda duk wannan daulan bai tsone min ido har in manta da addinina ba da al,adana na malam bahaushe don kullun zaka ganni saye da dan abinda zai rufe min tsiraicina wanda hakan ke min kariya ga duk narazana da iya shegen yan kasan da suke fama dashi.
Zan iyacewa Maya ce kadai wace nake hurda mai zurfi da ita don akwai yadda sosai a tsakanin koshi don mun karewa juna hakkin addinin mune tun farko wani bai shiga harkan addinin wani idan dan uwa na ibandan shi.
Maya kan da ace musulmace gaskiya da akwaita da rikon addini sosai sai dai kash ta kasance mai addinin suce na gargajiya ita.
A haka har hutu ya kare muka koma makaranta don ci gaba da darasin mu ba wani sokuni ko walwala a tare dani wanda yasa mayan ta kula da hakan.
Har yakai tana tambayana nake ce mata babu komai don ita a zaton ta ni ba matar aure bace saboda zata girme min sosai ga shekaru.
Ranan dai nake fada mata cewa nidin ai matar aure ce ta tsaya tana mamakin hakan don bata taba kowo hakan ba a fanta.
Take fadin babu wani alaman daya nuna ina da aure ai don komai nawa ya nuna still ni budurwace ai.
Da yake akwai yadda a tsakanin mu nan dai na dan bata labarina sama sama muka rabu tana cike da tunen halin da nake ciki din.
Na dawo gidane na tar da Fadila kuma a cikin tashin hankali wai danta daya mota ya bugeshi a hanyar zuwa makaranta ya rasu.
Ranan mun kwana cikin tashin hankali sosai a gidan don har ya jafar saida ya tausaya mata yana zaune a part din mu yana bata hakkuri.
Haka yasa tafiya zuwa Nugeria ya kama fadila din zata tafi ta barmu ke nan na dan wani lokaci kilama ra tafi ke nan ba zata dawo ba kuma.
Yanzu kam hankalina ya kara tashi sosai dason komawa gida dama itace mai debe muna kewa gashi itama din zata koma gida.
A cikin sati biyu ya gama mata shirin tafiya rana kan nayi kuka sosai ina ji dama ace nice zan tafi gida ba wani ba.
Baki ta fara bani tana fadin inyi hakkuri kada hakan yasa in sare in hakkura nagama karatuna kamar yadda yace tunda saura kadan ingama ai.
Don yanzu idan na koma gida ban karasa ba duk wahalan danayi ya tashi a banza amma a kalla in na kare karatun in ma rabuwa zamuyi ina da riban dana samu a wurin shi ai.
Tace nasan kina cutuwa da yawa zainab amma hakkuri baibar komai ba da rokon Allah nima nayi maki alkawarin zan dinga maki adduan akan wanan matsalan naku insha Allahu.
Da irin wanan ban bakin ta kwantar min da hankalina yasa aka kaita airport sai Nigeria ta barmu da halin mu a chaina mu kadai sai Allah.
Sam na manta da muyi wani zance da maya ranan muna hira take cewa dani tana son in samu lokaci in kai mata ziyara kauyen su don akwai abinda take son tataunawa dani a can amma fa idan na yarda.
Don tana son ta hadani da wasu kakanintane akan matsalana da mijina wanda tana son ta taimakeni a rayuwan ta itama kamar yadda nake taimakonta tun haduwan mu.
Shiru na danyi kafin ince ta bari in fadawa mijina zan kai mata ziyara tunda yasan muna tare da ita sosai a school.
Tace ba matsala idan naga hakan ba matsala zan iya fada mai niko hikimar yin hakan kada inzo in tafi bada sanin shi ba wani abu yaje can ya sameni bai sanda zuwana ba can.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.