Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel
Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 48 of 139
ZAINAB IDRIS MAkAWA🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
4ï¸Â⃣1ï¸Â⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
LITTAFIN KUDINE YAR UWA DON GIRMAN ALLAH KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA BA , IDAN KIN SAN DARAJAN ALLAH, , ,
DOMIN BIYA ZAKI IYA TURA KUDI TA WANAN LAYIN BAKIN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KI TURA KATIN WAYA NAGODE, , , ,
Bayan an zauna an natsu a dakin inna ina sai yan dabarun mata takewa hjy don taron ta duk da bata san ko wacece hjyn ba a lokacin.
Saidai cikar ido irin na hjy da kamala yasa kwarjinta ya dauki hankalin ko wa a gidan sai ga Asabe ta dawo tana fadin .
Sannun ku dai da zuwa ta kara fada tana kokarin shigowa daga cikin dakin takai gurfane.
Kaga Asabe do kinga yayar mu tazo da kama mai kyau har kina wani rawan jiki da zuwan ta a yanzu.
Duka inna takaiwa sa,adatu da bayan hannu tayi saurin gwaucewa tare da mikewa tsaye tana ja da baya don barin wurin tana magana ciki ciki.
Asabe na fadin rabu da ita sa,adatu ba hankali gareta ba ai koma me ye ai wanan zancan baya ne kike daukowa.
Duk abinda ke faruwa hjy na zaune ta lura da komai daga inda nake zaune ina mamakin yadda sa,adatu takewa asabe a yanzu.
Kamar ba Asaben da ko muryan ta mukaji a sa can baya sai gaban mu ya fadi don masifa da irin matsawa innar mu da sukeyi lokaci.
Amma sai gashi yanzu na dawo na samu suna mata abinda sukaga dama a gidan.
Haba dai sa,adatu ki daina haka mana na fada ina kallon ta don naga ran innan mu ya baci sosai a lokacin.
Kinga kawata yaki zonan ki kyale su naga sun taru a kanki ke kadai haka hjy ta fada tana mikawa sa,adatu hannu tazo wurinta.
A lokacin ne Asabe ke fadin ita wanan din ne hjy da kike aiki a gidan ta ko waye ita din tana kallona.
Kafin na bata amsa hjy tace a, a , aha nidin dai kakar mijin tane nice na haifi uwar mijin nata don haka ita din matar jikana ne yanzu.
Ikon Allah asabe ta fada sai mukaji zancen aure kamar a mafalki daga sama ba tare da wani sanarwa ba kawai.
Ai kin san aure habo ne shi idan lokacin yinsa yayi koda shiri ko ba shiri ranan sai anyi shi Allah ya nufa matar shice shima.
Har hakan ya faru da yar nan yarinyar arziki yar kirki aka dauketa aka mika a birni ba tare da an taba bin sawun wanan yar ba anga a inda take zaune ba.
Sai gashi ubangiji ya tarfawa garin ta nono ta shigo birni da kafar dama tayi gamo da arzikinta taci kuci har wani nata shima ya raba yaci ya huta a karkashin innuwar ta a yanzu.
Wani kuka Asabe ta sake daga gefen da take gurfane tana fadin yar nan naso cutan kaina da kaina da badan Allah ya gyara ba ki fada hannu na gari wa yasan hannun da zaki fada haka.
Na aikata abu a cikon duhun kai nabi zugin da ya jawo min zagi da zunde a gari kan na sayar dake a hannun yan birni.
Har zaure mai gari muke da iyayyen ki saida nayi rantsuwa akan ba sayar dake nayi ba a garin nan.
Allah da ikon shi an gama kulla min wanan sherin da kwana biyune zancen auren kin nan yazo muna garin nan a cikin bazata.
Wanda hakan kuma ya kara jawo muna kace nace a cikin garin nan wanda har yanzu mutane a kanshi suke wai ba a san mutum ba an dauki yarinya an bashi don kwadai.
Cike da takaici nake sauraren abinda Asaben ke fadi na rasa abinda ke mun dadi sai hawayen dake zubo min a lokacin a raina nace ni haka rayuwana zai kasance da barnan suna.
Wanan wace irin kaddaran rayuwace Allah ya jefoni a cikin sa don kawai ina ya mace nake gamuwa da wanan kaddarorin haka ko me ?
Da sauri hjy take fadin yo meye haka ana zaune kallau zaki sakawa mutane kula a nan haka godiya ya kamata kiwa Allah da yanufa ba abinda mutane ke zargi bane ya faru dake din.
Inna ma kuka take a lokacin cikin kunar rai tana fadin bari hjy munga abu a rayuwan mu kamar kaina farau haihuwa diya mata a duniya.
Diya mace alherine hjy ta tare inna tana fadi don ni nan nafi kowa sanin dadin hakan don uwarsu ce ta zame min gata ga zuri,a na.
Don haka ba za a zagi diya mace a gabana ba ban bada amsa ba don na haifa nasan dadin su a rayuwana.
Gyaran muryan da Abba yayi daga kofa inna yasa mu dan dago kai muka kalli kofan da alama daga barci yake a lokacin saboda yanayin shi ya nuna hakan.
Me kuma ya faru nake jin kamar kuka ke kenan baki gajiya dayiwa mutane kuka akan abunda baikai yakawo ba a gidan nan.
Bawan Allah kada kaga laifin yarinyar nan raba da da mahaifi ba abin wasa bane don kukan yanzu na zuwan yarta ne takeyi.
Sai akace don yarta tazo su mayar muna da gida kamar na makoki dama haka yana kallon Asabe data fada mai magana kamar ba Abban mu dana sani da farko mai taushi da sanyin raiba.
Fuska a daure ya juyo yana fadin mama sannun ku da zuwa ashe kuns hanya tafe ?
Hjy ta sauke ajiyan zuciya tana amsawa Abba gaisuwan a cikin dan sakin fuska sai bin kowa da kallo take tana mamaki a ranta.
Taci gaba da fadin tafe nake da jikana don taki sake jiki tun bayan zancen daurin auren nan dayazo muna bata a cikin walwala sam.
Shine na kawo ta gida zata kwana biyu mijin ta zaizo ya dauke ta su tafi don jerabawan da zata fara wani sati mai zuwa in Allah ya yarda.
Saidai zanso nasan ko akwai wace zamu samu daga nan da zata tafi ta zauna muna da ita a can gidan nata na Abuja.
Duk wanan bayani da hjy kewa iyayyena sai a lokacin nake jin komai daga bayanin da take masu din a yanzu.
Abban ya gyara zama yana fadin tau hjy abune dake son natsuwa a yanzu zamu zauna bayan tafiyan ki mu duba wace ya dace ta bita can din inda halin hakan.
Ba damuwa hjy ta fada tare da kara basu hakkuri kan yadda auren yazo batare da an gudanar da komai yadda al,ada ya tanada ba.
Duk sai naji na muzanta sosai yadda hjy din ta samu gidan mu duk da dama ai tasan tunda har na iya zuwa aikatau a birni babu abinda zata sama a gidan namu.
Ina tuna irin kallon kaskancin da Aishan mami ke min tun fara zancena da ya Jafar din wani kallon banza da raini take watso min aduk lokacin da zamu hadu.
Da ace daga cikin su ne sukazo gidan namu a haka Allah kadai yasan irin abinda zasu fada akaina kan hakan.
Saidai ita hjy babu hakan gareta zaune take saman tabarma da inna ta shimfida a dakin ta mike kafa hankalinta kwance dasu tana masu bayanin komai.
Abba ya mike ya fita yana fadin bari ya dan fita sai ya dawo a daidai lokacin da ya jamal ya bada tsaraban da sukazo dashi da kayana a shigo dashi gida ke nan.
Akuma fadawa hjy ta fito don rana nayi yau yake son ya koma Abuja ba zai kwana ba kaduna .
Har lokacin banga lantana ba ba kuma danta a wurin har nakai ga tambayan sa, adatu wai lantana fa ?
Saida ta tabe baki kafin tace dani tana dakinta mana tana bakin cikin da dawowan ki tunda tayi shela a gari da cewa wai an sayar dake gun yan birni.
Wanan bakin cikine irin na hassada ga mairabo taki ne don tasan yanzu kinfi gaban ta har abada don haka ki daina saka zancen irin su a gaban ki yanzu.
Fitan Asabe a dakin ya ba hjy dama yin zancen siri da innar mu sun dan dauki lokaci don gaba daya hankali na ga yan uwana da muke zuba hira agefe daya suna murnan ganina.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.