Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel
Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 74 of 139
ZAINAB IDRIS MAKAWAKwana biyu ina daki kwance a cikin damuwa bana fitowa ko falon gidan a inda muka saba dan zama dasu mama muna hira.
Asibitin ma suke zuwa su duba hjy don ni ban iya fita yanayina kamar nayi jinyar kwanaki nake jin kaina.
Ya jafar yakan shigo ya dubani na dan lokaci saidai zai kare tsayin shi har ya bar dakin ban dago kai na kalli inda yake tsaye ba hakan kuma bai nuna fushin shi ga yadda nakeyi mai din ba.
Ranan dai dana kwatanci ya fice gidan na dan ja kafana na sauka kasa babu kowa a falon haka yasa na dan nufi wajen gidan don nasha iska kadan ko zanji jikina ya kara sakewa.
Wasu tsuntsaye dake kiyo ne a haraban wurin suka dauki hankalina har yakai na shagala ga kallon su sun dauke min hankali yadda suke ciyar da junan su abinci.
Barka da fitowa matar yaya naji an fada a bayana koda ban juya ba nasan ko muryan waye don muryan su yana da kama dana dan uwanshi hakan bai hanani gane ko waye a wurin ba yake gaidani.
Dan juyowa nayi tare da kakalo murmushin don dole ina fadin ya jamal ina wuni a cikin ladabi shima dan gyara tsayuwan shi yayi yana amsa min lokaci guda.
Tare da fadin ashe kwana biyu baki da lafiyane duk da nasan sanadin rashin lafiyan naki mijin kine ya jawo maki shi .
Da sauri na dan dago kai na sauke a kanshi don jin abinda ya fada yace yes zainab na sani shine yaja maki wanan ciwon don halaiyan shi da kika fara gani wanda da farko yake boye muna hakan ko ?
Don mu kanmu bamu san da hakan ba saboda ya boye muna koshi waye a wurin mu saidai ni tun ganin yadda auren ku ya wakana dashi na sa ido ga harkan yaya don in gano dalilin shi na bijerewa mami.
Da kuma dalilin dayasa ya zabe ki a matsayin wace yake son luluba a cikin bargon arzikin ta ya fito a mutum sak kamar kowa.
Wai zainab kinsan ke din mai arzikine arzikin da ba kowa Allah keba irin sa ba sai kebabu daga cikin bayin sa .
Shifa arziki da kike ji a wurin Allah kala kalane gun mutanene suka dauka arzikin dukiya shine arzkin da kowa zai samu yayi alfahari dashi.
Allah nama bayin sa arzikine ta hanyoyi daban daban akwai masu arzikin "ya"ya akwai arziki na hali akwai mai arziki na baiwa da arzikin hakkuri da arzikin wadatan zuciya da dai sauran su.
Kamar ke zainab kina da arziki dana fahinta wanda Allah ya baki wanda ba kowane zai iya fahintar haka ban sai mai natsuwa zai gane baiwan da Allah yai maki zainab.
Kallon da nayi masa na ban fahince ka ba yasa yace yes Allah yai maki arzikin bawai da hakkuri wanda ba ko wace mace take da irin wanan baiwan ba haka.
Ki duba duk da karacin shekarun ki zainab amma kin iya rike sirin mijin ki a zuciyar ki ba tare da kin fadawa kowa yasan halin da dan uwana ke ciki ba.
Na gani da idona ba wani ya fada min ba irin halin da ya dawo maki a ciki gidan nan last two days da suka wuce don a buge ya shigo gidan nan ya tayar dake.
Ban sani bako wanan ne karon ki na farko da kika ganshi a cikin wanan halin idan kuma har kin sani tun baya na dai yaba maki wurin kokarin boye masa siri da kikayi.
Idona ne ya kawo kwalla lokaci guda yace no bana son kiyi kuka a yanzu don kuka ba naki bane zainab a yanzu.
Saboda yakine ja a gaban ki dake tunkaran ki a yanzu don sai da taimakon ki zamu samu har mu shawo kan wanan matsalan don wanan yakin zainab ba naki bane ke kadai yanzu ya shafi kowan mu a yanzu.
Yanzu yin fushi ko kauracewa ya J baya da amfani a garemu baki daya don ni nan na nuna mashi bacin raina yan kwanaki da suka wuce kan fahintar wasu halayan shi danayi da yake boye muna.
Sai na fahinci fushi ko bashi baya baya hanashi aikata sabon daya samu kansa a ciki saidai ma ya kara kangare muna ta wanan hanyan.
Zainab a yanzu ya zama dole muja ya J a jikin mu fiye da yadda muke a yanzu dashi mu sanman ma keda kike zama matar shi.
Don ta hakan har Allah ya taimakemu ya bamu sa,a akan wanan halaiyan da yake aikatawa a boye don zainab gaskiya matakin da kike kokarin dauka bashi zai sa auren ki dashi ya rabu ba a yanzu.
Yin hakan kuma kamar kara turashine ga abinda yakeyi a yanzu shike nan kinga rayuwan shi ya kara shiga wani hali ta sakacin mu ashe ?
Don ke kanki ba zaki so kiga wani cikin yana irin wanan halaiyan ba kinga shike nan ko yaushe kina cikin damuwan hakan fiye da kina gidan sa ashe.
Dama alkawarin Allahne duk wanda ya kama hanyar aljanna zaita haduwa da abubuwan da zuciyar shi bata so haka kuma wanda ya hanyar wuta zaita haduwa da abubuwan da zuciya keso .
Shi yasa akace daga cikin hakkuri da akeso mutum yayi cikin rayuwan sa harda hakkurin biyyaya don Allah .
Don hana zuciya aikata sabon data ginu akanta farat daya abune mai wahalan gaske sai a hankali ana jan hankalin maishi anayi masa nasiha da addua a hankali tare da nuni ga hukuncin da ubangiji ya tanadar kan abin sai kiga maishi ya bar abin ba tare da wani tashin hankali ba.
Don haka zainab ina rokon ki a yanzu kada kice zaki bar yaya don wanan halin da idanunki ya gane maki a kanshi dama wanda baki gani din ba a yanzu bana fatan hakan a gareki.
Don ni kaina bazan so mami ko wani namu musanman ma mama Ramatu dake nan yanzu tare damu har ta fahinci wanan abinda yaya keyi ko taji hakan daga bakin ki.
Don haka zainab hakkuri zan kara baki kan hakan saifa kin jajirce gami da masa addua da saka ido kan duk wani al,amarin daya shafi rayuwan shi.
Ki nuna kedin matar sunnace a gareshi wace tasan right din ta na aure bawai ina nufin sai kin fito fili kin nuna ya baki hakkin ki na matsayin ki na mata a garshi ba.
A,a a cikin hikima da basira irin naku na mata ya kamata ki fata yakin da kika shirya a kansa yanzu ta hanyar sake jiki dashi ki daina wanan ja bayan da kikeyi a yanzu gareshi.
Mijin kine zainab idan yayi ba daidai ba ki fito fili ki fada masa abinda yayi din baida kyau ga Allah da al,adan mu a sannu in yana da rabo sai kiga ya bari.
Katse shi nayi da fadin to amma ya jamal kana ganin a matsayina na ba kowa ba a gareshi yaya zai yarda yaji nasiha ta ?
Me zai hana zainab ya bani amsa zai saurara maki don nasan shi di yana son ki kuma yana tausayin ki a zuciyar shi.
Wanda hakan nema har ya yanke shawaran ya aureki ya kawoki gidan shi ku zauna a tare ku kuma rayu a tare dashi duk ritsi duk wahala.
A karshe ina mai kara baki hakkuri ka wanan kaddaran da kika samu kanki a ciki a matsayina na dan uwan ki yayan ki bawai kanin mijin ki ba.
Hawayen da nake dannewa ne suka zubo min lokaci guda nace ya in sha Allahu zan gwada sharanka a kansa nima a matsayina na kanwarshi kuma matarshi a yanzu.
Nagode zainab da kika fahinci ne kafin wani yasan wanan abi kunyar da yaya ke kokarin sakamu a idon duniya nima zanyi iya kokarina in dinga fadakar dashi kan abinda yake aikatawa din a yanzu.
Na barki lafiya ni zan je asibiti yanzu sai dai ina son wanan damuwan da tashi hankalin ki daina yinsa daga wanan lokacin ki fito a matar auren ki sak a gidan nan ba tare da kin damu da warning din kowa akan hakan ba.
Nina barki lafiya ya fada ya juya ya tafi ya barni a wurin ina binsa da kallo zuciyana kuma da dinbin tunane kan aikin daya dangantani dashi din a yanzu.
Duk da nasan dama wanan din aikinane yin hakan inda hali kuma da jajircewa ya zama dole in shanye duk wani damuwa don in ba haka ba zuciyana tana gab data tarwatse a yanzu.
Sake tambayan kaina nayi ta yaya zan iya duk wanan abubuwan yanzu don ni mace ce mai kunya da sanin ciwon kaina.
Don haka ko zanyi ba zan iya zubar da kimana da darajana don kawai ina son wani ya gyara halinsa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.