Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel
Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 5 of 139
ZAINAB IDRIS MAKAWA🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
3ï¸Â⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
LITTAFIN KUDINE DARI UKU NE KACAL DON SAMUN SHI ZAKIYI TEXT A WANAN LAMBAN DON LAYIN BAYA KASAN A YANZU KO KI TURO KATI WAYA KO KI TURA BANK DA WANAN LAYIN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK NAGODE DA KULAWAN KU GAREMU, , , ,
Ta dade zaune tana son mikewa zuwa daki don ta dauko takardan da take son turawa saidai jikin daya fara manyanta tana jin kiuya da nauyin tashi daga falon ta zuwa daki a lokacin.
Wani wawan tsuki taja a ranta take raya ya kamata dai ta samu wanda zai dinga taimaka mata wanan dawainiyar yayi yawa a yanzu gareta.
Wayan ta dake gefen tane ya dauki kira ta dauko tana kara jan tsuki sai dai ganin bakon lamba dake kiranta ne kuma ga layin special nomba ne ya bata mamaki.
Taso share kiran don bata san mai layin wayan dake kiran nata ba a lokacin wayan yana gap da tsukewane ta samu ta daga.
Muryan namijine yake mata sallama ta amsa da mamaki don har lokacin bata gane mai kiran nata ba dai.
Bayan sun gama gaisawa ne mai magana ke fadin hjy nasan ba zaki sheda mai kiranki ba a yanzu don an dade bamu hadu ba tun muna US rabon damu gaisa.
Sai mamaki hjy keyi a ranta tana fadin waye wanan kuma wanda ban gane ba dan tunane tayi kafin tace isma,il soba ko ?
Dan dariya ya sake tare da fadin abin mamaki gaskiya kinyi kokarin sheda muryana is about 20 years yanzu da bamu hadu ba.
Ai ba zan manta da muryan ka ba a duk inda naji shi ta fada tana daure fuska kamar wanda take wayan yana kusa a lokacin.
Yace hjy sai naji kina kasan har kusan shekara daya da rabi abin ya ban mamaki matuka har ki shigo kasan nan muna jaha daya ban san da hakan ba.
Yanzu ka sani ai wakila don bai zama dole irin ku su sanda dawowan nawa bane nan ta bashi amsa.
Watau halin na nan a yadda nasan shi hjy baki barin ko ta kwana har yanzu ashe ?
Jin tayi shiru ba amsa yace hjy dama naso muyi wani magana dake ne wanda ya shafi rayuwan ki sai dai naga kamar baki maraba da wayana a yanzu.
Kai isma,il kafi kowa sanin halina don haka babu abinda ya shafi rayuwan ka dani a yanzu dama nasan don ka bata min rai ka nemi layina don haka ina maka warning da kada ka sake kirana.
Dan murmushi taji ya sauke dama yasan za a rina idan hjy iyami ce don bata daukan maganin raini ko kadan.
Shidin yasanta ta dalilin yin karatu a tare ne duk da ya girme mata sosai ga haihuwa amma haka suke shan fama da ita don akwaita da kwazo da basira a lokacin da sukai karatun tana goyon danta na uku ne .
Kawar da zancen yayi ta hanyar tambayan ta yaran don sunayen su bai bace mai ba har wanan lokacin.
Wanan tambayan yaran daya jefo mata yasa ta dan sasauta mashi tare da amsa mai da suna lafiya .
Ance in kana son kama uwa rike yaranta yanzu zaka zama masoyi a gurin ta hakan ko ya faru da hjy har ta manta da fadan ta dashi take fada mai rayuwan yaran ta a yanzu.
Karshe dai yace sai sun zo don bashi kadai ne zaizo ba akwai magana mai muhinmanci da zasu so suzo yi da ita.
Nan ma saida hjy tayi korafi akai kafin ta kashe wayan tana kara jadda mai cewa idan yasan shirmene zai kawo shi kadama su zo din .
Shi dai dariya yayi yana fadin sai idan sunzo din zataji sukai sallama ya kashe wayan.
Kai hjy ta girgiza tana fadin mutane akwai tsegumi har suna daukan zancen abinda bai shafesu ba suna dangantawa da lamarin su.
Mikewa tayi don dauko takardan datake so daki har lokacin tana maijin zafi a ranta na ba gaira ba dalili wata kila kuma har yanzu haushin wayan da abokin karatun ta yayi matane oho ?
Kiuyan fitowa dakin tayi zuwa falon ta har akai kiran sallah ta samu ta mike don zuwa sallah.
Yanzu idan akwai abinda hjy ta tsana shine rashin son motsa jikin ta don hutu yariga da ya gama ratsa ko ina nata ga yaran da take zaune dasu baka more ne gaba dayan su son jikin su yama so yafi na hjyn yanzu don gatan da ake nuna masu.
Sai dai duk da hakan tana dan kokartawa tana sakasu wani abin can ba,a rasa ba sai dai zata sha mita da jini duk tana hakkuri da wanan.
Wani lokaci kuma zata zage tayi masu fada sosai akan rashin son motsa jikin da basa yi dan abu kadan zasuce sun gaji.
KAUYEN ANCAU
An kawo amaryan Abba wata bakace gajera bata da tsayi saidai akwai mazauna irin na mata gareta.
Ni dai banga abinda nagani gareta ba sai halin kiyayya kawai da Asabe ta dagwarawa mahaifiyar mu in bashi ba babu ta inda ta kama kafan innan mu.
Zaman su ba yabo ba fallasa don inna bata shiga tsabganta ko yaushe tana kofanta ita kuma amarya tana lungun Asabe.
Idan muna gida mune abokan hiran innar mu sai kuwa ranan da akace itace da girki ranan zan fara labe labe don ban yarda da tsarin Asabe ba .
Na cewa mu dinga kwana dakin ta haka yasa na share dan karamin dakin da ake tara tarkace a gidan mu dakin ba wani girma ke gareshi ba asalima madafane Abba yayiwa innan mu don da dama tana wahalan girki a ruwan sama.
Abba yayi fada har ya gaji don ko naje lungun Asabe da sunan kwana bana shiga dakin ta saidai in tsaya daga waje.
Idan na faki idon Abba ya shige zan dawo wanan dan dakin in kwanta dama mu uku ne masu dan wayau da muke zuwa kwana dakin Asaben.
Zakaji tunda asuba Asabe na fada wai an jawo mata kwanan wahala a daki yara sunzo sun hanata shakat daki suna damun ta da tusan dare ko tace wai an mata fitsari a daki.
Ranan da tace fitsari kanwata dake bi mun tace itama daga ranan a inda nake kwana zata dinga kwana don sherin Asabe ya isheta.
Sai lokacin Abba yasan ban kwana dakin dole yakawo ido yasa mun hakana muka mayar da dan dakin wurin zaman mu koda da rana ne a nan zamu zauna muyi tsabgogin mu.
Wanan baiwa Asabe ba don ganin yadda mukan saka innan mu a cikin nishadi wani lokacin har mu zauna ana hira da dariya .
Sai kuma hakan ya fara basu haushi suka kulla wani sherin a kaina wanda ya girgiza mu ga baki daya yan dakin mu.
Ranan monday da safe muna ta shirin makaranta tunda naga Asabe ta fito daga lungunta zuciyana ke bani akwai wani abu da zai faru a gidan don daga dakin da muke ina jin muryan ta a tsakar gida tare da Lantana Amaryan Abba suna dan zance kasa kasa.
Don ranan inna muce da girki a dan dakin mu muka kwana inna tunda ta fito ta dama kokon safe da zamu karya dashi kafin mu fita ta koma daki don ta shirya kananun da basu iya shirya kansu sai an taimaka masu.
Na fito da sauri kada in makara kofan innar mu na isa ina fadin inna ni zan tafi kada in makara.
Na juyo inda su Asabe suke da zuman in sallame su lokacin Abba daga daki yake fadin kin karyane Abu ?
Na karya na bashi amsa daga waje don ban shiga dakin ba tunda na girma innan mu ta koya muna hakan idan Abba yana ckin dakin namu.
Zoki karbi murtala ki rike ko fanke kya saya a hanya Abba ya fada daga dakin.
Tsiyan banza dama nasan kai ke koya masu kashin kudi don baka gudun Abin kunya kai kan wa yan nan yaya matan naka.
Karatun bokon dole duk yan uwanka wa kaga ya dage kan sai diya mace tayi boko haka ?
Badani za, ayi wanan abin kunyan ba kuke nan ko yaushe ku dorawa ubanku wahala don kawai baisan ciwon kanshi ba.
Gani kunan haihuwan yuyuyu da aka tara mai agida ace har mace bakwai ko daya ba kawar ba a cikin ku.
Daku da uwarku kunki ku barshi ya ji da abinda zai ciyar daku da wanda zai tara yai maku aure nan gaba.
Amma kullun in sata in maita sai ya lalube aljihun shi ya baku dan abinda ya kwana dashi ko kuma in bakuje makarantar ba uwar ku ta lalabe shi a daki.
To hakan ba zai yuyu ba don baku da uwar ku kadai na haifarwa shi ba don haka daga yau na kashe wanan bokon naki.
Aure zan maki shekara goma sha hudu ai kin isa aure har kina batun wuce munzali.
Gwanda ki tafi dakin mijin ki yaji da sauran yan uwan ki da suka rage kafin suma a fitar dasu sai gidan ya koma hondaku .
Bansan lokacin da Abba ya fito daga dakin inna ba don tunda ta fara magana na zuba mata ido ina kallon ta cikin al,ajabi da mamakinta.
Muryan Abba naji yana fadin haba dai umma aure fa yanzu ga Abu haba wani irin aure kuma kamar yadda taken nan.
Hae guda nawa Abu take da za ace za,ai mata aure a yanzu akaita gidan miji ?
Wani tsawa ta dakawa Abba tana fadin yi min shiru shanyaye kawai wanda baisan ciwon kanshi ba.
Dame su hansai da Adawiya suka fita ga shekaru da akai masu aure kuma suna zaune kalau a dakin mazan su har yanzu.
Abba yace Allah ya huci zuciyar ki umma ni gani nayi har guda nawa Abun take ne da za a ce aure yanzu.
To ai gaskiya umma ta fada inji lantana amaryan Abba ta fada aure ga ya mace shine wajibi.
Ba wani karatun boko ba can da yanzu shike kara lalata yara yanzu haka idan ance ma yarinyar mnan tasan komai game da aure kada kayi musu.
Ke lantana ahir dinki ga bata min diya da wanan kalamin naki sai Asabe tace kaji sauna yo ai gaskiya ta fada ko karya nakeyi Asabe ta tsatsareni da idanuwan ta na tsufa.
Bansan lokacin da kuka yazo min ba na juya zuwa cikin dakin da na fito don jin sherin da ake kokarin lakaka min da farar safiya haka a gidan mu.
Sauran magana ban jisu ba saboda kukan da nakeyi makarantar da ban tafi ba ke nan ranan don maganan Asabe tankar umurni ne ga Abba gama kowa a gidan.
A karshe dai na fito yin alwala nake jin lantana na fadin toke umma tunda kowa yasan kyauta na dan maciciji ne babu masunsuni gareta.
Ai baki kyale haka a zuba mata ido ba dadai kin nemi wani a cikin kauyen nan ki hadata dashi zaifi sai aji da sauran .
Don muddin tana gaban ku haka ba wanda zai kula sauran duk sai ai masu daukan daya kinsan halin garin nan sarai.
Duk wanan zance da sukeyi inna tana jin su bata ko nuna tasan ana zancen ba ta kawo ido ta sakawa kowa don nuna ka waici ga wasu mata na karkara.
Har kwana hudu sati na batun shigewa ban shiga school ba na gaji da zama daki mu don ko tsakar gidan mu na daina fita idan ba wani abu zanyi wajen ba.
Daki innar mu na shiga na saneta tana nade kayan data wanke na yara gaida ita nayi ta juyo tana amsawa fara nade kayan nayi sai inna tabar min nadin ta juya tana fadi.
Saliha tazo tambayan kitso nace ta tafi ta dawo don nasan halin ki sarai dan ajiyan zuciya na sauke ina fadin.
Ni inna banwa kowa kitso a barni inji da abinda yake damuna sai naga inna tayi murmushi tana kaiwa zaune gefen gadon famekan ta.
Tace ai dama haka ake son a ganki cikin kuntatawa da damuwa sai bukatan lantana da umma ya biya idan sunga kina wanan takura dama abinda ake so ke nan damu.
Shiru nayi ina nazarin maganan inna da bata kara dora wani lafazi ba bayan wanan data fada hawaye ne yadan biyo fuskana na share da sauri.
Don nasan ran innan mu ba zaiyi dadi ba itama don ban taba jin ta furta komai cikin zancen hanani zuwa makarantar ba sai yau da tayi mi hannun ka mai sanda.
Dan hira muke jefi jefi mukaji muryan saliha ta dawo tana tambayan kitson ina jin tana kwada sallama lantana na fadin wai waye haka ke damun mu da sallama ne.
Fitowa nayi daga dakin inna ina amsawa tare da fadin saliha shigo dama yanzu inna ke gaya min kin zo ai ina barci.
Saliha race wallahi nazo ko zan samu ki kwashe min kai zamu birni wurin bukin dan uwan maigidan mu ne.
Nace bissimilah shigo bari na dauko tabarma na juya zuwa dakin innan mu na dauko mata tabarma muka zauna zaman kitson.
Na koyi kitsone akan yan kanne na don yawan yawon neman kitso da kashin kudin da inna takeyi kan kitson mu.
Wanan yasa har na koyi kitso ina zama in masu har na hannu na iya ba wevean ba kawai don ina dake son kitson hannu wanan kuma a kanta na koya.
Yanzu kuma in muna makaranta nakan koyi kumshi a pepper har na fara zanawa kannena sai dai ba sosai na iya ba.
Wasa wasa tun daga ranan da naiwa saliha kitso mutanen unguwan namu ke shigowa wurina yin kitso ko su turo yaran su in masu.
Sai ya kasance har na fara mantawa da zancen hanani karatun da umma tayi yanzu.
Ga kudi baya katse muna dan abinda zamu kashe a kauye baya buwayan inna yanzu.
Don a wuni akalla muna dan rike dari biyu ko dari uku tundai idan akave weekend ne don ba wani kudi bane mai yawa kudin kitson kauye talati hamsim ne wani a kyauta zan mai ya tashi.
Ga Abba abin kara lalacewa yayi mai tun shigowan Lantana gidan shi abinda zamuci ma yana batun gagaran mu a gidan.
Don haka muke dan dora karamin tukunya mu dafa dan cimar da zamuci iyamu damu don Asabe ta fara a gaban mu zata dan dafa abu.
Saidai muji tana kwalawa Lantana kira tazo ta karba idan lantana ta karbo a gaban mu zasu zauna suci har tana santi don muji haushi.
Wani lokacin yan kannen mu sai su sa ido suna son ci sai inna ta doke su ko Asabe ta dinga fada ita ba zata iya ciyar da taron yan mata ba uwar mu data haifo mu ta nema ta bamu muci.
Da ku mazane ai da bamu kai haka ba a gidan nan da yanzu kuna wurin nema kuna taimakawa mahaifin ku.
IIrin wanan maganganun na kakar mu yasa muka dan fara dafa tukunyar gefe don kada kannen mu su koyi daukan ido ta wanan dalili.
Ranan inawa wata makwaciyar mu kitso kanwa saratu tana dafa fate don shi zamu gyara muci don Abba bai kawo komai a gidan ba tun safe.
Girkim ya dauko kamshi duk ya dume gidan da kamshi saratu na bakin murhu tana faman fita wuta don iccen baya ci sosai.
Sai ga lantana ta fito lungun Asabe gurin kwata inda muke wanke wanke kakarin amai ta fara da karfe da yaji.
Sai duk mukayi tsaye cirko cirko muna kallon ta da mamaki don bamu dade da jin dariyan su ba da asabe kamar ba sarakuwar ta bace lantana.
Sai ga Asabe da sauri ta fito tana salati tare da fadin yau may zangani haka Lantana lafiya meya same ki ?
Asabe ke tambayan ta a rude sai ga inna ta ma tafito daga dakin ta tana fadin Lantana meya faru.
Ganin Lantana na nuna gurin da saratu ke girki da hannun ta alama dai warin girkin namu wai ya jawo mata aman a yanzu.
Ja inna tayi baya don ta fahinci makircin da Lantana ke shiryawa a kan girkin da mukeyi din don muci tun safe bamu karya ba.
Wani guda mukaji Asabe ta sake wanda bamu fahinci ko na menene ba sai da tace .
Ahhaye nanaye Allah nagodema yau magaji ya bayana a gidana da yardan Allah.
Ta juya wurin saratu tana fadin ke kashe wutan nan ki bar girkin nan kada kija min hasara a gida don ku ba damuwan ku bane tunda bata son kamshin dahuwan naku.
Saratu ta mike tsaye ta fara buga kafa tana yaya zan kashe wuta kina ganin tun safe bamu karya ba.
Kada ki kawo min diban albarka nace a kashe wutan ku mutu idan bakuci ba mana waya damu daku wanan matsalan uwarku ce.
Wallahi bazan kashe ba tunda bai dahu ba saratu ta bata amsa saiga inna ta laiko daga daki tana fadin saratu jaye itace don Allah banson gardama da manya.
Tamayi gardaman dani Asabe ta fada tana nufar wurin randan ruwan mu ta debo ruwa a roba tana zuwa ta lemawa itacen da garwashin wuta lokaci guda wutan ya mutu.
Aiko saratu ta sake wani uban ihu tana fadin wallahi ban yarda Asabe tunda ba bamu abinda zamuci zakiyi ba tana magana ta nufi wurin murhun tana hawaye.
Muryan innace ke fadin karkiyi barshi hakana kuci ko bai dahu ba idan zai ciyu.
Wallahi inna bandade da zubawa ba tazo ta kashe wutan matar makwabtan mu da nakewa kitsone tace dauki dahuwan ki shiga gidan mu ki karasa girkin naki don Allah ku bar wanan magana.
Saratu tana sharan hawaye take fadin wallahi Asabe saina rama don ba yarda zanyi ba kun dafa naku kunci zaki hanamu dafawa yanzu.
Ranan dai sai gidan makwabciyan mu saratu ta karasa dafa abincin da zamuci ga Abba bai dawo ba har dare don haka da bafon faten ba haka zamu kwana da yunwa a ciki mu.
Saida safe ne nake jin muryan Abba cikin jin dadi yana fadin masha Allah abu yayi kyau Allah ya raba lafiya.
Ma,ana dai watau lantana ta samu ciki a gidan mu ke nan ni banji komai a raina ba a lokacin .
Don ban gama mallakan hankalin kaina ba da zan gane may hakan ke nufi damu sai can naji muryan Abba nawa saratu fada don me tayiwa Asabe rashin kunya kamar Abba zai doki saratu din.
Ban san ina Asabe ta tafi ba wai ashe ta fitane zuwa gidan wata mata mai bada magani ta ansowa lantana maganin baki kada innan mu ta zubar mata da cikin jikin ta.
A daidai wanan lokacin saratu ta shige lungun Asabe ta fasa mata babban randan ruwanta ba wanda yasan da shigan ta har ta fito daga sashen.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.