Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel
Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 80 of 139
ZAINAB IDRIS MAKAWAYa fito daga wanka da safe ya samu wayan shi dake ajiye saman bedside din shi yana ringing yayi saurin kai hannun shi ya dauka kada ya katse.
Bakon lamba ya gani yayi kamar kada ya daga saidai ya daure ya dauka don baisan wanda ke kiranshi da wanan layin ba.
Don tsayin kwanaki biyu ke nan maishi yana yawan kiranshi a daidai wanan lokacin don haka maishi yasan shi kenan farin sani yasa ya kirashi a wanan lokaci .
Ya dauka da hello muryan taju ne akan layin ya fara magana da fadin nasan kayi fushi dani sosai yasa na kiraka na baka hakkuri don banzaci hakan zai faru ba ni kaina zafin kishine ya sakani yin hakan a lokacin.
Saida ya gama sauraren shi yake fadin ka dauka dolene nake tare dakai dama ko kuma bazan iya zama idan babu kaiba.
Taju ya saki wani dan ajiyan zuciya yace kayi hakkuri bana iya rayuwa idan bada kai ba boss kasa ka maye gurbin na da son wani bayan ni.
Hankalina a tashe yake tun ranan da haka ya faru a tsakanin mu kayi hakkuri ka rike kaunar dake tsakani da kai bana iya jure ganinka tare da wani kuna rayuwa ina kallo.
Ya jafar yayi murmushi a tausashe kafin yace taju ke nan kana sane kayi kokarin tona min asiri don kawai wani bakin kishin ka na banza can.
Taju ya katse shi yana fadin Iam sorry boss banyi haka a cikin hankalina ba a lokacin kasan irin son da nake maka a rayuwana.
Jafar din yaja wani uban tsoki tare da furta is too late now don na dade maye gurbin ka da wani so ka manta da wanan a tsakanin mu.
Yana fadin haka ya kashe wayan shi taju ya kalli wayan yaga ya kashe abinsa idon shi ya runtse yana jin wani zafin son jafar din na ratsa zuciyar shi lokaci guda.
Don tunda ya samu jafar ya bar sauran abokan harkan shi don jafar mutum ne har mutum yana da tabbacin idan jafar ya barshi rayuwan shi yana cikin gararari ke nan.
Shiko jafar din wayar ya jefar saman gado ya koma gefe ya zauna ya tallafi kanahi da hannayen sa biyu zuciyar sa tana masa azalzala.
Don shi yanzu zuciyar shi ta kasu biyu don yasan kirsis yake da asirin shi ya tonu muddin wanan yarinyar mai wayau na gidan nan.
Bai mu maganan zancen karatun mu ba ko zancen tafiya ai bada mu za a tafi ba asalima dai dan kwana biyun nan na kula da yana yawan daure fuskan shi ga kowa a gidan.
Ni hakan bai dameni ba tunda dama ba wani shakuwa bane tsakanin mu saidai abinda na zata ko hjy ta zauna dashine shima kamar yadda ta zauna dani tana bincikena kila shima sunyi hakan dashi.
Ranan dai da safe muna zaune a dakin hjy yake cewa mu shirya zamu fita karfe hudu na dauka badani yake magana ba saida ya kalloni yana fadin bakiji bane na dago kai ina fadin naji a sanyayye.
Daga inda hjy take zaune naji tace umhumm kawai tana dan kawar da kanta gefe daya daga barin kallon kowa a dakin.
Mama Ramatune tayi karfin halin da matarka zaka fita ko damu duk don kayi magana ta baibai bamu fahince ka ba gaskiya a nan ?
Da ita nake mama akwai inda zamu tafi tare yau ya bata amsa daga haka ya fice ya bar dakin hjy ta bishi da kallo tare da fadin miskilin banza kawai ya kama daure fuska kamar bai taba dariya ba.
Fushi yake don nayi masa nasiha yake faman daure fuska haka don yasan yayi laifi yana gudun naci gaba da fada.
Jin hakan yasa na dago kai da sauri ina kallon hjy don bansan me tayi mai fada a kai ba itama din ni take kallo kafin ta kawar da kai tana fadin .
Ni dai na fada mai gaskiya don kada yaga kamar amana wasane duk wanda yai sakaci da rikon amana zai fada ranan lahira.
Karfe hudu shaf na shirya don gudun kada inyi laifi a gareshi saida na dan zauna zaman jiran shi kafin ya fito daga part din shi.
Ina dakina kwance ina jiran fitowan shi ya shigo dakin tun daga nisa yake karewa kyakyawan surana kallo.
Kyakyawan suran kafafuwana da ya dan fito har zuwa sharaban kafana suna waje don yadda na kwanta din a lokacin.
Ya tsaya ya shagalta da kallon su saboda yadda ya hangosu sunyi bul bul dasu tankar bana taka kasa dasu a yanzu.
A hankali ya tako zuwa inda nake kwancen na shagalta da karatun wani littafi dana tsunta a gidan na labarai.
Banji shigowan shi ba dakin haka ma takon shi zuwa bakin gadon duk ban ji shi ba a lokacin.
Sai ji nayi girshi a na ja min rigar jikina daya tattare har zuwa sharabana dake waje tunda ni kadaine a dakin sai ban damu da hakan ba.
Wani irin zabura nayi lokaci guda ina kokarin sake ihu don nasan halimatu dai ba zatayi min wanan haukan haka ba.
Na juyo da wani irin sauri ya jafar na gani tsaye a kaina ya mayar da hannayen shi ya rungume saman kirjin shi.
Da sauri na yunkura na tashi zaune ina kokarin gyara rigan nawa ya sauka da kyau kafin in dago kai in jefeshi da wani irin fitinannen kallo.
Yace cikin daure fuska ki tashi mu tafi kina nan kwance lokaci yana kurewa gaki nan kwance ?
Yana fadin haka ya juya ya fita daga dakin kai tsaye nima tashi nayi saida na gyara fuskana irin dabi,an mata kafin in fita na sameshi cikin mota zaune yana jiran fitowana.
Nayi mamakin ganin shi a gaba wurin mazaunin driver ke nan mu kadai zamu fita yau ba tare da kowa ba na tambayi kaina .
Kafin in iso ya bude motar na zagaya zuwa dayan gefen na zauna tare da rufo kofan bai tsaya jiran komai ba yaja motan muka bar gidan.
Tafiya mukayi mai nisa da gidan hankalina yana gun motocin danake gani tankar masu shi suka kera abinsu don kyau kafin naji yace may kika fadawa hjy har take tambayana zaman mu dake ?
Da sauri na juyo na dan kalleshi tankar bashi yai maganan ba don hankalin shi gaba daya yana ga tukin da yakeyi lokacin.
Kaina na mayar a wurin window motan naci gaba da kallon da nakeyi na motoci da gidajen su har ma da al,umman garin da nake gani kamar aljannu a idona.
Yaci gaba da fadin na dauka kina da wayau da farko ashe abin ba haka bane don na manta ke din karamar yarinya ce da bata iya rike siri a cikinta ashe ?
Daga cikin tsakiyan kaina nake jin sautin kalaman shi wanda babu tamtama idan nace zan bashi amsa a lokacin bazan fadi daidai ba.
Barin fada maki kiji daga yau sai yau ba hjy ba ko mami data haifeni kika kara fadawa magana na sai kin kwamce da baki sanni ba wallahi.
Wani irin juyowa nayi tare da kallon shi lokaci guda ina fadin kana dai wahal da kanka domin ni banga riban fadawa wani abinda kake aikatawa ba bayan Allah.
Allah kadai ya kamata nakai kukana gareshi ba wanin Allah can ba don shi daya halice ka kuma ya kawoni karkashin innuwan ka na zauna shi yasan yadda zaiyi dakai.
Naci gaba da fadi cikin muryan dake son nuna kuka nason zuwa min bakaji tsoron mahalincin kaba nawa zakaji yaya ?
Ya dago kai yana kallona ido da ido tare da sauraren abinda nake fadi babu kuma alaman tsoron shi a fuskana ko kadan.
Da sauri ya maida kanshi ga tukin da yakeyi zuciyar shi yana tafasa tare da jerowa kanshi tambayoyi wanda basu da amsa gareshi a lokacin.
Wani irin fisgan motan yayi lokaci guda saida tsoro ya kamani a zuciyana amma a fili saina dake da hakan ban yarda na nuna mashi hakan ba.
Fuskan shi kawai zaka kalla kasan rayuwan shi a bace yake wani babban moll ya packer motar sai daya dan sako iska daga bakin shi ta hanyar furzoshi da karfi lokaci guda alaman hade bakin ciki ya dan fadi a dake ki fita mu shiga nan ba tare daya kallo inda nake zaune ba.
Fita nayi kamar yadda yace dani din shima ya fito muka jera zuwa cikin wurin inda mutanene birjit wasu na shiga wasu na fita da kwalaye mai kama da jakka a hannun su.
Bai tsaya ba sai fannin kayan mata naga ya danyi magana mai kama da yare kafin matar ta nufoni tana washe baki.
Kaya take daukowa sai ta zaba tana gwadawa a jikina tare da yaba yadda yayi min kyau nidai ina tsaye kimkyam kamar an dasani a wurin muka koma fannin takalma nan ma tana biye damu a baya da taimakonta har saida yace sun isa.
Halimatu ma ta samu nata rabon don sayayya sosai mukai mata su man shafi da turare masu tsadan gaske ya saya muna .
Bayan ya biya mun fitone ya biya wani shago a nan ya barni ya shiga naga ya fito da shigen jakar da aka sako muna kaya a wancan shagon sai dai ya riko daya a hannun shi yana zuwa wanan din ya saka a gaban mota kusa da kafan shi sauran aka sa a bayan mota.
Hanyan gida ya dauko a lokacin har magariba ya dan gwauta ga yadda yanayi ya nuna na garin don wuri ya fara duhu ko.
Mun shigo gidan babu kowa nasan sun shige yin sallah a lokacin don haka nima na nufi dakina don sauri in gabatar da nawa sallah kada lokaci ya kara kurewa
Idan kin tafi kayan ku fa wazai shigo maki dashi dakin naji muryan shi yana fadin haka a bayana.
Naja na tsaya wuri daya ba tare dana juyo ba ban kuma wuce part dina danayi niyar tafiya ba duk da ina sauri.
Naji takon tafiyan shi sai muryan shi naji gap dani yana fadin banyi wanan maganan dake ba don ki fadawa hjy munyi.
Ba halina bane fallasa sirina wanan abune daya shafeni a yanzu ni daya har in baka tuba ka daina ba nasan watarana idon su zai ganan masu kamar yadda Allah ya nuna min nima .
Don Allah ba ai masa wayau ga duk wani abinda mutum yake ganin yana boyewa dole akwai wata rana da Allah zai fallasa shi ga mugun aikin sa.
Allah ya baka ikon ganewa ka tuba ka daina don kan ka juyoni yayi da karfi har saida na dan firgita don ban zaci haka daga gareshi ba a lokacin.
Da sauri nayi kokarin ja baya daga rikon dayai min din saidai na kasa hakan don ba karamin riko yai min ba a lokacin.
Wani zafi hakan naji har kasan raina.
Na dago a fusace don mashi kashedin hakan da yai saidai muna hada ido dashi kwarjinin shi da zatin shi ya hanani hakan gare shi.
Kaina na mayar kasa da sauri don ba zan iya jurewa irin wanan kallon da yake min ba a lokacin wanda na kasa fassara hakan a raina.
Shiru na dan lokaci kafin muryan mama ya shiga kunnuwan mu tana fadin kuma nan kuka tsaya ina dai lafiya na ganku haka ?
Lafiya mama muna dan maganane a nan yana fadin haka ya sakeni da sauri na juyo ina fadin sannu mama tace har kun dawo ashe ?
Mun shiga yin sallah ne yanzu ma wayana na manta dashi a nan inda na zauna nazo dauka shiko a lokacin har ya kai kofan part din shi don haushi.
Don ba haka yaso ba yasone ya ban wahala sai na raina kaina sai ga mama din ta kwafsa mashi don fitowan ta a lokacin.
Kayan da yake maga wani daga cikin yan aikin gidan ya fara shigowa dashi niki niki a cikin dan guntun turanci na ce dashi ya kai part dina mama tabi kayan da kallo.
Tace ashe ku sayayya kuka fita waini wanan abin naku na daure mun kai yau ina antyn mu dake fadin sai kuma tayi shiru ganin haka nace banyi sallah ba mama.
Jeki ki sallah kada ki makara don lokaci yaja sosai na juya da sauri na barta wurin na wuce zuwa part dina.
Sallah nayi kafin na samu wuri na zauna a dakin ban fito ba don injin nauyi da kunyan mama a yadda ta samemu dashi a falon dazun don haka nai zamana a dakin kawai.
Wanka nayi na shirya kwanciya na saka hijab saman kayan dake jikina na nufi part din shi har na shiga falon nasa .
Sai naga wanan dan jakkan daya riko da kanshi aje saman kujera har na dan wuce wata zuciya tace na koma naga meya sayowa kanshi ne haka bai bari wani ya dauko mashi ba.
Saida na kai zaune na bude ledab a hankali idona yai arba da kwalaben dake ciki kwalban kawai abin kallone.
Zuciyana bai yarda da hakan ba ina kkkarin karata ko meye a cikin kwalban naji an fisge kwalban a hannu na tare da fadin get out from dis part stupid yana nuna min hanyar fita.
Har abin naki yakai kiyi min bincike who give you dis right da zaki taba min kayana a hasale yake magana kamar zai mareni ko me ya tuna kuma oho.
Ya duka ya dauki saurab kayan nasa nima mikewa nayi da sauri na fice daga part din sauri zuciyana cike da zargin shi.
Ina shiga dakin na rufo kofa tare da saka ma kofan key na nufi gado na fada saidai ban kwanta ba ni ban kwance kuma bana zaune sai tunane nakeyi a raina.
Dama wai haka aure yake ne nake ganin mata suna walwala ko wani lokaci kaga kamar basu da damuwa a tare dasu.
Meyasa ya jafar yake min hakane koba komai yakamata ya rikeni tankar kanwarshi ta jini a gidansa tunda yasan yadda mukai aure a tsakanin mu.
Tunane kala kala nayi shi a wurin karshe na mike na dauro alwala don barci ya kaurace min gaba daya a idona ranan.
Sallah nayi raka,a hudu na dade wurin ina addua ina mika kukana ga Allah kafin naji sanyi a raina har barci ya daukeni.
Naso makara ranan don ban kwanta da wuri ba a gagauce nayi sallah na koma na kwanta sai barci kuma.
Kodana tashi shadaya na safe wanka nayi na fito bayan na shirya na fito don gaida hjy don nasa zata damu da rashin ganina da batayi da wuri ba ranan.
Da sallama na shiga dakin ta saidai ita daya na sama tana zaune tana nafila na samu wuri na zauna harta idar bandade da zama ba naji tana fadin zainabu kin fito ?
Eh hjy ina kwana ta amsa min a cikin fara,a tare da fadin ai mijin ki daya shigo nan nake tambayan shi yace jiya baki kwana da dadi ba.
A raina nace makaryaci ke nan shikan ya hada duk wani abin ki da Allah ya hana Allah dai ya shiryoshi ya daina wanan hakin .
Saidai a fili dan murmushi nayi ina fadin ciwo kaine kawai ai hjy kuma nasha magani ya bari.
Dole ki ciwon kai jiya kun fita kun dade tunda baki saba fita irin haka ba dama kin dai kara cin wani abuko yanzu bayan kin tashi.
Zan daici hjy na fada a cikin ladabi to kinga ga wanda suka kawo min niba dadin abincin su nake ji ba ki tashi ki diba kici yanzu.
Dole haka na mike na dan dibi kadan na zauna nan gabanta kinga da haka zaki ta kamo zuciyar shi don kinga yanzu shi na masa fada ya nuna min yayi biyayya ga magana na yanzu .
Don haka kiyi ta hakkuri bana son har uwarku ta gane wani rashin jittuwa yana shiga tsakanin ki da mijin ki ta yadda zata dara muna.
Kinga Ramatu da kike gani diya tace nasan halin abinna kamar me yanzu tana zaman idon uwarku ne a gidan nan nasan duk abinda suka kitsa kan zuwa nan da ita .
Don baki san yadda tafiyan ya wakana bake ta nuna idan bada Ramatu ba saidai a fasa tafiyan dole mijin ki ya yarda da hakan mukazo tare.
Don haka nake son kafin mu tafi ta koma ta fadawa uwartaku zaman lafiya kukeyi tare dashi kinga duk wani shirin su sai ya tafi a banza ke nan.
Saidai abindake wakana tsakani shi da dan uwanshi na rasa ko menene ya hadasu haka a yadda nasan su a tare nasu yafi zuwa daya.
Sai gashi yanzu naga suna wasan kura da kare kamar wani abu na faruwa a tsakanin su ko kinsan meya hadasu haka wanan abin ke faruwa ?.
Da sauri nace nima hjy haka na fahinta don ranan ma naji mama nawa ya jamal fada kan hakan yace da ita ba komai .
Saboda na gane hjyn tana son tayi min wayau manya taji wani abu daga gurin yasa na fasa mata hakan don ta barni.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.