Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel
Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 102 of 139
ZAINAB IDRIS MAKAWALITTAFIN KUDINE YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DON SAUKE HAKKIN WANI A KANKI, , ,
Alhamdullahi zan iya cewa don jikin yaya yayi sauki sosai kuma ina bashi kulawan daya dace sosai a matsayina na sunan matar shi.
Yar uwan shi kuma mafi kusa dashi a yanzu haka yasa na zage sosai wurin kula dashi din don shima a iya yin shi gaskiya yana nasa kokarin damu tankar yan uwansa na jini.
Don haka naba kaina shawara dama kuma kinsan mace ga rauni da sanyi hali a wurin namiji nima hakan ne yaci don shi kanshi saida yayi mamakin yadda nake bashi kulan a lokacin.
Ba tare da wani jin komai ba tsakani da Allah nake masa komai yadda ya kamata don shi kanshi ya fahinci hakan.
Safiyane yau na shirya cikin wani riga ja na daure kaina da ribon mai ja shima da farin duwatsu.
Dan gyale ja na dora saman kaina sai dai bawai rufe kai din nayi ba sosai sai kamshi da jikina keyi a lokacin .
Dakin na part din shi na nufa don gaida shi da kwana akwance na hango shi ya kurawa silling din dakin ido kamar mai tunane.
Kamar yadda na saba idan ni nazo gaidashi da kwana bashi ya sameni a zaune part dina ba.
Jin motsina baisa ya motsa a yadda na riskeshi ba har nakai bakin gadon na gurfa gwiwa bibiyu ina fadin yaya ina kwana ya karfin jikin kuma ?
Zainab na dago kai na kallo shi sai kuma naga ya danyi gajeren murmushi ya kawar da kanshi daga inda yake kallo.
Haka sai yasani tsarguwa da yadda yai min din ina a yadda nake ban motsa ba nayi shiru shima hakan baiko amsa min gaisuwan da nayi masa ba na safen dana
saba zuwa part din in gaida shi don da sadiya mukan zo gaidashi din ranan kuma ni daya nazo.
Sai can nace dashi a hada ruwan wankane ka watsa yanzu na fada ina kallon shi don jin amsan da zan bashi.
Ki hada nima ina son inyi wanka yau in dan fita tunda naji sauki sosai mikewa nayi zuwa ban dakin na hada mai ruwa kamar yadda yake son yi dashi tun ranan farko daya fada min yadda zan hada mai din.
Na hado ruwan na dawo na fada mai zan bar part din tunda ba wai wani hira mai tsawone irin na mata da miji a tsakanin mu ba dama.
Muryan shi ke fadin sai ki fitar min da tufafin da zan saka idan na fito tunda yanzu naga zaki fara aikin ki na mata a gareni.
Wani irin juyowa nayi ina kallon shi a cikin mamaki a fuskana don jin abinda ya fada din gareni.
Ba matsayin mata ya saka nake maka wanan ba a matsayi kanwa a gareka da kuma Allah nake maka komai don ka cancanci hakan a gareni .
Ina fadan hakan na sa kai na fice daga dakin don jin da nayi yace fita zaiyi a lokacin da ba haka ba idan na shigo bana fita haka zan zauna a wurin shi.
Duk da ba wani magana mai tsawo ko hira a tsakanin mu saidai kowa yayi sha,anin gaban shi a dakin ko ina tunane ko taba waya wanda hakan yakan daukeni wani lokaci mai tsawo a wurin shi.
Wanda bai sani ba sai ya dauka wani hiran arzikine ko wani abin miji da mata ya tsayar damu a cikin dakin lokacin.
Alhamdullahi gaskiya don jikin nasa yayi sauki sosai saidai da alama har yanzu baya jin karfin jikin nasa ko kadan.
Karfin hali irin na mazane kawai yakeyi yana fita don kada ya zauna don da mace ce nasan har lokacin nan tana kwance tana fama da jikin ta.
Saidai wani abin dana dan kula dashi a yanzu shine irin kallon da yaya yakan min wani lokaci kallo ne mai tare da ma,ana iri daban daban.
Na kasa fahintar dalilin hakan da yake min wani lokaci idan zamu hada ido dashi zaiyi saurin kawar da idon shi gareni.
Gashi a yanzu ya dora min nauyin hada mai ruwan wankan shi duk safiya duk da komai a hade yake amma dole sai naje na hada mai zai tashi yayi.
Haka cin abincin sa dole ina wurin har ya gama zamu tashi duk da ba wani hira tsakanin mu a lokacin.
Ga mami da ke kira yanzu kamar ta bude ido ta ganta a kasan takeji don zata kira akalla sau uku a rana tana jin halin da muke ciki a nan.
Wanda wanan kiran har ya soma samin zarginta kan dan nata watay ita duk abinda yakeyi ma bata ganin laifin shi ashe ga hakan don yadda naga ta damu da halin da yake a yanzu.
Har take fadin idan azumi yazo zasu shigo su ganshi su danyi azumi tare damu suna jiran Aisha ta karasa karatun tane aiyi bukin yayye su yasa basu zo a yanzu ba.
Tabdi ba zuwan mami din ba sai irin takura min da sukeyi idan sun zo da fanin laifina ko kyashin da baya boyuwa a fuskokin su.
Shiko cewa yayi yana farin cikin da zuwan su indai zasu zo din suyi azumin a tare damu zaiji dadin hakan..
A raina nace tunda kai da uwarka baku da matsala duk tudun laifin ka bata ganin hakan gareka sai ma so da take nuna maka zallah ai kace kana farin ciki da hakan .
Muryan shine ke fadi yana kallona yace zainab na san kema zaki fini jin dadin hakan tunda yanzu naga naku da mami din yanzo daya har tana maki sako a boye ko ?
Ban sani ba don wani aiki sai mami na sani da sauri na dago kai na kalleshi tare da fadi cikin mamaki sako kuma ?
Daga wurin mami yaushe mami tayi min sako dana zo kasan nan idan ma har mami zata aiko min wani abu ai ta hannun ka abin zai fito.
Hakane fa kuma ya fada yana murmushi yana batun mikewa tsaye na sake fadin sai dai idan ka manta baka ban sakon ba yana hannun ka ?
Banjin yana a hannu na gaskiya sai dai idan na manta nima nake ganin kamar ke ra aikowa anywhere forget it ba damuwa.
Bayan shi nabi da kallo har ya fice kafin in tabe baki ina mayar da kaina ga kujeran da nake zaune tare da lumshe idanuwa na nadan lokaci.
Tunda mami ta furta zata zo yake shirin zuwan su din duk da bai fads ba nasan abinda yasa ake wasu yan gyare gyare a gidan wanda ya dace.
Dare ne naga bai shigo ba yasa na shiga part din shi tunda nasan yana gidan bai fitan nan da yakeyi a baya yanzu ya daina tunda yayi ciwo baya yawan fita koda rana da ya dawo office yana gida sai kuma gobe idan ya fita.
Wando ne da riga tie a jikina baki rigar kuma yellow mai dan fadi wuyan shi ma da fadi sosai.
Sai dai rigan ya dan sauka ya rufe min mazauna na rabi kayan sun matukar karban jikina sosai sun dane min jiki da kyau.
A falon shi na saneshi zaune da kwalba da cup a gaban shi ya zauna ya mike kafafun shi saman karamin table din dake gabab shi .
Yayin da dukkan maballeyan riganshi suke bude mashi duk chest din shi a waje ya dafe kanshi da hannun shi daya kamar mai barci.
A hankali na tako zuwa inda yake zaune ganin kamar yana barci yasa dana kare mai kallo nake batun juyawa na bar dakin.
Ina zaki kin shigo kuma zaki fita yana sauke hannun shi data dafe goshin shi yake fadin hakan .
Kallon kwalban da cup nayi na turo baki kafin nace naga kamar yau dakin yafi karfin shigana ai don naga kamar ka gama warkewa yanzu.
Dan murmushi yayi yana gyara zama tare da fadin zoki zauna a nan mu sha tare don na yau din tare zamu sha dake ai.
Wa ni na fada har ina nuna kaina da hannuna nace Allah ya tsare ya kareni don ni na zabi na Allah da wanan na nuna da bakina inda kwalban yake.
Kanshi ya dan mayar ga makarin kujeran ya lumshe idanun shi a hankali yace yana taba wurin da yake zaune ta gefe zo zauna a nan nace maki ko ?
Kallin shi nayi kamar in tafi nake ji sai kuma wata zuciya tace min naga iya gudun shi ga hakan sai na tako na zauna kamar yadda yace min din.
Na zauna a dan takure ban sake jikina ba da zaman ya dago yana zuba abin a cikin kofi ya miko min yana fadin karba ki dan sha.
Wani kallo nayi mai ina kawar da kaina gefe daya nake fadin har abin yakai can yaya ka koya min shan wanan haramiyan abin ?
Dauki kwalban ki karanta idan na cutarwane na baki yana komawa yadda na sameshi da farko saman kujeran.
Ban karba sai mikewan da nayi na fice part din ga baki daya raina a bace ina tunanen irin halin yaya da abin haram ba komai bane a gareshi shi ?.
Har ni yakecewa yau wai nasha giya a tare dashi don kawai ya mayar dani yarinya ko me ?
Ko wawiya ya daukeni ko bakyauya har yanzu ban san komai ba kan hakan har yake kokarin juyani ga halaka.
Ranan banyi barci ba sai na daman sanin sa da nayi ga baki daya ina jin wani irin tsanar shi yana karuwa a zuciyana lokaci guda.
Washe gari ma kin shiga nayi wuri shi don karya shigo mi part sai naki bude ko ina da safe na lafe a dakina kawai.
Don ranan bamu zuwa makaranta daga ni har sadiya muna gida a kwance abin mu shidai ne mai fita baya dadewa koshi a irin wanan ranan.
Ganin bamu bude kofan mu ba yasa shi fita bai ganmu ba sai text da yayi min a waya dan guntu da cewa nina fita sai na dawo.
Na tabe baki ina jefa da wayan saman gado don haushi tare da fadin dan iskan mutum kawai ka fara bata kanwar ka kafin ka bata ni mana
Daya dawo din ma bai nememu ba part din shi ya nufa ya rage kayan jikin shi ya shiga ban daki ya watsa ruwa a jikin shi don yaji sanyi..
Sai bayan da yayi sallah isha,i ne ya fito zuwa part din ya samemu zaune a falon mu muna kallo sadiya ce ta fara gaidashi da dawowa.
Sadiya yau ba assignmemt din ke nan kika tsaya kallo a nan tace yaya ba test saidai zamu fara exam bada dadewa ba.
Ya kai zaune tare da kallon inda nake yana fadin ya zainab kuna lafiya dai ko yau banji duriyan ki ba gidan nan.
Baki na turo gaba ina fadin lafiya nake bagani ba yanzu a zaune au har yanzu fushi kikeyi kan wanan maganan ?
Dan dagowa nayi tare da kallon shi watau shi baima dauki hakan komai ba ke nan har yana tambayana yanzu.
Amma ke zaki iya bani abu insha ba tare dana sani ba koda abin zai wahalal dani a rayuwana idan nasha in dai bukatan ki zai biya ban damu da hakan ba ?
Wani kallo nayi mai na mamaki sai na dukar da kaina kasa kafin na dago nace nasan ko na baka ba wanda zai cutar dakai bane sai dai ya taimaki rayuwan ka ai.
Umm,humm haka kike tunane ko a naki zaton ban tunanen komai don nasan daidai nake ga abinda nayi balle ma banyi ba din sai abin da zuciyar ka ya baka kan hakan.
Mikewa yayi tsaye ya fara tafiya ina kule dashi a dan kwanakin nan idan yana tafiya wani lokaci sai ya dafe gefen cikin shi da hannu daya yakan iya tafiya da kyau.
Bin shi nayi da kallo har ya fice kodana juyo sadiya ta mayar da hankalinta gareni tana kallona.
Da sauri ta duka kamar bani take kallo ba nabi lafiyan kujera na kwanta ina tunane a raina kardai ace yaya ya fahinci na saka mai magani a dubai ?
Idan ko hakane na shugo uku ashe nawa ya sameni ke nan dashi tunda gashi ya fara sake min magana a fakaice kan hakan.
Kamar maya tasan halinda muke ciki sai gashi washe gari ta fito min da zancen tana tambayana ko nayi amfani da wanan maganin kamar yadda akace nayi din.
Ajiyan zuciya na sauke kafin na fara bata labarin abinda ya faru sai kawai naga tana tafawa tare da fadin ki godewa wanda kike bautawa da yasha wanan abin zee.
Don na yarda da aikin kakata hundred pacent kan wanan da wuya ya kara kallon wani abin da zaisha har ya fita hankalin shi.
Shi dayan fa kikai ga amfani dashi ta tambayeni nace ai lokaci guda duk na hada nayi amfani dashi tace Budah da cewan wai abin bautan su.
Baki tsoron hakan zai iya tabashi don karfi ke ga maganin sosai ashe da gaske da ake fadin ku bakaken fata kuna da karfin hali sosai haka.
Tsoro naji wani tunane yazo min dana tuna da yana yawan dafe gefen cikin a yanzu saidai ban san dalilin da yasa yake hakan ba da yake yi ?
A maraice na bata labari irin yadda yakeyi a yanzu tun bayan ciwon da yayi na fita hayacin shi a Dubai.
Dan tunane ta tsaya tayi kafin tace ina ganin sai mun koma wurin kaka muji ko akwai wani abinda yasa yake hakan.
Zamu iya zuwa yanzu na tambayeta don na riga da na tsorace a yadda ta nuna min illan abinda nayi lokaci daya ba daidai bane.
Dan duban lokaci tayi da dan tunane tace zamu iya don zamu iya zuwa mu dawo lojacin tashi ma baiyi ba a yanzu.
Mota muka shiga tafiya mai dan tsawo ya kaimu kauyen nasu dake da dan nisa da cikin garin mun samu kakan a waje tana shanya wasu ganyayyaki tayi muna taro na arziki.
Mun zauna an gagaisa ne maya ta kora mata bayani kamar yadda na fada mata tana mamulan baki irin nasu na tsofi take fadin .
Kinyi aikin yarinta yarinya amma yanzu shan maganin yakai kamar sati nawa a jikin shi na dan yi tunane tare da dago kai na bata amsa baikai wata daya ba ina gani.
Duduke ta mike zuwa cikin dan gidan ta ta dan dade ciki ta fito da wani abu kamar kankara da wasu dai maganin kala biyu a hannun ta ta miko min.
Karba nayi da hannu bibiyu cikin girmamawa take fadin ki masa amfani da wanan zai daina jin abinda yake ji din da yardan mai duka.
Don su basu yarda su ambaci Allah ba don basu san shi ba basu bauta mashi na karba ina istigifar ni dai bukatana kada ya halaka a sanadiya na shine fatana ban yarda da abin bautan ta ba tunda na fada tarko ko.
Mun dawo yamma yayi sosai don haka ina sauke maya gida na nufo don nasan yanzu sadiya tana gida zai turo a dauke ta .
A falon gidan gaba daya na samesu zaune tare dashi suna zaune shi yana waya ita kuma tana kallon tv na shigo a gajiye.
Da sauri sadiya ta taso tana rungumeni tare da fadin I miss you sister tun safe na shafo kanta dake bude ina fadin bakya ji baki son saka hula a kanki sadiya.
Na nufi inda yake zaune yana waya amma hankalin shi yana gareni tunda na shigo yana waya da hannu ya yafuto ni nazo dan hugging dinsa nayi ina fadin miss you.
Ya dan rungumoni na dago zan juya muryan shine ke tambayana me kika jeyi sea side yau da mamaki na dago ina kallon shi.
Na yadda har yasan inda naje na wayance da fadin munje duba wani projects ne a can bakin ruwan yaya baki kirani zaki tafi can ba saida na gani.
Da wasu course mate dina muka tafi ban san zamu dade a can haka ba na dauka zamu dawo da wuri na bashi amsa yace take time next time.
Bana son kuna zuwa nisa a garin nan don akwaisu da nuna wariyan fata wani lokaci kada wani abu ya samu mutum.
Nace insha Allahu a raina kuma sai mamaki nakeyi yadda yau kawai har ya gane na tafi wani wuri na daban ba cikin school ba.
Na dai samu na shige ciki don duk na gaji don na dan watsa ruwa don wani irun yunwa nake ji sosai a lokacin saboda banda ruwa ban iya cin komai a waje ko ruwan sai shanshi ya kama dole zan sha idan na fita.
Don kasan kafirai ne ba zan yarda ko bread din su inci ko snacks din su ba don amfani da man alade ba komai bane a wurin su su yasa nake kiyayye hakan.
Duk da yunwan da nake ji saida na rama sallolin dake kaina har isha,i saida nayi kafin na fito na nemi abincin da zanci.
Shine ya shigo ina zaune ya saka wani jallabiya blue a jikin shi tafiyan shi kawai zaka gane cikin karfin hali yake a yanzu duk ya rame ya zube har duhu ya danyi.
Zama ma da kyat ya kai zaune na dago kai na dan kalle shi cikin tausayi tare da sada kaina a kasa ina ci gaba da cin abinci don ba a dining na zauna ba.
Jin abincin ya fita min rai nayi tunda naga yanayin da yake ciki din zuciyana naji ba dadi lokaci guda.
Ban san lokacin da bakina ya furta mashi baka da lafiya har yanzu yaya don yanayin ka ya nuna hakan na fada ina ture abincin a gabana.
Hannu ya mika ya jawo plate din zuwa gaban shi ya dan diba ya fara ci ba tare da yayi magana ba saida yayi kamar cibi uku ya koma ya kwantar da jikin shi saman kujera yana dafe goshin shi yace.
Ban san meke damuna ba zainab kwata kwata na rasa gane kaina ga baki daya bana jin dadin komai a yanzu tunda ciwon nan ya kamani wallahi.
Komai gaba daya ya fice min a rai haka bakina bana son ko kadan in saka abu a cikina sai naji shi kamar wuta na saka indan naci.
Kaje asibiti na tambaya da sauri naje sunyi gwaje gwaje sunce basuga komai a tare dani ba har yanzu.
Innalillahi nace ko mami zamu fadawa ta san halin da ake ciki da sauri yace No kada ki fada mata tunda zasu zo ai ki barshi ki dai tayani da addua kawai shinafi bukata a yanzu.
Rabin addua na a kan kane ne ko yaushe yaya sai dai idan banyi sallah ba aiko na gode da wanan taimakon ke alherice zainab a gareni na sani ke sakon Allah ce zuwa wurina yanzu na gane hakan.
Dago kai nayi na kalle shi yace kwarai nasan da hakan ba yau ba zainab ke din kin kasance a yadda banyi tsamani ba.
Da farko wani sashe na zuciyana yakan min tambaya a kanki amma yanzu ta haska min matsayin ku a gareni daga ke har sadiya .
Ban kara gaskanta zuciyana ba sai wanan lokacin da na kwanta ciwo na samu taimakon da ban taba zato ba a wurin ku.
Zanma ce ke don kece mai komai da yadda hankalin ku ya tashi a kan hakan ya nuna min matsayin dan uwa ko mace a kusa da kai a yanzu.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.