Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel
Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 22 of 139
Daga dakin shi inda yake zaune yake kallon su shida jamal da shi kanshi baisan gidan akwai cctv ba sai yau ya girgiza kai tare da fadin wasu irin yara mami ta aje haka a gida.
Yaran nan ko mami ba zasu barta ba idan sun samu wuri ya fada yana mikewa zai shige daki sai kuma ya juyo yana fadin .
Kada inji zancen tv din nan a bakin wani a gidan nan ko mami kafadawa dashi zamu samu matsala sosai dakai a rayuwan mu.
Na dade ina zargin yara nan ba zaman banza sukeyi tare da mami ba tunda naji suna gidan nan zaune yanzu.
Hannu jamal ya daga duka biyu yana fadin believe me yaya kowa ba zan fadawa wana magana ba ko jalal ne yace is better for you don ban son yawan magana.
Nikan barci nayi sosai a dakin mami na samu gadon mami na haye ka laushi kamshi da sanyi na tashi yana shiga min hanci a hankali.
Duk da halin rashi lafiyan da nake ciki bai hanani jin dadin kamahin dake shiga min hanci ba lokacin.
Sai goma da rabi na dare na falka koshi mami ce da Aisha a dakin suke magana yasani bude idona sannu zee mami ta fada tana kallona tare da tambayana jikina.
Me zakici yanzu Aisha ta tambaya tana kishingide saman gadon mamanta da waya a hannunta tana kallo.
Mami ta kura mi ido tana so jin amsa da za bayar a hankali hannna ina share wayen dake kokarin zubo min a idona.
Tambayan ki ake ba kuka akace kiwa mutane ba a na tun safe nasa bakici komai ba a cikin ki .
Na amsa cikin karfin hali da fadin tea zan sha ina kokarin mikewa tsaye ina kuma zaki Aisha ta fada zanje inyi fitsarine na bata amsa.
Ina koarin nufar kofan fita daga dakin don ba daman in kewaya mami tana dakin ta don haka nake kokatin fita ba tare da nasan inda zan nufa ba a lokacin.
Sosai mami da yarta suka kula dani don sun nuna damuwan su a kaina sai anty salma da itama ba laifi don tana zuwa a kai akai tana gaidani da jikin.
Har naji sauki na fara fitowa falon don in bawa mami dakin da ko yaushe a dan kwana biyun nan ina kwance.
Ranan dana fara fitowa falon ne naga canji sosai wurin yan matan mami wanda hakan ya bani mamaki don fuska sosai suka sakarmin harda zolaya wai an taya naki sallamawa.
Ni dai nayi murmushi tunda ba saba haka nayi dasu ba dama duk da yadda nake hakana mike na yi aikin da zanyi a ranan don sai naga aikin da akeyi kamar baya fita da kyau.
Aiko mami na dawowa ta hauni da fada don ta gane nice nayi aikin cewa kawai nayi naji sauki mami.
Tadaiyi min fada ta fara cire kayan jikinta na fita dakin don bata wuri ta shirya a tsanake kamar yadda muka sabayi.
Sai data fito falo na koma dakin na gyara tare da nade kayan data cire a jikinta na wanko har bathroom din tas.
Tun ina jiran inji ance gobe ko jibi zamu tafi sai naji shiru saidai kawai ranan da muka cika sati da zuwa ranan da dare mami ke fadin su Rufaida su shirya zasu koma kaduna do hutun su ya kare .
Ina gurin jin haka yasa na kallo mami don banji tayi magana ba a ciki sai naji mami na fadin ina sane dake zainab ban manta da karatun ki ba ai.
Wata kila nan karatun naki zai dawo yanzu do zaman mu zaifi yawa yanzu a nan sai dai na duba naga abinda ya dace mami ta fada.
Basuji dadin yadda mami ta tsara ba don ba karamin dadi duke ji ga wanan zaman namu ba don ko yaushe suna fita shoping da yawo sun samu dakewa sosai don mami bata zana gida sai yamma take dawowa gida.
Dole ba don sun so ba suka fara shirin komawa kaduna salmace kawai bata nuna damuwanta a fili akan hakan ba wucewab sune yasa mami bani daki na kaina inda zan zauna kamar yadda nake da dakina a kaduna gidan ta.
Haka ba karamin dadi yai min ba sosai a raina don dama a takure nake saboda zama da mami da nakeyi daki daya.
ZAINAB IDRIS MAKAWA🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
1ï¸Â⃣6ï¸Â⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAU DA GOBE NA ALLAH NE YAN UWA MU RIKA SHUKA ALHERI DON WATA RANA A FADE MU KO BAMA KUSA, UBANGIJI ALLAH KA KARA MUNA IMANI DA DOGARO DA KAI YA ALLAH, , ,
IDAN NACE KI BIYA INA NUFIN NA KUDINE YAR UWA KI GUJI SHIGA HAKKIN DABA NAKI BA DON ALLAH ALLAH YASA MU DACE .
DARI UKU NE KACAL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DA AMINCI.
Zance tafiyan su rufaida baimun dadi ba don gidan ya kara komawa silent yanzu da suka tafi ashe dan mutum ko yaya kake dashi yana da rana a gareka.
Yau na kara fahintar hakan wanda dama nasan da hakan tun barina gidan da har nakan ji kewan yan gidan mu ga baki daya har Asabe da lantana.
Sai gashi dan sabon da nayi da zama da ukuban su Rufaidama yanzu ina kewan hakan gareni.
Sai ya kasance in zauna ni kadai ina faman tunane a guri daya idan kowa ya fita zuwa nasa tsabgan sai in rage dagani sai gwarawan yan aikin nan dake gidan.
Gashi ni ban saba dasu ba don ko yaushe a cikin yare suke su yau ma kamar kullun bayan fitan mami da Aisha data wuce school na gama gyaran dakin mami na koma dakina nayi wanka.
Na shirya a cikin wani bakin dogon riga da Anty Aisha ta ban zuwan mu Abuja don ganina da yan kayana kala hudu dana dauko da zamuzo kullun.
Dan kalin rigan na daura a kaina mai kawai na shafa a fuskana don ni ba gwanan kwaliya bace dama haka.
Duk da hakan fuskana ya dan fito fayau falo na dawo na zauna ina karyawa ina kallon tv daya zama min abokin hira yanzu.
Cibi biyu na kai ga bakina na orth din da nake sha muryan Nuriya matar yaya mamud ya ziyarci kunnena don ni nikan manta da itama a gidan tunda ita bata shiga mutane kuma bata barin yayan ta suna mamuwar kowa a gidan.
Fadi take ke zeey ki zo ki gyara min part dina yayi datti da yawa yau ina son a gyara min shi don Abbani yai magana kan hakan da cewa yaya mamud kamar yadda take kiran da dashi.
Yau kan na turza don bansan sanda bakina ya furta anty Nuriya yanzu nake karyawa idan na gama zanzo na bata amsa.
Ke yaushe har raini ya shiga tsakanin ni dake haka ta fada niko a raina nace wata sabuwa kuma waini mena tarewa mutane haka kowa yake jin haushina dan abu kadan zai zama min matsala babba ga kowa.
Maza ki tashi kije kiyi abindana sakaki kafin na bata maki rai ta fada a hasale tana mai tsureni da idon warning gareni.
Kokarin aje cup din dake hannuna nake naji muryan Jamal na fadin ke dauki cup din ki ki karasa karyawan ki kafun ya juya wurinta yana fadin.
Baki da tausayi wallahi yarinyar nan tun safe take tsaye sai yanzu ta samu kanta take karyawa zakice ta bar karyawa tazo maki aiki.
Wani juyawa tayi tana masa wani kallo tare da fadin kai kuma fa dan rainin wayau da zakazo kaja min raini a wurin yar aiki haka.
Aiki na sakata a part din mu kuma dole ta tashi ta tafi yanzu don yanzu nake bukatan ai min shi.
Bazata ba sai ta gama karyawa ya kara bata amsa yana kallona tare da fadin koma ki zauna nace ki karya idan kin gama sai ki tafi.
Ba abun mamaki bane don ka fadi haka jamal tunda kaganta haka kana da mugun nufi a kanta kamar yadda kuka saba yi a turai ai.
Sheri zaki min ya fada a hasale yana nufota ni kan hannu na dora a kai ina shirin yin ihu don yadda ya nufota sai Allah zai gyara yau a tsakanin su.
No no no jamal don Allah please kada ka tabata be a man kada ka karasa wurinta please.
Nan dai hayaniya ya kaure a tsakanin su ta fadi ya fadi karshe dai ta juya tana fadin ke kuma karamar yar iska kada kizo ki min abindana saki kiga abinda zan maki yau gidan nan.
Ba zatazo ba din kiyi duk abinda kikai niya a kanta jalal shima ya fada a hasale ta juyo tana fadin sai ku gayawa wanda baisan abinda kukeyi da ita ba a gidan nan.
Innalillahi ai bansan lokacun dana dora hannu a kai na fara rusa kuka ba karyawan da banyi ba ranan ke nan.
Don sukan tana wucewa suka tafi suna fadin yau zasu gamu a gidan nan dole sai ta fada abinda take nufi ko su casa ta son ransu nan suka barni tsaye ina kukan takaicin zargin da maman su Amir da Amirah tayi min kan tagwayen mami din.
Banda yadda zanyi duk da sunce kada in tafi haka na aje abin karyawa na na nufi part din anty nuriya din da zuman mata aikin data sani.
Gaskiyane part din kan yayi datti kamar ba mace a cikin sa da take rayuwa ko namiji yabar gutin shi haka za a iya kiranshi da kazamin namiji.
Sai kaga mace fes a waje amma kaje muhalinta sai ka raina mata wayau kan rashin gyaran wurin zaman ta.
Kayan dake saman kushin na duka na fara nadewa hankalina ya dauku ga abinda nakeyi kawai ba tsamani naji saukan mari a fuskana lokaci guda.
Na dago dan gani waye yai min wanan aikin na kara jin wani a tsakiyan fuskana tana fadin gobe in kara saki aiki wani dan iska a gidan nan yace kada kiyi.
Ke har kin isa me kika dauki kanki banda matsiyaciya kaskantatar yar aiki kawai kina nufin ni kyauki da wani halin ki can zai rudeni ne matsiyaciya mai zubin karuwai kawai.
An walla, , , , kofan da aka bankadone yasa ta kasa karasa maganan da take son furta min ta juya tana kallon wanda ke tsaye a kofan nasu.
Ni dai ina tsaye har lokacin zafin marin bai gama sauka min ba sai wani dishi dishi nake gani idan nayi yunkurin bude idanuna lokaci guda.
Muryan Jalal ne yake fadin idan kika kara dukan ta yau sai kin raina kanki gidan nan wallahi kinji na fada maki.
Jalal ya juya gareni yana fadin ke kuma fito part din nan tun kan ranki ya kai ga baci yayin da Nuriya ke kokari daukan waya don kiran mijin ta tana durawa jalal din zagi ta uwa ta uba.
Bayan mun fita part din ne ta kira mijin ta fada mai karya da gaskiya shi kuma ya hau karfe uku duk suna gida gaba dayan su don mami tace su hadu a gida.
Yayin da har lokacin ina daki tundana shige ban fito ba ga fuskana gefen idanuna ya hau ya rufe sosai har bana gani dashi.
Sai faman tunane nake a raina duk kokarina wajen kaskantar da kaina a garesu don gujewa faruwan irin haka .
Wanda mami da yaranta a kullun suke kokarin jana a jikin su suga dai na sake a cikin su wanda ni na kasa hakan don kada in shaga irin wanan matsalan a cikin su.
Ina nan a kwancen da nake ina faman tunane muryan Anty Aisha ya daki kunnena tana fadin zainab mami na kiranki a falo.
Na dago dan mata sannu da dawowa tana ganin fuskana tace ke meye haka fuskanki ya sauya lokaci daya ?
Cikin dakewa da karfin hali nake fadin sannu da dawowa Anty Aisha yyawa me ya sameki haka ta kara fada.
Ba komai anty na fada ina kokarin tashi daga saman gadon ta juya ta fita daga dakin.
Ina tafe na sa gefen gyalen dake kaina na dafe idon dashi abu ga farin mutum lokaci daya fuskan nawa gaba daya ya canza kala ga alamun hannun Nuriya radau a fuskana.
Gaba dayan su sun zuba min idanuwan su a kaina har na karaso inda suke zaune na kai kasa na fara gaida mami data kura min ido kamar ta suma da mamaki.
Kafin in dan dago ina kare fuskana ina gaida yayan nata zeey meye wanan ya bata maki fuska haka mami ta fada tana kallona don jin abinda zan fada.
Kowa falin ni yake kallo yayin da mami ta kara maimaita maganan ta gareni kafin in magana Nuriya tace nice na mareta.
Har mijin ta saida ya juya yana kallon ta don abinda ta fada lokaci guda cikin rashin damuwan da hakan.
Akan me kika duketa haka Nuriya mami take tambayan ta cikin mamaki har lokacin.
Don me zan sakata aiki mami take zuwa lokacin dana umurceta tazo don kawai wanan dan rainin wayau yace kada taje tana nuna jamal a hasale.
Shi dagowa yayi don yin magana sai lokacin Jafar ya dakatar dashi don tun zuwana kanshi na kasa yana dakilan wayan shi cikin ko in kula da wanda ke wurin gaba dayasu.
Jamal me zaka fada tunda ta riga data fadi itace tai mata hakan da bakinta yanzu ta kuma fadi dalilin yin hakan gareta.
Sai akace a duketa haka ko boyace na sayo ai ba za ai mata wanan dukan ba haka balle ba boya bace karbo ta nayi hannun iyayyen ta don kawai ta taimakawa rayuwana.
Ban kawo don wani aiki ko aikin wani a gudan nan sai nawa bukatan ni kadai da take min kuma tana da kokatin wurun aiwatar min da komai tun kan na fada mata abinda zatayi min.
Haba wanan dukan haka ai abin yayi muni komai tayi maki ai zaki bari in dawo ki fada min sai nayi mata fadan hakan .
Koni dana karbota wurin iyayyen ta aiba zan taba mata wanan duka haka ba don itama mutum ce kamar kowa a gidan nan.
Ok mami ke nan dai yanzu na fahinci da sa bakin ki yaran nan sukai min rashi mutunci ke nan wanan banzan yarinyar mara mutunci da asali ta fini yanzu a gidan nan.
Nuriya mind your language bakin ki yasan abinda yake fada bayan kiyiwa yarinyar nan irin haka kuma zaki kirani ki fada min karya don kawai ki hadani fada da yan uwana.
Dama nasan haka zai kasance ai don wanan yarinyar ba karya su Rufaida ke fada ba ta asirce kowa a cikin ku har mami din gaba dayan ku tasa an maku asiri a kanta.
Enough enough Nuriya bakin ki yasan abin fada a nan kada ki kawo muna wanan shirmen naku ba banza yaya mamud ya kara fada a hasale.
Tashi tayi tana fadin aida rama mata kayi zaifi da wanan hasalan da kakeyi don kawai na mari wanan .
Mami ne ta daka masu tsawa tana fadin ya isa haka ki dawo ki zauna idan ki gama fadin abinda ke ranki.
Kamar ba zata zauna di ba kome ta tuna sai ta kai zaune din tana kada kafa mami ta sauke ajiyan zuciya ta fara magana.
Da farko ke Nuriya a kanki zan fara don ba zan tsaya kina fada min magana cikin rashin mutunci a gaban diyana ba haka.
Don dan kuka shike jawa uwar shi jifa, sai dai kinci albarkacin darajan abu biyu da kike ci gareni har kullun a wurina.
Shine auren dana da kuma kasancewar ki uwar jikokina a yanzu wanan damar kike ci har kullun a wurina don ba zan so saka matar dana a gaba idan ba haka ba ke kinsan wani abin ko ance kiyi min shi ba zakiyi shi ba duk da kudin da kike takama iyayyen
Sai yaya mamud ya dukar da kanshi don ya gane me mami take nufi da maganan ta saboda halin Nuriya a ku)un magana ya taso itace bata da gaskiya.
Mami taci gaba da fadin saidai zanso ki gane cewa ba zan lamunci aibanta mi diya ba ko zargi su a kan zina.
Mami ni kar,a laka min abinda ban fada ba fa a nan don kawai ana jin zafina kowa ya taso sai yace banyi daidai ba .
Don hakane nake nisantar kowa a gidan nan hakan baiyi ba har sai wani ya takaleni kuma inyi magana ace banyi daidai ba.
Yanzun wanan mara galihun tafini daraja da kima a wurin ku ake nufi tunda itace mai gaskiya ke nan don kawai taimin ba daidai ba na hukuntata.
Who are Nuriya who are you by the way har kina wani fadin tayi maki laifi kin hukuntata akanahi ke kika dauketa aiki a gidan nan ko wurin ki take.
Ke ba zaki iya yin aiki ba ki zauna da masu aiki kuma kin hana hakan saboda bakin kishin dake damun ki.
Mikewa tayi tana fadin na hana ka dauki yar aiki mamud don ban so kai din ban yarda da kaiba da har zan dauko wata yar aikican in aje wurina.
Daga yau na hana kowa saka wanan yarinyar aiki ko taba lafiyan jikinta wallahi wallahi ko yaya nake da mutum a gidan nan ranan zai hadu da fushina.
Wanan yazama na farko na karshe a gidan nan da wani zai kara taba lafiyan wani zainab yace kamar kowan ku nan dan haka a bani guri ban son wani magana kuma daga yau.
Tana fadin haka ta mike zuwa dakin ta a fusace yayin da nake durkushe a gefe kujera tafiyan mami Nuriya ta mike tana fadin wallahi mu zuba da kowa a gidan nan kan wanan yar iskan kowa ya tabani tabashi zanyi.
Binta da kallo sukayi kafin su dawo da kallon su gareni inda nake rakube ina hawaye don tashin hankali dana gani ranan.
Da hannu ya nuna min hanya na mike simi simi na basu wuri yaya mamud ne ya kawar da shirun da fadin.
Ni Nuriya zata watsawa kasa a ido haka kwata kwata banji dadin zaman mu da ita kullun a cikin fitina muke.
Yau ma nasan haushi fadan da nayi mata na gyaran wuri ne ta sauke akan yar mutane haka.
Bai bari dan uwan ya gama zancen shi ba ya mike zuwa dakin mahaifiyar su data shige ranta a bace ya sameta dakin.
Shiko yaya mamud yaci gaba da fada da matar shi ranshi a bace yake fadin.
Ya mike yana fadin nasan maganin yar iska ai bazata zan mata a gidan nan sai ta gane bata da wayau.
Saidaya shige jalal ke fadin kamar da gaske din zai iya hakan yanzu kila hakkuri zaije ya bata.
Suma mikewa sukayi zuwa dakin mahaifiyar tasu suka samesu a nan suna wani hira da dan lelen nata a gurin.
Karfe biyar na bar dakina zuwa na mami don gyarawa ita kadai na samu a dakin da sallama na shigo dakin na duka har kasa ina gaida ita kafin in dago don fara aikin dakin.
Kinsha maganin dana aika akai maki dazun take tambayana nasha mami na fada ina wasa da yan yatsun hannuna a hankali.
Kamar zata sake magana sai kuma tayi shiru taci gaba da duban takardan dake hannun ta ko ina na dakin saidana gyara kafin in fito dakin kusa magariba yayi nan na samu matar da aka dauka don shara tazo ta fara aikin ta .
Don faruwan avi mami tasa a kawo mata yar aiki wanan mai sharan bahaushiyace ita don ina gaida ita take amsawa naji hausanta na gane ita din bahauace ba kamar matan nan biyu gwarawa masu girki bane.
Tun ranan shakuwa ya shiga tsakanin mu da matar da ake kira da hannatu yar ktsinawa irin matan nan ne da suka dade da fitowa bariki don har sigari take sha a boye.
Nima dai rabon in gan tane a cikinyanayin yasa na rutsa da ita can bayan daki ta labe tana shan abinta na juya da sauri zan koma naji tana fadin a cikin kokarin kashe tabar da sauri yar hjy kamar yadda take kirana dashi.
Ina nan ina wanan jarabar tsiyar da muka sawa kanmu ina dai ba zaki fadawa kowa ba halin da kika sameni wanan zancen.
Da sauri na girgiza kai tare da fadin indai nice babu maijin wanan a abakina insha Allahu ina kokatin wucewa don natsani warin taba a rayuwana.
Duk dan dakata min inzo har lokaci bata yarda dani don ta fahinci jikina yana rawa a lokacin.
Ina kallo ta ballo goro daga haban zanin ta tura baki tana taunawa ta kakabe zanin inda ta zauna a kasa tana fadin wanan abin ya zama muna jaraba a rayuwa.
Kinsan a zamani mu idan budurwa takai budurwa har bata shan sigari to bata cika wayayyan mace ba ke nan.
Tun wanan lokacin mula koyi wanan cacan kashi kudin don ko nairan ka ta karshe ke nan sai ka fitar kaya zakaji dadi.
Ni dai a kage nake na bar wurin nake fadin dama ban ganki bane a cikin gida sai nayi tunanen ko kina nan shine na biyo ki.
Yo ai ina nan kedai jarabarce ta motso min shine nazo indan rage zafi kai.
A tare muka jera zuwa cikin gidan idon ta mirsisi kamar bata sha komai ba taci gaba da sha,aninta
Cikin sati daya kawai mun saba da hanne wace na lakawa mama hanne nake kiranta da hakan don girmamawa .
Zama da mama hanne yasani cikin farin ciki da walwala sosai don zata zauna tayi hira dani kamar sa, anta nake gun ban iya bata amsa har yakai yazu ina bata zamu zauna tana ban labari ina kwasan dariya.
Da sunan kwana hudu sai gashi mun share wata a abuja lokacin ne mami ta fara shirin ziyaran kaduna.
Wanda gaba dayan mune zamu tafi gidan a yadda naji suna fada mahaifiyar mami ce bata da lafiya shine za a tafi gaida ita.
Shiri sosai mami keyi don zuwa gida nikan nafi kowa murnan hakan kamar ance damun isa zan tafi ancau ne ranan.
Ni kan na dauka yaya Jafar ya koma inda ya fito ne ashe wai tafiya sukayi tare da su jamal sai kwatsam gasu sun dawo ana saura kwana daya mu tafi kaduna.
Mama hanne kan tunda tayi arba dashi tasha jinin jikin ta a zaton ta wai yanayin sa yai kama dana yasanda tunma dataga security din shi ta kara tsurewa da al,amadin shi.
Take tambayana nake fada mata dan mami ne amma ni ban san aiki da yakeyi ba, ta sake fadan mutum.haka ba yar dariyan nan ko fara,a a fuskanshi.
Dariya sosai nayi har ina dukawa a inda nake zaune sai kamshin turaren shi mukaji lokaci guda.
Key din shi yake miko min ba tare da yayi magana ba, amma na gane me yake nufi dakin shi yake so a gyara mai ke nan.
Yana miko min ya juya ya futa a cikin wani irin tako na mazan zamani da suka suka san ta kan duniya sosai yake tafiyan.
Ban tsaya jiran komai ba na mike don cika umurni duk da mami ta hana inyiwa kowa wani aiki ita da kanta takan umurceni da inje in gyara mai dakin nasa.
Tura kofan nayi na shiga dakin da sallama duk da nasan ba kowa a daKin hakan bai hanani inyi sallama ba.
Idonane ya fara arba da wani kwalba dake aje saman table din dakin nasa ga abin cikin sa an zuba a kofi ansha an aje rabi.
Da mamaki nake kallon abin don ban taba ganin kwalban abin sha irin sa ba nidai na fara kawar da takardun dana gani a saman wani table naji an turo kofa da karfi an shigo dakin.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.