Complete Hausa Novels

Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel

Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 78 of 139

Duk aikin da yakeyi a ranan rashi bace yake idan ya tuna abinda ya faru a daren jiyan tsakanin mu ya rasa laifin waye a cikin mu har hakan ya faru.
Shin laifina zai gani ko laifin Nabil daya bude kofan ko kuma laifin shi da sakacin shi yasa har hakan ya faru.
Da bai bada daman in shigo shiyan in dinga kwana saboda dan maganan da mama tayi ba da duk haka bai faru ba a daren jiyan.
Inda Allah ya gyara banga komai daya faru ba a tsakanin su da tashin hankalin da zai shiga a yau yasan yafi wanan girma.
Da yanzu asirin shi ya gama zubewa a idon kowa don yasan ba zan iya rike kaina ba a lokacib mutane zan tara masa a gida don wauta.
Gashi har raini yana son shiga tsakanin mu don dan abinda idona ya ganar min ranan yakai yanzu ban tsoron shi kamar da can baya.
Ji itin kallon dana watsa mai a daren jiyan da sauri ya tambayi kanshi ko dai yarinyar nan tasan abinda nake yine tayi min irin wanan kallon ya tambayi kansa.
Da sauri ya girgiza kanshi tare da fadi a cikin hausa kai ina bata gane komai ba kawai dai nike tunanen hakan.
To wanan kallon tsanar fa na meye take min shi haka a daren jiyan don kawai ganin wanan gay din a karo na farko a part dina ?
Koma dai meye ya zama dole in canza komai yadda wani bazai taba fahintar komai ba saidai jamal fa ya tambayi kansa yana dan murza goshin shi.
Idon shi ya lumshe yana dan juya kujeran da yake zaune a kai ya zurfafa a cikin tunane.
Karshe ya furta a fili wama zai yarda da wanan idan har sun fada tunda ba ganina akayi dumu dumu ina aikatawa ba ai.
Zan fara da zainab don dole in tsawata mata kan ta fara zargina da wani abu na tabbatar da haka zata ja bakinta ta rufe gum.
Har yamma ranan bai samu tsinana komai ba a office ya dai kula zuwan su a garin nan yana son ya jawo mashi koma baya aikin shi a yanzu don haka sai ya jajircewa abin.
Dama hakan yake gudu ya faru dashi gashi kuma yarinyar da yake dauka ba wayau komai a tare da ita tana shirin jawo mashi matsala babba.
Ya mike yana mamakin kansa wai yau shine da jin kunya da nauyin arinyar daya raina ma wayau ya fito daga office din driver shi yazo ya jashi saida suka hau hanya yake tambayan shi inda zasu tafi asibiti ya bashi amsa ba tare da dago kai ba.
Ya samu hjy a zaune tana shan fruit salad da jamal ya sayo mata don tana yawan shan yayan icce sosai tun a gida yasa tun ranan data fara sha take sa ya sawo matashi tasha don yafi mata wanan abincin nasu na kasan dadi a bakinta.
Turo kofan yayi da sallama sukai arba da jamal dake zaune a gefen gadon yana duban yadda take shan fruit din a cikin tausayin ta.
Shima idon shi ya mayar kan tsohuwar data dago tana amsa mashi sallaman shi tare da fadin a,a maigidan ka samu isowa ke nan ?
Ina nan tare da wanan sabon mijin dake son kwace maka ni a yanzu don naji na fara son shi a yanzu fiye da kowa.
Dan murmushi jin abinda take fada ya karaso bakin gadon dashi yana fadin kinji sauki ke nan tunda har kin fara zancen miji yanzu.
Yo za a fasa zancen mazane tunda gaku har ku biyu a gabana ai duk inda kaga mata sun kai uku a zaune zancen ke nan balleni da har biyu ke bori a kaina koma ince uku don mamud ma kullun muna gaisawa dashi a waya.
Kice ke kasuwane dake haka ashe ban sani ba zan jaye don ba zan iya takara da kowa ba akanki don haka daga yau a fitar dani a cikin lissafin mazan.
Mikewa ya jamal yayi zubur ba tare da magana da kowa ba ya nufi hanyar fita daga dakin hjy ce tasa murya tana fasin kai kuma jamilu ina zaka a zaune kalau.
Fuskanshi ya dan bata kafin yace zanje nan wajene in dawo ba dadewa zanyi ba ai ya fada yana kokarin tafiya.
Yaka zo nan nawa ta fada a cikin damuwa don tana lura a yan kwanakin nan kusan haka suke da dan uwan da zaran ya shigo sai jamal din ya fice daga dakin.
Daga inda yake tsaye yana kokarin zaunawa yace barshi kawai ya tafi ba gani ba a a jafari ba yau ba ina kule da abinda ke wakana a tsakanin ka da dan uwan ka yanzu ?
Zama yayi yana murmushi ba tare daya kalli idon tsohuwar ba jamal din dake kofa a tsaye bai juyo ba bai kuma wuce ba.
Ta yaya kuke zaton zumunci zai dore a haka kai karami har kayi karfin halin yin fushi da yayan ka meyayi zafi haka tsakanin ku har ya kawo wannan ?
Kaine babba jafari a sanadin ka kuma muke zaune a kasan nan yanzu don me ba zakayi hakkuri da kanin ka ba koma me yayi ma matukar abin bai sabawa addinin ku ba .
Wani irin malolon bakin ciki jamal din ya hade kafin ya juyo yana fadin a cikin daurewa nifa hjy babu komai a tsakanin mu .
Don haka zan tafi ya fada yana kokarin juyawa ta mika mashi dakuwa da hannun ta tana fadin karbi nan dan nema ka maidani tsohuwa ban san komai dake wakana a gabana ba ko yanzu ?
Bajin dadin uwarku bane ta sameku a wanan halin don babu uwarda keson ganin rashin jittuwa a tsakan yayayen ta ba a duniyan ko wacecw kuwa.
Basai naji abinda ya hada ku fada kaida dan uwan ka ba kuyi kokari dai ku dinga tausa zuciyar ku don Allah .
Koma meya faru a tsakanin ku don Allah babu komai hjy shi yarone ai yasa yake wanan fushin dani haka ya jafar ya fada.
Wani irin kallon tsana ya watsawa dan uwan nasa kafin yace in ni yarone ai Allah ba sa,an kowa bane yana kallon duk abinda bawan sa keyi a ko ina yake daga haka ya juya ya bar dakin tare da barin hjy da mamakin shi.
Don bata taba ganin yayi fushi irin haka ba a gabanta ta juya tana kallon jikan nata dake zaune a gefen ta tana fadin.
Akwai wani abinda kake aikatawa ne mara kyau jafari don wanan kalamin nasa ya sakani a cikin duhu sosai.
Ki tambayeshi mana hjy shida ya fada ni dai nasan ban aikata komai ba da har zai fadi hakan ya fada cikin daure fuskan shi.
Dan hira mai kama da nasiha hjy ta dinga jansa dashi har suka kai wani lokaci kafin ya mike yana fadin shi zai tafi don zai biya wani wuri kafin ya karasa gida.
Sai bayan fitan shi ba a dade ba jamal ya shigo mata da leda a hannun shi yana sallama ta kalleshi ta kawar da kanta gefe .
Au fushi kike dani don kawai na batawa masoyin ki rai hjy to tunda bakya son gani na bari in koma inda na fito ashe.
Ka koma Nigeria idan ka tashi tafiya dan nema marasa ta ido har zaka tsaya kana daukan wanan zafin haka da dan uwan ka dake gaba dakai.
Hjy ke nan ya fada yana girgiza kanshi tare da fadin bai fada maki abinda ya hadamu ba ke nan ya tafi ?
Saida ta dan harare shi take fadin kai ka tsaya ayi maganan ne daka fita ku dai daina hakan baida kyau wallahi irin haka ke kawo matsala a cikin zuria kaga na baya yana raina na gaba dashi idan an saka ido sai abin yai girma.
Hjy badai gaisuwa bane ya jawo hakan to zan gaidashi zancen ya kare hakan yai maki ko ya fada yana kallon fuskanta.
Dan mere baki tayi tana kallon shi daga saman har kasa tana fadin zauna naga kamar abinci ka sayo zakaci yanzu ko ?
Naci a waje ya bata amsa wanan kena sayowa shi yana kokatin bude ledan daya aje a gefen shi kamshi ya bure dakin.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.