Complete Hausa Novels

Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel

Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 138 of 139

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ASSALAMU ALAIKUM YAN UWA MUSULMAI BARKAN MU DA YAU BARKAN MU DA GIDA FATAN ALHERI GAREKU A KULLUN, , ,

Haka abubuwa a kwana nan biyun suka taru sukai muna yawa ga abin daure kai mutum na gani a filin Allah don abinda zai baka mamaki bini bini mami zata kirani wai tana ban labari yadda abin yake faruwa a can kaduna.
Yanzu ma din hakane ina zaune misalin sha biyun rana wani kiranta ya shigo min sai naji gabana ya kara faduwa don nasan wani maganan daya dangaci wancan din na uwar Rufaida da ake fama a yanzu.
Ina dauka da sallama tana fadin wai zainab kin san matan nan har akanki wai taje gidan boka ai muna asiri in tsane ki da duk wanda ke tare dani.
Sai yau dai da mukaje gidan tana ganina ta shiga tono tonon asiri tana hintar kanta tana fadin kinfi karfina iyami kin fi karfina .
Sai abin ma yaso ban dariya amma na daure a fili ina fadin wa,iyazu billahi mami me wanan matar take nufine dake ?
Mami naga dai duk yadda akeyi kin masu a rayuwa ga yarta kuma a hannun ki kina rikewa tsakanina da Allah.
Mami din tace to ai zainab baki sani ba wai ashe ko zaman Rufaida din wurina wai ashe da dalili sun shirya hakane don ita Rufaida din ta auri daya daga cikin diyan dakina.
Wai ashe kuma jafar dinki take so shine suke faman neman asiri da zasu samu kan jafar dani da kuma karya wanan asirin da yanzu ya kare take wanan fallasan haka.
Na nisa tare da fadin O ikon Allah ita kuma kalan nata rayuwan ke nan mami, ba zata iya dogara ga Allah yayi mata mafita ba na rayuwa sai ta danganta rayuwan ta da gidan boka da malamai ?
Su saba ne da hakan tun farko ni kingani na ban taba yarda da irin wanan halin bin malamai da bokaye ba a rayuwana.
Komai yazo nakan saka hannu bibiyu in rungume shi in fadawa Allah damuwa akan lamari injira sauki daga gare shi.
Allah yasa mufi karfin zuciyan mu na fada tace to amin kedai zainab aisu masu wanan irin halin zakiga kullun a cikin talauci suke.
Saboda hassada da bakin ciki suka sakawa zuciyan su da haka mukai sallama da ita wanda nasa ko zuwa dare zata kara kirana a kan zancen.
Ina kashe wayan nake fadin a fili Allah mai iko yau nice da mami haka muke hiran arziki a tsakanin mu.
Dama hakkurine da wuya duk abinda kaji ana fadin kayi hakkuri a kansa har ka iyayidin insha Allahu hakkurin ka baya zama banza.
Yau da banbi maganan magabata na da shawaran manyan dake tare dani da ban kaiga cin ma hakan ba a rayuwana.
Shine ya shigo dakin yayi tsaye tare da tsura min ido kafin yace dawa kikw magana hakane tun dazun nake jin ki.
Dan dago kai nayi tare da saurin mayar da kaina kasa don yanzu tun faruwan wanan abin a tsakanin mu bana iya hada ido dashi sosai a yanzu din.
Mami ce ta kirani take ban labarin mamab su Rufaida na bashi amsa kai tsaye kafin inji yace kai mami tasaka zancen matan a ranta sosai.
Ni na riga na barta ga Allah ga duk abinda tayi min nasan dai ban taba cuta mata ba a rayuwa tunda nake ta iya min wanan mugun sihirin haka.
Ni yaushe ne matar nan zata bar gidan nan wai ya tambaya na gane fadila yake nufi don haka nace dashi ina ga rokon ta danayine yasa ta janye tafiyan har lokacin tafiyan mu.
Kina ganin hakan bata sabawa dokan aikin su ba ya tambayeni yana kallona nace bana jin hakan don da zai saba din ba zata yarda ta tsaya ba ai.
Kafada ya daga tare da fadin ok a fili idan dai ta tashi ga wanan ki bata ya miko min key da envelope sabo na karba tare da masa godiya kamar nice akaba kyautan .
Ko ban san komai ba nasan wanan makulin motane ya bata ya juya yana fadin ida ta tashi sai ta tambayi Hadi driver zai nuna mata motar ta dauka.
Na kara mashi godiya ya fita daga dakin sai abin ya ban mamaki kwarai da gaske don ban taba tsamanin zaiwa fadila irin wanan kyautan ba haka.
Dakin ta na nufa kai tsaye bata cikin dakin yasa na fito na shiga surun sadiya a can na samesu zaune suna kallo nace ashe kina nan yanzun daga wurin ki nake tafe ai baki dakin.
Tace ina nan tare da mutumiyar muna kallo sakon ta dake hannu na na mika mata ta kalla a cikin maki kafin ta karba daga hannuna.
Yayan mu yace a baki idan zaki tafi naga ya dace in baki tun yanzu don ki sani ta bude baki cikin mamaki sai kuma tace wanan duk nawa ni kadai a take yanayin ta ya sauya.
Sauka tayi daga saman gadon sai kawai naga ta zube a kasa tana godiya kai haba anty bani ya kamata kiwa hakan ba ai na fada ina zama.
A sanadiyan ki ai na samu duk wanan alherin da ace banyi zaman lafiya da kuma tsakani da Allah daku ba duk wanan alherin ba zan sameshi ba ai.
Sadiyace ta katsemu da fadin yaushe zamu tafi gurin su inna anty ta jefo min tambayan nace ina gadai a cikin satin nan ne don baiyi magana akan tafiyan ba har yanzu.
Ke nan zakuyi tafiyane kuma nace eh zamu mayar da hjy daga nan mu wuce gida muyi masu sallama.
Lalai hakan na da kyau ku koma kafin ku bar kasan nan zaifi amma kuma kune zaku mayar da ita gida ke nan na dauka mamice zata kaita gida ?
Mami yanzu haka tana kaduna a can zamu samesu don gaba dayan su suna can kadunan kwana biyu ke nan da tafiyan su.
Naji hjy na fada jiya a waya wai mami tayi hakkuri ta bar zancen ga Allah sadiya ta fada ba zata iya kyale zancen ba don ko waye dole hankakin shi ya tashi .
Amma tunda Allah ya mata fada a yanzun gaskiyane ta barta da Allah zaifi laifi akai mata ke nan ko fadila ta fada ?
Eh to laifin ne nan dai na dan fada masu komai sama sama tayi saurin fadin ummhum nasan da hakan wallahi don inda ta taba zuwa a kanki wani lokaci an fada min hakan .
Sai dai abinda bai shafeka ba tunda bashi ya kaini ba a lokacin yasa ban dauki zancen da karfi ba mun dan dade muna hira kafin mu watse a dakin.
Duk kwana kin nan yaya bai kara cewa zai nemini ba nima kuma naji dadin hakan da darene mun kwanta yake fadin ya gama shirin tafiyan hjy mu shirya gobe da yamma zamu kaduna daga nan muje anchau muyi sallama dasu.
Allah ya kai mu na fada ina gyara kwanciya naji saukan hannun shi yana fadin ban son zuwa kaduna a yanzu don gaba daya garin ya fice min rai.
Dan juyowa nayi ina fadin laifin mutum daya zai shafi sauran yan garin itama din da tayi ai Allah ya fitar ma da hakkinku tun a nan duniya ta fara ganin mugun halin ta.
Kome mutun zai aikata idan ba alheri bane a rayuwan shi banzane don komai dadewa sai ya tambayi mutum ?
Abinda nake tunane ke nan a yanzu na rasa me nayiwa wanan matar har bata sona haka ?
Bakai tawa ba da farko ta dauka ta cuci mami ne don da ita take hamaiya bada kai ba.
Ajiyan zuciya ya sauke tare da dora hannun shi saman jikina naji gaba na ya fadi lokaci guda duk da tsorin shi da nake yanzu har ya san da hakan.
Shine dalilin da ya dan sarara min ya kyale ni a yanzu din amma ni kuma sai nake ganin ai rashin sabawa da zama da mace da bai iya bane yasa bai wani damu da kulani din ba.
Ko wanan ranan gaskiya nasha bakar wahala gun yaya don bai tausaya min ba haka ya koma kamar wani zaucace a gareni.
Washe gari mun isa kaduna bayan sallah magariba gidan na mami shiru da a yanzu duk sai na ganshi wani iri can kamar bashi ba.
Kodan yanzu idona ya bude da ganin ginan zamanine oho abinci mukaci kawai yace wai mu fito mu tafi .
Nayi mamakin jin ba a gidan zamu kwana ba ashe abinda ban sani ba shine yana da wani irin keraren gida cikin kaduna ashe haka ma ya mamud shima a yanzu ya bar gidan mami din.
Gidane na gani na fada na shiga tsara nayi mamakin hakan sosai danaga gidan lafiya lau komai ba laifi gida ya hadu.
Nan ma dai din bai kyakeni ba don mun zuba soyayya a wanan gidan sai dai kawai a kawo muna abinci daga restaurant muci safe da yamma .
Ko gidan mami bamu lekawa sai dai su ya jamal dake dan leko mu a ranan mu na ukku a gidan ne da dare muna falo bayan mun gama cin abinci wayan shi yai ringing ya dauka.
Naji yana fadin ina gida mana lafiya jin hakan yasa na dan dago ina kallon shi daga inda nake kwance na dan kishin gida saman jikin shi.
Banji me akace ba yace ku shigo mana ina kokatin jaye jikina a nasa don jin abinda ya fada din amma kuma sai naji ya rikeni ya hana in tashi din .
Ga mamakina Aisha ce suka shigo tare da wani saurayi da ganin shi irin samarin nan ne yan karya diyan masu kudin garin.
Mun gaisa dasu idon saurayin yana kaina hakan yasa ya jafar din kara daure fuskan shi sosai yake fadin umm, humm .
Kince kina son ganina ne akwai magana fadi abinda zaki fadi ina sauraren ki sai ta dago ido ta kalleni kafin tace dama magana nazo muyi yaya a kan magana na da Hashim gashi nazo maka dashi ku gaisa.
Yace waye shi tace kai tsaye shine wanda nake so kuma mami bata yarda ba har yanzu ya kalli yarin yace mami din ta fada maki haka da bakin ta sai tayi shiru.
Nan ya fara yiwa guy din tambayoyi yana bashi amsa kafin yace da ita alright zanga mami din muyi magana da ita kafin in tafi.
Daga haka ya fita batun su ni kan ba wani maganan kirki ne a tsakanin mu ba tunda na fahinci wani irin daukan kai da take min tun dawowan mu din kasan na kama kaina ga al,amarin ta ga baki daya.
Sallama sukai mai suka tafi ya tashi ya rufe gidan ya dawo ya zauna yana fadin ban san meke damun yarinyar nan ba zata kwaso min wanan ta kawo mi shi har gida.
Haba dai gidan dan uwanta tazo fa ba wani wuri ba kuma da gani tana son yaro nan sosai yasa tazo wurin ka ka taimaka masu .
In ba haka ba ai ya mamud ma yana garin da gurinshi zasu tafi ba wuri ka ba amma kuma ta zabi nan din tazo.
Wayan shi ce ke ringing ya dauka saurare ya tsaya yi har na wani lokaci kafin naji yace yanzun nan suka fita nan ita dashi.
No ban samu mata fada ba don tana tare da yaro a lokacin ni dai mikewa nayi ya bini da kallo don ranan sadiya tabi ya jalal da yazo zuwa gidan mami wurin hjy saboda idan muna daki da yaya ita kadai ke zama ba abokan hira.
Ya gama wayan ya shigo daki ya samu na shiga wanka koda na fito yana tsaye a wurin window kamar mai tunane.
Zama nayi bakin mirrow ina shafa mai yazo ya tsaya a bayana yana fadin ana magana kan Aisha kin bata rai.
Ba tare dana juyo ba muna facing din juna a cikin mirrow din nace dashi shi sha,anin aure ne yaya ba ai masa haka tunda shi take so har ta kawo shi gareku ai idan ba laifin sai ku bari tayi abinta.
Wa zai bari ta auri wana guy din kece yarinya da baki san komai ba wanan da ganin shi tashin waje ne bai koyo komai ba a can sai iskanci .
Wani kallo nayi mai da sauri don jin abinda ya fada din yace yes nasan abinda zakice ai ko nayi nawa a lokacin ina kokarin danne hakan a kasata ai.
Amma baka zaton auren shi din a dalilin ta zai iya gyaruwa ya bar wanan a kidar ya dawo dai dai ba dai wanan din ba na fada maki ke yarinyce ya wuce ya shige ban daki ya barni zaune ina tunane.
Ban san yadda sukayi da mahaifiyar su ba ni dai ranan sai ga Aisha din da gani tasha kuka tun a gida don idonta da yayi ja ga duk wanda ya ganta.
Sun dade da dan uwan nata a dakin shi suna magana don ta shigo ni fita nayi muna waya da Nafisa da tace zasu shigo dasu umma.
Ta fito ko sallama ban samu ba ta fita tana sharan hawaye su umma suka zo gidan sai hankalina ya dauku garesu na manta da zancen nasu.
Ranan a gidan su umma suka wuni tare dani da zasu tafine yayi masu alheri mukai sallama suka tafi.
Mun je gida mun samu Asabe na cikin wani hali na rashin lafiya kai tsaye yace a kawota asibiti kaduna wanan kuma ya kara dauke hankalin mu sai dai Asabe din duk da gatan data samu lokaci yayi ba magani a wanan jinyar ta rasu tana saka muna albarka ni dashi har innan mu.
Mun kuma koma can gida muka kwana daya na dawo kaduna daga nan muka dawo Abuja .
Sai muka fara shirin tafiya sai kuma ga zazzabi har saida na kwanta asibiti don jirgitan danayi ga zazzabin.
Hankalin jafar din ya tashi sosai da ciwon nawa sai da mami take ce masa kowa fa haka yakeyi idan an samu juna biyu duk da hakan bai gane me mami din take nufi ba.
A karshe dai tana murmushi take fadin nifa naga kamar matar ka na da cikine amma a bari saka makon ya fito a gani.
Ciki mami ciki ke ga zainab din sai kuma ya shafo kanshi zuwa fuska yana dan murmushi ya rungumi mami din lokaci guda.
Itama mami din dadi taji a lokacin tana dan bubuga bayan shi tare da fadin Alhamdullahi jafar tunda baka halaka ba ga baki daya gashi yanzu har zaka iya haihuwa ashe.
Koda na falka suna zaune su uku sun tasani gaba suna kallona dan binsu da kallo nayi na dan lokaci kafin in dan motsa baki ina gaidasun
Suka amsa tare da yi min ya jikin nace da sauki ina yun kurin tashi don aman daya tayar dani daga barci a lokacin.
Shine yake tambayan ina zan tafi da yaga ina sauka daga gadon da sauri na kaaa magana sai dana ns bude baki wani amai yazo min da sauri na nufi wirin da nake zaton ban dakine a wurin daga gefen dakin.
Tin ina amai a duke har na koma yi tsugunne haka yssa shi shiga bayin yana min sannu na fito a galabaice bayan na kurkure bakina da ruwan daya ban.
Wasa wasa wanan ciwon saida yasa muka kara kwanaki a kasan don jikina yaki dadi sam ga mutane sai faman zolayata sukeyi da sunan mai ciki da har lokacin ban yarda da hakan bani.
A haka muka tatara muka koma Chaina sai dai saboda yanayin jikin nawa yasa yace in nemo wace zamu zauna ko a gidane mu tafi tare.
Akwai wata babban yar malam dake gida auren ta ya kare kuma bata taba haihuwa ba gorin kishiya ya fitar da ita gidan miji tana gida zaune da itace zamuyi tafiyan don kanwa take ga innan mu ke nan don haka muke kiranta da mama Ladi.
Duk da mami bata so hakan ba a cikin ranta ba wai bata son zuwa da ita din bane don tana bangarena a,a.
Saidai a ganin ta matar ba zata iya bani kulawan da ya dace ta bani ba don tana yar kauye har ta kula mata da abinda ke cikin cikina a yanzu.
Ba wata dole din da ita muka tafi hakana don na nuna ita nake son muje don yadda nayi zama da mahaifiyar mama ladi din maizube.
Ban samu wani wahala ba ga tafiyan don mun isa lafiya sai dai barcin da nayi tayi bayan saukan mu din.
Zaman mu da mama ladi ba wani matsala a cikin shi don ina jin dadin zama da ita sosai kuma ina bata girman ta na uwa a gareni haka shima a bangaren shi kamar yadda yaji muna kiranta da mama Ladi hakan yake kiran ta dashi.
Yayin da sadiya kan tuni ta koma school din su don tana da permition na barin wurin dan lokaci daya daukan mata.
Ban yarda na zauna ba tun da muka dawo duk da laluran dake gareni na ciki din bai hana mai da hankali wurin tsare ibada na ba don samun kariya a wurin Allah.
Haka itama mama ladi mace ce mai yawan ibada sosai bata da wasa wurin aiwatar da ibadun ta .
Tsorona kada yan wanan kungiyan su kawo muna hari ko su kara jan ra,ayin shi ya koma cikin su tunda yanzu sunga ya barsu kwata kwata bai tare dasu.
Don tunda zamu dawo mami tayi min magana akan na taimaka na mayar da hankali akan shi sosai don Allah don ita da son samune ma ba zamu koma wani kasa ba a nan gida zamu zauna tare dasu.
Wanan na rike a zuciyana ina kallon duk wani shige da ficen shi a yanzu din bana yarda in yi nisa dashi ko a dauki lokaci banji inda yake ba.
Sai hakan kuma ya kara jawo muna shakuwa sosai dashi don ko ban kirashi ba shi zai daga waya ya kirani yaji lafiyan mu.
Har mama Ladi na fadin don lura da tayi dashi idan ya dawo aiki sai yazo inda nake ya rungumeni a jikin shi ya dan zauna tare dani na dan lokaci.
Take fadin wai irin wanan zaman namu ba na malam bahaushe bane da iyakarshi da mace sai idan dare yayi yana da bukatan ta.
Nayi dariya ina fadin mama aiko a hauwan na da can baya ke irun wanan dabi,an na yanzu kan sun waye suna abinda ya kamata suyi na kulawa da iyalin su.
A kwana a tashi har cikina ya isa haihuwa a lokacin mami wayan ta ko yaushe kiran mu takeyi taji halin da nake ciki.
Har dai Allah ubangiji ya saukeni lafiya na haifi da na miji mai kama da ubanin shi sak don bai raga su da komai ba har tsayin su da irin yanayin yayan mami duk ya kwaso su sak.
Basu wani tsayar dani ba a asibitin don ina da lafiyana na dawo gida duk abinda kakan maya ta bani da an haihu na fadawa mama ladi komai tunda na karbo maganin.
Don haka batayi wasa wirun bashi maganin ba tun a asibiti tayi dubaran dura mashi ya fara sha yana bata fuska.
Sai dai abinda ya dan sa jikina sanyi shine yanayin yaya jafar din game da haihuwan nawa dana zata zai nuna farun cikin shi sosai ga hakan.
Sai banga hakan ba ga fuskan shi sam kamar yanayin shi yana a cikin damuwa a ranan ya dan dade tsaye a kan yaron yana kallon shi kafin ya juya ya fita ya bar dakin.
Na bishi da kallo haka har muka dawo gida sai ya zauna yayi shiru shi kadai kamar mai tunane ganin hakan da nayi ne yasa na fahinci akwai wani abu a kasa wanda ni din ban sani ba.
Wanka na fito mama da Sadiya suna zaune dashi ta gama shirya shi na dan kalleta nace mama zaki iyayiwa yaron nan hayakin nan da malam ya bamu da sauran maganin shi duk a dura mai koda kadan ne ki kuma shafa mai su.
Tace mai zai hana yanzu kuwa hakan tabi ko ina da hayakin bayan ta gama masa komai yadda ya dace naga kuma ta daga shi tana addua har muna iya jin abinda take karanto mashi a lokacin.
Mun kwanta lafiya Allah kuma ya tashemu lafiya tunda asuba naji ana buga muna kofa na fito daga wanka ke nan kamar yadda mama ta umurceni da yi.
Muka kalli juna da mama Ladi din kafin ta nufi kofan ta bude kai mama Ladi ta san kanta sosai a wurin addini gaskiya don zuwan ta ba karamin rana yayi min ba.
Shine tsaye a kofan idon shi a kan mu yake fadin lafiya dai kuka kwana ko yake tambaya ba tare da ya amsa mata gaisuwan da take mashi ba.
Lafiya kalau gashi har tayi wanka shi kuma dan yanzu nake batun in masa yana da rai ko ya fada .
Ban san lokacin dana dan sake man dana dauko zan shafawa jikina ba a lokacin na nufi wurin gadon da yaron ke barci shida sadiya hankalin su kwance a lokacin.
Hannuna nakai a daidai saitin kirjin yaron kafin na mayar zuwa hancin shi naji numfashin shi yana sauka lafiya.
Na dago ina kallon shi daga inda yake tsaye ya tsura min ido nace dashi me hakan ke nufi ban gane wanan tambayan da kai min ba yanzu ?
Nima ban sani ba ya fada yana barin dakin zaune nakai dabas na kalli mama Ladi da itama mamaki ya kashe ta a wurin ta kasa magana a lokacin.
Kada ki dauki wanan wani abu wata kila dai mafalki yayi daku ya razana ai kinga kamar a firgice yake koda ya shigo dakin .
Na bude baki da kyat ina fadin mama kashe yaron nan zasuyi don tun jiya a asibiti naga hankalin shi a tashe sosai daya tambaya akace namijine na haifa.
Wanan sai Allah ya isa ya kashe bawan sa zainab kada ki sa hakan a ranki har kikai ga yin sabo tunda zargi kike masa yanzu.
Har in ma akwai wani kulli tattare da yaron nan Allah yafi mai shi da sherin shi duka don mu da ayan Allah muka dogara bama tsafi bama tsubo.
Duk wanan zancen na mama hankali bai kwanta ba mikewa daga inda nake zaune a gurguje na shirya na fita daga dakin zuwa wuri shi.
Na sameshi yana sintiri a dakin yana rike da casbaha a hannun shi daga shi dogon jallabiya a jikin shi lokacin.
Jin motsina yasa ya dan juyo yana kallo na har na karaso inda yake tsaye din har yanzu yana numfashin normal ya kara tambayana.
Nace eh sai dai ban gane dalilun wanan tambayan dakake tayi kan yaron nan ba tun dazun na tambaye shi.
Bai ban amsa ba illa juyawan da yayi zuwa bakin gadon shi ya zauna na bishi da kallo kafin in iya daga kafa zuwa wirun shi din naja na tsaya.
Don gaba daya na fita hayacina tunda na fahinci akwai matsala kan yaron nan dan mala,ikin Allah dako nonon uwa bai fara iya jaba sai ma da darene kafin mu kwanta mama ta matsa a fara koya mashi jan nonon da taimakon ta ya dan fara kamawa bawai ya iya jan ba.
Ko ka bada jinin shi ne dama ka barmu a cikin duhu na tambaye shi a cikin wani irin kakausan murya dake nuna ba tsoro a zuciyana lokacin.
Sai lokaci ya dago kai ya kalleni idanuwan shine suka kada sukai wani irin ja dasu lokaci guda yace nasan ba zasu barshi ba zainab .
What na fada a razane kagin in koma fadin innalillahi wa,inna alaihi raju,un nakai zaune kafin in fashe da wani irin kuka lokaci guda .
Hannun shi naji a jikina yana kokarin rikeni zuwa jikin shi nayi maza na jaye ina fadin kada ka tabani mugu azzalumi kawai.
Nayi nadaman sanin ka a yau din nan yaya da wanan rayuwan bakin cikin zan dinga riska a tare dakai na kwamace Allah ya kasheni kafin in girma har in sanka.
Wani kallo yai min da jajayen idanun nasa yace cikin karfin hali zainab ni kike kira yau da azzalumi haka a gabana.
Nace idan ba azazlumi kake ba me kake jafar jin na kira sunan shi kai tsaye haka a karo na farko yasa ya danyi min wani irin kallo kafin yace dani.
Ban zata a yanzu zaki min wanan judgen din ba ke da kanki bayan kin fi kowa sanin tubana da nadamana na gaskiya shi har ga Allah.
Akan me zan shede ka bayan ga abinda ka fada a yanzu kuma tun jiya din naga alaman damuwa a tare dakai don bakayi farin ciki da haihuwan yaron nan ba.
Fine naji kin gani din kuma kin gane amma ya kamata ki saurareni tunda har kinga damuwa a gareni.
Ni nasan ka,idan sune har idan mutum ya kubuta daga garesu zukaga da gaskiya ya barsu din sai sun dauki fansan akan abinda ya haifa idan namiji ya fara haihuwa a duniya.
Cikinane yabada wani irin sauti kulululu, , , lokaci guda numfashina naji kamar zai tsaya a lokacin kafin naji yana fadin saidai nayi mamakin ganin basu taba yaron nan ba har ya kwana yana numfashi.
Akwai abu dayan biyu zuwa uku walau addu,an mune dana yan uwa Allah ya karba .
Walau kuma addau,an ya hade da tsarin da kikai muna amfani dashi don gaba daya basa son zuwa wurina don sun daina bibiyata sam a yanzu.
Kokuma yaron nan ya soma cin abinci ko kafin suzo gareshi yaci wani abu ko yasha nonon ki shine dalili zainab ba wani abuba don haka ki daina zargina da hakan.
Allah yafisu jini dana dana yafi karfin tsafi ko wani abu don ina tare da Allah da ayar Allah a tare dani.
Dana ya sha zamzam da dabino haka kuma yasha nonona tun daren jiya din ba zasu iya min komai da yarda ubangijin mu Allah.
Ba zasu iya ba har abada na sani don da zasu iya din da sunyi suma sun fada kuma sun barmu din sai dai tsoron wanan nakeyi dama akan su.
Nasan da diya mace ce basu ko kallon ta yarinyar ta tsira ke nan shi yasa ake son bawa idan zai tuba ga sabon da yaiwa Allah yayita har kasan zuciyar shi.
Kuma tsakani da Allah ya tsarkake zuciyar da mu,amulan shi ga kowa sai Allah ya tsaya mashi ga duk al,amuran shi .
Na gane hakan a yanzu da kuma wani samir da hakan ya faru dashi don a yanzu yaran shi biyar komai sun kasa yi dashi da iyalin shi.
Haka nima na tsira ke nan zainab tunda har yaron nan a yanzu shima ya gagaresu tabawa ke nan har abada dashi da duk wani dan da zan haifa a bayan wanan din.
Jin hakan yasa na dan tsagaita kukana ina fadin dama Allah ya fada duk wanda ya barshi yabar imanin shi da kariyan shi daga abin ki.
Sabon Allah baida wani fa,ida sai tarin nadama a karshe da wahala da mutun zai dinga gani a rayuwan shi.
Yace wanan haka yake zainab tashi muje na kara ganin yaron nan in masa addua don ya tsira ya kuma tseratar damu daga wanan bala,in nasu har abada insha Allahu.
Jikinane yayi sanyi lokaci guda na kasa motsawa daga inda nake zaune din hannu ya kai ya mikar dani daga aurin muka fice daga dakin.
Tun kan mu karasa dakin muke jiyo kukan yaron muka isa da sauri yana hannun mama Ladi tayi masa wanka tana masa gashi nayi mamakin hakan ashe da abin gashinta tazo irin namu na gargajiya na gida .
Ya dade tsaye yana kallon yadda mamadin kewa yaron kafin ya fice cikin walwala da annuri a fuskan shi.
Gado nabi na lafe ina sauke ajiyan zuciya a hankali tare dayiwa Allah godiya bisa kariyan da yake bamu a kullun nayi ta tasbihi har barci ya daukeni ban sani ba.
Sai can na tashi a dan firgice ina kallon inda yaron yake goye a bayan mama ganin na motsane mamake fadin ki tashi kici abinci ba a son cikin mai haihuwa da yunwa ko kadan .
Hamdala nayi namike na tashi na shiga ban daki sai da darene nake fadawa mama komai daya faru sai bayan ta gama mamakin hakane tace insha Allahu Allah ya fisu yafi karfin tsafin su kuma.
Yan gida sun kiramu gwargwado sun muna barka mami ta nace akan sai yan suna sunzo anyi suna a nan chaina.
Dole ya yarda din suzo ciki masu zuwa aka bawa bangarena mutum biyu mami kuma ta kafe dole da inna a cikin masu zuwa din .
Don tazo taga inda nake zaune da badon hakan ba inna ba zata taba sanin inda mu biyu diyan ta muke rayuwa ba.
Sai ta wanan dalilim suka zo tare da Nafisa kawata daga kaduna suka zo da ita sai bangaren su ya jafar din suma mutum uku sun zama su biyar sukazo muna sunan.
Satin su biyu a wurun mu suka juyo suka dawo yaro yaci sunan mahaifin su jafar din Isma,il suna kiran shi da Anur.
Farin cikin inna nan baya musaltuwa don bata iya boye hakan ba saida muka kebe ne nake fada mata komai daya faru dani a rayuwan aure tunga farko har karshe kodana kai karshe inna na hawaye .
Tace Lalai zainab ABU CIKIN DUHU SIRINE yanzu kabar mutum a yadda ka ganshi kada ka tona cikin sa zakaga abinda baka zata ba idan ka tona din.
Musanman wa yan nan masu kudin na zamani da zakaga mutum yayi arziki a cikin dan kankanin lokaci ba a san inda ya samu arzikin shi ba.
A haka kuma zaka ga mutane na shige masa don kawai su samu abin duniya a hannun shi Allah ne sheda ban yarda kin zauna da bawan Allahn nan don nasan yana da abin duniya haka ba.
A,a Allah ne shedan zuciyana ya kuma ga manufata a hakan na baki hakkuri don halarcin mahaifiyan shi a garemu.
Nafisa ta amsa da fadin haba mama ta yaya zaka san irin haka har ka dauki danka ka kai wanan wurin koda kana da yaya da yawa ai akwai tausayin rai ko ?
Don ma shi jafar yana da imani da tausayi da halin halarci a zuciyan shi yasa abubuwan suka zo mai da sauki haka.
Sun tafi sun barmu da kewan su ina shayar da dana da yayi wayau ya girma har lokacin ban daina bunshi da addua ba da neman taimako munayin shi gaba dayan mu gidan.
Ban mantawa mun fita da ANNUR da baban shi lokacin ina da karamin ciki a jikina ciki na biyu muka hadu da philis a wani mahada.
Yana ganin nin mu saida ya kadu na shedashi bayi saurin fadin A,uzubillahi mina shetanin rajin .
La,ilaha illa anta subuhanaka inni kuntu minal zalumin sai ji mukayi daram yayi hatsari nayi mamakin yadda ya jafar bai nuna yasan shi ba a wurin .
Muka tafi muka barshi a cikin wani hali mutane sun taru a kanshi har muka dawo ina mamakin hakan a zuciyana daga baya nake jin wai ashe daga hadarun nan bai kara tashi ba har ya mutu a hakana karfin ayan Allah ya hau kanshi na fada a zuciyana.
I zuwa yanzun da nake baki labarin nan haihuwana ukku duka maza muna kuma lafiya na kara karatu yaya yai min hanya an daukeni aiki a wani babban company a nan chaina ina aiki.
Bukin kanwata sa,adatu yazo lokaci daya dana Aisha da Na,ima shine zuwan mu Nigeria da yara na uku lokacin don koda hjy ta rasu kakar su jafar bamu samu zuwa ba a lokacin ina da cikin dana na biyu.
Tunda Nuriya ta kyala udo ta gammu ta kasa biye kishin ta ga hakan don duk yaran data haifa matane bayan dan ta na farko.
Har yakai ta kasa boye hakan a zuciyan ta sai da ya kai har mamu tayi mata kashedi kan hakan kada tarihi yazo ya maimaita kan shi .
Ayin buki lafiya nasu Aisha aka farayi kafin na kanwata sa,adatu mun shiga mun fita nida kawata Nafisa da baka gane kawance ne kawai a tsakanin mu don mun zama yan uwa itama tayi auren ta a jos har da yara biyu.
Nan nazama abin kallo ga mutane wanda baisan irin rayuwan dana sha a baya ba yana min kallon na more miji.
Ni kuma ina masu kallon basu san ABU A CIKIN DUHU SIRI BANE.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.