Complete Hausa Novels

Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel

Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 60 of 139

ZAINAB IDRIS MAKAWA
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ZAINAB IDRIS MAKAW🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅

5️⃣0️⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

YAR UWA IDAN KIN GANI KARKI KARANTA IDAN BAKI BIYANI HAKKINA BA NA FITAR MAKI DA HAKKI NA FADA LITTAFIN KUDINE DON ALLAH, , , ,

Kina jina malam ya fada na amsa a sanyayye da ina ji malam kada kisa damuwa ko kadan a wanan mafalkin naki don har gobe haske na gaban duhu.
Matuka kina rike da ayar Allah a tare dake babu wani shedani ko wani mahulunkin da zaiyi galaba a kanki face sai in hakan mukaddarine daga Allah dama yana a cikin kaddaran ki.
A iya binciken da nayi na gano wanan mutum wani shedanine dake tare da mijin ki a kullun wanda ya sha alwashin ganin bayan duk wata macen da zata rabi mijin naki.
Ba akanki kawai yake shedan shi ba duk wata mace hatta uwar data haifeshi da zai iya sai yayi sanadin raba alakan shi da ita.
Saidai a garemu wanan abin matukar zaki rike adduan dana baki kafin kuzo wanda shi din makamine dama ga mumuni ga bayin da suke mika al,amarin su gurin ubangijin su koda yaushe.
Malam shidin ba mutum bane kamar yadda nake yawan ganin sa a mafalki ko na tambaya a cikin sanyin murya da damuwa.
Murmushi naji malam din yayi tare da fadin a buncike na dai shi din mutum ne kamar kowa saidai shedanin gaske ne na kwarai.
Hasbunallahu wani imal wakil na fada a sanyaye tare da sauke ajiyan zuciya don tsoro da fargaban da ya ziyarci zuciyana a lokaci daya naji malam din yace.
Saidai abinda nake so dake Abu shine ki kwantar da hankalin ki da sannu zaki fahinci waye shi wanan mutum din cikin masu alaka da mijin naki.
Shi mutum masheranci ba kasafai kake saurin gane shidin makashin ka bane sai idan ka kwantar da hankalinka a sannu zaka fahinci duk wani mai binka da sheri a doron kasa ko ta wurin maganan sa ko yanayin kallom sa gareka da dai sauran su.
Mun dauki lokaci tare da malam yana kawo min ayan Allah da hadisai har saids hankalina ya kwanta naji duk tsoron dake raina a lokacin yana gushe min a lokaci guda.
Bayan sallama da malam din na koma gaban gado na zauna da wayan a hannuna na fara tunane wanan wani sabon kaddarane kuma ke shirin tunkaroni a yanzu.
Ina zaune ashe hawaye na zubo min ban sani ba sai jin muryan anty fadila nayi a kaina tana fadin me kuma ya faru haka zainab ke kadai a daki zaune kina hawaye haka ?
Kaina dago ina sauke sanyayyen ajiyan zuciya ina kare mata kallo tana tsaye da wani leda a hannunta fari ta karaso shigowa cikkn dakin tana maimaita tambayan ta a gareni lokaci guda.
Meya farune kuma don nasan ba zaki zauna haka kawai kina zubar da hawaye haka ba ke kadai a daki zainab ?
Ki saki ranki dani wallahi na fada maki ni mai taimakon kine ko da yaushe zainab don ciwon ya mace na mace ne yar uwanta ko kuma zancen fadan da mijinki yayi min ne ya sakaki wanan kuka yanzu ?
Kaina girgiza ina kokarin kakaro murmushin dole a fuskana kada ta dauka wani abu nake boye mata haka don ban da niyar fada mata wanan sirin nawa.
Nace anty ba komai bane kawai tunanen makoma na a gidan nan nakeyi sai hawaye yake zubo min ban sani ba ina kokarin share hawayen dake fuskana din.
Dafani tayi tana fadin kinga irin mazan ku dama tsada sukeyi koga matayen auren su idan kinga mutum da kyau ga ilimi ga dukiya uwa uba wayewa lamarin shi gaskiya sai a hankali dama.
Nasha fada maki ba sanya zakiyi ba saifa kin dage zainab a wanan zaman naku kada ki damu da duk wani hali da yake nuna maki a yanzu .
A sannu a hankali komai zai daidaita a tsakanin ku ke barin fada maki gaskiya daga yan mata har manyan matan barikin garin nan.
Duk idon su akan irin mazajen nan suke ko yaushe burin duk wata mace a yanzu shine ta samu gidan hutu irin wanan ta yadda zata shiga tsara ta nunawa duniya ita watace a gari abin kwatance.
Ke bari ma dai in maki na mahaukaci ai yanzu idan kayi sa,a ka damki namiji kada kayi sakaci dakoma wayeshi kama abinki ki damke ta yadda matan waje zasu gane ayya yana gaba da tsakuwa wurin taunawa.
Don haka kama jiki kafin yazo ki nuna mai ke yanzu ba da bane a gurin ki kinsan kanki kinsan ajin ki ta yadda zaiji shayin yi maki wani iskancin su na maza can.
Dago kai nayi da sauri ina kallon ta don jin abinda ta fada ni ta yaya zanwa mutum kamar ya jafar wani sallo ko kissa can har yasan ni din mace ce ta fada a duniya.
Tace kina mamaki ko zainab zakice nace maki lokacin da zaki kama shi a hannun ki kina juyawa yadda kike son abinki da kowa zaiji a ransa dama ace shine a matsayin ki a lokacin .
Jin abinda ta fada yasani sauke wani irin ajiyan zuciya mai dan karfi don jin zancen ta nakeyi kamar almara a kunnuwa na.
Har yaushe hakan zai faru da take ta fada a gareni ni din da ban ko gama sanin matsayina ba a zuciyar shi har take min hasashen hakan yanzu.
Kina da kyau da zaki sace duk wani zuciyan da namiji zainab irin kiran ki maza da yawa suke so a rayuwan su saidai in hakan bai samu garesu ba dai.
Kin koga yadda kika koma a cikkn kan kanin lokaci zainab yanzu wasu kayan ne na sayo maki irin wanda ya kamata mace na sakawa a cikin gidanta don jan hankalin mijin ta ba yanzu zaki amfani da wanan kayan ba sai lokacin da mijin ki ya dira a kasan nan.
Dan murmushin yake na sake mata a fuskana kawai ta fara daga kayan har kala biyar babu wanda zan iya fita ko falon gidan dasu a ganina balle wai gaban shi ya Jafar din da take nufi.
Godiya nayi mata a fili a zuciyana kuma fadi nake Allah ya sauwaka min sakace wata karuwa can riguna haka duk a bude kamar rigan turawa marasa tarbiya.
Zai maki kyau sosai ta fada tana kara dagasu tare da fadin ina gani su naga sun dace dake sosai yasa na sayosu tunda akwai kudi a hannuna.
Nagode na kara fada a cikkn kulawa da nuna girmamawa a gareta kuma na kula da hakan yayi mata dadi sosai ta mike tana fadin don Allah ki saki ranki na fada maki saifa kin jajirce sosai ba a sanya a harkan aure.

Kwana biyun nan nikan na mayar da hankalina a wurin addua ne sosai da kai kukana gun ubangijina Allah kuma sai nake jin natsuwa da kwanciyan hankali yana kara shigana ko wani lokaci.
Hakama maizube na kula da tana tayani da addua don itama tana bata lokaci sosai wurin fadawa Allah al,amarin mu.
Falon gidan muke zaune bayan sallah la,asar wanan ya zama muna kamar dabia a gudan a wanan lokacin mukan hadu nan mu dinga fira da juna ana dariya.
Wanda hakan kan min dadin a rayuwana har in manta da wani abu a tare dani gashi a sannu ina matawa da tsoron mami a cikin zuciyana.
Saidai tunanen hjy da kewan ta har yanzu yana nan daram zaune a raina don tsohuwar ba abun mantawa bane a rayuwana don jinta nake kamar itace Asabe kakata a guna.
Yun hadarin yamma ya zama kamar al,ada a garin abuja din haka yanzu ko an hada bai faye damuwan mu ba kamar farko.
Da wandone baki irin na mata mai dane jiki a jkina iyakarshi idon kafana hakan yasa santala santalan kafana fitowa fili gasu fari sol dasu don tsaban samun dadin da nake ji yanzu tare da rashin wani aiki da banayi a yanzu yasa kafan ya kara min haske sosai.
Sai dan riga irin na mata dake dan bude daga kafadunshi zuwa iya gwiwana mai launin kalar kampala jikin rigan wanda ya dauki kalar jikina da kyau.
Sai hula dana saka a kaina mai ribon ta baya ya gashina dana daure yasa yadan dago ya kara min kyau.
Wanan duk aikin anty fadilace wace take matsa min da nayi wanan shigar tun ina kunyan hakan har nazo na daina ina fita hakan kamar yadda ta umurceni dayi din.
Ruwane ya gwauce kamar da bakin kwarya muna zaune muna hiran mu bamu daga a falon ba don sanin lokacin sallah baiyi ba a lokacin.
Duk da ruwane mai karfi da akeyi hakan bai hananu mu jin dirin motoci da horn a gaban gidan ba lokaci guda saidai hakan bai wani damun ba don ji muke kamar hadirin ne haka.
Don haka hankalin mu kwance muke hiran mu batare da kawo komai a ran mu ba lokacin sai ji mukayi kawai an turo kofan falon da muke zaton a rufe yake.
Don bamu barin kofan kasafai a bude hakana a namu zaton yana rufe a lokacin ashe a bude yake jin aturo kofan yasa hankalin mu ya koma a kofan lokaci guda.
Shine ya shigo falon ba tare daya dago kai yasan damu a falon ba yana dan kakabe ruwan daya dan taba mai jiki daga waje wajen shigowa gidan.
Gaba dayab mu a cikin mamaki muke kallon kofan don jin anturo da mamaki karara a fuskokin mu sai ganin shi mukayi tsaye yana kakaban ruwa a jikin shi.
Kafin ya dago kai ya sauke idon shi garemu idanuwan shi masu haske kamar kwan lantarki ya kura min ido da maki a fuskan nasa.
Tsaban rudewa da fargaba yasani mikewa lokaci guda don rabona da ganinsa yanzu kusan shekara daya ke nan ake batun rufewa tun bayan daya dauko mu a kauye tare dasu maizube da halimatu ya tafi sai wanan karon dana gansa.
Idanu ya kara watso min sun kara fari da girma gasu dal dasu tankar hasken lantarki saboda tsaban jindadin da yake samu.
Ga wani girma da kwarjini daya kara baiyana mai alaman jin dadi ya zaunu mai a yanzu fiye da lokacin daya barmu a baya.
Masangalin kujera na dafa a cikin kyarman murya nake fadin sannu da zuwa yaya .
Sai lokacin ya dan yi kamar wanda yai shock a cikin basarwa da dakewa ya amsa da uhmmm yana karasowa cikin falon.
A daidai lokacin ne kuma aka sake turo kofan saiga wanan yaron nasa ya shigo dauke da jakkar kayan shi yar karama.
Shima tsayawa yayi yana kare muna kallo cike da fara,a anty fadila take masu sannu da zuwa da signal ta nuna min in karbi kayan a hannun yaron nasa da yake rike dashi a bayan shi.
Na karasa cikin takon da bansan inayin shi ba zuwa inda suke tsaye din na dan gwauta ya jafar din zuwa amsan yar jakkar kayan.
Sai cewa yayi cikkn wani murya mai shrge dana mata barshi kawai zan karasa dashi ciki ya fada yana kokarin wuce inda nake tsaye.
Da sauri anty fadila ta amsa da fadin is her duty give it to her ya dago yana kallon ta a cikin mamaki kamar ba zai bayar ba sai kuma ya mika min jakkar.
Kamar kullum wanan yaudararen idon nasa ya watso min wanda na riga dana saba ganin wanan kallon nasa tun ina a gidan mami zaune idan sun shigo tare da yayan.
Zama sukayi a falon yana gaiswa da maizube da halima datake murnan ganin yaya din sai faman washe baki da takeyi don ganin sa.
Bankai kayan dakin ba don a rufe yake tun lokacin kitchen na nufa a can na samu anty fadila tana hada masu abin sha tana ganina tace good oya dauki maza kikai masu wanan.
Na dauko har lokaci yana zaune suna hira da maizube sama sama na dire masu ruwan da drinks a gaba shi kamar yadda ta koyar dani din inyi idan ya shigo.
Wanan yaushe ta koma haka yaron nasa ya fada a daidai lokacin da nake mikewa daga dukawan danayi ina aje ruwan cikin kashe murya.
A takaice na amsa masa da kwanaki wanda ni kaina bansan zanba da amsar hakana ba alokacin fito min tayi a bazata.
Kaishi kawai ya girgiza cikin wayayencewa gami da basar da disgashin da nayiba take.
Na juya zan bar wurin naji ya din na fadin dawo ki zuba muna yanauin maganan sa kamar a kasalace yake a lokacin.
Na dawo badon naso ba na fara zuba masu a hankali abin mamaki sai bayan na zubane wanan yaron ya mike ba tare daya dauki nasa yasha ba yana fadin.
Zai fita yaga sauran wa yanda suke tare dasu a waje ba tare da ya jafar din ya bashi amsa ba yaba zaune ya dafe kanshi da hannun shi daya har ta fice falon bai masa magana ba.
Dauka nayi nikan na mika mai a cikin ladabi da girmamawa sai naji yana fadin thank you bayan ya karba daga hannuna.
Banyi mamakin jin kalman daga bakin shi ba don godiya ga bature ba wani abu bane wanan na saba da godiyan su tun a gidan mami.
Saidai naji dadin hakan a raina don godiya wata kalmace mai nuna yabawa ga mutum ga wanda akaiwa hidima.
Yana gama sha ya mike tsaye ya nufi hanyar dakin da yake shine nasa din a gidan wanda har lokacin dakin yake rufe.
Ina ganin ya shige na sauke wani irin ajiyan zuciya lokaci guda kamar wace ta tsira daga wani abun tsoro.
Maizube ne ta fara mikewa tana fadin wanan yaron yai muna bazata shigowa haka babu sanarwa a garemu Allah yasa dai abincin da akayi zai gamshe shi.
Anty fadila tana kitchen din zata bada umurnin abinda za a girka masu yanzu na fada ina kokatin zama.
Ke kuma ina zaki zauna nan miji yana gari ai tashi zakiyi kije inda yake ko da wani taimako da zaki masa yanzu.
Wani iri naji a raina idan naje mezan masani don dai kawai in basar da zancen ta sai kawai na mike kamar zan nufi dakin sai bayan ta shige dakinta na dawo na shige nawa ba tare da nayi abinda tace min din ba.
Ban dade da shiga daki ba wayana ya dauki kara da mamaki na isa inda wayan yake na dauka anty fadilace ke fadin kina inane ?
Daki na bata amsa a takaice tace ki sameni a kitchen kai tsaye ta kashe wayan haka yasa na mike tsaye nafito zuwa kitchen din.
Nan na samu sunata aiki a kitchen din tare da banufar dake dafa muna abuncin a gidan tana min bayani muna aikin har muka karasa daidai lokacin da aka shiga sallah magariba don dama yanayin hadarin ne yasa garin duhu kamar magariba yayi a lokacin.
Bayan mun gama jera komai nakaiwa su maizube nasu a dakita na koma dakina don gabatar da sallah na.
Wanka na farayi kafin nayo alwala nafito na tayar da sallah din ban daga daga gurun ba sai danayi duka sallalolina gaba daya nayi kafin in tashi in gyara jikina.
A cikin wani dogon riga har kasa mai laushi sai kaina dana gyara tare da daura dan kwalin rigan ta hanyar sako bellen daurin gefena duka biyu wanda yin hakan yabada wani ma,ana a gareni.
Fitowa nayi falon ban samu kowa a falon ba sai kayan abincin da aka jera masu saman table masu kyau na zamani da daukan ido wanan duk aikin anty fadilace.
Ina shirin komawa bayan na karewa falo kallo da irin kamshin dake tashi a cikin sa saboda gyara na musaman daya samu dan shiga dakin danayi don yin sallah.
Anty fadilace ta fito take fadin yyauwa dama yanzu nake shirin shiga surin ki na kiraki ki samu mijin ki a daki ki fada mai abinci na dinning ki kula da wanan matukar yana gari a tare dake wanan yana a cikkn aikkn ki daga yau.
Dan jin nayi ina tunane a raina na yadda zan iya tunkaran shi da wanan zancen kamar ta shiga zuciyana taga abinda nake tunane a lokacin.
Take fadin kwaliyan ki yayi kyau matuka yanzune kika nuna min kina amfani da shawaran da nake baki kullun.
Don haka sauran aiki yana gareki kije ki sameshi a dakin shi tunkan ya fito hakan zai kara kawo kusanci a gareku ko yaushe.
Idan kuma ya fito ki tabbatar da kin zauna sai idan ya gama ci kina zaune a gurin wanan ma wani isimine na mata da mata da yawa suke sakaci dashi tana gama fadi ta juya don barin wurin
A hankali na ja kafana zuwa dakin bakina yana cike da addua na tun kari dakin nasa yayin da gabana sai faduwa yake min din tsoro da fargaba abinda yin hakan zai iya jawo min idan na kai kaina gareshi din.
A kofa na tsaya na da runtse idanuwana tare da tattaro karfi da kuzari azuciyana na kai hannu ina kwankwasa kofan.
Kusan sau uku ina kwankwasa kofan kafin naji ana kokari bude kofan daga ciki hakan ya dan sani ja baya a hankali tare da tsoron hakan a raina.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.