Complete Hausa Novels

Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel

Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 109 of 139

LITTAFIN KUDINE KI BIYA DARI UKU KI KARANTA YAR UWA DON ALLAH KI GUJEWA SHIGA HAKKIN WANI YAR UWA KAN ABIN DUNIYA, , , ,

Na san mai karatu zakiyi mamaki jin abinda na fada akan fadila hakan kuma ya samo asaline tun ranan dana fara gane waye fadila a gurin mu.
Ranan kishin ruwa kawai ya tayar dani a cikin dare na fito don neman ruwan da zan sha a lokacin.
Banyi amfani da ko wani irin haske ba don nasan inda ruwan yake sauri kuma ya hanani tsaya na dauki ko wayana in haska.
Har na dauko ruwan zan fito naga kamar gittawan mutum a falon namu karami.
Naji tsoro iya tsorata nayi shi don haka na samu wuri na lafe a bayan kofan kitchen din muryan fadila naji tana waya a hankali.
Tana fadin wallahi duk dabaran da zanyi in gane wani abu a gareta nayi shi har yanzu ban gane komai ba a wurin ta .
Don yarinyar akwaita da shegen wayau tsiya don wayau ta yafi karfin shekarunta sosai wallahi.
Na saka ido sosai don in fahinci wani abu a gurin shi na kasa fahintar hakan duk da janta danayi a jiki sosai abu daya na sani shine.
Yana shan cocaine din amma baya harkan sayarwa don aikin sa a nan yana jawo mai babban riba da samu fiye da zaton me zaton hakan.
Shiru tayi tana sauraren me ake fada mata a wayan kafin tace zan saka ido kafin tafiyana yazo sosai zan kara gano wani abu a hakan.
Kara lafewa nayi sosai inda nake boye ina mamakin ta a raina kafin naji tayi sallama da maishi tana kashe wayan ta dan haska ko ina ta koma daki.
Sai dana dan dade ban fito daga inda nake boye ba kafin na fito na koma daki cikin tunanen wacece fadila din ?
Haba abin mamaki ne ace mace wayayya kamar fadila tana aiki irin wanan haka sai dai mutum ya duba ga irin yanayin da kasan mu ke ciki na rashin aikin yi zaisa mutum yayi duk wani aikin daya samu don dogaro dakai.
Tun wanan ranan na kara tsorata sadiya a kanta ta kuma tsorata duk tambayan da tayi mata takan zo ta fada min da amsan da ta bata a lokacin.
Sai gashi bayan kwana biyu tana fada muna gida zata wai mahaifiyar tace ba lafiya a lokacin.
Yanzu yana da wuya kayi saurin yarda da mutum farat daya irin haka Allah ya taimakeni ga zurfin cikina.
Nidin na kasance irin mutanen ne da basu da yawan sake magana ga kowa idan hakan ba ya kama dole bane.
Idan zan tuna duk hiran mu ko sakewan da zanyi sai dai ita din ta kasance mai ban shawara ko tayi magana akan abinda tagani da idon ta tana bugun cikina.
Kinji dalilin daya sa yanzu nake ja baya da zancen fadila din duk da bansan dalilin kasancewar ta a cikin mu ba har wanan lokacin.
Bamu hadu da yaya J ba sai washe gari misalin sha biyun rana da nake ganin fitowan shi ke nan daga barci.
A falo ya same mu na gaji da kwanci na fito muna zaune da sadiya fadila ta bar wurin zuwa kitchen duba masu aiki a can.
A daidai lokacin tana dawowa yake fadin pretty ya kike na dan dago kai na kalle shi tare da fadi cikin wani yanayi lafiya ya gajiya ?
Akwaishi wallahi sai yanzu na tashi ki bani abinci na danci zan fitane yanzu ya fada yana zama a gefena kaina dago kafin inyi magana ta juya zuwa wurin da za, a shirya mashi abincin kamar yadda ta saba yi.
Yadda muke zaune zaka dauka mu din wasu ma,aurata masoyan juna a lokacin don ya zauna ya dan kwanto min a jikina .
Fadin an hada table da tayi yasa na rigashi mikewa na nufi dinning din ina duba abincin ya biyoni a baya.
Zama yayi na fara zuba mai abincin bayan na gama na samu wuri na zauna a gefen shi zakace zaman arziki mukeyi dashi a lokacin yadda muke nunawa.
Yana ci muna dan hira har lokacin daya kare ya goge bakin shi ya mike ya danyi hugging dina yana fadin sai na dawo.
A dawo lafiya nayi masa na mike na bar wurin cin abincin nan koma inda na tashi ba da farko dakina na nufa.
Ina shiga daki take cewa sadiya da alama dai yanzu sun daidaita tsakanin su ko take tambayan sadiya din ?
Dama ba daidaitane a tsakanin su anty ta tambayi fadila din cikin mamaki sanin halin sadiya yasa ta basar da zancen itama sadiyace data shigo take fada min yadda sukayin.
Bani da wani buri a yanzu illa inji ya kawo zancem zuwan mu gida wurin iyayyen mu duk da ko gidan mami ma da yake garin bamu je ba suma basu leko inda muken ba har yau kwanan mu biyu da zuwa kasan.
Tunane nayi dan ganin dacewan hakan ya dawo da yamma nake fadin yaushe ne zamu gidan mami mu gaida su din duk da nasan kai ka tafi ko kun gaisa ko.
Ko yau ina can tunda na fita muna tare dasu idan kun huta sai mu tafi lokacin da kuka shirya hakan ya bani amsa.
An jima zamu idan Allah ya kaimu na fada ina shirin barin dakin naji yace sai ki fitar da tsaraban da zaku kai masu idan zaku tafi.
A cikin mamaki nace ba wani tsara dama dai turarene sai wasu jewels dana sayo da zamu zo na fada ina kallon shi.
Tsara yana dayan dakin nan sai ki duba kiga abin daya dace ku kai masu a ciki da duk wani wanda ya dace aba shi tsaraban.
Ba mamaki don sanin halin sa nace angode kawai na fita zuwa dakin don duba kayan suna daure har lokacin ba a bude su ba.
Don haka ban san ko meye a cikin kayan ba na juya na fita na koma daki da niyar fara shirya fitan da zamuyi din.
Ban fadawa kowa zancen fitan ba ko sadiya don gudun ta fadawa wani hakan sai bayan sallah magariba nace taje ta shirya inji yaya zamu fita.
Ta juya da murna ta fita nima na zauna ina idar da isha,i na shirya wanan dakin na koma na samu an bude kayan a lokacin na shiga duba ina zaba.
Kayane irin na tsaraban mata da maza sai wasu abubuwan da ban sani ba na dai dauki wanda zan dauka na fito.
Shiyasa aka kwasa zuwa cikin mota da zamu fita da muka fito na rufo kofan da key din dana gani a wurin na zare key din har kofan da zai sada mutum da part din mu da nasa sai da na rufo na jefa key din a jakkata.
Wani iska ne mai dadi ya daki jikina har hanci mai dadi muka tako a hankali zuwa wurin motan dan shi a baya muka barshi bai fito ba.
A hankali motar ke tafiya muryan sadiyane ke fadin anty tace bata san zamu fita ba wai.
Baki fada mata zaku fita bane ya tambayeni daga gefena nace ban fadawa kowa ba ya sake fadin har fadilan ?
Ban fada mata ba don ta canza yanzu a sanin da nayi mata a baya ke sai yanzu kika san da hakan ya tambayeni ?
Na juyo na dan kalleshi yake fadin na sani ita din yar sandan ciki ce bincike takeyi a kaina sai dai tana dauka ban sani bane .
Sai dai ya akayi ke kika san hakan ya tambaye ni cikin son jin amsa nace zuciyana ne ya bani hakan ban fada mai komai dana sani game da ita ba.
Amma kina da abin mamaki zainab yadda har kika gano hakan da sauri da kanki game da fadila din ?
Idan ina zaune da mutum tsakani da Allah nake zama dashi shiyasa Allah ke nuna min ko waye maishi da sauri haka ban taba zama da wani mutum da wani manufa saidai kai da muke zaune ka munafunceni.
Oh really ?
Ya fada kanshi na duke yana duban wani takardan dake hannun shi hankalina na mayar ga titi da muke tafiya.
Har motan ya sha kwanan da zai sada mu da gidan mami din dake wani katon unguwa mai gine gine masu kyau da daukan hankali.
Gaba daya sai gidan ya canzawa sanin danayi mai a baya saida muka fito ne a cikin mota na tabbatar da ba wancan gidan bane da muka zauna dasu a baya.
Allah ya gani ban shiga gidan da wani manufa a zuciyana ba lpkacin sai gashi muna shiga komai ya canza a lokaci daya.
Da farko mun shiga da sallama mun jero tare da yaya sai sadiya dake dan bayan mu kadan tana biye damu a bayan mu.
Ko kaine wa dole mu baka sha,awa yadda muka shigo gidan a lokacin gaba dayan su suna falon mami din a zaune har Nuriya da yaran ta kamar wani abu sukeyi a lokacin.
Jalal kan ya amsa muna sallama da nuna murshin da ganin mu yana fadin a, a mutanen chaina ne yau a gidan namu haka ?
Sai ya jamal daya dago cikin mamaki yana fadin a, a zainab kuma kun zone ashe sannun ku da zuwa a cikin fara,a.
Ya jalal mun sameku lafiya na fada tun a tsaye kafin na juya wurin ya jamal ina fadin ya jamal ya gida ya aiki ?
Zainab ai sai mutum ya dauka kema yar chaina din ce ko yar wani nahiyar larabawa yadda kika koma din nan inji ya mamud ya fada cikin yar fara,a.
A daidai lokacin dana zube gaban mami itama sadiya ta zube kamar yadda taga na zube din muna gaida mami.
Sai ji nayi ya jafar shima ya zube a kusa dani yana fadin kamar yadda na fada mami ina wuni mun samuku lafiya.
Duk suka kwashe da dariya banda mami data daure fuska tana fadin kai yanzu bakaji kunya ba ace kuna kasan nan tun shekaran jiya amma sai yanzu matar ka zata shigo gidan gaishe mu ?
Haba mami kin san suna tare da gajiya nine nace ta bari su huta sai na kawo su na kuma fada maki ai a waya.
Kaina yana sade a kasa koda take wanan maganan can na dago na dan kalli inda yan matan gidan da ya mamud da matar shi suke zaune nace yaya mun same ku lafiya anty ya gida ya yara ?
Kafin nace kuma anty mun sameku lafiya ya gida ya aiki da karatu duk a lokaci guda na jera masu gaisuwan a tare.
Sai ya mamud ne da anty Na,ima suka amsa mun da fara,a suna fadin munzo lafiya ya can ni sai lokacin ma nasan ashe Nuriya matar ya mamud ta kara haihuwa ashe .
Don na ganta da yarinya karama dauke a jikin ta da alaman har an yayye yarinyar ma a lokacin .
Muryan mami naji tana fadin sarauta dai da jin kai irin na samun wuri har zainab ce yau za a ce wai tana hutun gajiya irin haka a rayuwan ta.
Da sauri na juyo na dan kalli mami din kafin naji ya jalal yace haba mami sai kace ita din ba mutum bane naga ke idan mun dawo har karin ruwa ake maki fa.
Gasu dai gwanin ban sha,awa kamar ace da yara suke tafe shine abin zaifi burge mutane ai ba a tafi uwar duniya a dawo haka babu ko kwai ba.
Nuriya ta fada tana wani irin dariyan shu,umanci a fuskanta wanan kuma sai idan da Allah kike jayayya don shine mai bada haihuwa lokacin da yaso kuma a inda yaga dama.
Zainab tashi muje ya J ya fada yana mikewa fuskan shi a daure da sauri ya mamud yace ku tafi ina yanzu kuna shigowa zaku tafi kuma.
Dole mu tafi don ba zan lamunci cin fuska irin haka ga iyalina ba ga kowa duk wanda yace zai taba min mata kamar ni ya taba don haka ba zan dauki wanan ba.
Kayiwa matan ka iyaka kan sake zancen daya shafeni idan ma haihuwan takewa zainab gori dashi ai ba zainab bane mai laifi don nine raggon namijin dana kasa bata cikin ta haifa.
Falon yayi tsit a lokacin kamar babu kowa a cikin sa sai Nuriyan ne tayi karfin halin fadin yo ni ai da wasa kuma naga dacewan hakan na fada don yaci ace yanzu kun fara aje iyali ai.
Kai wanan halin baiyi ba wallahi kamar kuna jirace da yarinyar nan tazo ku gasa mata magana haka.
Duk da dai mami ke kika fara bada hanyar yin hakan sai dai ku sani a yanzu kuna falon kaf banda mami babu wace ta kama kafar zainanb ko mijin da komai da har zaku tare ta da wanan zancen haka.
Kema mai haihuwan aiba rawa ko kida kikayi gaban Allah ba ya baki su da kika tareta da wanan zancen mara dadin ji jamal ya fada yana jan tsuki ya bar falon a fusace.
Nuriya ke nan yanzu dai kinji idan ma dama kina jiran inxo ki gasa min wanan maganan ne haka daga shigowa na kamar kina jirace dani.
Na fada a daidai lokacin dana mike tsaye sadiya ma ta mike tana manne dani kamar taga abin tsoro a falon.
Gaskiya haka baiyi ba Nuriya at,list ai kya bari ta huta kafin ma ki fadi abinda ke ranki ai Aisha ta fada.
Ballwma ko an raina dan tsuntsu ba acin shi da gashi don anyi sake dan zaki ya girma ko gaskiyar jamal ne Nuriya zainab dai ba abin yarwa bane yanzu don muje ta muna goma na arziki gaba dayan mu nan Na,ima ta fada tana mikewa.
Saida safe mami na fada ina bin bayan ya j din daya fara tafiya a lokacin kafin na juyo ina fadin ga tsaraba nan mami da muka zo dashi ayi hakkuri dashi ba yawa.
Na sa kai nabi bayan shi ins jin ya mamud na fadin kin gani mami saida nace kada kiyi wanan zancen a gaban su tunda ya fadi uzurin shi kika yi a gaban wanan mara hankali da tunane.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.