Complete Hausa Novels

Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel

Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 111 of 139

ZAINAB IDRIS MAKAWA

HASBUNALLAHU WANI IMAL, WAKIL YA HAIYU YA KAIYUMU BIN RAHAMATIKA YA ASTAGIS , , , ,

LITTAFIN NAN NA KUDINE YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DA SAUKIN FAHINTA BA TARE DA DAUKAN HAKKIN KOWA BA A KAN KI YAR UWA, , , , ,
DON KIRA 08036959257 KO 09026931792 ACCOUNT ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK, , , , , , ,

Kwana biyar rabon mu da gidan mami har ranan ya J bai leka gidan ba tun mami na boye zafin hakan da take ji har ya kai ranan ta zauna a falo suna magana da yaranta ta sako zancen rashin zuwan shi gidan da baiyi ba.
Kowa yai shiru a falon sai jamal ne ya bata amsa ba tare da ya dago kaiba yake fadin mami ya zaizo kuna masu cin fuska irin haka ko waye ma ai dole yaji zafin hakan.
Shike nan kada a fadi gaskiya don kawai ya dauki yarinyar tafi kowa ko me zaice tayi laifi kada a fada.
Harni zainab zata ce saita huta zata zo gaidani da ace matsiyatan mahaifan ta ne garin nan har zata kwana uku bata gansu ba ?
Haba haba mami wanan abin fa ke batawa ya j rai daku ko ya iyayyen zee suke ai yanzu an zama daya dasu mami jalal ya fada.
Ji wani maganan banza da wa suka zama daya wa yan nan kaskantattun mutanen Aisha ta fada tana wani kauda kai.
Ke ni kike fadawa maganan banza haka ku mi shiru mami ta fasa a hasale tana zarewa kowan su idanu lokaci guda.
A daidai lokacin ya mamud ya shigo falon ganin yadda ya samesu kowa ranshi a bace yake fadi tun kan ya zauna.
Ba wanda ya bashi amsa sai ya juya wurin mami yana fadin mami mai ya faru kuma na ganku rai a bace ?
Barsu da batun banza kasan su jamal da jalal kamar wa yanda yarinyar nan zainab ta asirice su basu son ayi zancen ta ko kadan.
Zancen me kuma mami ina dai anyi wanan zancen ya tafi waya tayar da maganan kuma yanzu ?
Nice na tayar kan zancen rashin zuwan shi gidan nan yau kwana biyar ke nan da yin wanan zancen bai leko ba.
Zaizo mana mami abinda akai masu ne ba a kyauta ba idan ke kin fada masu ita wanan mara hankalin ina ruwanta da rashin haihuwan su har yanzu ?
Ko ita din da take haihuwan yaushe ta iya kula da yaran da har take fadawa wani bai haihu ba ?
Ta samu wurine a wurin mami don taga mami ta saka yar mutane a gaba akan danta yasa itama ta fadi hakana jalal ya fada .
Ya salam yaran nan me kuke son mayar dani ne yanzu bari kuje dukkan ku rayukan ku zai baci dani wallahi kan wanan zancen.
Kiyi hakkuri mami ya mamud ya fada yana kaiwa zaune kafin yace barin gwada kiran jafar din yanzu muji in lafiya yake don na kirashi yake ce min yana wani aikine.
Ya kira shi saidai bai dauki wayan ba har ya katse ya kara kiranshi wayan ya nuna yana busy.
Yace kin gani duk na kira busy yake saka min harni fushin ya shafeni ke nan ya fada yana kallon uwar tasu.
Yayi fushi mana indai don kan yarinyar nan ne zainab mai shegen bakin wayau su na yan kauye yarinya kwarkwar da shegen bakin wayau zanyi maganin ta ai don ba zan yarda ya kara barin kasan nan ba tare da kara aure ba.
Da sauri duk wanda ke falon ya dago kai yana kallon ta don jin abinda ta fada din .
Kai haba mami kada ki soma wanan abin don zai zama tonun asiri a garemu baki daya tunda kinga ko zainab din dai hakkuri takeyi dashi ai.
Hakkurin me mamud kune baku gane wanan yarinyar ba tun farko ni yanzu na dawo daga rakiyan ta ai.
Tunda na gane me take hadawa kan dan uwan ku idan da baida amfani a gareta zata zauna dashi tsawon wanan shekarun hakane ?
Tunda ta kasa shawo kanshi ai gara a auro wace zata zama silar barin komai nasa zaifi ta fada tana kawar da kai gefe daya a hasale.
Wanan shawaran naki baiyi ba mami sam wallahi don ya j din ba zai taba yarda da hakan bama wallahi .
Ke dai ki barshi a yadda ya zabawa kanshi illa dai a tayashi da addua shine abin yi a yanzu don wallahi tonawa kai asiri kawai za ayi ga hakan.
Ya mamud na shiru jamal ya dauka yace kai mami ina kika samu wanan shawaran kuma yanzu ?
Ya fada yana kallon ta yace kindai san waye ya jafar ai kin kuma san haiinsa idan zainab ta zauna ta rufa maku asiri duniya bata jiku ba wanan da zaki aura masa itace zata zama silar tona maku asiri a duniya .
Wai kanshine farau wanan halin idan na kara masa aure ai ita yarinyar da zan aura masa ba wata bace ta daban a cikin yan uwa zan aura masa wace ta waye ta san kanta har ta taimaka masa ya daina wanan halin da ake masa zaton yana yi.
Au mami yanzu baki yarda yana komai ba ke nan ya jamal ya tambaya cikin mamakin jin abinda mahaifiyar tasu ta fada.
Idan ma yanayi sai ka dauki laspeaker kayi shela zai fi ma sauki idan da har na yarda da zancen ku yanxu ban yarda da hakan ba.
Lalai mami akwai abinda ke damun ki ya mamud ya fada tare da fadin ke da kanki ba wani ya fada maki wanan abinba duk da mun san da haka amma ke kika gani fa da idanuwan ki.
Nayi da kai na gansa a wani halin a lokacin ko wani ya fada ma hakan cewa yaga yana aikata wanan abin .
In ma har zargi ake masa a bari ya kara auren sai mu tabbatar da hakan daga bakin wata ba a bakin wanan yar sherin yarinyar ba zainab.
Duk shiru sukayi sai can Aisha da har lokacin bata sanda zancen ba tace wai ma har me yake aikatawa haka mai muni da ake ta wanan zancen wai ?
Iyaka dai zainab tace yana neman mata ko ba a nema ita aka nemeta ne wai da ake wani tarewa kada a kara masa aure .
Waya gane me take samu ina gidan su da yan uwanta kawai take aikawa inba wanan karon data kawo muna wanan tsaraban ba haka ?
Ya jamal daya mike ya watsa mata wani irin harara daga inda yake kafin ya juya ya fice falon suka bishi da kallo cikin mamaki.

Yana zaune dan falon dake part din shi saidai wanan karon ba komai yake yi ba zama yayi kamar mai tunanen wani abu a zuciyan shi.
Kafin wayan shi dake gefe ya dauki kara ya kalli wayan saida ba sunan mai kiran nasa wanda hakan ya bashi mamaki waye zai kirashi da bakon lanba ne ?
Ya raya a ranshi yayan shi mamud ne ya canza layi don kin daga mai kira da yakeyi a kwanan kin nan.
Ya dai daure ya daga kiran ba tare da yin magana ba muryan jalal yaji a wayan yana gaidashi ya amsa yake fadin bros kwana biyu gashi har yau mami tana zancen ka.
Ya J rashin zuwan ka yasa mami tana shirin karayi ma aure don ta dauka laifin zainab ne hakan .
Wani murmushi ya sake a fuskan shi yana fadin aure fa jalal ita mami din ta fadi hakan yace wallahi yau take fadin hakan a gaban kowa dake falon .
Nan dai ya kwashe komai ya fada mai a cikin bacin rai har yana fadin ni bansan meyasa mami take kin zainab dinka ba yaya ga Nuriya da take mata iskanci amma bata ganin hakan.
Kada ka damu jalal ta dai fadi hakan ne kawai amma tasan ai banda ra,ayin mata biyu a rayuwana.
Bai tsaya jin ta kanin nasa dake fadin kada ka bari ta san ni na fadama don tayi warning din mu kada wanda ya sanar ma da hakan.
Ya kashe wayan ya mike tsaye cikin hasala zuwa dakin shi don ya watsawa jikin shi ruwa kafin nan ya fito.
Ya fito ya samu miscal har uku a ciki hardana jalal din daya kara kiranshi sai na ya mamud bai kira kowa a cikin su ba don yasan zance dayane dai suke kiranshi a kai.
Fitowan shi yayi daidai da shigowan ya mamud gidan muna gaisawa sai gashi taro na musanman aka hadawa yaya din a babban falon gidan da akayi don karban baki maza.
Sun gaisa yake tambayan shi ko lafiya kwana biyu bai shigo ba yake fadin lafiya kalau yake yana hutu ne a gida kawai.
Kana ganin rashin shigan ka gida wurin mami hakan da kayi shine mafita a gareka yanzu.
Dan murmushi ya sake tare da fadin mamud ya kake son nayi da mami meye laifin yarinyar nan zainab mamud ?
Idan mami bata godewa zainab ba ba kuwa zata hattare ta ba haka tana kokarin maida mun mata abin tsana a gareta.
Shima mamud din dan murmushi ya sake ma dan uwan nasa yana fadin duk mun san da hakan mun fadawa mami din komai.
Amma ta nuna ba hakan ba ni yanzu hukuncin da take son dauka a kanku don kawai maganan wanan mara hankalin Nuriya da mami ta hau shine matsalan dake shirin kunno muna kai a yanzu.
Wani matsala ke nan ya tambaya kamar bai san komai ba a kai sai mamud din ya dan dukar da kai kasa yana fadi a sanyaye mun dai fada mata zatayi kuskure idan tayi hakan don zai shafi gaba dayan mu gaskiya.
Duk zancen da sukeyi a kunnen fadila sukeyin shi kafin J din yace dashi ku barta duk wance zata aura min taje ta aura zata gane true colour dina lokacin.
Dan kallon fargaban jin abinda ya fada da fadila tayi mai yasa shi fadin fadila live dis place please.
Da sauri ta mike daga zuba ruwan juice din da takewa ya mamud ta koma ciki da sauri cike da biyayya a gareshi don bin umurnin shi.
Hakan baisa ya je gun mami din ba saida aka dauki kwanaki ya tafi bai wani tsaya ba suna gaisawa ya juya ya fito fuska a daure.
Nikan a lokacin ba abinda nakeyi sai sha hakkuri don mu samu ya sallameni zuwa gida gashi a bangaren fadila gulman abinda taji yana cin ta don a gaskiya duk da tana aiki akan shi ne hakan bai hanata sona a cikin ranta ba duk da ta kulla da ina ja baya da zancen ta a yanzu don ba kamar da muke ba sai mu zauna ba wani zance mai tsawo kamar yadda muka saba a baya da ita.
Satin mu biyu da zuwa Nigeria sai ga wayan sa,adatu take fadin ai gata ta hanya zuwa wurun mu inna ta aiko ta ta duba lafiyan mu.
Sam banji dadin hakan ba duk da hakan yana cikin karamawan iyayye a gare mu don asan mu din muna da gata yin hakan kamar al,adane na malam ba haushe.
Don inna tayi tayi da Abba a samu wanda zaizo ya dubamu da saukan mu amma sai Abba din ya hau fada kan hakan dole inna taja bakin ta tayi shiru.
Shine karshe suka yanke shawara a daki da yaranta kan sa,adatu ce zata zo Abuja ta dubamu da dan tsaraban da inna din ta hada muna kamar su dambun nama datayi mai yawa sai man shanu da kwai da dubula.
Duk a gidan malam mijin mai zube inna ta bada kudi aka hada komai a can da tare zasu zo da maizube din sai aka tashi ranan da zasu zo din wani a cikin yan uwan maizube din ya fadi ya rasu da asuba.
Shine dalilin da sa,adatu ta biyo hanya ita kadai duk da bata taba zuwa Abuja ko wani wuri mai nisa irin hakan ba sai wanan ranan.
Jin haka yasa na bugawa yaya waya ina sheda mai zancen zuwan sa,adatu din dake hanya tafe shima yayi mamakin hakan yake tambaya tana ina yanzu nace tace sun kusa shigowa gari don motan safe ta biyo zuwa Abuja din.
Bai dawo gidan ba sai tare da ita sukaje tssha aka dauko ta niki niki da robobi tsaraban da tazo muna dashi din.
Munyi murnan ganin juna da yar uwan mu har mun manta da duk wanda ke wajen a lokacin yadda muka makalewa juna don daukin ganin .
Sai cewa ya j yayi kuyi a hankali kada ku kayar min da matana don Allah duk aka kwashe da dariya a wurin yadda mukeyi saida ya ba kowa sha,awa don hakan na nuna akwai shakuwa da kaunan juna a gare mu.
Daki muka shiga bayan gama murna sai mamakin yadda muka canza take yi har ta kasa boye hakan.
Fadilace ta kawo mata abinci har dakin don gaskiya ina gani kokarinta wuri kaskantar da kai da takeyi don aikin ta wurin boye ko ita waye gare mu ta nuna aikin da ya kawota garemu shine takeyi a gidan.
Yau dai naga sa,adatun nan da nake yawan jin labarin ta gun ku ta fada tana aje turen abincin a gaban mu nace ga anty fadila sa,adatu.
Ta juyo tana fadin ayo itace ashe gaskiya yayan mu tana yawan ban labarin ki anty sannu da dawainiya an gode fa.
Ni kaina naji dadin hakan da sa,adatun ta fadawa anty din sai na karbe da fadin wallahi sa,adatu ko ya j yana fadin banda kamar anty a rayuwana shi kanshi yafi yarda da ita sama da kowa a rayuwan shi.
Yana daukan ta tankar yar uwa a garemu yanzu don ya wuce zaman aiki a tsakanin mu sai zumunci da rufawa juna asiri a yanzu don shi yanzu bai san abinda zai saka mata dashi ba.
Wani irin yanayi ta nuna a fuskanta lokacin da nake fadin hakan ta dan sake dariyan yake kawai tana dagawa a sanyayye ta bar gurin.
Tana fita na bita da kallo a fakaice kafin muryan sa,adatu ya dawo dani daga kallon fadila din tana fadin .
Anty wanan gidan naku kamar a turai mutum yake ni ai ban gama kallo ba don kawai kada na bar abin kunya na shigo.
Ki gama mu fita sadiya ta fada da take kwance rub da ciki tana jagulan wayan sa,adatu din dake hannun ta tana dubawa.
Munyi hira sosai ranan a daki muka wuni sai bayan la,asar yaya Jafar ya shigo dakin ya same mu zaune mun baje tana muna hiran Asabe da Lantana na fafatawan da ake tsakanin su yanzu.
Sai dariya muke kwasa ina kwance a gurin dana sallame sallah ita kuma sa,adatu tana saman rogh din dake tsakiyan dakin sadiya na saman gado kwance.
Gaida shi sa,adatun keyi ya amsa tare da karasa shigowa dakin ya nufi bakin gado ya zauna yana tambayan ta mutanen gida ?
Tace duk suna gaida shi su inna sunce ai masu godiya kafin su hadu na alherin daya aika masu shekaran jiya dashi .
Dago kai nayi da sauri na dan kalleshi bai nuna komai ba yi yayi kamar bai ganni ba ma na kallon da nake masa.
Yanzu karatun ki yayi nisa ko ya tambaye ta tace insha Allah muna two hundred level ke nan yace ashe kun fara nisa sosai .
To ya zancen ku da baba yanzu dai ya amince ki karasa karatun naki kafin zancen auren naki ko mu tsaya mu sha buki kafim mu koma ne ?
Ya tambayeta a cikin zolaya tace Abba ai case ne wallahi ni ba do kai ba yaya ai ba zai yarda naci gaba da karatuna ba a yadda ya dage din nan .
Yanzu ko shiru baya zancen ma sam idan ba nayi masa wani laifi ba kuma a kan lantana ce dake zugashi zakaji yace yar abu kaza aure zan maki in huta ai.
Ya kwashe da dariya zakace ba ya j bane ya sake haka a gabanta yana kwasan dariya nice na katse su da fadin ga sako nan inna ta aiko ma dashi ina nuna masa kayan da tazo dasu din.
Abinka da wanda bai saba da hakan ba ya dago kai yana fadin wanan meye haka da yawa aka aiko muna kuma ?
Sadiya ce ta sauko saman gadon da take ta fara bude mai roban dake cike da dambun nama kafin ta koma gana kwai dana man shanu .
Yake fadin kai wanan duk namune haka amma inna tayi dawainiya da yawa gaskiya.
Ai kaima kana dawai niya dasu sosai har su rasa bakin godiya sa,adatu ta fada yake tambayan sadiya cikin basarwa wanan din da kika bude da farko meye shi sady ?
Tace barin debo ma kaci kaji dambu ne na nama aka soya yace a hakan na tuna mami idan tazo ana kawo muna shi muci muna US.
Ta debo mai a lokaci nace sai a dibarwa su mami a kai masu don wanan dai yayi muna yawa kan a nan.
Bai ban amsa ba sai diba da yayi ya fara ci wanda hakannda yayi yai muna dadi sai godiya yake daids ya danci sosai muna hiran mu da sa,adatu bai ce komai ya mike yana fadin zaki kwana biyu a nan ke nan ko ?
Eh to kwana biyu din innan mu tace nayi na koma kada Abban mu yayi fada idan na dade yace ba zai yi fada ba ai a wuri mu kike ba wani wuri ba.
Mu yaushe zamu tafi ina tare zamu koma da ita idan zamu tafi na tambaya yayi kamar bai ji me nake fadi ba yasa kai ya fita.
Wai mu ba zamu gida bane yayan mu sadiya ta tambaye ni nace sadiya ban san me yake nufi da tafiyan mu ba har yanzu sai ja muna rai yake yi.
Kai wai meye a zuwa gidan da kuka matsa dayine ina dai dole ku tafi kafin ku koma ai .
Ki bari kawai sa,adatu bafa komai muke mashi a nan din ba kawai kuntatawa iri na mazane kawai.
Anty a gaskiya kinyi dacen mijin aure ga hankali ga natsuwa gashi da son yan uwanki kamar nasa kowa yana fadin hakan gaskiya ki godewa Allah da wanan rufin asirin da yai maki ke kan.
Wani iri naji a raina sa,adatu ke nan ke fadin haka ina ga iyayyen mu da ya riga ya saye nasan akwai aiki a gabana kan abinda nake kokarin shiryawa nan gaba ke nan.
Don su ba zasu gane ABU A CIKIN DUHU SIRI NE BA ni kadai nasan irin rayuwan da nake yi da ya jafar din don ko sadiya dake zaune damu nasan kirkin shi zata fada a gida idan hakan ya taso .

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.