Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel
Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 58 of 139
Jafar da tun safe hankalin shi na ga ya sake kiran Fadila yaji ya jikin nawa saidai kuma aiki yai masa yawa yau din sai dare ya samu kansa yana hutawa a gidan sa.
Wayan shi dake gefene ya dauki kara ya dan dago yana kallin wayan da mamaki don gani mamice ke kiran shi a lokacin.
Duk da yasan a can Nigeria yanzu akwai sauran lokaci dare bai wani yi ba a can ya dauki wayan kafin kiran ya katse mai.
Da sallama a bakin shi ya daga wayan tare da mika mata gaisuwa a cikin girmamawa kagin ta furta dalilin kiran nata garshi.
Ba tare data amsa mashi ba take fadin Jafar wai me kake son mayar da kanka a cikin kune ?
Duban wayan dake hannun shi yayi cike da mamaki kalamin mami din yana fadin mami nayi wani laifi ne yanzu kuma ?
Au baka ma san da kayi min ba daidai ba ke nan ashe har yanzu kana nan da zancen yarinyar nan zainab har wata can wai kanwarta tana kokarin cusa kanta gun yaran nan a school din su.
To kayi gagawan yiwa zainab da duk wani nata iyaka da zuri,ata a garin nan tunkan ranku gaba daya ya gama baci gareni.
Jafar din ya kasa gane me mami take fada don haka ya natsu da kyau yana gyara zaman shi do n kara fahinrar inda zancen nata ya dosa dashi.
Idan kana son kanka da lafiya na fada ma ka sallami yarinyar nan zainab tun kan raina ya gama baci dakai a gidan nan.
What mami ya fada dan jin abinda ta fada a kan zainab din wace ke matsayin mata a gareshi duk da yasan auren bawai wani abu ya daukeshi ba shima.
Yace mami amma kinsan akwai aure ai a tsakanin mu dan haka babu zancen saki a tare damu mami kinsan da hakan.
Jafar ni kake fadawa akwai aure a tsakanin ku in yarda tunda nasan baka fito ta inda ya kamata ace zan yarda da hakan ba.
Kamar yadda na aurar da dan uwanka a inda nake so haka kaima nake da burin maka aure na gata kowa ya san da zancen.
Bazan taba amincewa da wanan aure naka ba na fadama gata da daraja kamar ko wani da zan ma a kasan nan ban yarda da auren da zaka sa mutane su kalle da ban san komai ba.
To wallahi kaji na fadama koda wasa na kara jin zancen wanan yarinyar ya fito a bakin ka gabana saina bata maka rai fiye da yadda bakai tsamani ba.
Dan haka na gargade ka da ka ja mata kunne akan yayan gida dan karsu kara nuna sun sansu ko a ina ne kuwa.
Jafar din dake jin zancen mami din kamar al,amara dan ya shiryawa hakan ko wani lokaci yace.
Mami za a kiyayye ba zasu kara shiga harkan diyan ki ba ko jikokin ki insha Allahu zan tsawara masu kan hakan.
Har ta gama fadan ta sai hakkuri yake bata ranshi idan yai dubu ya gama baci da hakan don shi sam baiga abin fadan mami ba a nan.
Aikin da baiyi ba ke nan dan gaba daya ranshi ya gama baci da zancen mami din a hankali idanun shi suka soma sauya launi.
Ya dinga jin zuciyar tana masa radadi da zogi ya mike zaune game da dafe kanshi tare da sake wani irin huci mai zafi lokaci guda.
Ba shakka har idan ya yarda da abinda mami din su keso a gare shi komai zai iya faruwa dashi a karshe.
Don haka ya zama wajibi garshi ya jawa zainab kunne kan duk wani abinda ya shafi mami dawani nata .
Saidai kuma ta yaya zaiga laifi zainab di bayan tana gida kwance bata da lafiya a inama ta fita har taga wani da mami ke wanan maganan haka wai.
Shi a rayuwan shi ya rasa gane dalilin wanan kiyayyan da mami takewa wanan yarinyar da bata san komai ba a game dashi.
Idan ma taimako ne ai ita zainab din ta taimaka amma son zuciya ya rufewa mami din ido ta kasa gane hakan ta ko ina saboda wani dalili nata can na daban.
Ba shakka son zuciyar mami din yayi yawa ga wanan magana data kasa hakkura da jerabawan ubangiji a gare shi .
Don haka ya zama dole ya nunawa duniya yarinyar nan tana zaman matar shine da kowa ya kamata ya sanda hakan yanzu .
Ba zai damu da wani ra,ayi ko son kai da mami ke shirin nunawa ba a nan don sam yarinyar bata da laifi asalima ai laifin nasa ne gaba daya bana yar mutane da ya jefa a tsaka mai wuya ba.
Duk da yasan da ita kanta zainan din idan hankalinta yazo ta mallaki hankalin kanta akwai kalubali mai yawa a gaban shi.
Wanda yasan kafin lokacin zai iya magace komai a tare dashi da duniya ba zata zargeshi ba kan hakan.
Wanan wani damane ya samu da zaiyi amfani dashi don kawai ya fitar da kanshi daga wani tarko da mami ke shirin dana mai wanda zai dawo ya damesu gaba daya.
Da kyat ya tashi ya iya kulle kofan shi do baya bukatan kowa ya dameshi a wanan lokacin yana da bukatan ya kebe kanshi shi kadai ko zai samu natsuwa a wana lokacin.
Zazzabi mai zafine ya rufe shi a wanan lokaci tare da dumbin damuwa a zuciyar shi tabbas da mami tasan koshi waye ba zata tsaya tana fada akan shi ba.
Da mami ita kanta ba zata yarda ya auri yarta da ta dauko amana ya gani a gaban ta har yaga dacewan ta da wanan dama nasa ba ya kulla alakan aure da ita.
Wani iri yake jin kanshi a lokaci daya ga azaben ciwon kai dake damun sa ga matsanacin kasala gaba daya ya rufe shi a lokaci guda sai yake jin duk zaman garin ma ya fita mai a rai tankar ana hura masa wuta a jikin shi.
Wani irin nadama da dana sanin biyewa abokai na kurciya ya kamashi a lokaci daya a haka har gari ya waye mai duk da bugun kofan da yake ji ana masa baisa ya bude kofan nasa ba a lokacin.
Kwana biyu ya dauka a gida bai fita ba don yanayin jikin nasa da yake ji wanda ba komai ya haddasa masa hakan ba sai tsananin samuwa da halin da yake ciki.
Ya mamud ne da ya sha kiran shi a waya ana fada masa yana barci har yakai ga fahintar dan uwan nasa baida lafiya ya samu mami da zancen.
Da farko mami bata tayar da hankalin ta ba saida sukai waya da babban yaron shi yake fada mata yadda jikin ogan nasu ya tsananta a lokacin hankalinta ya tashi.
Da kyar ta samu aka sadasu a waya dashi take fadi a cikin tsigar lalashi jafar baka da lafiya baka kira gida ka fadi.
Yanayin yadda yake magana ya kara sa mami a cikin damuwa ta kara kwantar da murya gareshi tana fadin meke damun ka hakane friend ?
Mami kirji na da zuciyana kamar zasu fashe nake jin su ina jin zuciyana kamar an daure min shi gaba daya na rasa abinda yake damuna.
Mami tace kayi hakkuri ka daure kuje asibiti dukkan al,amari ubangiji yasan dashi ka daina saka aiki ko wani damuwa a zuciyar ka hakan nan.
A haka mami ta samu ta rarashi dan lelelen nata har dai yaji zuciyar shi yadan sausauta mashi daga irin kuncin da yake jin kansa a ciki lokaci guda.
A bangaren mu kuwa bamu san wainar da ake toyawa ba iyaka dai anty fadila ta kasa samun shi a waya.
Tun hakan yana damun ta har takai ga furta min cewa kwana biyu fa bata samun oga a waya idan ta kirasa.
A cikkn rashin ko in kula nake fadin anty isan ya damu ai shi da kansa zai kiramu yaji lafiyan mu wata kila aikine yai masa yawa.
Kai ta gyada min alaman a,a zainab raina yana ban ba lafiya dai sai dai duk abinda ake ciki zan barshi zuwa gobe ko jibi idan bai kiraba zan nemi abokin sa na nan muji ko lafiya yake a can.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.