Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel
Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 130 of 139
ZAINABASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAH JUMMA,AT MU BARAK YAN UWA MUSULMAI ALLAH YA SADAMU DA ALHERUN DAKE CIKIN WANAN RANAN AMIN, , , , ,
Bin yadda yake kwance a cikin wahala kowan su keyi jamal ke fadin yana numfashi kuwa ?
Yanayi ya mamud ya bashi amsa ai don zainan ma ta taimaka ta bashi wani magani dazun ya sha shine har yake hakan.
Da sauri mami ta juyo ta sauke kallon ta gareni tana fadin me kika bashi ya koma haka zainanb me kika shirya kike son ganin bayan shi a yanzu.
Wallahi idan wani abu ya samu dana bazan taba yafe maki ba kema sai naga bayan ki har iyayyen ki.
Kai haba mami wanan maganan bai dace ba haka dan Allah ba don yarinyar nan data take tsaye a kanshi ba ai bamu san halin da yake ciki ba.
Wa yasan hanlin da suka tsunci kan su zuwa wanan lokacin da badon ita data bashi wanan maganin ba dazun da wallahi kila da yanzu mun rashi ga baki daya har abada.
Itace tafi kusan dashi take zaune dashi tasan irin laluran shi a yanzu don haka ba zamu zargeta ba mami, kan halin da yake bayan duk munsan da abinda yake damun shi a nan.
Jamal ne ya fara fadin gashi kuma mami kai brother asibiti haka kamar tonon asirine a wurin ki a garin nan sai nake ganin kamar a samo yarddaden likita a dauko shi gida yazo ya dubashi a nan.
Nima haka nagani ya mamud ya fada daga gefe mami kan ta koma ta zauna saman kujera ta kurawa dan nata dake kwance a kasa cikin wani hali sai hawaye take sakewa a lokacin.
Bata iya furta komai a wanan lokacin don bakin ciki da takaici da yai mata yawa a zuciyar ta ina zata kai wanan abin kunyar da jafar ya dauko mata a cikin iyalin ta yanzu .
Kai kome zasu fada a kaishi asibiti kawai wallahi a dubashi a san halin da yake ciki zaifi jalal ya fada.
Nima dai abinda naga yafi ke nan Aisha ta sake fada daga inda take zaune a takure a lokacin na dago kai da sauri tare da fadin .
Don Allah kada ku kai shi asibiti a cikin wanan halin da yake ciki haka ku taimaka ku rufa mai asiri da akaishi asibiti gara dai likitan yazo gida ya duba shi don Allah.
Ya mutu kike so Aisha ta fada a hasale tana kallona kamar zata cinyeni danya a lokacin da take wanan maganan cikin kunan rai take tambaya na hakan .
Mami ta dagp kai tana fadin gaskiya zainab ta fada fitar dashi haka zuwa asibiti tonan asirine kamar yadda kuka fada da farko.
Don haka kai mamud wani likita kake ganin zamu nemo a wanan case din nasa yanzu har lokacin idon ta na kansa inda yake kwance tana kallon shi.
Ina gefe ina sauraren shawaran nasu kai mutum dai ba abakin komai yake ba lafiya itace jarin ga mutum da ya kumce ma ka rasa komai, komai arzikin ka kuwa.
Wani likita ya mamud din ya kira yace a bashi dan lokaci yana tafe duk zaman da nakeyi wurin bakina na dauke da addua a lokacin.
Tun ina yi a boye har na fara fitar da sauti ina karatun a fili duk suka bini da kallo kamar kullun amanal rasulu nake karanta mashi sai yasin haka ma wanan lokacin shinakeyi a hankali suna saurarona.
Dakin yayi tsit sai muryana dake tashi a lokacin can ya dan motsa hannun shi kadan alaman yana son ya falka a lokacin.
Gaba dayan mu ido muka zuba mai kafin can ya bude idanun shi da kyat yana fadin zainab bani ruwa in sha don Allah ba wanda zai gane me yake fadi a lokacin don muryan shi daya dakushe bai fita sosai.
Na dago kai na dan kalli ya mamud dake kusa damu ina fadin wai ruwa yake son sha.
Bashi wanan can da kika rufe dazun ya sha tunda a kwai sauki sosai daya sha shi dazun na tashi a daidai lokacin da mami ke fadin ruwan meye wanan din sauran kuma duk suka bini da idanu har na dauko ruwan dake rufe a gefen gado cikin cup din glass.
Na kawo mai tare da dan kiran sunan shi ina fadin yaya ga ruwan ya bude idanun shi da kyat ya sauke a kaina.
Dan yun kurawa yayi don ya sha ruwan dake hannuna ya kafa kai yaja sosai kafin kuma ya dakata na dan lokaci ya dago kai ya kalleni.
Muryan ya mamud din ne yake fadin shanye mana jafar don Allah yana da amfani a gareka sosai.
Ya dan daga kai ya kalli inda ya mamud din yake kafin ya mayar da kanshi ga kallon dakin ga baki daya sai a lokacin yasan a kasa saman ties yake kwance don neman wa jikin sanyi a lokacin.
Muryan mami da yaji tana fadin kasha maganin mana jafar ka tsaya kana kallo kuma da sauri ya juya inda take tana zaune tana magana saman kujeran dakin nasa.
Sannun da yan uwan ke masa ne ya kara juyawa wurin su yana kallon su kamar bai ganesu ba a lokacin.
Karbi ruwan kasha yaya na fada daga inda nake tsungune ina bashi ruwan da zai sha ya juyo a hankali ya karbi ruwan daga hannuna.
Tunda ya kafa kai bai cire a cup din ba sai daya shanye ruwan ga baki daya ya miko min cup din na karba daga hannun shi.
Ki kamani in koma saman gado ya fada a hankali don haka sai na aje cup din sa sauri har yana faduwa kasa .
Ban damu da hakan ba nayi saurin kai hannu ina kamashi ya mike a hankali muke tafiya har zuwa bakin gadon ya dan zaunan kannen nasa suka kara mashi sannu ya amsa da kai kawai.
Har saida ya kwanta sannan na dago ina sauke ajiyan zuciya ya jamal dake tsaye ya tokare jikin shi da mirrow dakin yace dani sannu zainab da kokari.
Nayi dan murmushi na juya inda na aje cup din na dauka tare da nufan kofan fita daga dakin kai tsaye.
Fitana daga daki yayi daidai da mikewan mami ta nufi bakin gadon da yake kwance ta zauna a gefen shi a hankali jin hakan yasa ya dan juyo kai ya dan kalli wurin.
Ganin mami ne ta zauna a kysa dashi yasa ya dan juyo gareta yana fadin yaushe kuka shigo mami ina barci ko na dan samu barci ke nan ashe.
Don jiya bamuyi barci da dadi ba dagani har zainab a wahalce muka kwana a gidan nan amma yanzu naji sauki sosao barci kawai nake ji da kasala ya fada yana gyara kwanciyan shi.
A falo na samu su fadila da sauran yan aikin gidan suna zaune a cikin jimamen meke faruwa ne sunga su mami sunzo rai bace.
Gashi kuma har lokacin basu ga na fito part din ba hjy tana ta aika sadiya a duba ko lafiya anace mata ban fito ba.
Suna ganin fitowa na fadila tare da mai aikin wanke wanke da shara su kayo kaina suna gaidani sauran ma suka biyo bayan su suna gaidani.
Na amsa ina wucewa har na dan taka nake fadin anty in ganki mana ta biyo bayana da sauri sauran ma suka watse a lokacin.
Tunda basu ga wani alaman komai a tare dani ba muna shiga dakina a tare tana bayana nake fadin ko za,a samu freash meat da milki a gasawa oga yau baya jin dadin jikin shi tun daren jiya.
Aiya da sauki ko ta tambaya nace yaji sauki yanzu sosai yana can tare da su mami da yan uwan shi don Allah a gasa mai idan za a samu a aika da wuri na fito da kudi ina mika mata.
Take fadin jiya an bada kudin da za ayi sayayya barin aika a ciki a sayo komai yanzu ta fada da sauri tana fita na dan bita da kallo.
Wanka na shiga don a matse nake a lokacin ina shiga na sakewa kaina ruwan zafi sosai don har saida naji ya kama min jiki na goga sabulu na fito .
A gurguje na shirya duk da barcin daya cika ni a lokacinn don har idona sun fara nauyi a lokacin don barcin da nake ji.
Saidai babu daman yin hakan gareni don su mami dake gidan a lokacin dole in koma in sallamesu kafin su tafi.
Saidai ina shiga dakin ban samu mami da Aisha har jalal a dakin ba sun fita zuwa dakin hjy su gaisa da ita .
Sai ya mamud da jamal tare da wani likitan da aka kira shi ya jafar din yana zaune ya dan jingina jikin shi da gado.
Ina shigowa suka dan kalloni sai na dan tsargu da hakan na daburce ina tambayan mami su har sun fitane ?
Ya mamud ke fadin sun shiga wurin hjy yanzun nan da likita ya shigo zai duba jafar din na dan juyo ina gaida likitan kafin na sake juyawa zan fita daga dakin.
Muryan ya makud ke fadin ki tsaya zainab ga maganin da likita ya bashi da lokacin da zaisha idan time yayi na dan dakata likitan yana yi min bayanin komai.
Na tsargu da irin kallon da yaya jafar din ke min yasa ban ko tsaya fahinta ba na juya na fice daga dakin, wanan halin da yaya jafar yake nuna min na kishi a gaban wasu.
Dakin hjy na nufa a nan na samesu zaune nake gaida hjyn da kwana bata amsa ba take fadin ke yar nan ashe abinda ke faruwa ke nan har wa yanda basu kwana a gidan ba sunji sunzo mu bamu sani ba.
Kiyi hakkuri hjy ban fito bane sai yanzu ya mamud ne ya kira ya fada masu bani bace na kira na fada a ladabce.
Yanzu ya jikin nasa da sauki ko nace yana ma zaune suna hira na fada sai ga fadila ta shigo tana fasin madam an gama komai kamar yadda kika ce ayi.
Na amsa da godiya ina fadin gani fitowa in duba mami ke fadin bari su leka ta ji me likitan ya fada game da jikin nasa ni dai kafin su fito na bar dakin kai tsaye.
Na samu sun shirya komai yadda ya dace na dan duba kafin na dauka na nufi dakin nasa dashi suna cikin dakin dukkan su a lokacin na samu likitan ya mike yana tsaye suna magana da mami na shigo dakin.
Kai tsaye na kai gaban shi na aje na dauko dan stole na dora akai ban kai ga mikewa ba mami ke fadin wanan meye kuma aka kawo mashi ?
Duk idanuwan su yana kan abincin na bude va tare dana bata amsa ba kamshine ya game dakin lokaci guda da tururin abincin yana tashi sama.
Gurfane nakai a gaban shi tare da dan dago kai ina fadin a zuba da yawa zakaci ko ya dan kada kanshi kadan ba tare dayayi magana ba na fara zuba mai a hankali saida ya dan kai yadda yake tunanen zai iya ci yace ya isa.
Good likitan ya fada yace wanan ya dace dashi a yanzu yadda yaji jikin nan dole sai irin wanan abincin dama normal milk danye na tsiyayya mai tare da ajewa gefe na mike tsaye duk suna kallon abinda nakeyi a lokacin.
Juyawa nayi zan fita yake fadin ina kuma zaki ki zauna muci don nasan kema baki karya ba har yanzu zan tafi in duba sadiyace ban gata ba tun dazun na bashi amsa na fita.
Gaskiya zainab tana da kokari wallahi tasan duk abinda ya kamata ba sai an fada mata ba jalal ya fada Aisha ta amsa da gadkiya kan .
Da gaskiya gun sadiya din zan tafi don duk abinda nakeyi hankalina yana gareta na rashin ganin ta da banyi ba din.
Tana kwance ta rufe jikinta wai sanyi take ji alaman dai bata da lafiya ke nan na karasa wurin ta hankali tashe.
Ina kware abi rufan tare da dan kiran sunan ta ina tambayan ta meya sameta ta nuna min kanta ke ciwo.
Fadila ce ta shigo dauke da abinci a ture take fadin dama yanzu nake fadin kila baki san bata da lafiya ba haka ashe kina nan ma.
Ta aje kayan tana fadin dama ina son in fada maki daren jiya bamuyi barci ba a gidan nan duk wanda ya kwana a gidan nan a jiya yaji tsoroa gidan nan da bamu san dalili ba.
Allah ya taimaka daga hira sadiya tayi barci a wurina nan muka kwana a dakina a tsorace sai kusan asuba muka daina jin tsoro .
Basar da zancen nayi ta fadin kai kodai iskan da kukaji anyi jiuan ne kuke jin kamar motsine anty tace wata kila ko hakan ne wallahi.
Nan dai muka zauna a tare mukayi break fast a daki mu uku muna hira wayana ne ke ringing a lokacin na dauka .
Malam ne kakana jin na ambaci sunan malam din yasa su kallona muna gaisawa na mike na fice a dakin .
Mun dade muna magana dashi yana ban labarin artabu shi da bakin shi a daren jiya din inda yai nssaran koran su fata fata ta yadda ba zasu kara tunkaranshi ba da yardan Allah.
Nan ya fada min wasu abubuwan da zanwa jafar din nayi mai godiya bayan munyi sallama na fito zuwa dakin hjy na samu tana sallah a lokacin.
Na juya na fita daga dakin fafila ke fada min su mami sun tafi ya mamud yace naje na duba jafar din da suka bari shi kadai a dakin shi.
Na shiga na samu ya dan mike zai watsa ruwa shigowana ya jiyo yana fadin wanka nake son inyi ko zan kara jin karfin jikin nawa a yanzu
Bari na gyaro ban dakim na fada ina kallon shi jikin shi yayi wani irin radau radau kamar yasha duka ko sunyi fada da wani a lokacin.
Bi jikin nasa da yaga inayi da kallo yasa ya dan juyo yana kallln jikin nasa yace wanan kike kallo aiba komai bane tunda sun barni da raina.
Ke nan su din ne suke baka wanan wahalan na tambaye shi ina kallon shi yace ya zasu dani tunda yanzu na daina duk wani abinda suke so na taka masu doka suke gani
Zaman lafiya shine kabi tsarain su da dokan su a zauna lafiya ko kinsan kwamciyan kinan a tare danine dalilin wanan azaban da nake sha a yanzu.
Na zargi hakan dama tunda naga wanan wahalan naka yayi yawa a yanzu idan har shiga dakin zai saka su dinga baka wahala haka zan daina shigowa yaya don su daina.
Kina tsoron hakan ne ya tambaye ni nace ba wai tsoro hakan nakeji ba tun farko yaya ka riga da kashiga kungiyan su yanzun ko ya zama dole a bisu a sannu don ka zauna lafiya dasu din .
Dan murmushi ya sake a fuskan shi tare da fadin koma me zasuyi min a yanzu sai dai suyi don na daina wanan harkan har abada ke nan insha Allah.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.