Complete Hausa Novels

Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel

Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 75 of 139

Yana zaune ya dafe kanshi da hannu daya kamar yadda ya saba idan yana cikin damuwa a hankali ya juya yana dan sauke ajiyan zuciya.
Ya zubawa desktop din dake gaban shi ido ya rasa gane me yasa ya kasa cire tunanen wanan yarinyar a zuciyar shi haka ?
A hankali kifa kansa saman hannun shi tabbas yana da yakinin yanzu ba tausayin zainab da kuma son ya taimake kamar yadda yai alkawari da farko bane.
Yana jin burbushin wani yanayi daba zai iya fassara ko me ye ba a zuciyar shi don yarinyar ta zame mashi kamar wani bangare na rayuwan shi a yanzu don yana jinta kamar ba zai iya rayuwa mai farin ciki ba idan yai nisa da ita.
Sai dai yana matukar tausayawa kansa da yarinyar domin kuwa yasan idan zasu tabbata a haka rayuwan su a cikin garari zai tabbata don ba zai iya tabukawa kansu komai ba a zaman su.
Kamar an tsikare shi ya dago a yadda yake da sauri yana fadi a fili idan ta gujeni fa don sanin koni waye a yanzu ?
Ko kuma ta kasa boye hakan a zuciyar ta har ta fadawa wani wanan maganan da yake siri a tsakanin su don yarintan da yake a kanta tayi kankanta rike wanan sirin a zuciyar ta yanzu.
Wayan shi ya zaro daga gaban aljihun yana kokarin kiran layina sai a lokacin ya tuna ai banda layin kasan nan da zai kirani dashi a yanzu.
Wani wawan tsuki ya sake tare da fadin Oh shit wanan wani irin wauta nayi da sakaci ai hakan sai na kara saka zargin wani a kan hakan .
Mikewa yayi tsaye lokaci guda yana shirin fita daga office din tare da tatara kanyan shi dake yashe saman table din.
Daga haka ya fito da sauri drivern shi daya hangoshi ya karaso inda yake don ya karbi yar jakkan dake hannun boss din nasa.
Mota ya shiga baya an bude Allah Allah yakeyi ya isa gida yayi mata warning kan zancen don ya fahinci ta dan warware da safe kafin ya fita.
A falo muke zaune muna hira dasu mama da suka shigo suna ban labarin sun hadu da wata yar kasan data dinga zuba masu yare a cikin masifa suna mayar mata da zagi da hausa.
Muna cikin dariyan hakan sai ganin shi mukayi a daidai lokacin ya shigo duk da ba a daidai lokacin yake dawowa gidan ba.
Idon shi a kaina daya shigo falon yana mamakin yadda ya sameni yau ina dariya don bai taba samuna a haka ba tun zama a gidan nasa.
A cikin daurewa da danne zuciyana na samu kaina da masa sannu da zuwa ina danne zuciyana don har lokacin ina mai jin kyaman shi don ina kallon a cikin yanayin dana ganshi a ranan.
Amsawa yayi a cikin basarwa kamar yadda ya saba yi ako yaushe yana kokarin shihewa muka samu muryan shi yana fadin ke zainab zo ki sameni a ciki daga haka ya shige zuwa part din sa.
Ina mamakin jin haka a raina na tsinkayi muryan mama tana fadin kai wanan yar da shirme kike har yanzu miji ya dawo baki tashi ki taresa irin na yan zamanin nan har sai ya bukaci hakan a gareki ?
Dan turo baki nayi a gaba ina nuna bazan iya hakan ba halimatu ta saka min dariya na juyo ina fadin mama zan mari wanan yarinyar fa idan bata daina ba.
Jeki zan mata fada mama ta fada itama tana kunshe dariyan ta dan wautan yarintar data gani a fili a gareni tare da fadin shi kuma jafar abinda ya sayawa kansa ke nan yanzu ?
A part din nasa na sameshi a falon shi tsaye yana sintiri kamar wani abu na damunsa a lokacin na shigo na sameshi a hakan.
Banyi magana ba ya juyo yana kallona na dan lokaci kafin yace me kike fadawa su mama ?
Ban fahinci tambayan ka ba na tambaya a hankali naji yace kin fada masu ke nan ko ?
Me na fada na sake tambayan shi cikin karfin hali ido ya tsura min kamar yana son fahintar wani abu a gareni kafin ya juya yana fadin shike nan ya fara tafiya.
Ai basai na fada masu ba inshine tunanen ka kai da kanka idan baka daina ba zaka sheda masu kokai waye watarana.
Wani irin juyowa yayi lokaci guda yana kallona ni babu fa,idan fadin wanan yanzu a bakina do abin kunyane a gareni don haka inama fatan Allah ya rabaka da wanan kazamin hali naka a yanzu yaya.
Daga haka na juya na fara tafiya na barshi a wutin cike da mamakina nima tafiya nake ina mai yaba karfin halina na yaba bajinta na haka a gareshi lokaci guda.
Ina fadi a fili ashe zan iya kamar yadda ya jamal ya gaya min saina cire tsoro a zuciyana na dasa mashi shakkana da tsoro a ransa.
Dakina na fada na mayar na rufe tare da fadawa saman gado ina runtse idona wasu hawayene suka silalo min lokaci guda.
A fili na furta yaya meyasa ka zabi wanan rayuwan a tsakanin rayuwan da zata zubar maka da darajan ka da kimarka a idona lokaci guda.
Me ake da dan giya a rayuwa gara in rufe ido in koyi tujara akan hakan tun yanzu don in samu makamin yakarshi akan wanan harkan.
Shima mamaki ne ya kasheshi a wurin wai haka yarinyar nan take dama koko yanzu ne ta fara hakan don ganina da tayi a cikin wani yanayin da bai dace ba.
Zanyiwa tufkan hanci tun kan raini da wullakanci ya shiga tsakanin mu nan gaba da ita don ba zan lamunci karamar yarinya ta rainani ba.
Zuciyar shice ta bashi amsa lokaci guda da fadin kai ka ja da baka yarda ta ganka a wanan halin na buguwa ba.
Ido ya runtse lokaci guda yana maijin zafin kansa akan hakan ya bude kofa ya shiga dakin ya bi da kallo lokaci guda.
Sai lokacin taju da yaima korar kare a ranan ya fado mai a zuciya don gashi yanzu yana son shi a kusa dashi ba halin hakan don yadda yake jin kansa yau ba zai iya daure hakan ba.
Kayan jikin shi ya dan tage ya shiga bandaki ya watsa ruwa a jiki shi ya fito sallah ya gabatar kafin ya fito don yaci wani abu a cikinsa don rabonshi da yaci abinci tun daren jiya daya dan sha wani ferfesun da suke sha wanda ke kara masu karfi a jiki.
Falon ya fito tare da danna kararawan kitchen don kiran daya daga cikin masu dafa abinci a gidan julie ce ta fito da sauri don tasan kiran maigidan ne a lokacin don shi kadai ke danna kararawan kiran su bakinshi basu taba kiransu haka ba.
Tazo ta dan duka cikin girmamawa tare da fadin can i help you sir ba tare daya dago kanshi yace ta kawo mai abinci yaci ta juya da sauri tana fadin an gama.
A daidai lokacin ne kuma na fito daga part dina zuwa falon wanan karon na sauya kayan jikina zuwa wando da riga masu kame jiki don fara gwada shawaran anty fadila dana yanke a raina.
Tafe nake kamar bansan yana falon ba zaune na nufi wurin tv ina kokarin kunnawa tun shigowana falon ya sauke idon shi a kaina.
Da sauri ya kawar da kanshi kamar wanda yaga wani abin tsoro a lokacin yana dan shafan kanshi don dan kwana biyun nan da yayi bai sha komai ba ko shakawa.
Yana jin kansa a wani irin yanayi na daban da ke sakasu a cikin wani hali har zuwa lokacin da julie din ta kawo mai abincin kanshi na duke a kasa yana shafa a hankali don yanayin da yake jin kansa a lokacin.
Tana ajewa take sanar mashi ya dago kai da jajayen idon shi da suka rine masa yakai kallon shi ga abincin .
Kiran ta yayi don har ta juya zata wuce ciki yace ta dawo ta bude abinda ta dafa din daga inda nake ina jiyosu nace ta tafi ta barni in bude mai na fada cikin dakewan zuciya.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.