Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel
Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 67 of 139
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ZAINAB IDRIS MAKAWA🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
5ï¸Â⃣6ï¸Â⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAR UWA UBANGIJI ALLAH YA KARA MUNA IMANI YASA MU CIKA DA KALMAN LA,ILLAHA ILLAH MUHAMMADAN RASULLILAH ALLAHUMA AMIN, , , ,
Hannuna ta rike na wani dan lokaci tare da sauke idanun ta gareni tana fadin ance mijin naki baya kasan nan ashe ya koma inda yake ke nan.
Ganin gani kusa da mami a inda take zaune har kamshin jikina yana dukan hancin su daga ita har Aishanta.
Yasa mami jin wani irin tsana na ya kamata tundai data dubu yabayina gaba daya na canzawa sanin da tayi min a baya can.
Hakan yasa ta mike dan barin dakin ga baki daya ranta kuma a bace da abinda idonta ya gane mata game dani din lokaci guda .
Don a kullun zata ganni sai taji tsana da take min yana kara karuwa a zuciyata duba ga yadda danta ya gyarani cikin dan kankanin lokaci kadan.
Ina kuma zaki hjy ta tambaya a cikin yanayi zafin ciwo har lokacin hannuta ya rike da nawa take fadin.
A zuba min abincin da zainabu ta kawo min inci tana rufe baki Aisha da kanta ke duke saman wayan ta tace kai amma hjy nan dazun nan fa aka gama fama dake kici abinci kika ki ci.
Yanzu kuma kice wai a zuba maki wanan da baki san ma komeye a cikin sa ba don gulma da iya yin ki na tsofi.
Uwarke ce gata gabana yar iyayi a zuba min abuncin gidan jikana in ci inace dazu da abinfa mamuda yakawo min na karya dashi.
Sam basu ji dadin wanan maganan tsohuwar ba a lokacin babu yadda zasuyi dole aka bude abincin a lokacin sai kamshi ya bude dakin lokaci guda.
Ya mamud ne ke fadin zako taci ko don wanan ganyen da akai amfani dashi don alaihu ne da anty zanci kaidai da albarka hjy ta fada a hankali.
Ina kallo don keta Aisha ta zubo mata da yawa tana wani toshe hancinta kamar maijin warin abincin a hancinta.
Da sauri anty fadila ke fadin kai ina zata iya cinye wanan abinci haka mai yawa ai saidai dan kadan yanzu tunda bata jin dadin jikin ta.
Ban iya bawa mutum abu kadan ba ta fada a dan hasale tare da nufar hjy da abincin bayan ta gama fadan bakar magana ga anty fadila din.
Da kyar hjy ta dan tashi zaune tare da taimakona a daidai lokscin da mami ta fake ga waya ta fice daga dakin ke ban.
Fitan ta yasamu sakewa don har ajiyan zuciya na dan sauke a hankali don naga ta fice daga dakin hankalina ya koma a kan tsohuwar dake jin jiki a lokacin karfin hali kawai takeyi a yadda take din.
Mun dade a zaune kafin mami su shigo tare da kawayen ta su uku dakin wani kallon banza suke bina dashi hakan yasa na kara shan jinin jikina sosai.
Sannu sukaiwa hjy din tare da fatan samun lafiya a gareta daga nan suka buge da hira wanda yai kama da haibaici a gareni.
Muryan hjy ne daga kwance take fadin kowa dai ya iya wanke allonsa sai bangon ya tsage kadangare ke samun wurin labewa.
Kai mutum bakai kayi kanka ba balle kayi wani shi dan mutum dama ba abin rainawa bane a duniya wata dan hakin nan daka raina wata rana yazo ya tsone ma ido.
Shiru dakin yayi na wani lokaci kafin dayar matar da tun dama na santa a gidan mami din ta fara mikewa tare da fadin babba Allah ya kawo sauki tare da aje mata kudi gefen gadon ta ta bar wurin.
Kusan duk haka sukayi suna ficewa daga dakin kafin mami ta mike tana bi bayan su a can waje suka tsaya suna gulmana .
Ba komai suke fada ba sai cewa da matar nan ta farkon fita da tayi daga dakin kai hjy wanan yar ko zaki iyata nan gaba ?
Sai dayan tace aini imani duk ya kasheni gani wanan yarinyar gaskiya hajiya danki yaki sauraren ki a kanta don gaskiya wanan yar matar manyace sak.
Ki duba lokaci guda yadda yarinya ta sake a baki daya kamar wata da wani a kasan nan ina ga ta kara nan gaba don ba iya nan zata tsaya ba.
Humm bari kedai hjy dada ni kaina abin yana ban mamaki sosai a raina canzawan wanan yar a cikin kankani lokaci haka kamar abin hadin baki.
Don yanzu ma baya ko saurarena akanta dana dauko mashi zancen zai nuna min baya so shifa matar shi yake so .
To ba,a barshi banza ba hjy ina kuwa zai saurara maki akanta yana ganin wanan a tare dashi ai ba zai saurare ki ba.
Ni ai yanzu matsalata hjyce don naso yi masu koran kare a asibitin nan sai dan bakin nan hayaniyar shi ya tayar da hjy daga barci da yau na nuna mata iyakana a wurin nan.
Kai da kin barsu dayan matar da batayi magana ba tun fara zancen gaba dayan su kallonta sukayi lokaci guda.
Taci gaba da fadin aurene dai ya riga da yayi shi don haka nidai naga kiyi hakkuri kawai ki bar yara nan su zauna lafiya a tsakanin su tunda kinsan halin wanan yarinyar tun farko.
Ki duba fa ita matar namuda fa bata gaida kowan mu ba har muka fito dakin nan yanzu ina laifin wanan din da har kasa ta gaidamu tunda tasan mu din yaya muke dake.
Amma dai hjy karima zancen nan naki baimun dadin ji ba wallahi akan me zaki wani ce ta barshi da matar sa wa zata nuna a matsayin mahaifin matar shi ranan da hakan ya taso.
Kai hjy saudat kina wani zance wallahi yaushe har haka zai taso din kowa fa da ubansa yake tunkaho komai lakacewan shi kuwa .
Nidai a wanan zancen hjy maryam hakkuri zan baki kiyi hakkuri ki zauna lafiya da yarinyar nan kada aje har girman ki yakai ga faduwa a wurinta wata rana don zuciya bata da kashi.
Daga haka ta fara takawa zuwa wurin motar ta inda driver ke jiranta su tafi ba tare da ta tsaya koda yin sallama dasu ba.
Muyi sallama dasu don ba fuska a garemu da zamu dauki lokaci a wurin su don haka muka fito don mu tafi bayan hjy din ta dan samu barci a lokacin.
Ashe da daren ranan batayi barci da dadi ba haka yasa washe gari ya jafar yanke shawaran zuwa Nigeria din don hankalinshi ya tashi da yadda ake fada mai ciwon nata.
Ban san da zuwan shi ba saidai nayi sa,a mun aika da breakfast da abincin rana asibitin duk da mami tayi magana da aka kai na safe din amma bamu fasa aikawa dashi ba.
Don ko washegarin da jikin nata ya rikice mun tafi asibitin mun duba jikin nata duk da mun sameta tana barci a lokacin.
Har muka fito kuma bata falka daga barcin ba sai ya mamud ne yace zai fada mata munzo idan ta tashi kuma ya fada mata din don da aka kai abincin dare take fadin tana gaidamu gobe akawo mata abinci da wuri don abincin gidan mu take iyaci nasu mami yana da yaji sosai.
Can cikin dare muke jin ana dokan kofa kusan tare muka fito lokaci guda da fadila saida ta tambaya yake fadin shine ta bude kofan.
Ta bude da sauri ya shigo muna mai sannu da zuwa ya karba muna yana kokatin shigewa part din shi yar jakkar hannun shi aka shigo mai dashi ciki na karba don in kai mai daki.
A tsaye na sameshi a dakin yana kokarin cire kayan jikin shi sama sama na gaiyar dashi na fito saida safe ne ya fice zuwa asibitin .
Ya dade a can har muka aika da abin karyawa kamar yadda muka saba bawa driver ya kai ko anty fadila taje da kanta.
A can aka sameshi tare da hjyn da sauran yan uwa da sukazo daga kaduna don duba jikin tsohuwar da suke jin ya matsa mata ana fama da ita yana son zai wuce da ita can a dubata taki yarda.
Wai ita tafi son a barta ta mutu a dakinta idan mutuwa ya tashi zo mata ana dai ta fama da ita taki yarda har lokacin da ya dawo gida don ya huta saboda gajiyan dake jikin shi din na tafiya.
Barci sosai yayi daya dawo sai yamma ya tashi don kansa tunda dai mu ba shiga part din mukeyi ba sai idan wani abu ya taso yake kaini part din nasa.
Har mun gama abinci da za a kai har fruit's salad mun hada mata ko zata sha duk wanan dabaran anty fadilace don kawai a burge mami dama wanda ke wurin lokacin.
Fitowan shi sai cewa yayi in shirya mu tafi asibitin a tare duk wanan yana cikin hikimarshi na kawar da idon mutane ne a kan mu.
Hakan bai zama min bako ba a wirina don nasan yakan yi mun hakan idan yana son fita tare dani wani lokaci kafin ya tafi.
Dakin makil yake da yayan hjy din da sukazo zasu kuma kwana a nan kashe gari su koma wurin su biyar ne mata sai maza ukku.
Ana faman hayani da dararaku kamar ba mara lafiya a dakin ya shigo ina biye a bayan shi fuska murtuk don halin daya samesu din a ciki.
Suna gaidashi yana amsawa sama sama bai tsaya ba sai bakin gadon da hjy take kwance mama Ramaru tana kusa da ita suna da magana.
Yake fadin hjy na fada maki ki yarda mu tafi a kaiki asibitin can a dubaki ki daina wanan wahala haka don Allah.
Budan bakinta sai cewa tayi bazan tafi ba sai idan da matarka zamu tafi nima wanan kafan yana damuna wallahi.
Dakin ne yayi tsit sai mami da tace aiko tare da Ramatu zaku tafi hjy tunda dai Ramatu tafita sanin komai ai .
Ta yaya zamuyi tafiya zuwa gidan shi matarshi na nan idan ba da ita zamu tafi ba saidai a fasa wanan tafiyan kuna abu kamar baku da lissafi a zuciyar ku.
In dai wanan ne ai mai sauki ne har in kin yarda din zaki tafi yaya mamud din ya fada yana dan dariya.
Ya juyo gareni yana fadin zainab ko ba zaki rakata ba tunda hankalinta yafi kwantawa da tafiya dake din can ?
Dan murmushin yake na sake a fuskana mami tace dama ai burin ta ke nan ita tunda iyakarta kaduna Abuja dama.
Yanzu ko abin nema ya samu ga ba saban ba ai sai tafiya hjy rigima kawai kike son dorawa mutane kan tafiyan nan.
Wani iri naji kamar hawaye zasu zubo min lokaci guda don yawan muzantanina gaban mutane da mami din ke mun .
A cikin dakewa na daure Allah ya taimakeni hawayen bai zubo min ba sai dan dukar da kai danayi kasa sauran mutanen dakin duk sun zubo min ido a kaina.
Ji nayi ya riko hannuna yana fadin mami yarki ai ta waye yanzu ba kaduna ba ko Abuja ba ko inama zata iya shiga yanzu ai ya fada yana kokarin rugumeni a jikin shi cikin rashin damuwa da duk wanda ke dakin a lokacin.
Kai jafar a gaban mu kake kokarin rugume matar ka don ka saba da dabi,un ku na turawa a can mama Ramatu ke fadin hakan tana mashi dakuwa.
Mama ai matatace ko ina ina iya rike abata wanan shike nuna irin son da nake mata ai kuma ku sheda koba haka ba besty na ?
Ya dan rugumo kafadata zuwa jikin shi yana dan murmushin da shine iya dariyan shi a hankali na lumshe idanuwana don irin abinda naji a lokaci guda.
Kada ka bata muna yarinya din nasan zainab na da kunya ita mama ko kin mata ita din matanane a yanzu ?
Kai jafar kaikan a Allah shirye ka yanzu kan sai a barka inda aka ganka wanan aure ya saka zama mara kunya yanzu.
Mama ai idan ban kulata kuma bakwa jin dadi don amana take garemu baki daya a wurin nan ai.
Ni kaina nayi mamakin yadda ya bushe idon shi haka a wanan lokaci yana zuba masu rashin mutunci mutumin da baya magana sai yaso hakan.
Yanzu dai kinji mamaku tace saida matana zatai tafiya don itama tasan amdanin ta gareni ai shike nan gobe za a fara shirin tafiyan mu a tare.
Amma sai naga kamar ku tafi kawai da Ramatu don ko anje da zainab din can me zata iya maku banda karin nauyi kuma.
Wata daga cikin matan tace ba haka hjy je so ba ai gara dai a tafi da ita din zaifi ko banza ai gidan mijin tane za a.
Ni dai ina daga tsaye ina jin irin shawaran da ake yankewa a kaina akan tafiyan da hjy tace ayi dani tare da ita.
Mami bar wanan zance don Allah tunda hjy ce ta zabi yin hakan ya mamud ya fada a dan hasale yana kawar da kanshi gefe daya dan baiji dadin yadda mami din take nuna min a gaban mutane ba.
Saida muka fito daga asibitin yana waya har lokacin da muka baro dakin wani kuka yazo min lokaci guda tun ina kokarin rike kukan ban san lokacin da yazo min ba da karfi.
A rude yake fadin subbahanallahi ke ke maye haka wani abin akai maki yanzu ko meye ki keyi kuma zaki tayarwa mutane da hankali a banza.
Ban sauraren shi ba illa sheshekan kukan da nakeyi wiwi kamar an aiko min da mutuwa don bacin rai.
Umurni ya bawa driver da karfi ya dakatar da motar har na bayan suka tashi dakan motar da muke cikin sa Allah dai ya gyara basu dake mu ba din.
Wai me ke faruwane haka kika tayarwa mutane da hankali haka da kukan banza kaina na nade cikin gyalen dana yafa a jikina sai sharban kuka nake babu kakautawa.
Shirune ya dan biyo a mitan bayan security din shi sunzo ya karesu ta yanyar dakatar dasu da hannun shi suka koma baya da sauri.
Can na dago kaina a hankaki tare da hade hannayena a wuri daya ina fadin don Allah yaya ka mayar dani wurin iyayyena don mami ba zata taba kauna naba muddin ina tare da kai.
Ke kanki daya kuwa kike fadin wanan maganan gareni yanzu zaman mami kike a yanzu ko nawa da tasoki ko kada ta so ki ai ba akarkashin ta kike ba .
Dan Allah rufe min baki kada na saba maki yanzu a wurin nan haka kawai dan shagwaba zaki saka mutane a gaba kina min kukan banza.
Dan Allah yaya kayi hakkuri ka mayar dani gaban iyayyena ba zan iya zama haka mami tana kina a kullun ba tsanar da mami take min yana min yawa a zuciyana.
Maimakon inga yayi fushi sai kawai naji ya dan rungumoni zuwa jikin shi yana rarashi a cikin tsigan da ake rarashin yaro idan yana shagwaba wa iyayyen shi.
Saida yaga nayi shiru ya ba driver umurni ya tayar da motan har muka kai gida ba wanda yai magana a cikin mu.
Mota na tsayawa nayi saurin kokarin budan motar ta gefen da nake zaune saidai motar tana rufe har lokacin ba,a bude ba.
Sai lokacin na dan juyo da fuskana zuwa duban shi a hankali da fuskana daya koma ja saboda kukan da nasha a lokacin abu ga faran mace take gaba daya fuskana duk ya sauya kalar ja lokaci guda.
Ban yarda mun hada ido dashi ba nayi kasa da kaina don nauyin shi da nake ji yadda ya zuba min ido yana kallona da yanayin dana kasa fassaran shi ko na tausayine ko kuma wani abu.
Ki share haayen ki ya fasa a hankali don kada su dauka anyi maki wani abune idan kika shiga masu haka kinsan halimatu nada wayau sosai zata iya gane kinyi kuka.
Dole badon naso ba na share fuskana da gyale na yana kallona har lokacin kafin yaba driver umurnin ya bude motar na fita a hankali shikan ko motsi baiyi ba alaman fita daga motar.
Haka na dinga hada kafana har na shige cikin gidan nayi arzki babu kowa a falon suna cikin dakunan su do magariba daya kawo jiki.
Gado na fada na saki wani kuka gwanin ban tauayi ni kadai a dakin har na gaji naba kaina hakkuri na mike don gabatar da sallah saboda lokacin dake wucewa .
Ina wurin da nayi sallah a zaune na kasa tashi aka turo kofan dakin nawa fadilace ta shigo don ta duba ko mun dawo a lokacin ta samu mun dawo din.
Kallo guda tayi min ta fahinci cewa nasha kuka tare dani da sauri take fadin zainab meke faruwane yanayin ki ya nuna kinyi kuka haka mai yawa.
Zuwa tayi inda nake zaune din tare da zama a kusa dani tana fadin meya samu kuma zainab kun fita lafiya kin dawo da kuka haka ko yayi maki wani abinne kuma.
Kai na girgiza idona yana kawo hawaye nace a cikin kuka mamice dai ta tsanane bata kaunana har cikin ranta yanzu.
Meye laifi ne anty don kawai ya jafar ya aureni meye laifina tasan bada yarda na haka ya faru ba tsakanin mu ?
Baki da laifi zainab kowa ya sani amma zata daina ai idan ta gane hakan ba laifin ki bane kema nan gaba zata gane dantane mai laifin bake ba ni abinda na yarda dashi ke nan kedai ki kara hakkuri zainab.
Bafani nace ai tafiyan nan dani ba anty hjy ce ta kafe sai dani zata yarda ta tafi can inda yake zance ba zan tafi bane ni ?
Dake zai tafi zainab ta tambaya cike da mamaki a fuskan ta tana kallona kai na gyada mata alaman eh.
Za ako samu matsala wallahi saidai idan kin daure hakan ba komai bane zai zamo maki alheri ta wani bangaren rayuwa.
Anty idan mami ta barni ke nan har haka zai faru ni dai kawai gara yaya yace ya sakeni ko rayuwana zai zauna a cikkn sallama yafi.
Ina amfanin wanan zama namu da mukeyi hankalin kowa a tashe gara kawai ya sallameni na koma gidan mu in zauna a gaban iyayyena ko kasa sukeci muci shi tare dasu.
Ki bar fadin wanan magana kiyi addu,a Allah yasa hakan shine alheri a rayuwan ki dama kowa da abin ya shafa.
Anty kina ganin haka zamu zauna da sunan aure tsakani da mami da danta har ma da kowa daya shafi mami din ?
Yanzu fa a asibiti babu wanda ya nuna damuwan shi a kaina danaje sai hjy hjy kuma kinga ai tsohuwace basa jin maganan ta ko a yanzu.
Duk zasu bari ta fada amma fa idan kin jajirce wa kowa haka zai faru nidai shawarana har gobe gareki shine .
Kiyi kokari shakuwa da sabo ya shiga tsakanin ki da mijin ki har ki fahinci wani abu daga halayen shi na boye da baki sani ba tayi min wanka da jurwaye cikkn maganan ta.
Kaina daga hawaye naci gaba da zuba min a idona take fadin kwarai zainab don ba mami bace matsalan ki a yanzu matsalan ki shine mijin ki ya daukeki a macen aure ya dauko ki.
Kada kiji ina yawan fada maki haka ki dauka da wasa nakeyin zancena a a zainab akwai matsalan da nake hango maki nan gaba wanda yafi wanan da kika saka a ranki duk na mami shirmene gaskiya .
Anty wani matsalane wanan na tambaya cikin son karin bayani daga gareta kafin tayi murmushi tana fadin ba zaki fahinceni ba a yanzu.
Saidai shawaran da zan baki shine ki sa ido ga wa yanda mijjn ki yake mu,amula dasu sosai ki fahinci wani irin rayuwa yakeyi dasu.
Musanman wanan taju din don ni sam ban yarda dashi ba amma don Allah ki boye wanan zancen a cikin ran ki har lokacin da zaki gane wani abu din.
Sai ta kawar da zancen data dauko din da fadin yaushene tafiyan naku yanzu kuma mu a nan za a barmu ke nan ko me ?
Ban sani ba anty saidai tunda hjy za a kai asibiti ban tsamani tafiyan zai dauki lokaci ba don naji yana fadin za a soma shirin tafiya daga yau din nan.
Kai amma zanso na danje maki wani guri kafin tafiyan duk da hakan ba matsala bane gobe insha Allahu zan fita na dan je wani guri ai gara da naji da wuri tun lokaci bai kure muna ba.
Don haka kada ki yarda ki saka uwar miji a damuwan ki don irin su mami hakan suke son gani a gareki ko yaushe sai ransu su kuma yayi dadi da hakan .
Sun san komai ya lalace maki ke nan daga bangaren su har na mijin naki baki ba sauran kwanciyan hankali a tare dake.
Don haka ki saki ranki ki duba matsalan mijin ki dake gaban ki ba wanan shirmen ba da tana da iko ko auren ki ba zaiyi ba ai.
Ta fita ta barni da funanen meye wanan matsalan da kullun take kiramin ne ni har yau na rasa gane me hakan ke nufi waine wai ?
Ina shiri kwanciyane ya shigo dakin nawa ina saman mirrow zaune halimatu bata dade da fita a wurina ba don tun tafiyan msizube ta koma kwana tare da anty fadila watarana kuma mu duka ukun muke kwana a daki guda idan mu kadai ne a gida.
Wuri ya samu ya zauna bayan na amsa maushi sallaman daya shigo dashi fuskan shi a kaina yana kallon yanayi na a lokacin .
Saida ya zauna yake fadin kin gama kukan shagwaban naki ke nan ke sai yaushe zaki girma ne wai a gidan nan?
Daga cikin mirrow na dago kai muka hada ido dashi nayi saurun dukar da kaina kasa da sauri don ba zan juri kallon da yake min ba din saboda yanayin da hakan yakan sakani idan yana min wanan kallon.
Gobe sai ki shirya zamuje ai maki photo na fita waje saura idan mun fita kuma ki min wanan shagwaban naki da kika iya .
Ban tankashi ba har ya kare maganan shi ya fita waje sai lokacin na sauke ajiyan zuciya tare da fada da kaina watau shi wanan mutumin bai ma san ina yi ba ke nan ya mayar dani wahalalallah .
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.