Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel
Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 6 of 139
ZAINAB IDRI MAKAWA🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
4ï¸Â⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
LITTAFIN KUDINE DARI UKU NE KACAL GA MAI BUKATA TARE DA IMANI DA SANIN AKWAI HISABI GOBE KIYAMA.
DON ALLAH YAN UWA MUJI TSORON ALLAH GA DAUKA HAKKI A KAN MU TA WANAN HANYAN SAYAR DA LITTAFI A ONLINE MUKE SAMUN CIGABA DA RUBUTUN DA MUKE MAKU KADA KIJI HASARAN BAMU HAKKIN MU KODA KADAN NE .
Sai salatin Asabe mukaji a tsakar gida tana ta faman rabka salati da fada tare da zagi ga duk wanda yai mata wanan aikin.
Babu wanda ya tanka a cikin mu har innan mu saiga Lantana ta fito tana fadin meya farune umma ?
Meye ma bai faru ba randar ruwana tun tele tele na samu a fashe yau sai nasan wanda yai min wanan ta,asan a gidan nan ta fada tana zare ido.
Lantana tace kema umma da wani zance kike ai wa zaiyi wanan banda yaran gidan nan ko Akuyar ki ta fada mata.
Badai Akuya ba su din daine zasu aikata min haka saboda bakin ciki da mugun hali yau dai ai za,a yita ta kare ko a biyani randan ruwana ko kuma yasan inda zaiyi dasu nagaji wallahi .
Ta karasa tare da juyawa wurin randan ta nufa tana hada guntayen sakainan da suke wurin a warwatse a kasa.
Ranan wuni jininin wanan abin tayi babu wanda ya fito yace shi ya aikata hakan sai lantanane ke taya ta fadan.
Abba na dawowa da wanan zancen aka tare shi kira ya kwalawa innan mu dake daki ta fito.
Cikin yaran nan wayaiwa umma wanan barnan ya tambaya yana kallon fuskan ta.
Malam ina zan sani tunda ba yawo nake dasu ba balle duk cikin su babu wanda ke yawan shiga wajen umma ko tana nan balle bata gidan yau tun safe.
Asabe tayi caraf tana fadin waya sani ko ita dince tayi wanan abin don kawai tsaban bakin ciki dake cinnta.
Aure daine na karawa dana ga kuma abin arziki har an samu saidai bakin ciki ya kashe mutum din sai anyi ma yayan ki dan uba a gidan nan.
Wanan bai taba damuna ba umma kin sani in ma za a karo mai biyune rana guda su shigo su haihu a rana daya bai taba damun rayuwana.
Kana dai jin wuyan matar ka yayi kauri har tana fada min bakar magana haka a gaban ka.
To kisha kurmin ki wanan din ce dai guda na aura mai kuma baki so hakan ba dake da diya matan naki da suke tayaki kishin.
Allah ya baku hakkuri umma randan ruwa ne dai ban san wanda ya kashe maki shiba .
Makirci daine kiyi tayi aiga diya mata nan maki zube a gida har yau babu wanda ya sallama da sunan kiran su.
Shiga dakin inna yayi daidai da soma fadan Abba Asabe na fadin in fito da miji cikin samarina Abba yace kwarai kuwa da gara dai in fara rage su nima zaifi min sauki tunda har sunyi wayau yin hakan yanzu.
Idan ma bata da tsayayyene akwai wanda zan hada ta dashi ai shi a shirye yake ko yanzu idan har na bashi.
Abba yace a, a umma gara dai a bari ta kawo din da kanta zaifi tunda kin ga yadda yar gidan muddi suka kare kan hakan yanzu.
Gashi kullun maigari maganan shi ke nan a bar yara su zaba da kansu da ai masu dole.
Ai ba dole bane tunda shidin wanda zan hadasu din yana son ta ai itama zata so shi tunda bata kaishi gata ba.
Koma dai menene umma don Allah kada a soma hakan banda zarahin zuwa birni sharia tunda kinga can ake kai mutun kai tsaye.
Jin hakan yasa Asabe tabe baki tana juyawa zuwa wurin ta tare da fadin ni banga ranan haihuwan diya mata ba a rayuwana ko kadan.
Inna dake daki kuka take darza a hankali batare da fitar da sauti ba balle wani ya jita.
Alwala nayi na nufi dakin ta sanin Abba ba dakin yake ba na samu inna zaune tayi tagumi a wurin data idar da nata sallah.
Inna kada zancen su Asabe ya tayar maki da hankali har ki shiga damuwa tunda bake kika ba kanki diya mata ba ai.
Meye laifina a cikin wanan zance yar mairo don kawai na haife a mata yasa umma ta dauko tsangwama ta dora min ni meye nawa a ciki.
Su suke raina diya mata ina saboda in kin kula Asabe ba da bukatan ilimin addini ko kadan ne matar da ko alwala bata tsaya ta koya ba .
Idan kuma za a gyara mata tace ina mutum ya fito ta kashe shi ai kinga fadin hakan daga bakinta ba abin mamaki bane jahilcine ke damunta daga ita har yar koran nata.
Bashi yafi damuna ba yar mairo yadda yanzu mahaifin ku yake kokarin juya min baya tun lokacin zancen cikin matanshi da umma tayi.
Ina kallo zai sayo mata abu a gaba zai bata idan nayi magana yace min tana da lalura dole a lalabata ai.
Inna kema idan kina son abin ai sai ki fitar da kudi ki saya idan baifi karfin ki ba kiyi hakkuri ki saka masu ido Allah ba azzalumin kowa bane ai.
Sallah nayi har na idar tana zaune tana faman tunane kafin ince niko inna sai nake ganin kamar saratu ne tayi wa randan ruwan Asabe ta,asa don abinda tai muna ranan .
Don dazun naga sanda ta fita zuwa lungun Asabe bata dade ba ta dawo daki tana dariyan kyata.
Amma idan itace ta aikata hakan sai na bata mata rai yau inna ta fada a hasale.
Da sauri na tare inna ina fadin a, a inna idan kin doke ta zasu gane kiyi mata fada kawai don Allah idan ta shigo.
Kwafa innayi ba tare da kara furta komai ba ta mike tsaye ta tada sallah don isha,i da ake kira lokacin.
A daidai lokacin saratu ta shigo gida tana wakan ta mai kama da habaici a fakaice .
Gamu munzo taron dangi, bama tsoro kugafar bama tsoro har zuwa karshen wanka tanayi tana rawa kafin sallama ta shigo dakin inna kai tsaye.
Ganin muna sallah yasa itama ta juta ta suri buta ta shiga bandaki ta dade a ciki kafin ta fito tayi alwala lokacin har sauran sun shigo dakin ko suna sallah.
Nice na fara idarwa don Inna ta tsaya dogon adduan da takeyi bayan sallah.
Fatima ki tashi kuci abinci kada kiyi barci bakuci abinci ba cewa da yar karaman kanwar mu data kwanta tana shirin barci.
Mikewa nayi don in raba muna abincin da mukayi tunda rana tuwo ina tayi muna da miyar ganye da gyada shine mukaci da rana sai koko da take cika roba ta aje don mai yara bata yarda ta rabu da koko a dakinta a kauye.
Saratu na shigowa take fadin yanzu ma tuwon ne zamu kara ci nace idan kin tanadar muna wani abin ba sai kici ba.
Sallah ta tayar har ta idar daga inda take fadin Abu bani abinci na zanci in kwanta ne yau barci nake ji.
Ba zaki biya karatun ki ba ke nan yau barci zakiyi tace na gaji ne yau sosai na dibar muna abincin sai da muka faraci dakin hayi tsit a lokacin.
Don inna ta horemu da hakan tun muna yara har muka gama kowa yaje ya wanke hannu muka dawo tana gyara wurin kwanciya inna tace.
Saratu may yakaiki wurin inna har kika fasa mata randar ruwanta yau don kawai ki jawo min sabon masifa cikin gidan nan ina fama da kaina.
Juyowa tayi inda nake ta dan kalleni kafin tace wani inna wallah, , , , bata karasa ba don tsawan da inna ta daka mata da rufe min baki tun kan na mareki wurin nan.
Shiru tayi har inna ta kare mata fada bata sake magana ba don fada sosai inna tayi mata tana shiru har inna din ta gama.
Ina jin tayi shiru nace ni inna gaskiya gobe zanyiwa Abba maganan karatuna gashi har zamu fara exam din shiga wani zango ban tafi ba.
Idan kinga zaki iya ai gaki gashi nidai babu ruwa na tunda kikaji umma tace kin daina boko to ki barwan nan zacen a hakan.
Har muka kwanta ba kara magana ba sai faman tunane nake a raina don ba abindake damu kamar rashin karatu da ban fita yanzu na riga da na kwallafa rai ga boko nace ni nurse zan zama idan na girma.
Washe gari baba bai fito dakin lantana da wuri ba har kowa ya gama shiri ya fita don sauran suna zuwa makaranta basu fada kangin Asabe.
Hankalina yana wurin fitowan baba daga daki lantana sai wuran goma ya fito tare da ita tana mai rakiya don kawai kada yace zai biya wurin innar mu su gaisa.
Har yasha dan kwanan fita daga ciki gida na fito da sauri na same shi ina fadi Abba ina kwana.
Ya tsaya tare da juyowa yana fafin yar mairo kun tashi lafiya ina kannen naki sun fita ko ke nan ?
Nace a sanyayaye sun tafi baba sai na fara hawaye daga inda nake tsungune ina dan gogewa da gefen hijabi na.
Me ya sameki kike kuka haka da safe Abba ya tambayeni cikin kullawa kasa bashi amsa nayi sai sharan hawayen da nakeyi a lokacin.
Lantana dake tsaye gefen shi kamar bodyguard din shi ta tabe baki tana fadin ya wuce dai zancen auren ta da umma ke fadi.
Kai haba lantana wani zancen aure kuma yanzu gun yar mairo adaiyi hakkuri ta karasa karatun nan datasa a gaba har kwana nawa yarage ta karasa idan muna raye.
To ai naga kai umma take tausayawa a cikin zancen nan kamar rage maka nauyine umma ke kokarin yi ga hakan.
Ya juyo wurina yana fadin kinga yar mairo kije kiyi hakkuri har in zauna da umma in fahintar da ita ko Allah zai bamu sa,a a kanta.
Lantana dake jin mu ta karyar da kanta gefe tana fadin gamu gani ai indai umma ce a gidan nan.
Na bude baki da kyar ina fadin don Allah Abba ka taimaka min na karasa karatuna ko iya secondary din ne in tsaya.
Taysayinane ya kama Abba lokaci guda sanin yadda gun ina kankanuwa nake son boko har irin dagewan da nakeyi kan karatun a yanzu.
Yayi karfin halin fadin kada ki damu yar mairo insha Allahu zaki karasa karatun ki har ki more a rayuwan ki, duk da lantana na fadin malam kasan fa ka makara kada kwastama su dinga mitan hakan.
Haka yasa Abba ya wuce badon yaso ba don tausayina da yaji a lokaci guda ya rufe mashi zuciya.
Bayan fitan baba lantana ta juyo ta dubeni a lalace tana fadin iska na wahal da mai kayan kara.
Lantana wurin Asabe ta nufa ta fesa mata yadda mukayi da Abba tunda naga ta nufi can zuciyana ya raya min hakan.
KADUNA GARIN GWAUNA
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.