Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel
Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 59 of 139
🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
4ï¸Â⃣9ï¸Â⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
FATAN ALHERI AKULLUM YAN UWA MUSULMAI TARE DA FATAN CIKAWA DA IMANI A GAREMU HAR KULLUM, , , ,
Alhamdullahi na kammala karatuna lafiya tare da fatan nasara ga abinda muka rubuta dan ni kaina nasan da na sha wuya wurin mayar da hankali ga jerabawan dake gabana.
Har ubangiji ya bani nasaran kammalawa lafiya na dawo zaman jiran tsamani daga bangarori daban daban na sha,anin rayuwana da nake fuskanta.
Don yanzu ban san makomana ba a rayuwa gashi wasa wasa mun share wata uku a gidan ya jafar din dake a garin abuja tare da maizube da halima sai anty fadila dake tare damu a gidan.
Bani ba har maizube da halima gabaki daya mun sake sunyi kyau sun canza jikin su ya nuna jin dadi a tare dasu duk da babu inda muke fita a gidan saidai komai akwai na more rayuwa.
Traning kan na samu gwargwado kamar yadda anty tayi min alkawarin samu daga gareta don a cikin dan lokaci kankani na canza yanayina ga baki daya ya koma na wace ta waye ta fara sanin kan duniya.
Gashi a lokacin na shiga ganiyar budurcina da kyau ko ina nawa ya ciko ya cike ga baki daya lokaci guda.
Ashe da gaske samun kwanciyar hankali da cima mai kyau yana karawa mace budewa da jin dadi a rayuwan ta idan tana samun hakan tare da ita don na sheda hakan a kaina yanzu.
Ga farina na asali da ya kara fitowa fili a yanzu nayi wani irin fari na ban mamaki dani kaina bansan ina dashi ba sai a yanzu danayi wanan cikan haka.
Saidai a yanzu na kula da maizube hankalin ta ya koma ga iyalin ta duk ko da daulan duniyan da muke ciki don yanzu daya biyu zakaji tayi zancen gida daga bakinta.
Wanda hakan ke nuna hankalinta ya koma gida ko kuma ta zauna ta rabka tagumi sai kai maga ba zataji me kake fada ba a lokacin.
Nima sai hakan ya fara damuna don nasan iya kokari tayi yadda duk akeso ga dan uwa gareni don ba abun wasa bane babban mace kamar maizube ra baro dakinta da mijinta har tsawon wanan lokaci haka.
Hadari sosai aka hada a garin lokaci guda yanayin garin ya canza ga baki daya dukkan mune zaune a falon gidan.
Maizube ne ke fadin ikon Allah lokaci daya yanayin garin nan ya canza da alama dai damana ya tsaya ke nan a garin nan.
Fadila dake gefe zaune take fadin ai abuja ya wuce haka kedai mama don a take suke samu ruwan sama akai akai.
Don ma yanzu damanan bai gama shigowa ba yasa ake dan hada hadarin yana washewa .
Wani irin iskane kamar guguwa ya taso lokaci guda ya turnike garin muna jin yadda karan iskan ke kadawa a lokacin daga falon da muke zaune duk da ko ina glass di falon yana rufe.
Mikewa halimatu dake gafena tana gyaran farcen ta tayi na bita da kallo tare da tambayan ta inda zata a wanan lokacin.
Kai tsaye take fadin zan leka waje ne inga idan hadarin sosai ne aka hada kafin na bata amsa maizube ke fadin wanan ya akwai bakin iyayin tsiya da ita.
A cikin wanan iskan haka kowa ya rufawa kansa asiri kike zancen fita ke ?
Ai da alama ma ruwane ya sauko a yanzu anty fadila ta fada saboda iskan dake kadowa da kanshi ruwa mai nuna alaman sabuwan damana a lokacin.
Wani irin ajiyan zuciya na sauke don yanayin da ya tuna min da abubuwa da dama a cikin raina Allah ya gani ina jin dadin wanan irin yanayin tun ina karama idan anayin sa a gari.
Fuskana dauke da murmushi nake fadin lalsi ruwa ya sauko kuwa dan ga kamshi yanayi ya canza a lokaci guda na fada.
To bashi yasa nake son fita waje ba naga ruwan farko hakimatu dake tsaye tana cika ta fada a shagwabe.
Ke kan wanan ya da badan a kauye yahanasu ta haife ki ba dakin ce asalin ki ba anchau bane nan gaba.
Kai haba uwargidan malam wanan kuma ai ba da halimatu kadai kike zancen na ba don mu duka ai yan anchau din ne na fada ina dan dariya.
Yo ai da kina da irin rawan kan wanan yar da ba haka ba Abu wanan da itace a matsayin ki ai ko gidan nan kila da bamu zo shi ba.
Anty fadila tace zakuzo mana mama ai halimatu harda watan kauye ke damunta don taki ta waye har yanzu .
Amma ita zainab ai kinga saukin kanta yana kaita ga cin riban duniya lokaci guda saukin kanta har ya kaita ga mallakan maigidan nan a matsayin miji a gare ta.
Mama in fada maki ko yan birnin samun mijin irin wanan ba karamin aiki bane a garesu don nima a karon farko dana ga zainace a matsayin matar wai ba karamin mamakin hakan nayi ba a raina.
Sai yanzu dana zauna dakune nake gane hikimar shi nayin hakan da yayi don shima ba karamin sa,an hakan ai yayi ba a rayuwan sa don mama ka auri macen da zaka iya juyata ka tsayar da ita inda ka ajeta a yanzu ba karamin aiki bane gaskiya.
Yo kina wanan ancen haka ke fadila mufa na kauye har gobe akwai biyayyan aure da girmama miji a garemu har yanzu duk ko da muma din muna da masu kaifin kai a cikkn mu.
Ina amdanin wanan irin rayuwan da mata sukeyi a yanzu na halaka a garesu mace ta dunga fita inda taga dama kamar ba aure ne akanta ba ?
Wanan ba wayewa bane illa shiga halaka da yawacin mata suke jefa kansu a ciki a yanzu don dan abin nan da suke rainawa zai iya kaisu wuta lokaci guda.
Ai mama yanzu mu bamu dauki wanan a bakin komai ba don mazan da kansu hakan suma bawai ya damesu bane yanzu.
Suna ko kona ku don sun barku da Allah yana kallin wanan bakin al,adan da kukeyi ne a yanzu mace ta fita da sunan zuwa gida daya sai ka tsunceta har kasuwa ko wani gidan buki kai har ma wai da zuwa gidan gaisuwa a hakan.
Mama Allah dai ta kyauta anty fadila ta fada tana kokarin mikewa tsaye tare da fadin ruwan nan sosai yau akeyin sa don ga lokacin salla har ya karaso bamu sani ba.
Mikewa mukayi lokaci guda don zuwa yin sallah kada mu makara yayin da ake ta faman sheka ruwa har lokacin kamar ba ruwan sabon damana ba.
Har na idar da sallah ruwa akeyi kamar da bakin kwarya yadda ruwan ya gwauce a lokaci guda mikewa nayi na gyara komai yadda nake so a dakin kafin mu fito falo don cin abincin dare da bamu ci ba alokacin.
Mun ci abincin mu lafiya mun dan taba hira kafin mu shige saboda sanyin da garin yayi a lokacin wanda hakan ke iya saukarwa mutum da kasala da nauyin jiki.
Dakin a gyare yake tsab don haka ban tsaya jiran komai ba na saka kayan barci na fada saman gado duk da barcin da nake ji a lokacin hakan bai hanani yin addu,oin dana sabayi na kwanciya ba.
Mafalkin nan dai dana saba shine yazo min yau ma din wanda hakan yasa na falka a razane daga barcin na zauna gami da salati a bakina ina hada gumi a fuskana.
Wanan mafalkin yana damuna na rasa me hakan ke nufi dani wai a rayuwa don a cikkn zamana a wanan gidan kusan sau hudu ke nan ina wanan mafalkin haka wanda na kasa fadawa wani wanan maganan.
Saidai na yau din ya zama dole in tun kari wani da wanan zancen ko zan samu mafita a gareshi.
Tunane na fara tsakanin anty fadila da maizube wa zan fara tun kara da wanan abin dake damuwana a rai sai hankalina yafi kwantawa da in fadawa maizube don itace dai tawa ko banza.
Wanan kuma ai kamar sirinane duk da na yarda da fadilan itama a zuciyana amma dai hankalina yafi kwantawa da mauzube din a yanzu da nake shawaran wanda zan tun kara da zancen abinda nake yawan mafalkin shi din.
Washe gari bayan na idar da sallah na dan dade a zaune a gurin kafin in mike zuwa wurin maizube nayi sallama daga kofa ina jiran umurnin ta na inshigo dakin da take zaune a cikin sa din.
Ta amsa min da fadin Abu ce yanzu nake tunanen in sameki ai don ban sani ba ko kun tashi ko kun makara da wanan bakon yanayin na yau da muka tashi dashi na damana.
Na tashi tun asuba na fada ina karasawa cikkn dakin tare da samun wuri na zauna ina gaida ita da kwana tana amsa min gaisuwan .
Dan shiru ne ya biyo baya kafin tace ina lafiya dai Abu don yanayin ki ya nuna kamar kina da damuwa a ranki ko ?
Matar malam wallahi ina da damuwa sosai a zuciyana don wani irin mafalki nake a gidan nan kusan karo na hudu ke nan idan ban manta ba ina wanan mafalkin haka.
Subbahanallahi ta fada tare da kara mayar da hankalinta gareni a cikin nuna kulawanta a gareni sosai don jin abinda nake kokarin fada mata a lokacin.
Sannu a hankali na zaiyana mata yadda mafalkin ke zuwa min a kullun tare da yadda nake falkawa a cikkn matsanacin faduwan gaba da ciwon kai.
Ido ta tsura min na dan lokaci kafin ta sauke ajiyan zuciya tana fadi a hankaki babban maganace wanan Abu.
Don wanan maganan saidai mu nemi gaban malam ko yana da wani haske da zai kara muna a cikin wanan mafalkin naki.
Abu waima kina addua kafin ki kwants barci kuwa don shedan yakan ari fuskan wanda ka sani wani lokaci yayi wasa da hankalin bayin Allah.
Wallahi maizube bana yarda in kwanta da ba tare danayi adduan kwanciya a tare dani ba kamar yadda aka koyar dani hakan.
Allah ya kyauta ya mayar da koma menene ke shirin faruwa dake alheri a garemu baki daya yanzu nasan malam yana wurin wazifan safe sai zuwa anjima bayan goman safe za a same shi gida.
Zuwa wannan lokacin sai mu nemeshi a waya ai masa bayanin komai a tsanake yadda zai iya fahintar mu ya bamu haske akan wanan magana.
Allah ya kaimu anjima na fada bayan sauke ajiyan zuciya danayi don jin kamar har na samu haske kan wanan matsalan dake tunkaro rayuwana a yanzu.
Haka na mike zuwa dakina wanka na shiga na gyara jikina tsab na fito na dan dade ina kwalliya a gaban mirrow kafin in fito daga dakin.
Falo na samu su maizube an zuba masu abinci suna ci a dining ita da halimatu nima zama nayi don mu karya a tare ko zan samu inci da yawa saboda damuwan dana sakawa kaina a lokacin kan mafalkin da ya tsaya min a rai.
Wanda na kasa gane me haka ke nufi dani wai waye kuma wanan da bana ganin fuskanshi a mafalkin na ko yaushe idan nayi irin wanan mafalkin saidai inga bayan maishi.
Muna tsaka da cin abincin ne fadila ta fito daga dakinta tana fadin yau da wuri haka kika fito ?
Dan dariyan yake na iya mata ba tare da bata amsa sai ina kwanan dana jefa mata kafin ta kai zaune itama tana kokarin diban abinci don ta karya itama.
Na riga kowa aje cibin dake hannu na ina kokarin tashi a wurin naji fadila na fadin yau ina son indan zaga gida na diba su na kwana biyu ban lekasu ba.
Jin hakan sai yai min dadi a raina har nake fadin anty ashe yau gida zasuyi bakuwa kin kai sati baki fita gidan nan ba ai.
Zainab bana son fita ko yaushe ne kada a bata min aikina kin san yanzu mutum ake kiyo ba dabba za a iya fadawa maigidan nan bana zama ko ina wayan fita har hakan ya ja min matsala ga aikina.
Hakane maizube ta fada inda kake samu baka wasa da wurin samun ka don yanzu mutane sun baci da gulma.
Kamar yadda na saba mata tun bayan danaji tana da yara a gida da tabarsu gun mahaifiyar ta nakan dan bata abu takai masu idan zata tafi dubasu din.
Tana murmushi ta karba tare da fadin bakya dai gajiya da dawainiya da yaran nan naki zainab ko yaushe suma suna damuna da zasu zo inda anty mai sweet take muka sa dariya a tare.
Bayan fitan tane muka samu kiran malam din maizube ce ta fara masa bayani kafin yace a ban wayan yaji daga bakina.
Na karba nayi mai bayanin komai yadda nake gani a cikkn mafalkin sai fada yake ikon Allah saida na kare bayani yake fadin.
Naji komai da kika fada zainab insha Allah zan duba in gani abinda ke gudana zan kira insha Allah saidai duk da hakan ki daure ki kara kaimi wurin yin addu,a da sadaka domin sune kariyan mumuni.
Na amsa da insha Allahu malam mukai sallama na kashe wayan tare da masa godiya maizube ke fadin kinga hakan yafi kada mu zauna a cikkn duhu har wani abu yazo ya same ki.
Rashin fadila a gidan yasa gidan ya koma muna shiru yau dan karfin kan gidan itace dama zata dinga yi wanan yi wancan idan muna zaune a falo.
Tunane barkatai nake yi a zaune don abinda zai biyo fassaran da malam din zai min nice har da tunanen ko jinina ya jafar din ya bayar ?
Ko kuma dai dama manufan shi a kaina shine ya halaka min rayuwana yasa ya nace da zancen aure na dayayi ba tare da wani kwakwaran hujjan akan hakan ba.
Bakin gadon dakina na karasa na zauna tare da zuba tagumi abin duniya ya dameni a lokacin a raina .
Ba komai nake ba sai dan banzan tunane da dana sani wanda yafi a kirga na abinda zuciyana ke kiyastamin kan ya jafar din da mami.
Har barci mai nauyi ya daukeni a haka ban sani ba sai falkawa nayi wuraren karfe biyar na yamma .
A razane na mike akan gadon a zatona har magariba yayi a lokacinn saboda yadda gari yai duhu sosai da sauri na fada ban daki na dauro alwala na gabatar da sallah azahar da la,asar a tare don naga lokaci yayi.
Falo na fito halimatune kawai a falin zaune tana kallin wani hausa film a tauraron dan adam na zauna ina fadin halimatu shine baki tasheni inyi sallah ba ?
Ta dago tana fadin yayan mu na shiga in tashe ki naga kin samu barci sosai nafito na barki kada naja maki ciwo.
Sallah ai yana gaba da komai na bata amsa tare da fadin kinci abinci ko tace tun dazun mukaci da maizube itama tana maganan baki fito ba ai.
Anty bata dawo ba har yanzu na sake tambayan ta bata dawo ba ta bani amsa tana mayar da hankalinta wurin tv dake aiki.
Ban dade da zama ba aka turo kofan shiga gidan anty fadila ce ta shigo da kaya niki niki a hannun ta tana sauri don feshin ruwan da aka fara lokaci guda.
Anty kin dawo na fada inda nake zaune tana fadin kin gani sai yanzu ban farga da hadari a garin ba sai ganin wuri ya rufe kawai nayi ina kasuwa.
Ina can kuma mijin ki ya kirani yana min masifa dan yace a kai maki waya nace bana kusa dake ya fara min sababi.
Wai ya kira baki dauki waya ba yasa ya kirani yana tambayana kina inane ya kira baki daga waya ba .
Barci nayi anty tun bayan fitan ki na kwanta sai yanzu na falka na fito amma don me zaiyi fada dake mutumin da ba damuwa yayi da kiran mu ba ko yaushe.
Fada sosai fa yai min har saida hankalina ya tashi na baro gida ba shiri wai bamu dauke shi da muhinmanci ba da zan fita meyasa ko text ban masa zan fita ba.
Idan wani abu ya same ku fa bana gidan ke fada sosai yayi yau din kan hakan ta fada tana kokarin kaiwa zaune.
Uhm kawai nace ba tare danayi magana ba dan ban san me zan fada ba taci gaba da fadin na gano yana da dan saurin fushi sai kin kula da hakan.
Don namiji mai saurin fushi yana da wuyan sha,ani sosai irin su idan sun soma shiru kawai ya kamata mace tayi masu har zuwa lokacin da zai sauka da kansa.
A,a kin dawo fadila maizube ta fada tana fitowa daga part din dakunan kwanan mu haka yasa muka mayar da hankakin mu wurinta.
Saida ta zauna take fadin yanzu dai garin nan ashe baida wuyan samun ruwan sama akoda yaushe.
Wayan hannun tane yai kara ta dauka tana fadin baya baida kadan malam ne yake kiran layin na ta mike ta bar wurin zuwa inda tafito da wayan a hannun ta.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.