Complete Hausa Novels

Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel

Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 39 of 139

ZAINAB IDRIS MAKAWA
[25/12, 14:51] +227 98 36 59 34: 🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅

3️⃣2️⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ASSALAMU ALAIKUM WAHAMATULLAH YAR UWA BARKA DA WARHAKA FATAN ALHERI GAREKU YAN UWA MUSULMAI UBANGIJI YA TAIMAKI MUSULMI A DUK INDA YAKE AMIN, , , ,
LITTAFIN DAI NA SAYARWANE DON ALLAHU MU SAHILEWA JUNA DANI DAKE KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA BA DON KI SANI NA FADA IN FITAR DA HAKKIN HAKA GAREKI, , ,

Gaba na faduwa na nufi wurin kayan saidai ganin yadda na gyara komai ba haka na samesu ba yasa faduwan gaban nawa tsananta sosai.
Kaf na bincike kayan basa wajen haka ya kara tayar min da hankali muryan mami ne naji tana kwalla min kira dakin hjy yasa na fito ba tare dana gama bincika ba.
Ina shiga dakin da sallama a daidai lokacin da nake fadin mami gani ita kuma take fadin fadin ina kudin tare da kallona.
Na duba inda na aje ban gansuba mami na fada a dan firgice don a rude nake lokacin dan rashin ganin kudin da banyi ba.
Kamar ya baki gani ba dazun nan fa da zan fita na barsu saman gado dama na fitarne akai lami kasuwa ta sayo cefane.
Mami basa nan inda na aje asalima kayan ba,a jere suke ba yadda na barsu wani ya taba wurin kayan.
Wa kike nufin zai shiga dakin mami ya taba wani abu a gidan nan baya ke saiko mami din dake da dakinta.
Ni ai tasan ko kaya zan dauka itace mai miko min ban damu da daukan wani abuba ciki ba.
May ta canza haline ta fara dan hali yanzu tunda taga kudin kamar banza a gidan Aisha ta fada a cikin wani irin yanayi tana dukar da kanta kan wayan ta.
Wallahi mami ban dauka ba a nan na saka yanzu kuma ban samesu wurin ba an canza masu wuri.
Ke zeey kada ki kawo min rainin hankali wani yarona kikaga ya shiga dakina balle ya kai har cikin wardrobe dina bayan ke ?
Haba haba yar nan yau kuke da ita a gidan nan meya kawo wanan zance haka babu dadin ji sam wanan zance bai dace ba ai haba dai ku dinga tunane kafin ku furta magana man.
Wanan tsohuwar haka kike fa ga magana ta gaskiya zaki daurewa karya gindi ke hjyn nan sai sakawa mutane baki ga zance baki san abinda ke faruwa ba.
Ke yar nan nizaki kawowa diban albarka yan zamani dubani da kyau banyi kama da tsofin banza ba da jika zai iya kawowa rainin wayau yan zamani.
Ko uwarki kyaleta nayi take min yadda takeso a gidanta nazo kinga ko a karkashinta nake yanzu.
Idan bashi ba ita ta sanni sarai tasan binta nake kafin in kai ga juya mata baya ga duk iya shigen da kuke zubawa a gidan nan.
Hjy kiyi hakkuri Aisha wani lokaci haka take abindaba wasa ba sai ta mayar dashi abin wasa a wurin ta.
Iyami wanan ne zancen wasa kina zaune tana kokarin dorawa yar mutane halin daba nata ba yau yar nan take gidan nan tare daku.
Ada can batai maku haka ba sai yanzu ne zaku dora mata halinda ba nataba don kawai a bata mata suna .
Shin ko kin mata ne da wanan watarana itama wani gidan zata idan an wa yarki wanan sherin yaya zakiji a zuciyar ki ko ince yaya zamuji a zukatan mu.
Yar nan amana take a wurin mu da duk kowa naki don karbota akayi a hannun iyayyen ta Allah ma,aiki yanzu kuma a binta da wanan barnan sunan haka.
Kuka nake wiwi mara sauti don hawaye ke tsiyaya a idona ina maijin dacin satan da mami da yarta ke kokarin dora min.
Nagodewa Allah nagodewa wanan tsohuwar datayi min tsaye ta hana kowa ci gaba da abinda ake shirin min don dai na fahinci kamar sheri ake kokarin min a gidan kan kudin.
Muryan mami ne ya katse min tunanena tana fadin hjy bafa wani abu bane kudin ne kawai akeson sanin ina ta zubasu don a kiramin lami su tafi kasuwan wanan kuma ta tsaya nata shirmen.
Jeki ki kara dubawa da kyau ko ina a dakin ko kin manta da inda kika sakane.
Na amsa da to da sauri na barsu a dakin na nufi dakin mami ko ina nake dubawa banga kudin ba na rasa yadda zanyi in fadawa mami ban gani ba a dakin ko ina na duba babu kudin a inda na ajesu.
Da kuka na dawo dakin daga kofa na dan tsaya ina fadin mami bangani ba na duba a wurin gaba daya kayan basa wurin.
Jeki Allah ya sauwaka ta fada a cikin wani daure fuska tare da fadin jeki ki kiramin lami a kitchen a bata wani kudin tunda wacan kan an kwashe ke nan sai dai ba zan kara lamintan hakan ba gaskiya.
Allah ya kyauta hjy ta fada tare da fadin nidai nasan ba yar nan ta dauki kudin nan ba tunda ba yau take daku a gidan nan ba komai bai taba faruwa ba irin haka.
Idan da yarnan tana dauke dauke da tuni ansan da hakan kadafa a maidani tsofuwar banza don nagane abinda ake kokarin kullawa yar nan kuma ba zan taba yarda haka ya faru ba.
So ai da laifine, laifin namu ya kamata mu gani domin shine ya nuna yana sonta ba wai yarinyarce ta nuna tana son shi ba balle mu dauki laifi mu dorawa yar mutane ga banza.
Don haka iyami ina shawartan ki ki dauki yar nan ki maida ita hannun iyayyenta tun kan shedan ya zugaki ki aikata abinda ba daidai ba.
Amma idan har yar nan tana zaune gidan nan tare daku kuna kokarin dora mata laifin daba nata ba.
Hjy nima naso hakan tun farko saidai ina tunanen maganan ki kan yaron nan kada ta koma gaban iyayyenta ya bita can ba tare da sanina ba wani abu yazo ya faru a tsakanin su.
Ko tana nan a gaban ki idan Allah ya nufa akwai aure a tsakanin ku sai angi iyami.
Kada ki manta a kullun ina tuna maki baya ki daure yadda Allah ya turo yarinyar nan a karkashin ku har danki yaganta ya nuna yana ra,ayin ta.
Shin me zai hana ki daina hattaran yar nan ki sanya ido ga danki shida ke faman bibiyar rayuwar mutane haka.
Ita metayi za aga laifinta waya take masa ko binshi takeyi, ko kulashi take tana bibiyan shi inda duk ya saka kafa ?
Daki iyami shike wa yarinyar nan duk wanan abinda na lissafo maki a gidan nan kullun yar nan a tashin hankali take gidan nan .
Don haka ina gargadin ki karo na karshe da ki takawa danki burki ya rabu da yar mutane tunda dai baki aminta da wanan abin ba.
Don iyayyen yarinyar nan suna can suna fadin kina nan kin rike amanan yarsu da hannu bibiyu basu san ba haka ba yarsu na nan cikin ukubar ki don kawai danki yace yana ra,ayin ta.
Hjy kin san halin dan yau shi jafar na rasa gane kansa kan wanan abinda yanace sai zeey ni fa bawai niki zeey din nan bane don ina kyamarta ko wani abu.
A, a ba hakana bane zabin nasane ni sam bai kwanta mun raiba don idan har ilimi ko kyau ko wayewa ko arziki yaron nan nasan duk zai iya samo macen data tara wanan abin gaba daya da kansa.
Amma wai hjy sai ace yau yaron nan ya kafe shi sai zeey a cikin kasan nan abinnne da ban haushi da ban mamaki don yi iya tunane na rasa gane dalilin shi na wanan kafiyan tsiyar ta kare tare da jan tsuki mai nuna takaici.
Koda ta dago kai sai duk ta tsargu da irin kallon da hjy kemata don haka ta dukar da kanta.
Mikewa tayi don barin dakin iyami hjy ta kira ta fuska a daure cikin murya mai kaushi mami ta amsa da na,am hjy cikin girmamawa.
Tace wai me yake damun ki ne iyami zaman turai fa ba hauka bane mami tayi shiru tana sauraren yar uwan nata.
Hjy ta sake daga murya cikin bacin rai tana fadin kul naji wanan maganan batar kudin nan ya karde gidan nan har yawuce iyamu nan rayuka zasu baci fiye da tsamani.
Don ina da tabbacin yarinyar nan bata taba maki komai naki a gidan nan don da tana tabawa da tuni an gama gane ta.
A, a hjy aini na gama maganan don ya, , , , sallaman lamine a kofan yasa su yin shiru gabaki dayan su tace lami muje falo in baki sakon a can.
Na dade a inda nake ina hawaye saida naga mami ta koma daki sun gama da lami naja kafata da yai min nauyi zuwa dakin namu.
Ina shiga tsohuwar ke fadin kina ina tun dazun acikin yanayin damuwa na iya budan bakina da kyar ina fadin waje na zauna.
Kinga sake ranki idan kin so nasan bazaki taba wanan halin banzan daba a sanki dashi ba tun farko.
Hawaye masu dumi naji sun fara saukomin a idanu hjy ta nuna min matukar tausayawan ta gareni tana ta bani hakkuri.
Hakan daya farune yasa ranan gaba daya na wuni sukuku dani a gidan ban ko leka falo ba ina kwance a daki zazzabi yana neman rufeni sosai.
Panadol hjy taban nasha sai barci koda mami tasa murya ta kirani sai hjyn ce ta amsa tana fadin banjin dadin jikina na kwanta.
Kamar mami zatayi magana sai kuma tayi shiru don tasan idan tayima yanzu hjy zata kareni gareta ne.
Karfe takwas ya kira wayan ina barci ba wanda ya daga wayan har saida y kara kiran hjy ta dauka zuwa falo don wani ya karba min .
Aisha ce da hjy zaune saman doguwar kujera suna zaune sama a guri daya ta mika mata wayan tana fadi karba min wanan wayan don Allah yar nan tasha magani ta kara kwanci.
Wayar waye wanan ta fada tana karban wayan a hannun hjy din mami ta dan juyo ta kalli wayan tare da kawar da kanta gefe.
Receive din wayan tasa tare da kara wayan a kunnen ta sweety rowan daukan wayan ma kike min kuma tun dazun ina kira ba a daga ba .
Ehhy, , , ya J to ba ita bace yace Aisha yah kuna lafiya lafiya ya mami na kira bata daga ba gata nan tana kokarin karawa mami wayan a kunnen ta.
Don't dear touch me with dis dirty phone mami ta fada a dan hasale Aisha sorry mami a dan shagwabe.
Ta mayar da wayan a kunnen ta yace bar mami nasan akan yaran nan marasa tarbiya take fushi dani haka.
Where is my baby girl ya fada cikin katse Aisha din tace who ya J ?
Yace the owner of the phone wai wanan stupid girl din zeey tana daki tana fushin banza after she steel mami money .
What, ya fada dan karfi kamar a fili yake kusa dasu ba a waya ba yace it can't.
Wani irin wasane wanan da sata kuma satan kuma na kudi hjy dake gefe tana fadin kai amma keko an daiyi yarinyar kawai a gurin nan.
Ban wayan mara mutunci ina saidana gargade uwarki kar zancen nan ya fita har yakai kunnen yaron nan.
Hjy why are you always abusing me bata dauki kudin nan bane ko me kina wani kareta can mami dake daga gefenta take wani tunane yazo mata lokaci guda.
Take fadin Aisha meyasa kika fara yawan surutu ne yanzu sai kuma ta juya harshe a cikin turanci tana fadin kinsan hjy akwai tsufa a tare da ita ki daina biye mata kuna haka mana bana jin dadi haka nima lalaba abina nake ta karasa fadi ki bata hakkuri please.
Hjy yi hakkuri bansan kin fadi haka ba ai ta fada a cikin fushi hjy da ranta ya gama baci take fadin yanzu ai kanku ake ji yar nan .
Duk abinda ake waya a kunne take har lokacin a hannun hjy data fisge gun Aisha yana sauraren duk abinda ke faruwa lokacin.
Idanun shi ya runtse a cikin takaici da bacin rai why mami zata tsani yar mutane haka har su dora mata mugun tabo mai zafi hakan nan.
Ga kalman da baffan shi ya fada dazun cewa don zeey ya kama masu yara yai masu wullakanci don kawai yana takama shi mai arzikine ko yafi kowane yake gani.
Ya dade a zaune inda yake duk da dare ya soma sai yaji sam ba zai iya kwana bai fadawa wani daga cikin mutanen nan wanda baida wani aboki ko shakiki da sukafi mai yanuwan shi na jini.
Baida aboki ko wani amini a kasan daya wuce mai yan uwan haihuwan shi kasancewan shi wanda bai tashi a kasan shi na ainihi ba Nageria.
Haka yasa komai da zaiyi anan ya mamud ne mutum na farko da yake nema ga shawaran shi kamar yadda shima ya mamud din bai wasa da lamarin kanin sa don yana masa biyayya yadda ya dace ga kyautatawa ko yaushe a tsakanin su.
Sai kuma yan kannen shi biyu jamal da jalal sumafi dinkewa da jamal don halin su da yazo kusan daya sosai.
Bayan su akwai Bukar dan kanin mahaifinsu wanda kusan akwai dan shakuwa sosai shima don zai iya cewa shine mutum na farko ds ya yarda dashi bayan yan uwan nasa.
Don tun suna yara bukar din yake nuna ra,ayin shi akansu har wanan lokacin da suka kai hakan bai daina kula dan uwan nasa ba duk da yasan shi din mutum ne da baida saurin sabo lokaci daya.
Ya mamud dake shirin kwanciya tare da matarshi Nuriya yajo kiran dan uwan nasa ya shigo mai don yasa ba halin shi bane kira a cikin dare.
Furta suna shi da yayi ne yasa Nuriya dake gefen shi dan dagowa da sauri tana kallon shi da mamaki don ita a nata rayuwan ta tsani duk wani dan uwa mijin nata.
Tundai shi da take ganin yafi mijinta da komai a rayuwa kamar mijin nata, yana son mayar da kanshi a karkashin shi yanzu wanda ita kuma irun matan nan ne da basu son hakan.
Jafar ya akayine ya mamud ya fada lokacin daya dauki kiran na dan uwannasa normal ya fada saidai ina so zuwa safe ka bincika min meke faruwa a gidan nan don Aisha was telling that that girl ta saci kudin mami wanda nasan sheri ne wanan suke kokarin mata.
What sata kuma ya mamud ya fada da dan karfi wanda hakan yasa Nuriya dago kai ta dan kalleshi cikin mamaki don jin abinda ya fada.
No nima nasan da hakan wanan yarinyar ba zata taba haka ba jafar saidai idan wani sheri kuma ake kokari kulla mata yanzu which is bad .
Yanzu dare yayi sun rufe muma nan muna shirin kwanciyane da safe zan binciki hjy in fara jin abindaya faru.
Ya samu ya lalaba dan uwan nasa suka kashe wayan Nuriya take fadin wanan yarinyar ce tayi sata kowa ?
Ba sata ba kan yau take gidan nan tare dasu wani dai abinne kila yake faruwa a tsakanin su har haka ya faru.
Dama nasan haka zaka fada don har kai ina zargi akan wanan yarinyar da farko don kawai dan uwanka ya rigaka furta mata sone kaima nasan da hakan zakayi.
Da mamaki ya dago yana kallon ta tace eh na sani don yarinyar macijiyace babu namijin da zai ganta farat daya baiji yana sonta ba sai dai bakin tabo ya yanke mata kadari ai.
Don warin talauci da yake binta ita din kaskantatace a idon kowa don bakin talaucin iyayyenta har kasa riketa sukayi suka turota aikatau a birni.
What noses talking kike fada haka me yarinyar nan tayi maki haka wai kika tsaneta kema ina yanzu kika gama fadar dan uwana ke sonta da bakin ki .
Bazan taba lamunta hakan ba yarinyar nan abin tausayine bata da matsala da kowa a gidan nan ki duba yadda take kula yaran nan tankar ciki daya suka fito dasu duk da tasan ke baki son hakan da takeyi masu din.
Bai bata wani kafa da zata fadi wani abuba akai dole tayi shiru ba don taso ba ta kyale zancen a ranta.
Washegari na tashi da zazzabi mai karfi wanda har ya tayar da hankalin hjy a dakin ta nufi gurin mami tana fadin yar nan fa iyami zancen nan har zazzabi ya saukar mata jiya bamuyi barci da dadi ba.
Budan bakin mami sai cewa tayi wanan kuma ai matsalantane tunda nida taiwa laifin ban dauki wani mataki ba a kai balle ta zauna tanawa mutane ciwon banza a gida.
Anya ! Iyami kina da tausayi yanzu kuwa hjy abinne da ban haushi tun jiya nake ganin take taken yarinyar nan ita a dole gata mai zuciya ko.
Mikewa mami tayi ta ballo magani tana fadin ta sha wanan zai sauka idan na fito zan shigo in dubata.
Hjy dai ta karbo maganin cikin sanyin jiki dajin kuna a ranta yadda gaba daya yar nata ta sauya akidarta ga baki daya har yakai tsohuwar tana zargi a ranta kodai wani abu ya shiga kan mami din ne.
Nasha magani cikin ikon Allah naji daman jikin nawa gashi ina son zuwa inyi aikina a daki mami kuma ina jin tsoron shiga dakin yanzu.
Babu yadda na iya haka yasa na sauko daga kan gadon a hankali na dan zauna a bakin gado hjy data fitowa ban daki ta dauro alwala ta ganni a zaune take fadin.
Alhamdullahi sauki ya samu ke nan nace eh hjy ya fada min ina kokari tashi tsaye take fadin ina kuma zaki tafi yanzu.
Zan tafi in gyarawa mami dakine na bata amsa koma ki kwanta babu inda zaki yanzu kina jin jikin nan yarta ta gyara mata idan ta matsu.
Ban iya furta komai ba dole na koma na kwanta don bazan iya mussawa tsohuwar ba don nasan wanan tsakanin sune da mami kuma don nasan baida wuya hakan ya zama wani matsala kuma.
Kara rufa nayi har barci ya soma daukata naji hjy na fadin in tashi in kara karyawa kafin barci ya daukeki.
Zan tashi na fada ina gyara kwanciyana ya mamud yayi sallama a dakin ta amsa mashi suka gaisa ya samu wuri ya zauna.
Ina daga kwance ina jin hiran su a cikin ba, a kafin yace wanan da take rufe haka meya sameta ne kuma ?
Zazzabi ke damunta tunjiya gata nan a kwance yace subbahanallahi shine ba a kaita asibiti ba take kwance a gida haka.
Uwarku ta bata magani shine ta dan samu saukin nan Allah ya kara sauki ya fada kafin yace jiya da dare jafar ya kirani yake fada min wani zance mara dadin ji wai Aisha ta fada mai yarinyar nan ta satarwa mami kudi yaya zancen yakene hajiya ?
Dama nasan za a rina saidana gargadi uwarku kan zancen nan amma ta bari zancen nan yakai kunnen yaron nan.
Nawane kudin yaya jafar ya tambaya zaka biya mata ne mami ke fada daga kofan No mami ba wai zan biya bane kawai dai tambaya nakeyi don in sani.
Ka koma ka fadawa wanda ya aikoka cewa dubu dari ukune ina jiran inji alernt ta fada a cikin gatse ta juya inda nake kwance ina hawaye tana fadin ke zeey jikin bai saki bane ki gyaro min daki ni fita zanyi.
Nice nan na hanata zuwa don kowa yasan da ciwo a dakin shi ai don haka sai idan taji sauki.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.