Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel
Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 113 of 139
HASBUNALLAHU WANI IMAL WAKEEL YA HAIYYU YA KAIYUMU BINRAHAMATIKA YA ASTAGIS, , , ,
BARKAN MU DA SHAN RUWA UBANGIJI ALLAH YA KARBA MUNA IBADUN MU YASA MUNA CIKIN YANTTANTUN BAYIN SA YA SADA MU DA RAHAMOMIN SA YA GAFARATAWA MAGABATAN MU YASA MU GAMA DA DUNIYA YA TSARE MUNA ZURI,AN MU DAGA FITUNTUNUN DUNIYA ALLAHUMA AMIN, , , ,
Yan uwa nayi rashin kanwar mahaifiyata hjy hazeena Ahmed dake aure a garin zuru matar Ahmed jolly provose na yauri.
Allah ya karbi ranta bayan gajeren jinya datayi anshan ruwa lafiya da ita ranan asabar ciwon kai da ulcer yayi sanadiyan barin ta duniya a ranan ta rasu tabar yara biyu a duniya da fatan zakuyi mata addu,a irin na addinin musulcin nagode.
Ba wanda yasan da zuwan mu ranan sai gani mu akayi mota ta tsaya da baki a kofan gidan mu idon mutane dake shawagi a lokacin ya dawo gare mu.
Sai ganin Sa,adatu data fito farko daga motan ya dawo da hankalin su sanin cewa bakin gidan mune wanan.
Saida na dan dade ban fito a motar ba ina daukan jakkata da sauram kayan dana rike a hannuna kafin na zuru kafata farare da suka canza dan samun daula a yanzu waje.
Kafin gaba daya na fito daga cikin motan nida sadiya kusan lokaci guda muka fito daga motan kallo ya koma garemu nan kowa ke fadin albarkacin bakin shi a kan mu.
Don wasu na tambayan ina sa,adatu ta samo turawa wasu na fadin yartane da yar uwanta da akace suna turai zaune an sayar dasu ga wani mai kudi sai kudi yake turowa iyayyen su ba a san ko suna raye ba daga cikin irin maganganun da Lantana ke yadawa a garin game damu.
Na juya ina magana da driver kafin na juyo na fuskanci shagon tsoho baba iro wanda na bari ds kaya cike a ciki a baya inda mafi yawan mazan unguwan mu ke zama da can amma yanzu banga kayan ba .
Ba kuma jama,a da yawa a wurin basu fi su biyar zaune wurin ba a ranan na dan daga masu hannu tare da fadin baba iro mun sameku lafiya ?
Da sauri suke amsa min tare da fadin cewan wani a cikin su kungaji aina fada maku itace don bata da girman kai kaf a cikin su.
Nidai na shige ina jin su ban tsaya kula su ba don maganan da suke fadi a lokacin game damu din.
Sa,adatu ce a gaba muna bayan ta muka shiga da sallama Lantana na wanki a part din ta ta dago kai don ganin wanda ya shigo don sai ka shiga ta cikin tsohon part din mu zaka shiga kofan da zai sadaka dana innan mu a yanzu tunda basu bude kofan su na baya da aikai masi Abban mu ya hana hakan duk cikin dokan lantana a lokacin.
Wanda ba don komai tayi hakan ba sai don duk wanda zai shigo wurin inna mu tana gani da kuma abinda za a shigo gidan dashi din.
Sa,adatu bata tsaya bin ta nata ba duk da ta dago tana muna kalon mamakin data kasa boyeshi a lokacin a fuskanta don zaka gane a rude take da gani mu din.
Wurinta na nufa da yar fara,a a fuskana ina fadin anty Lantana mun sameku lafiya tunda ita ta kasa magana sai idon data waro a bude a lokacin.
Can kamar a firgice take fadin ai Abu kune tafe ashe sannun ku da zuwa a yadda ta tareni wanan karon naji mamaki matuka tankar ba Lantana bace.
Na duka ina daukan yarta dake zaune tana kuka ga yarinyar ko wanka safe ba ai mata ba sai tsamin dauda da ke fita a jikin ta .
Uwar ke fadin kada ta bata maki kaya Abu fitina take ji dashi halinta ke nan kukan banza ko yaushe.
Bayan na dauki yarinyar na juyo ina fadin mun sameku lafiya ya bayan rabo cikin kame kame har lokacin take fadin ahe zaku zo yau bankoji ana fada ba.
Nace ba wanda yasan da zuwan mu a yau din shiyasa ina Asabe da cewa kakan mu tana wurin ta ta ban amsa sai bina da kallon mamaki da takeyi.
Ihun kanne da suka fito daga part din innan mune ya dauke muna hankali duk suka zo suka kankame muna a jiki nida sadiya dake makale dani duk inda na saka kafata.
Lah yaya kika dauki wanan mai dattin haka ta bata maki jiki kanwata ta fada a cikin gatse don lantana taji haushi.
An dauke ta din ai ita ba irin ku bace da kuke raba daya biyu a gidan nan an dai ji din a ajeta kada ta bata mata jiki.
Ban tsaya ta kansu ba don zasu iya rikidiwa a wurin nake gani don haka na nufi part din asabe kakan mu ina tambayan su hanyan part din.
A wurin asabe din sun tsaya suna wagala tsohuwar da tsokana wai mu din bakin turawane mun zo muyi mata alluran riga kafin tsufa ne.
Ita kuma ta yarda da maganan su ta shiga yin bare bare ban taba riga kafi ba tun zamanin shagari da akai muna lamba a hannu ina lafiya sai yanzu za a zo min wani allura can.
Asabe wai baki gani ni bane Abuce fa na fada ina kallon ta ina murmushi tace tana kallo a cikin mamaki.
Abu dai Abun dana sani sai kawai ta fashe da kuka tana fadin hakan ta rungumeni tana fadin.
Abu ashe zan ganki kafin na mutu Allah na godema da ka nuna min yaran nan sun dawo garemu lafiya.
Ana ta fadin mun sayar daku ga mutumin da bamu sani ba don munga kudi ya rude mu sai gashi mutumin arziki da alherin sa yana ta turo muna da abin arziki a gidan nan kai da kai.
Sai da muka dan dade a part din na asabe tana faman bamu dariya kafi mu taso zuwa part din innan mu har lokacin yaran lantana suna biye damu a baya har lokacin.
Asamau kanwata ta juyo cikin hattara tana fadin ku kuma ina zaku haka kuna wani bin mu a baya ?
Da sauri na juyo ina fadin haba asma,u ki daina hattaran su haka mana jin muryan Lantana mukayi daga bayan mu tana dauke da ruwan pure water da ta sayo muna tana fadin.
Haka suke masu ai komai bakin cikin ku kuwa sai kun gansu a cikin gidan nan wa yanda sukai gadon mugun abu a zuciya.
Duk da zancen nata ya dakeni a zuciya don nasan gun innan mu take nufin sun gado bakin halin ta manta da nata halin ita garesu.
Ko taga yadda na danyi da fuskane sai cewa tayi ga ruwa mai sanyi kusha na juya wurin asamu din ina fadin karba an gode anty lantana.
A waje na samu innan mu bakin baranda tana jiran shigowan mu da sauri na karasa jikin inna din sai hawaye suka zubo min lokaci guda don murna.
Sa,adatu na shiga part din mu take fadin inna bani makulin kofan nan na baya a bude a shigo da kaya ta mika mata a daidai lokacin ne aka fara shigo da kayan da muka zu dashi din na tsaraba da ya sayo muna.
Yayin da lantana ta koma ta kasa ta tsare a kofanta taga an shigo da abinda muka zowa inna dashi gidan zuwan mu.
Drivers din basu tsaya ba kamar yadda ya umurce su da sun sauke mu su juyo da mota daya zasu bar daya a gurina a nan don zirga zirgan mu a garin.
Haka yasa suna gama sauke kayan sukai muna sallama duk da nasan ya sallamesu hakan bai hana na kara masu alheri ba da zasu tafi.
Falon na inna ya hargitse da hayaniya lokaci guda kowa sai fadin albarkacin bakin sa yakeyi a lokacin kan mu.
Gyaran muryan da Abba yayi yasa kowa natsuwa a falon nan aka shiga gaida shi da dawowa gida yana amsawa sadiya ce ta taso ta rungume shi.
Farin cikin Abba bai boyu ba ga ganin yadda muka sauya gaba dayan mu yake fadin wai sadiya ce wanan ko yar gidan gwaunan jahan nan ?
Duk aka kwashe da dariya a falon sai lokacin na fito daga cikin daki ina fadin Abba sannu da dawowa ya washe baki don gani na yana fadin a, a Abu kune haka tafe ?
Yaya shi maigidan naki da mahaifiyar shi tare da yan uwan shi shine tambayan Abba a gareni cikin nuna jin dadi da rikon da suke min a can.
Allah sarki ABU CIKIN DUHU SIRRINE yanzu shi Abba yana tunanen zaman mutunci muke dasu a baki daya har nayi wanannsauyin da yake gani a tare dani a yanzu.
Muryan Abban ne yake saka masu albarka kan kokarin da sukeyi damu a can hakan yana fadin wa yan nan mutanen sai godiya kawai Asiya.
Da cewan innan mu ya fadi sunan ta kai tsaye don jin dadin abinda idon shi ya gane mashi bai san na badinin dake a boye ba a lokacin.
An dan taba hira kafin ya mike don fita yana fadin bari je a nemo abinda za ai masu kafin yamma yayi ya fita.
Har kwana biyu ina gida iyakata na fito daga part din mu zuwa wurin Asabe da lantana mu gaisa in dawo dakin mu bazan kara fita ba sai kuma washe gari.
A rana ta uku da zuwan mune na shirya zuwa gidan su maizube don mu gaida su tunda mun saba sosai yanzu dan zaman mu da ita a abuja kafin mu koma chaina akwai shakuwa sosai a tsakanin mu da ita yanzu don lokaci lokaci muna waya dasu.
Don idan nabi ta mutanen dake shigowa ba zan fita zuwa ko ina ba garin nan don tsaraban da ina ta zauna ta rabawa mutane unguwa da yan uwa yasa suke shigowa gaishe mu.
Cikin wani dinkin yan mali na shdda marron colour dinkin har gwiwa yakai min ga farin lace da akai mai kwaliya dashi duk jikin kayan.
Duk da ba dadin daura zanin nake ji a yanzu ba haka dai na daure na daura don sanin gidan da zan tafi wurin malam ne mu gaisa amma da abinda zai kaini kuma a kasan zuciyana.
Mun fito a cikin shiri na tsaya da inna muna magana take fadin idan mun fito mu gangara mu gaida wasu yan uwanta nace to inna.
Ni da sa,adatu ne a gaban motan tana nuna min wasu sabbin gina har na dauki hanyar da zai kaimu gidan malam din.
Muk tsaya a kofan gidan malam din da mota na bude muka fito suka kwaso kayan muka shiga ciki.
Farko munci karo da kishiyar su wace itace amarya a gidan tana ganin mu take fadin shike nan ma yaya ga wace zamu gaidawa anjima tazo har gida.
Nan suka fara fitowa suna muna sannu da zuwa muna amsawa kafin mu zube a dakin maizube ana sabom gaisawa da yaushe rabo ?
Munyi hira sosai dasu kafin kafin su watse suh bar daki ya rage sai mu da ita take tambayana ya bayan rabo ?
Na danyi murmushi kafin nace wallahi maizube sai alheri saidai har yanzu muna nan kamar yadda kika sani.
Ta dafe kirji tana fadin ban fahince ki ba zainab kina nufin har yanzu ba wani abu a tsakanin ku dashi ko me ?
Kallon sa,adatu dake zaune nayi sai na kawar da kai da sauri ta gyara zancen ta da fadin har yanzu ace ba shiri dake da yan uwan shi haka ?
Sa,adatu ta cabe da fadin wallahi maizube nima shedane kan hakan dan zuwan nan da nayi kwana biyu sai dana sheda hakan.
Nan ta shiga ba maizube labarin abinda ya faru tsakanin mu da mami a gidan ta ranan tace ikon Allah wanan matar da karfin hali take ashe.
Zamani na abinda dan ka ya kwaso har idan baida illa akaima sai ka ruguma da hannu biyu tunda ba Allah ya hana hakan ba.
Saidai idan da illa ga abin zaka nuna kinsa gareshi har sai ya gane abinda kake nufi da hakan.
Amma wanan kamar tana jayayya da ikon Allahne hakan shiyasa nake son na bar masu gidan har danta na fada a sanyayye ina dukar da kai kasa duk suka kaleni.
Ki bar mata danta anty ai sai taji dadin hakan tayi nasara ke nan a kanki wallahi ke suka samu sukewa hakan da nice da duk sun gane kuren su har wa yan nan yan matan gidan nata masu yiwa mutane kallon raini din.
Amma kice zaki bar mata danta dama ai haka take so ita ki barshi din tunda dama ba zaman ku a tare take so ba dashi.
Tana fadin hakan ta mike tsaye tare da fadin ni barin kewaya kinji fitsari ya cika min mara tun dazun wallahi ta fita daga dakin.
Maizube ta kalleni tana fadin amma yanzu kun daidaita da mijin naki a tsakanin ku nan ma kaina iya kada mata alaman a,a takaice na dan fada mata abinda zan iya don ta fahinceni.
Hankalin maizube yai matukar tashi a lokacin sai maimaita cewa takai har wanan lokacin kana zaune da mutum kamar dutse ba abinda ke gudana a tsakanin ku haka ?
Gaskiya wanan ba abinda za a kyaleki bane zainabu don a gaskiya kina cutuwa da yawa sai dai dole ki san yadda zaki bulowa mutane da maganan a yanzu.
Maizube wanan ba wani abu bane illa ranshi daya fita ga mata sai yan uwan shi maza yake bi shine matsalanshi kawai.
Jam jam wa,iyazu billahi wanan abin da muke ji dauri a jakkar magori shine ya kawo garemu yanzu ?
Shigowan sa,adatu dakin yasa mukai shiru kowa da abinda yake sakawa a zuciyar shi cikin mu a lokacin.
Anty muje kinsan ba nan kawai zamu tsaya ba gashi malam bai dawo gida ba har yanzu.
Zan dawo na yini a nan na fada ina mikewa don nasan maizube din zata fahinci mai nake nufi da hakan dana fada ai.
Mukai masu sallama muka fito daga gidan zuwa gidajen da inna ta umurce mu da mu tafi idan mun fito gidan malam din har gidan mahaifiyar Lantana nasa muka je mukai mata alheri bayan mun gaida ita sa,adatu ta cika fam dani kan zuwan mu gidan.
Sai bayan la,asar muka dawo gida a gajiye mun samu wai anyi fada da innan mu da anty lantana wai an fake da zuwan mu Abban mu yana shiga lungun inna ko wani lokaci yanzu.
Wanan maganan shi ya kawo fitina har suka kaure da fada a tsakanin su don kishiya bata raina abin fada kullun.
Ana hakane muka shigo gidan a daidai lokacin da Lantana ke fadin mijin yae taki dake yankan kai yana turo maku kudin jini kuna kashewa keda ubansu.
Muka karasa shigowa muka samu ko wace na tsaye cirko cirko rayukan su a bace sunyi shiru don ganin mu.
Kamar ba zan tanka masu ba har na dan wuce na juyo ina fadin haba innan hakan ba girman ki bane yanzu ai shi kadai na fada na shige part din inna abina.
Saidai ina tunanen a raina wanan maganan ke nan ina ga sun san gaskiyan ko waye mijina a gaba me Lantana zata fadawa innan mu ke nan ?
Dakuwan da muka dawo dashi daga gidan wata yar uwan inna na bude ina rabawa kannen mu kan na fara ci na dibarwa yayan lantana nasu akai masu.
Nan sa,adatu ta hau fada ba za a basu ba ai yanzu muna ji ta gama zagin innan mu da mijina tana masa kazafin da ba shi ba a tsakar gida.
Nace naki ne ko nawa sa,adatu duk me tayi don kanta ai itama ta haifa kuma zasu girma ai taji idan da dadi abinda takeyi din.
Inna ta shigo nake mata maganan don Allah ta bar biyewa haukan lantana suna zama daya haka a gaban mu.
Dama shi me son fada maka magana yakan jaka fadane ya samu kafan fada ma magana a cikin fada din.
Yar nan bar wanan matar mara hali ko yaushe ita burin ta shine taga ba, a zauna lafiya ba a gidan nan.
Nan dai na bawa innan mu hakkuri aka bar zancen kowa ranshi ba dadi ga abinda ya faru din ranan.
Sai bayan kwana biyu ina kuryan dakin inna kwance da dare bayan kowa yayi barci inna ta sameni ta zauna a bakin gado inda nake kwance.
Na dago da sauri ganin ta shigo ta zauna a wanan lokacin nasan magana ya kawo ta wurina ke nan.
Yar baba meye damuwan ki da har kika kasa fada min kike shiti yankewa kanki hukuncin da bai dace ba badon sa,adatu taji kudirin ki ba kan hakan.
Wani abu ta fada maki nayi inna na tambaya cikin mamaki don na manta da munyi wanan zancen a gabanta.
Hukuncin da kike shirin dauka don kawai mahaifiyar mutymin nan bata kaunarki da danta har yanzu.
Wani dan murmushi na sake a fuskana kafin na fara silalo da hawayen takaici na dago kai na kalli inna cikin karfin hali na toshe bakina ina fadin .
Inna ba don mahaifiyar shi nake son rabuwa dashi ba don akidarshi ce daya kaucewa addini nake son barin shi.
Wani ka)on mamaki inna tayi min kafin tace dani kin ko san abinda kike fada yar nan mutum kamili kamar wanan zakiwa sheri don kawai bakya son shi ko me zaki mai wanan kazafin ?
Kallon ina nayi nan dan lokaci kafin na girgiza kai ina hade wani kololon bakin ciki daya tokare min makogorona dama nasan za a rina idan na fito masu da wanan zancen ai.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.