Complete Hausa Novels

Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel

Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 73 of 139

Ina kwance a dakina duk da hasken ranan daya gauraye daki a lokacin ni duhu nake gani a dakin ko ina saboda daci da radadin da nake ji a zuciyana.
Ga tunane ya tsaya wuri daya cak don ban san abin yi ba a yanzu don banda wani mafita da zai fisheni ga kangin shi a kasan mutane.
Ina daga kwance kaina na kallon sama saboda nayi kukan har na gaji nabawa kaina lafiya don idona daya fara yi min dishi dishi a lokacin.
Jin an budo kofana baisa na dago kai naga mai shigowa dakin ba a lokacin illa ina kwance a yadda maishi ya sameni.
Tun daga kofa ya hangoni yadda nake kwance din nayi motsu mutsu dani alaman nasha kuka har nagaji tun daren jiyan.
Jikinshi yaji yai mai sanyi a lokaci guda shi kanshi yasa bai kyauta min ba yana tsaye ya rasa abinda zaice min sai faman kallon .
Kallona ya tsaya yakeyi ya rasa kalman da zai fara min magana dashi wanan ne rana na farko daya taba jin kunyar wata ya mace a rayuwan shi bayan mahaifiyar shi.
A da kan bai dauki abinda yakeyi a matsayin wani abu ba face holewarshi da lokaci kawai sai gashi yau yarinyar daya raina ma wayau a da ya fara jin kunyarta a duniya.
Da kyar ya iya kaiwa zaune a bakin gadon a kusa dani yayi gyaran mutya yana fadin lafiya kike zainab na ganki haka ?
Ban dago kai na iya kallo shi ba tunda ya zauna a wurin ina a yadda nake a kwance din har lokacin dan girgiza kai yayi kafin yace .
Wai bakiji ina magana dake bane zainab meke faru dakene kika koma haka lokaci guda ?
Jin abinda ya fada yasa na dan juyo kadan na kalleshi a cikin takaici da jin hsushi da tsanar shi lokaci guda daya sauka min a zuciyana.
Da kyat na daure cikin sanyin murya nace damuwata ba matsalan ka bane yaya abinda ya shafeni ni ya shafa.
Yanayin muryan da nai magana dashi dole yaba mutum mai saurare a lokacin tausayi a lokacin don gaba daya muryata ta dakushe dan kuka.
Yace amma ai hakkin ki yanzu a kaina yake duk wani damuwan ki ya shafeni ko don haka ki fada min damuwan ki nace ko menene ?
Ko kuma a yadda kika ganni a daren jiyane ya sakaki daukan wanan matakin a yanzu kina son ki halaka kankine ko kuma addu,a ya kamata ki min a matsayina na mijin ki a yanzu.
Addua ?
Addu,a fa kace ?
Kai bakaiwa kanka addu,a ba ka daina wanam halin sai nice zan ma addua a karba min ?
Yaja dogon numfashi bayan jin abindana fada ga mamaki daya hanashi kwakwaran motsi don dai yasan girma ya gama faduwa ke nan .
Inaga nasan sauran abinda yake aikatawa bayan wanan ashe da rashin kunyar yafi wanan da bai taba zato ba a wurina.
Numfashi ya sake ja tare da fadin to tashi muje asibiti a dubaki idan lafiya kike a yanzu ?
Barshi don ni lafiyata kalau a yanzu yaudaran ka kawai ne abinda ya dameni a zuciyana .
Ya jafar ka cuceni ka yaudareni ka yaudari iyayyena da suka aura min kai a matsayin miji yau suji mijin da suka aura min suke kiranka da surukin kirki ashe tsohon mashayin dan giyane haka basu sani ba.
Haba ya jafar ya kake son nayi da rayuwana da halinda muke ciki da mahaifiyar ka da yan uwanka zanji ko da wanan halin rayuwa naka na boye da Allah ya baiyana min a daren jiyana gani.
Lokaci daya yaya kazo kashiga rayuwana ka nuna isa da gadaranka a kaina don kawai ina karkashin mahaifiyar ka ba tare da kayi tunanen nawa rayuwan ba.
Na hakkura a hakan nake zaune tare dakai don biyayya ga iyayyena duk da mutane da dama sun san da wata manufa ka aureni don ni din ba ajin auren ka bace ai.
Amma haka na hakkure nake zaune tare dakai duk da mami har gobe ta nuna bata ra,ayin zamana dakai.
Wace matakace da kai yaya ranan da ka tsaya gabab mahalicin ka don kare kanka a wanan rayuwan ka tuna fa shi mutum ba a bakin komai yake ba ga Allah.
Yanzun nan Allah na iya ikonsa a kanka kana takama da lafiya da arziki da ilimin ka zai iya mashe ka gawa lokaci guda.
Ko kuma ya karbe lafiyan da kake takama dashi lokaci guda zai iya maisheka miskini mara moriya kana kuma a raye.
Kukane yazo min har na kasa karasa zancena na juya na fara kuka sosai a cikin tashin hankali da bacin rai ga abinda ya faru din.
Kai ya dukar a kasa don wanan maganan dana fada yafi komai nauyi a wurin shi sai yaji wani irin gumi yana feso mashi lokaci guda gashi ya rasa abinda zaice dani don yasan gaskiya na fada mai .
Don nauyi mami da yan uwanshi a iya su zancen zai tsaya idan sun san da haka nawa iyayyen kuma da wani ido zai iya kallon su idan har sunji.
Don haka sai ya zuba min ido kawai yana kallona da mamaki kamar ranan ya fara ganina a duniya.
Nima ban fasa kukan takaicin da nakeyi ba can naji yakai hannun shi saman kafadana yana fadin is OK kukan ya isa haka nasan na aika abinda Allah ya haramta ga musulmi .
Saidai ina rokon ki da ki taimakeni ki mun adduan Allah ya rabani dashi har abada a rayuwana yadda ya fada a cikin wani murya mai ban tausayi zakace bashi yake maganan ba.
Majina na share da kyalen dana aje a wurin don share hancina tunda safe kafin na dago kai ince ko nayima addu,a yaya tunda kai baka da niyar bari ba fasawa zakayi ba ai.
Shikan yau mamakin zainab din yakeyi a ransa sai fadin yake ashe haka wanan yayinyar take ina kallonta shiru shiru ashe akwai aiki ja a gabana rana data gama gane koni waye ?
Saidai a fili yace waya fada maki bana addua akan hakan ko yaushe abune dai idan Allah ya jarebaka dashi yana da wuyan sha,ani.
Duk cikin maganganun da yai min a lokacin babu kalman ban hakkuri ko nadama a tare dashi don a gadarance yake fadan maganan shi kamar yadda ya saba idan yana magana.
Kinci abinci yau ya tambaya a karshe banza nayi dashi ba tare dana bashi amsan tambayan nasa ba sai ajiyan zuciya da nakeyi don kukan dana sha a ranan.
Kinga yanzun dai ki tashi kiyi wanka ki fito mu sauka kasa kici abinci don kada wani ciwo yazo ya kamaki kuma ?
Ba zan iya cin komai ba don bakina bai da dasin cin wani abu a yanzu na fada ina gyara kwanciya ta hanyar dunkulewa a wuri daya.
Yana zaune shiru banji ya motsa daga inda yake zaune ba sai can naji yayi ajiyan zuciya da karfi ya mike tsaye.
Ni a zatona ya fice daga dakin ne a lokacin ashe ban dakina ya shiga ya hada min ruwa mai zafi sai ji nayi mutum yana kokarin cicibana lokaci daya.
Don Allah yaya ka bari bana jin yin komai a yanzu zan tashi idan zuciyana ya sake min bai tsaya saurara min ba sai daukana da yayi dani yana shiga ya tsomani a cikin bahon wankan dake ban dakin .
Lokaci guda na sake wani irin ajiyan zuciya a tare dani juyawa yayi ya fita ya ban wuri a yanzu kan idona ya bushe don na nemi kuka na rasa a idona.
Haka na daure na watsa ruwa tare da alwal bayan na cire tufafin dake jikina na samu har na gama na fito a zatona yana dakin har lokacin don haka ban yarda na fito ba sai dana leka naga baya dakin.
Zani da hijjab dina na dauko a wardrobe na nufi inda nake sallah na tada sallah ina sallah naji an kwankwasa dakin an shigo.
Ashe julie ce ya umurta da takawo min abinci ganin ina sallah tana ta mamakina har tana tuntube a dakin wurin aje kayan abincin da ta shigo min dashi.
Saida na gama sallah na mika kuka ga ubangiji kafin na mike na samu wasu kaya na zura a jikina ban ko kalli abinda ta aje min a dakin ba.
Na koma bakin gado na zauna ban koma kwanciya ba sai ga mama da sallama a dakin a karon farko data shigo dakin nawa ke nan tun zuwan mu kasan.
Amsa sallaman nayi halimatu na biye da ita a baya mama ke fadin zainab ashe bakiji dadin jikin ki bane sai yanzu mikin ke fada muna.
Ni na dauka yau yana hutune ai kuna tare shiyasa ma ban yarda wanan yar taragagan tazo inda kike ba don yau banji fitan shi ba shima.
Dan dariyan yake cikin katfin hali na kakaro a fuskana ina fadin tun darene bana jin dadi mama .
Tace haka dai shima ya fada muna ai kwa fadawa mutane tunda gamu a gidan ai yanzu ina dadin hakan da kukayi ai ko sannu kawa mutum.
Tana kai aya ta dora da fadin yace kinki cin komai tun safe ga abinci nan yasa a kawo maki sai ki daure kici don Allah don yace yayi yayi kici kin kiya.
Badon naso ba don biyayya ga mama Ramatu na daure na kurba ruwan shayin bayan shi ban taba komai ba a kayan ina gamawa na koma na kwanta har lokacin suna dakin tare dani.
A bakin su nake jin wai ya fita zuwa asibiti ya duba hjy amma ba zai dade ba zai dawo a raina nace shi dai ya sani don ni na tsane shi a yanzu.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.