Complete Hausa Novels

Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel

Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 84 of 139

ZAINAB IDRIS MAKAWAZuwan fadila garin yayi muna dadi sosai dan yanzu muna sakewa sosai har mun fara fita mu kaidai da kafa muna dan zaga unguwa.
Saban da can da muke zama a tauye a gidan bamu fita da mun dawo school munci abinci muka shiga sallah magariba bamu fitowa sai kuma gobe idan Allah ya kaimu zamu fita.
Ranan da babu karatu kuma a daki zamu wuni zaune sai mun gaji zamu dawo falo mu zauna mu danyi hira kafin mu shige.
Yanzu gidan ya koma muna kamar muna gidan mune Anchau a gaban iyayyen mu don yadda muka dauki fadila takar wata jinin mu.
Abu na farko data fara yi bayan zuwan ta shine karban girkin tana girka muna irin abincin mu wanda muke iyaci.
Don komai akwaishi saidai dafuwan ba iri daya bane da nasu na can sai masu girkin suka koma kallon ta kuma idan tana aikin.
Suma sai ya kasance basa iya cin kalan abincin mu idan ta girka wanan ba karamin jin dadin hakan nayi ba don yanzu kan muna cin abincin mu cikin sakewa ba wani kyamar komai a gare mu.
Ranan muna zaune da dare fadila ta jeho min tambayan da banyi zato ba wai zainab sai naga kamar har yanzu ba a dakin mijin ki kike kwana ba ?
Tambayan yazo min a bazata da sauri na dan dago kaina dubeta kafin in saki murmushin dole ina fadin kai anty fadila ke nan.
Ina kwana a can mana saidai ba kullun nake zuwa part din nasa ba na bata amsa a sanyaye ko ta fahinci wani abune ga amsan dana bata .
Sai cewa tayi amma ya kamata ki mai da hankali sosai ga mijin ki baki tunanen haihu ne har yanzu a rayuwan ki.
Buri ko wace ya mace ne idan anyi aure taga an fara aje iyali tsakanin ta da maigida tundai wanan uwar mijin naku da bata son ki da danta ko kadan.
Ko yanzu ta daina nuna maki wanan tsanar da take nuna maki da farko ne don irin su wani lokaci idan sunga an fara aje iyali a tsakani suna zubar da makaman yakin su su so matar a karshe ko dan haihuwan dake tsakani.
Shiru nayi ban tankata ba har ta gama bayanin ta tadaro a karshe da fadin na sha fada maki tun tuni ki dinga kutsa kanki gareshi zainab ko zaku samu shakuwa da juna.
A hankali na dago kai sai ga hawaye suna sulalo min a fuskana da sauri tace ki rufa min asiri ki daina kukan nan banzo kasan nan ba saida wasu sharuda da aka kidaya min su.
Yarda da amanan dake tsakani mu yasa har na fito maki da wanan maganan a yanzu don dan fahintar danayi na yadda kuke zama a tsakanin ku.
A hankali nakai hannuna ina share hawayen dake fuskana tare da fadin insha Allahu anty ba zan ja maki matsalan da aikin ki zai tabu ba a wurin shi zan dinga kiyayye duk wani abinda zai jawo maki matsala a wurin shi.
Zancen gaskiya kuma anty tsakanina da yaya babu sakewa ko shakuwa a tsakani mu har yanzu muna nan yadda kika san mu dashi sai ma wasu halaiyan da ba,a san yana dasu ba a can sai a na nasan su.
Don gaskiya sai nayi shiru na kasa fada mata komai don rashin ganin dacewan hakan ko yayane dai shi din miji ne a gareni kuma tankar dan uwa yake a wurina.
Tona mashi asiri kamar tonawa kaina ne yanzu don ko inna ba zan iya fadawa maganan nan haka kai tsaye ba don haka sai naja bakina nayi shiru ga fada matan.
Itama bata matsa ba sai ta sani sai naji ta dauko wani zancen tana fadin kinga ai dama dole kiga wasu halaiya na daban dabaki saba dashi ba don haka ki daure kici jerabawan ki zainab.
Allah ya nufa na bata amsa saiga halimatu ta fito da wayana ga hannu tana fadin an kiraki ga waya na karbi wayan daga hannun ta ina dubawa.
Layin Nigeria ne aka kirani dashi don haka nayi kira nima kira uku aka dauka nayi sallama muryan sa,adatu ne a layin .
Ina dauka take fadin yayan mu nayi waya yau innan mu ta saya min da kudin da mijin ki ya aiko mata dashi shine ta diba ta sai mun waya dashi.
Nace Sa,adatu nayi maki murna da samun waya ina innan mu da sauran yan uwa tace duk suna lafiya kalau nace innan mu tana kusane ?
Ta amsa min da gata nan nace a bata wayan ta karba muka fara gaisawa nace inna kin daina kirana .
Bana son ina damun kine yar mairo kada mijin ki ya daukemu marasa hankali tunda shi yana kira lokaci lokaci shekaran jiya ma ya turo muna kudi nida mahaifin ku.
Don Allah kiyi muna godiya nace to inna sai kuma tace ni kan nace ba wai yanzu cikin ki yakai wata nawa ne musan shirin da zamuyi.
Ciki inna na tambaya da mamaki tace eh a sanyayye ciki mana banaji kamar ana fadin cikine dake ba kwanakin baya da mukayi waya daku.
Banda komai inna na fada ina dan dariya Allah ya kawo mai albarka naji ta fada a sanyayye kamar bataji dadin abinda na fada ba na zancen cikin.
Muka daiyi sallama na kashewan ina ajiyan zuciya koda na dago kai anty fadila na kallona tun lokacin dana ambaci cikin .
Kinga zance na ya fara fita ko duk wata uwa ta aurar da yarta tana son jin wanan albishir din mai dadi a bakin ta don samun karuwa.
Ranan wanan tunanen ne ya hani barci sai juyi nakeyi ni kadai a daki don halimatu tana dakin anty fadila tun zuwanta a can ta koma kwana.
Babu kuma daman ince ta dawo daki ta gane a dakin nake kwana ba wurin shi ba ashema duk boyona ta gane hakan do wayau babba bai daya dana yaro.
Nayi tunane sosai kan sakon da yake turawa iyayyena a kai a kai kinga ke nan ko na fadi wani hali nasa na daban ba lalai bane a yadda da hakan.
Don haka na bar wanan zancen a raina tunda nasan wanan abinda yakewa iyayyena yana daga cikin abinda mami bata so a gareni dama.
Tun zuwan fadila garin ba wani sakin fuska a gareta dashi sai dai gaisuwa ya amsa mata kamar yana tsanan ta fuska daure.
A kwana a tashi ba wuya a wurin Allah har gashi mun samu hutun makaranta mun gama zangon farko.
Halimatu ta rigani samun hutu don haka take gida a zaune tare da anty fadila kula kan yana bamu shi yadda ya kamata har nakan ji mamakin hakan a raina.
Har yakai muma mun samu namu hutun zamu dan huta a gida na kwana biyu ke nan duk da hutun ba mai yawa bane sosai.
Mun fara hutun mu dadi dadi sai nazo na fara samun matsala da ganin wanan Nabil di ya dawo gidan namu kamar da can baya.
Har yakai yanzu ma yana nuna min tsana irin wanda na fuskanta a wurin taju da farko shina wana sai yazo min da sabon sallon daya fara saka zuciyana a tunane.
Ranan dai na yanke shawara a raina zan gwada shawaran anty fadila in gani idan zai yi amfani a gareni.
Tun kan ya dawo gidan na caba kwaliya da ire iren rigunan da yake sayo min bana sawa don nuna tsirecin su a gareni.
Doguwar rigace mai guntun hannu baikai wuyan hannu har kasa ba sai wani uban tsaga dake iya nuna har cinyar mace idan ta zauna ko tana tafiya.
Na daure kaina da ribon ta baya don gashina yanzu yana samun gyara sosai saboda ina gyara a kai akai don zuwa school wani lokaci ma daga school zan tsaya in gyara kaina kafin azo daukana.
Kaina ba dan kwali dawowan shi yayi daidai da gama shafa komai na kamshi a jikina koda ya dawo bai samemu a falo ba daki ya nufa kai tsaye.
Na mike nabi bayan shi saida na tsaya na saita kaina a falin kafin in sa kai in shiga masa kai tsaye na tura kofan na shiga.
Yana tsaye a wurin fridge yana saka kankara a kofin daya dura ruwan giyan shi ciki har na karaso bayan shi bai sani ba sai ji yayi na kwanto mai a baya ina fadin sannu da dawowa yaya.
Wani irin zabura yayi cikin kaduwa da mamaki ya juyo yana kallona har ruwan nasa na kokarin zubewa lokaci guda.
Ya juyo yana fadin what is this noses zainab zaki zo min haka kin raini da yawa ko har yaushe kika fara irin wanan wasan haka dani.
Kaina na dukar kasa a hankali ina maijin wani iri a raina na disganin da yayi haka a lokacin .
Godiyana ga Allah mu biyune a part din lokacin babu kowa da bansan yadda zanyi ba ranan don da kunya ya rufeni gaban maishi a lokacin.
Dan marairace fuska nayi cikin daurewa duk da raina ya baci nace yaya kewan gida yau nakeyi yasa nayi hakan tunda kaine dan uwana a kusa yanzu.
Hannu naji ana tafawa a bayan mu da mamaki na waigo ina kallon mai shi wanan dai Nabil din ne a bayan mu daga shi sai tawul daure a kugun shi.
Yana takowa inda muke tsaye ganin shi a tube yasa nayi saurin dukar da kaina kasa da sauri dafa kafadan shi yayi tare da fadin .
Wellcome home dear yayi saurin baudewa tare da barin wurin da muke tsaye din ya nufi kujera da kofin shi a hannu ya zauna.
Wani irin juyowa nayi na watsawa Nabil din kallon tsana ido da ido yace a cikin yar murya ta yadda ni kadai dake kusa zan iya jin shi.
Mind you or else ya nunani da dan yatsar shi na hannu sai a idon yaya jafar din naji ya daka mai wani tsawa yana fadin .
Don't be silly Nabil dont you know she is my wife in life ko ka manta da warning din danayi ma a kanta ne tun farko.
Cikin wani irin murya ya dan rausaya kai yace Owoo wifery sam na manta da hakan ita din ne tana son min shishigi a rayuwa.
Ina tsaye sororo imani ya cika min zuciya da kalaman su lokaci guda na rasa maganan wanda zanyi nazari a cikin su yanzu.
Ko ma dai meye shi ya jafar din ya tsaya min a lokacin ya nuna ni wani abune ai a gareshi ga Nabil din.
Sai dai zancen Nabil din dake min warning a kan yaya din ne na kasa fassara ma,anan hakan gareni dayasa yake ban warning haka ?
Da karfin halin dana fara koyo a dan shiga mutanen dana fara yanzu sai ban yarda na fita falon ba don inga abinda Nabil din zaiyi idan na tsaya din.
Wurin da yaya yake zaune na nufa na zauna gab dashi ya kurbe abinda yake sha din tare da aje cup din yana fadin .
Zainab wai meke damun ki hakane yau kike wanan halin da ban sanki dashi ba da farko ?
Nace just ina dai son zama a kusa da kaine na fada ba tsoro ko kunya a idona ko kadan naga Nabil din ya juya zuwa sama.
Nabishi da kallo kafin in mike tsaye na bar wurin batare da kara furta komai na bar falon nasa zuwa part dina.
Gado na fada a yadda nake ban sauya komai nawa ba don bacin rai ina nazarin maganan Nabil a raina da yadda ya nuna min kishin shi a fili yau din.
Har nagaji barci ya daukeni a hankan ban sani ba sai ji nayi ana gyara min kwanciya na bude idona da sukai min nauyi ga barci ga kuma damuwa a tare dani lokaci guda.
Shine a kaina tsaye yana fadin zaki kwanta ki bar kofan abude haka kowa ya rufe kofan shi sai ke ?
Ka barshi hakan ba matsala bane na bashi amsa tare da komawa na kife a kwance ina jin shi saida ya dan dade a kaina tsaye kafin ya juya ya fita tare da rufo min kofan.
Saida na dan dade kwance a wurin kafin in daga a hankali zuwa kofan na rufo don tsoro hakan ya kamani lokaci guda.
Ban kwanta ba na cire kayan dake jikina zuwa rigan barci na na shiga ban daki na dauro alwala sallah nayi ranan sosai ina mika kukana ga Allah .
Kafin in daga saida naji duk wani damuwa ya fice min a raina lokaci guda na lalaba zuwa gado tare da kashe wutan dakin.
Washe gari ban leko waje ba don yanayin dana tashi a ciki haka kawai nake jin gabana yana faduwa min sosai.
Kamar banda lafiya da kyat na iya tashi na bude kofa misalin tara da wani abu na safe.
Komawa nayi na kwanta saidai kuma ba barci nakeyi ba nadai lefene kawai a saman gadon.
Naji an turo kofan yayan mu barci ne kuma kafin in dago in ce ba barci nakeyi ba anty fadila take fadin rabu da ita idan barci takeyi mana.
Ba barci nakeyi ba idona biyu na tashi tun dazun na fada ina dagowa daga kwancen mukai arba dasu.
Suna tsaye alama ya nuna sunyi wanka a lokacin don kowan su tsab yake a cikin shirin shi ina kwana nayiwa fadilan ta amsa tare da tambayana lafiya kike kuwa yau ?
Fuska na dan bata ina fadin jikinane dai wani iri nakw jin sa yau kuma haka kawai nake jin faduwan gaba a tare dani.
Kiyi addua koma meye Allah ya mayar muna dashi alheri daga haka mukaji takon takalman shi ya shigo dakin nawa.
Da sauri fadila ke gaishe shi ya amsa mata a irin yadda ya saba amsawa dan dama da halimatu ta gaidashi ya amsa mata din cikin dan sakin fuska kadan.
Takowa yayi har zuwa bakin gadon da nake a zaune tsakiyan gado yace ba zaki gaisheni bane ko har kin gama kewan gidan naki ?
Shiru nayi masa a raina nake fadin kai kuma kagama watsewan ka ba a yanzu ka fito kamar wani mutumin kirki dashi ?
Ai in babu me ganin ka Allah yana ganin ka bansan na fada a fili ba har ya jini ki min adduan hakan in daina nima ba yin kaina bane hakan.
Wani kallo nayi mai ina turo baki gaba tare da dan murgudawa ina kokarin kwanciya na bashi baya .
Ya juya ya fice daga dakin har na gaji da kwanciya natashi nayi wanka sai to one na fito falon gidan ban samu kowa a falon ba yasa na wuce zuwa dakin su kai tsaye.
Barcin su sukeyi hankali kwance don haka ban tayar dasu ba na dawo dining don duba abinda ke akwai na danci.
Waya na dauka ina video dashi ni kaidai a falon na rasa abinda zanyi inji sanyi har na aje wayan yana ta daukan abubuwa da kanshi a dining din saman jikina cikin mantuwa.
Bread na dauka da jam na dan fara cizawa jin shi nayi ba dadi a bakina duk son shi da nakeyi sosai ranan sai naji bai mun dadi ba sam a bakina.
Na dan taba hakana na aje ina wurin zaune kafin inji tako a bayana wani na tafe wurin na dan juya kadan don ganin mai zuwa a lokacin mukai arba da Nabil da yai kusa dani kamar zai shakeni.
Da sauri na mike tsaye tare da fadin innalillahi wa inna alaihim raji,un are you going to kill me cikin wani murya mai sauti na fada ina nuna shi da yatsa.
Ya nunani da yatsa shima yana fadin ki fita hanyar man dina idan ba haka ba nayi sanadin ki a gidan nan gabaki daya wanan shine warning na karshe da zan maki man bayayi dake.
Dan yatsana na daga sama ina nuna mashi nace Allah kadai yakai can ba wani mahaluki ba wallahi inkuma kana mamakine hakan ne ka gwada ka gani idan kaima baka bar duniyan nan with fulconfideces nake magana na.
Wani irin shu,umin murmushi ya sauke a fuskanshi kafin yace yarinya kina da karfin halin sosai nake gani.
Yatsun shi ya dan kada yana fadin nayi warning dinki akan jackson for the last time idan baki ji ba kuma ke kika sani.
Har ya juya nace bakaji ba mana sunan shi jafar ba jackson ba kuma ni din matarshi ce ta sunnan annabi don haka a yanzu dai banga wani mahalukin da ya isa yai min warning akan mijina ba sai mahaifiyar shi dake raye.
Wani kallo ya watso min yana kada kai nace kwarai zan rubuta in aje ko wani abu ya sameni a kasan nan kaine don ka fadi hakan da bakin ka .
Kafada ya daga min alaman ko oho nina sani yana sauke wani shu,umin murmushi na zaki gane kuren ki ai yarinya.
Ni kuwa a kasan zuciyana karfin hali nakeyi kawai don duk lokacin a tsorace nake dashi ina Allah Allah wani ya fito daga cikin dakunan gidan ya ceceni don na gama tsorata dashi saidai ban yarda na baiyana hakan ba a fili har ya gane hakan.
Ya juya ya tafi yana wani tafiya sai a ranan na gama kwankwance yadda yake ashe, zakace mace ce shi sak don in ba karya nakeyi ba ni har wetlips nagani a baki shi.
Ya tafi da kamar minti goma saiga halumatu ta fito inda nake tana fadin yayan mu kin fito ashe yanzun na fitone in dubaki ai.
Tana zama a kusa dani saman daya daga cikin kujerun falon ta kai hannunta ta dauki wayan dake saman jikina tana tabe tabe a cikin sa.
Ashe zata shiga ta samu wayan na recording sai tayi min serving din shi don kada tayi laifi a gurina idan ta fita kai tsaye.
Surutu take min ban iya bata amsa ba don sabon fargaban daya darsu min a zuciyana kuma na shi Nabil din kan abinda ya fada min kafin ya tafi.
Mikewa tayi da wayan a hannun ta ta nufi part dina tana shiga gado ta haye ta kwanta tana jagulan wayan haka na shigo na sameta a dakin.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.