Abu Cikin Duhu Complete Hausa Novel
Reading file: Abu_Cikin_Duhu_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 120 of 139
Kwance nake ringingine ina tunane umma ta shigo dakin ta sameni a hakan take f
adin tun kan ta karaso yata kin fara kewan gida ko ?
Jin hakan da nayi yasa na dago kai da sauri ina dan murmushi tare da fadin kai umma ina dai tuna wani abune daya daure min kai umma.
Nan na bata labarin abinda malam ya fada min ranan na kare da fadin umma shi nake tunane wa zai masa wanan aikin haka a cikin yan uwan nasu ?
Kai duniya ai in fada maki yata haka duniyan nan ta koma yanzu wallahi sam mutane basu da imani a zukatan su yanzu ko kadan.
Wanda bakai tsamanin ko tunanen zai iya cuta maka ba shine zai cutama din don haka ne akeso a kullun mutum ya mayar da hankalinsa sosai kan iyalin shi.
Zakiga mutum ya nuna maki so da kauna kamar ya hadeki a ransa don kauna amma shine zai koma baya yai maka sheri bari ma in maki na mahaukaci yan ciki daya ma a zamani nan sai su cutawa junan su fa.
In har hakan da kakan ki ya fada maki gaskiyane bai kamata yanzu a ce kin bar mijin ki a cikin wanan halin da yake ba a yanzu kinzo nan kin zauna haka zainab .
Saura kiris ki cin ma nasaran ki sai dai kuma shedan ya rudeki yayi maki huduban tsiya da kika bi kina kokarin goge ladan ki kan hakan.
Zainab ba zan cuta dake ba ko kadan yadda na dauki nafisa a gareni yanzu haka nake jin ki a zuciyana.
Don ke din yarinyace mai hankaki da sanin ya kamata don haka hakkuri zakiyi na mayar dake gun iyayyen ki ayita ya kare a tsakanin ku dasu da mijin naki.
Don zama da boyon ki a nan yanzu baida wani fa,ida a gareki zainab hakkuri ya kamata kiyi da mijin ki koda kin koma gida kici gaba da daurewan da kikeyi da farko a kansa kina masa addu,a .
In Allah ya yarda ubangiji ba zai bar wahalan ki ya tafi a banza ba zainab Allah yaga zuciyar ki da niyar ki a kanshi.
Shima kuma din nasan ya sani abu daine idan ka riga daka saba shi a rayuwan ka yana da wuyan bari ko kuma ki masa uzuri wata kila wani lalurane yake damun rayuwan shi har ya kasa kaiwa gareki zainab Allah masani.
Hawaye nake yi duk da nasan gaskiya umma take fada min duk a cikin zancem nata ya zama dole di inyi biyayya gun umma in koma gidan mu gaban iyayyena ayita ta kare din kamar yadda umman tace din.
Bakina na bude da kyar nace umma ba wai wanan zaman da mukeyi dashi bane matsala a gareni sai yadda mahaifiyar shi har yanzu ta kasa gane hakan a nata bangaren .
Take tsanana ni da iyayyena kan zamana da dan nata wanan shi ya saka bana kaunar komawa gidan shi a yanzu.
Ina ruwan ki da ita zainab ina tana gidan ta kina naki sai kun hadu ko kunje zata ganki kuma duk abinda zata fada shi ba zai taba daukan hakan ba tunda yasan hakkurin da kikeyi dashi ai.
Shike nan umma zan koma koda baizo din ba zan nuna masu nidin diyace idan Allah ya yarda da sauri umma ta riko min hannu tana saka min albarka ina amsawa a kasan zuciyana .
Haka nafisa data fita zuwa kasuwa ta dawo ta samemu da umman tana ban baki itama ta zauna sunayi tare a gaskiya nafisa da mahaifiyar ta mutanen arziki ne matuka.
Don yayan tane yayi kokarin neman mota don nasi yana ajiyene a gidan kamar photo kawai baya aikin komai suna kallon shi.
Motar abokin shi ya dauko mukai tafiyan dashi samako mukayi muka bar kaduna dan lokaci kadan muna anchau.
Sai ganin mu akayi kamar daga sama don ba wanda yasan da zuwan mu a wanan ranan.
Wanan dawowan yayiwa innan mu dadi sosai don nan take ta nuna cewa ai dama ba wani wuri na tafi ba gidan yan uwan ta naje ganin su .
Wanda hakan baiwa Lantana da tabi makwabta tana fada masu ai yaji nayi na gudu ba,a san inda na tafi ba .
Sai gashi na dawo gida a cikin salama sai hakan kuma yai mata zafi a ranta har ta kasa boye bacin ranta.
Taro na sosai su umma suka samu daga innan mu da yan uwana inda suke nuna su din yan uwan innane ga mutanen gidan mu din.
A nan suka wuni don umma basu tafi ba sai data gana da Abban mu suka dan tatauna kan matsalan mu Abba yace zasu zauna dashi ai suji dalili hakan daga bakin shi.
Malam kuma godiya yayiwa umma sosai bisa irin kokarin da tayi na dawo dani gida a cikin salama ba tare da rayuka sunkai ga baci ba.
Don Abbana shi kan bai boye yana goyon bayan jafar ba har lokacin don
nunawa yayi na koma naci gaba da hakurin da nakeyi da mijina.
Tunda hakan sirin mune baki daya dani dashi yanzu ai tunda bai rageni da komai ba bayan wanan matsalan kuma yace yana neman maganin hakan don kawo karshen matsalan dake damun shi din.
Kafin su umma su tafine kuma sai ga Abban ya canza shawara ya samu su umma a falon inna yana fadin ni hjy naga tunda yarinyar nan ganin mu dai tazo yi dama .
Ya kamata ta shirya ta koma dakinta kawai tunda dama lafiya suka rabu da mijin ta ai yin hakan kamar zai kara muna girmane a idon sa.
Da sauri inna tace a, a, a dai tsaya har yazo din aji ta bakin sa zaifi da sauri umma da ta fahinci hakan zai iya kawo masu matsala a tsakanin su tace hakan zaifi gaskiya.
Don haka basu bar garin ba aka saka ranan komawa na muna daki muna jinsu lokacin mutuwace kawai banyi ba don ta kaicin abinda abba din yayi min.
Shike nan ni nasan yanzu banda baki a wurin mami don wanan zai jawo min abin fada sosai a wurin su .
An aje umma zata dawo su rakani har abujan idan ranan yayi ita da maizube zamu tafi haka aka aje zancen komawan nawa.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ZAINAB IDRIS MAKAWAASSALAMU ALAIKUM YAN UWA MUSULMAI FATAN ALHERI A GAREKU KO YAUSHE ALLAH YA BAMU IKON BAUTA MASA AMIN, , ,
LITTAFIN KUDINE KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA YAR UWA ALLAH YA BADA IKON SAUKE NAUYI AMIN, , , , ,
Duk wani motsi da yunkuri da naso yi don daukarwa kaina fansa kan wanan halin na ya jafar iyayyena sun hanani motsawa .
Daga mai fadin yin hakan kamar tozarcine ai a gareshi sai mai fadin may ya ragani dashi da zan gujeshi ko don yadda ya dauki dawainiyar karatuna dana kanwata ai zan hakkura na zauna in rufa mai asiri ba tare da wani ya jimu ba.
Magana dayace ya karya min gwiwana shine maganan innan mu da tayi min tana fadin ki kara basa dama kiyi hakkuri ki koma ko Allah zaisa ya gyara nan gaba.
Idan kinga bai gyara halinsa ba kinga kina iya daukan mataki a lokacin ke nan don gaskiya ba zanso ace ki rabu da wanan bawan Allah ba ko dan kiyi sanadin kubutoshi daga halakan da yake ciki a yanzu ma.
Haka kuma mahaifiyar shi data sa ido taga karshen zaman ku dashi ko dan haka ba zan so ace kinbar shi a yanzu ba a daidai lokacin da yafi bukatan ki a kusa dashi ke nan yanzu .
Sai gashi kina kokarin goge ladan da ya kusa zama rabon ki a wurin Allah don ba karamin jahadi kike kokarin yi ba tunda har Allah ya fara kwatoshi daga halaka ta dalilin ki a yanzu.
Wanan kalaman na inba ne suka kashe min jikina sosai har na dinga zubar da hawaye don tausayin kaina da sauran yan uwan da suka samu kansu a irin halin da nake ciki a lokacin nan .
Ba wanda yasan irin yadda zuciyar ka yake ji a irin wanan zaman da mutum keyi da mai iri halin nan sai ma mutane ko sun sani din suyi kokarin dora maka laifi don kawai kayi kara na dan lokaci guda.
Don wata ko na sati daya ba zata iya daukan hakkurin da kai kakeyi a gidan auren irin wanan ba .
Irin yadda inna ta nuna min yasa na tattara komai na barwa Allah zan koma nayi hakkuri don abubuwa biyu zuwa uku don kwadayin na zama silar shiruwan shi.
Na biyu kuma don farin cikin iyayyen da naga komawan nawa suke bukata kawai gidan yaya jafar a yanzu.
Sai kuma uwa uba don mami da yan matanta da inna da umma suka nusar dani yadda komawan nawa gidan ya jafar din zai zafafa masu rai idan na koma don su burin sune suga nabar shi ga baki daya .
Sai kuma irin su Lantana yan bayan fage a garin mu dake da yawa wurin saka ido suga nabar gidan jafar din a samu abinfada a karshe.
Ire iren tunanen da nakeyi ke nan a raina har na amince da zuciyana zan koma gidan na rugumi hakkuri a zuciyana.
Ana gobe zan koma bayan magariba mukaji sallaman malam mijin maizube a kofa innan mu zan iya cewa a iya wayau na wanan ne karo na farko da malam din ya tako har gidan mu.
Bayan gausuwa da dan barkwancin da akayine ya bukaci kowa ya barmu a falon dani dashi a lokacin a haka suka fice suka barmu dani dashi sai dan shiru ya biyo baya bayan fitan kowa falon kafin ya kira sunana a lokacin.
Na dago kai na amsa a dan kunyace ya fara fadin duk da nasan sherin shedan ne daya rudeki har kika kai ga aikata hakan don kina ganin mu bamu damu da damuwan ki ba ko wani abu haka ?
Sai dai zainab ina son ki sani shi hakkuri bai taba faduwa kasa banza a rayuwan bawa duk mai hakkuri mawadaci ne watarana.
Don haka zainab ki koma dakin ki ki kara hakkuri na dan lokaci muga abinda Allah zai maki sakaiya dashi ga hakan.
Don yanzu insha Allahu kina kiris ne da ki cinye jerabawan ki fa Allah ya dora maki a gidan shi na kirashi yazo munyi magana dashi ta fahinta.
Jin hakan yasa na dago kai da sauri na kalleshi kafin in mayar da kan ina mamakin hakan .
Malam yace kwarai na kirashi ba tare da kowa ya san da hakan ba kuma yazo mun zauna munyi magana dashi ta fahinta ya fada min komai yadda ya daxe na kuma fahinci inda matsalan yake yanzu.
Basa wani a nan gidan yasan da zuwan shi ba garin nan ko a gidan nan naku bani tsamanin wani yasan da zuwan shi din.
Don haka yanzu sai kin kara jajircewa kan wanda kikeyi a baya zainab nasan kina kokari sosai amma ki kara a kan wanda kikeyi a baya.
Insha Allahu muna sa ran abunuwan zasu zo da sauki don mawuyacin abune mutum ya shiga wani kungiya su barshi ya fita a ckkin shi salin alin ba tare da wani tangarda ba.
Balle shi din da suke ganin kamar samun shi a cikin su wani babban kamu sukayi a hakan yanzu kuma yace zai fice cikin su ba tare da ansha wahala ba.
Jin hakan na dan dago kai a tsorace na kalli malam yace kwarai nasan ke baki san da wanan zancen ba ai burin ki kawai shine kiga ya bar aikata abubuwan da yakeyi ko ?
Kamar yadda mahaifiyar shi da yan uwan shi duk basu san da wanan zancen ba suma a wuri su.
Ba abin mamaki bane a wanan zamanin idan kaga mutum yana wandakan shi ka dauka ya samu damane kawai a banza kabar mutum kawai a yadda ka ganshi don bakasan zuciyar shi ba.
Tsorone ya kara kamani lokaci guda amma sai malam din ya kara wayar min da kai yadda zan fahinta.
A karshen maganan nasa ne na gane wa yan nan abokan nasa na chaina shi dasu kamar wani gungiya suke cikin sa da yasa ya jafar din kara fadawa a cikin halaka.
Ga kuma nan gida mai binshi da sheri da son ganin komawa bayan shi a kullun sun masa aiki tun yana karami da iyayyen shi basu farga da hakan ba.
Malam din yaci gaba da fadin don haka yanzu aikine ja a wurun ki ko kun koma din ba zaki zauna hakan ba ki kara komawa wuri wanan matar koda abinda zata kara baki a hakan .
Duk da nasan insha Allahu har in kinyi aiki da wa yan nan abubuwan da muka hada mai abubuwan zasu zo da sauki sosai kema kanki sai kinsha na tsarin jikin ki din zasu iya waiwayan ki a ko wani lokacin kan hakan.
Ya miko min wani dan ruwa daga cikin aljihun babban rigan jikin shi yace karbi wanan ki shanye duk yanzu.
Da yardab ubangiji saidai ta Allah ba nasu ba don wanan makaru ne sosai majarabi ne kwarai na sani.
Ina hawaye na karba da hannu biyu na bude dan goran nayi bissimillah na kafa kai na shanye kamar yadda yace inyi din.
Ya kara miko min wasu kulli da zanyi wanka da hayaki tare da wasu addu ,a da aka rubuta min zan dinga yu safe da yamma don tsari.
Da wanan tunane na zancen mu da malam na kwana a raina ina faman tunane a raina watau a zamanin nan ko wani gida da kalan nasu matsalan ke nan na rayuwa.
Zama haka kai sakw bayayi ke nan sai mutum ya hada da neman tsari a wurin Allah da yawaita sadaka da kyautatawa gun mabukata shine zaman lafiya ga bawa.
Washe gari karfe goma na safe muka bar garin mu cike da bacin ran rabuwa da gida da zamu sakeyi na tsawon wani lokaci kuma don ban sa rau yaya zai kara bari nazo gida kuma ba nan maza.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.