Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 10 of 227
Cewar Maleek Abiey ya saka dariya, ba team din Arsenal yake ba amman yana supporting dinsu domin sun san abun da suke yi ba kamar Manchester United ba.
“Kuma Arsenal din idan aka cire manyan yan wasanku biyu sauran ba za su iya yin komai da kansu ba”
Haka suka yi ta gardama akan kwallo da yan kwallo kai ka rantse da Allah su kadai a gidan domin muryarsu kawai ake jin tana tashi a bangaren, ba su ba ba Mahaifinsu ba domin tsohon dan kwallon kwando ne, ya san in and out na wasanin da yawa na duniya. A take laulayi da dan bacin ran da Maleek yake ji ya washe fess daman haka yake so ya zauna yayi ayi hirar abun da ya shafi maza tare da maza yan'uwansa, ya kan ji sakewa da sukunin zuciya da nishadi kamar kar a rabu, mahaifinsa kuma ya fi kowa fahimtar abun da yake so wannan ya saka yake kokarin faranta ransa.
AMEER POV.
“Me ya hada ka da Balarabe?”
Ya aje spoon din da yake cin abinci da shi ya kalli Momy ko be tambaya ba ya san ita ta fada, domin ita kadai ta san abin da ya faru kare da karau a gaban idonta aka yi komai.
“Tambayarka na ke”
Daddy ya fada rai a bace, sai kanensa suka kalli Ameer, ba za su ce basu saba gani ba sai dai ya zama kamar bakon abu ne a gurinsu Daddy yayi ma Ameer fada ko ya nuna masa bacin ransa akan wani abun ko da kuwa ran nasa be masa dadi ba.
“Aiki na saka shi yayi min shirme”
“Shi ne zaka daga hannu ka mari babban mutum kamar Malam Balarabe?”
Ameer ya masa kallon mamaki domin a gurinsa ba wani abun ba ne.
“Daddy a karkashinmu yake”
“Shi ya baka damar ka wulakanta shi?”
Daddy ya kalli Safna.
“Je ki kira Malam Balarabe”
Safna ta mike tsaye domin cika umarnin mahaifinta, Ameer ya bita ta kallo kamin ya juyo ya kalli mahaifinsa kamar yayi magana sai kuma ya saka hannu ya dauki spoon dinsa ya cigaba da cin abincin, Baba Balarabe ya shigo bakinsa kumshe da sallama, Daddy da Momy suka amsa masa ban da Ameer dake kara jin haushinsa har a yanzu.
“Ranka ya dade gani”
Daddy ya kalli Ameer fuska babu alamun wasa ya ce.
“Ba shi hakuri”
Not just him even Momy da kanensa sai da suka kalli Daddy with shock balle kuma da aka bawa umarnin.
“Hakuri Daddy for what?”
“For marinsa da ka yi”
Baba Balarabe yayi fararat ya ce.
“Babu komai Alhaji, ai komai ya wuce tun jiya, hakurin da ka ba ni ma ya wadatar”
Daddy ya daga masa.
“Babu ruwanka a wannan maganar, Ameer umarni nake baka ka bashi hakuri na ce”
Wasu takwayen numfashi ne suka fito da gudu daga cikin Ameer suka fita ta hancinsa suka suka shiga da gudu kai kace wani yakin duniya ake a jikinsa, ba komai ba sai bacin rai. Baya son ya kunyata Daddy a dole ya bude bakin da halshe ke hadewa da hakori ya ce.
“Ka yi hakuri”
Daddy ya daka masa tsawa rai a bace.
“Say his name and ask for his forgiveness”
Ameer ya kalli Daddy yana jin kamar ba a taba wulakanta shi a duniya ba irin yau.
“Ka yi hakuri Balarabe”
“Baba Balarabe”
Daddy ya maimaita.
“I'm sorry Baba Balarabe”
“In Hausa”
“Ka yi hakuri Baba Balarabe”
Ya fada muryarsa na rawa irin rawar bacin rai da bakincikin an saka shi bawa wanda yake gani kaskantacce hakuri. Daddy ya kara dowara da na shi.
“Ka yi hakuri Malam Balarabe”
“Babu komai na gode da karamci Alhaji Allah ya kara kusanci da ma'aiki”
Baba Balarabe ya fada cikin farinciki domin a gurinsa Daddy ya gama masa komai tun da ya mutunta shi duk da kasancewar a karkashinsa yake. Sai da Baba Balarabe ya fice sannan Daddy ya kalli Ameer da ya matse spoon din hannunsa hannunsa nata rawa kamar mai jin sanyi.
“Karka sake dagawa wanda ya haife murna balle har ka saka hannu ka mareshi, saboda yana neman abun da zai ci a gidanku ba shi yake nufin Allah baya son shi ba, kuma ba shi zai baka damar wulakanta shi ba, na baka dama ka ji dadi rayuwa ka yi yadda kake so saboda ina kaunarka, na barka dukiyata ka wataya ka yi yadda kake so saboda kar wani ya fika jindadi ko gata, ban yi haka saboda ka wulakanta na kasa da kai ba, ban yi haka saboda na nuna maka akwai banbanci tsakaninka da talaka ba, ban yi haka dan ka wulakanta mutumen da sai Allah ya tsayar da ni ya tambaye ni akan me na bar ďana ya wulakantasu ba, duniyar da ta tashi ka gani ban tara ta dan ta gurbata tarbiyarka ba”
Yadda ko wane harafi da lafazi yake fitowa daga bakin Daddy ya sanar da iyalansa bacin ransa akan abun da ďan da yake kauna fiye da komai a duniya ya aikata. Ameer ya saki spoon din ya mike tsaye ya fice daga harabar da suke karyar kumallon yana jin yadda duniyarsa gaba daya take tafasa tana fitarta da bakin hayakin kara mai matukar yaji da kaifi saboda bacin rai, da za a fasa zuciyarsa a yanzu wata kila da an tararda goraba da garwashin wuta a ciki. Bedroom dinsa ya shiga, duk wani abu da yake a kasa sai da yayi ball da shi yana ta buga kafarsa a kafa yana cizon baki kamar zai fasa Iips din.
“Duk saboda kai Maleek aka min wannan abun”
Ya nufi gurin da ya saba aje keys dinsa ya dauka ya fice. Kamar wanda baya son rayuwarsa haka yake tukin yana sauka daga kan titi sai kuma ya hau, sa'arsa daya babu motoci sosai a titin unguwarsu. Gurin daya yada zango a jiya a nan ya sake yada zango a yau din ma, sai dai a yau cikin motarsa yake zaune bayan ya bude murfin motar yana ta kallin itatuwan dake gurin, tunanin abun da zai yi rama wulakanci da Maleek yayi masa amman ya sake ta ina zai rama idan ya kulla wannan ya kwance wacan.
“Sannu dai”
Ya ji an fada bayan mintuna uku da wucewar wata mota ta gabansa ta dawo baya ta faka bayansa, dagowa yayi ya kalli kyakkyawar budurwar da idanuwanta suka taba arba da ita, kunnensa na kokarin turawa kwakwalwarsa daddadar muryarta domin tuna inda ta taba jin muryar.
“Sannu dai”
Ya samu kansa da amsawa duk da kasancewar yana cikin bacin rai.
“Kamar kai ne mutumen jiya mai bura ko?”
Yayi murmushi da be san ta inda ya fito masa ba ya fito daga cikin motar.
“Shi ne”
“Yau ba busar ko kana cikin damuwa ne?”
Ya kalleta da mamaki a fuskarsa.
“Kina nazartar halayyar dan'adan ne?”
Ta yi murmushin daya kara mata kyau.
“Ina zaune tare da mahaifiyata, ina yawan fahimtar damuwarta, hakam ya bude min kofar fahimtar damuwar wasu”
Ya dan tabe baki try to smile sai kuma ya boye shi.
“Wani ne ya bata min rai, ina ta kokarin ganin na rama that's why I'm here”
“Miyasa ba zaka yafe masa ba?”
“Be cancanci yafiya ba, ya wulakanta ni kuma ya saka mahaifina ya wulakanta irin wulakancin da ban tana mafarki ba, yayi min abun da na fi tsana a duniya”
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.