Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 174 of 227

Ameer ya amsa da kai yana kallon Ummi dake kallonaa with so much joy.

“Good Morning”

Maleek da Mahmood suka gada baki gurin furtawa bayan sun gama kallon junansu da mamaki, su ma dai da kai ya amsa musu. Abiey ya mike tsaye da murmushi a fuskarsa ya ce.

“Good, idan ka gama ina son magana da kai Son”

Maleek ya mike tsaye daman tun shigowar Ameer da Waira a dinning din yake jin kamar yana kan ƙaya. Abiey ya juyo ya kalleshi

“I guess you're not the only Son here, i'm taking to Ameer, shi nake nufin idan ya gama ya same ni a ciki akwai maganar da zan yi da shi not you”

“O.... O.... Okay...”

Maleek ya fada har sau biyu a ukun ne ya samu hada kalmomin, hakan kuma be saka shi fasa barin dinning din ba, suka fice tare da Mahmood suna kuskus, Namra kuma ta nufi stairs. Sai da Abiey ya fice daga sashen sannan Ameer ya kalli Ummi da mamaki ya ce.

“Me yasa Abiey yake min haka this time? Is he up to something?”

Ummi yaja kujerarta baya ta mike tsaye ta nufi inda yake zaune ta shafa kansa ta sumbanci saman kanta ta kwanto da shi jikinta.

“No ko kadan, addu'ar da na dade ina yi ce Allah ya karba min a yanzu, farinciki da na dade ina son samu a tare da duka yayana ne Allah ya kawo min cikin sauki”

Sannan ta kalli Waira ta ce.

“Waira ni ban tsane ki ba, karki kalleni a baibai, kawai ina kokarin ganin na shirya tsakanin yayana ne”

“Anjima nake son na tafi”

Waira ta fada, Ummi bata ce mata komai ba ta saki Ameer ta nufi hanyar dakinta. Ameer ya mike tsaye yayi serving dinta sannan ya zuba na kasa.

“Abiey yace be yarda ki tafi ke kadai ba, sai dai a rakaki kuma sai an sanar da jami'an tsaro ina ganin ya kamata ki hakuri har zuwa gobe saboda ayi komai cikin kwanciyar hankali, kuma Maleek da zai raka ki zai samu lokaci ya shirya kamin time din”

“Bana son kowa ya raka ni, a garin ba a karba baki, kuma za a iya cutar da wasu saboda ni, ko kuma ma laifina ya yafe su”

“No ba zan iya bari ki tafi ke kadai ba Waira, ko da kuwa kashe wanda zaku tafi tare za'ayi, i know baki sona a kusa da ke, shiyasa da Abiey ya ce na rakaki na zabi Maleek ya rakaki, saboda kin fi sonsa kuma hankalinki zai fi kwanciya idan yana tare da ke sama da ni”

Kamar tace masa kai ma ba tsanarka na yi ba, kawai da zancen aurena da kai ne bane so, sai kuma ta samu kanta da jin nauyin kasa furta haka. After sun gama breakfast din Ameer ya nufi dakin mahaifiyarsa wato Ummi, first tambayar da yayi mata is.

“Kin san abun da yasa Abiey yake son magana da ni?”

Sai ta girgiza masa kai.

“Ban sani ba, be fada min zai yi wata magana da kai ba ban san komai akan abun da zai tambayeka ba”

Ya juya ya fice daga dakin yana tunanin kondai Abiey zai roki wata alfarma a gurinsa ne akan Waira shiyasa yake masa magana kamar daman can babu wata kiyaya ko tsanar juna a tsakaninsu. Be san bangaren Abiey ba, dan haka yayi ta bude dakunan da suke corridor kamin ya isa babban falon dake cike da sanyin ac. Abiey yana hakimce saman kujera sanye da jallabiyar da ya saka tun safe sai wayar dake hannunsa yana duba yanar gizo.

“Bismillah Ameer shigo ciki”

Ameer ya cire talkamin kafarsa for the first time saboda zai shiga gurin wani. Ya isa cikin falon sai ya zauna a kujerar dake nesa da wanda Abiey yake zaune, zuciyarsa na raya masa abubuwa kala kala akan kiran da Abiey yayi masa, ko da yake hausawa sun ce karka ji tsoron kira ka ji tsoron laifin da ka aikata. Shiru ne yayi ta wanzuwa a cikin falon na tsawon lokaci kamin Abiey ya dago ya kalleshi ya ce.

“Da gaske baka ra'ayin raka Waira garinsu?”

Yayi jimmmm kamar mai nazari sannan ya daga kai.

“Yeah akwai abubuwa da zan yi masu muhimmanci a nan, kuma zata fi jindadin tafiya da Maleek din dai”

“Okay, na yi magana da Imam na sanar masa komai tace zuwa 11pm na zo tare da yarinyar zai musuluntar da ita, kuma ya gabatar da ita a gurin mata yan'uwanta da za su nuna mata yadda zata yi addinin, su fada mata wasu abubuwan da suka kamata”

“Hakan yayi kyau”

“Abu na biyu ina son mu tattauna da kai ne akan ciwon mahaifiyarka, likitanta ya fada min tana bukatar a kwantar da ita a asibiti for now, ni kuma na san halinta bata son zaman asibiti maybe ma yana daga cikin dalilin da ya saka nmta boye mana ciwon tun farko, i know bata bukatar tashin hankali a yanzu shiyasa bana son takura mata cewar dole sai ta tafi asibiti, amman na san tana sonka kuma tana jin maganarka zaka iya lallaba mana ita ta yarda ta kwanta asibitin hakan ba yana nufin rasa rayuwarta ba, no saboda a samu damar bata kulawar da ta kamata, and ina tunanin ko da zata kwnata ba zata wuce sati a nan ba saboda ina tunanin fitar da ita waje, ko ba komai a can sun fi mu kayan aiki da kula da marasa lafiya yadda ya kamata amman me ka gani? Ban yi maganar da kowa ba, kawai na fi son na fara jin ra'ayinka ne”

Ameer ya dan yi shiru yana mamaki ace yau shi ne Abiey yake tambayarsa shawara akan Ummi, be tambayi yayansa ba.

“Zamu iya fitar da ita India ko Egypt suna da asibiti mai kyau da kwararun likitoci da suke kula da wannan bangaren kuma na ga ana yawan kai masu irin ciwonta kasashen, akwai kuma London can ma suna da asibiti mai kyau”

Abiey yayi murmushi yana jinjina kai.

“Good ni ma tunanina zuwa can zai fi, amman dai na yi shiru na ji irin shawarar da zaka yanke ne, zan yi magana da Maleek da kuma likitan sai mu ga inda ya kamata”

“Okay”

Ameer ya mike tsaye.

“Ameer, please feel free to talk to a duk lokacin da kake bukatar wani abu, ko da kuwa shawara ce, kuma ga yan'uwanka nan please ka manta da komai ka zauna lafiya da su ko dan saboda mahaifiyarka, ka dauke ni a matsayin uba, na san kana kallona a matsayin wani makiyinka no ba haka ba ne, akwai wadandansu dabi'u da bana so a cikin halayyarka, kuma ina ganin kamar ka dauko hanyar sauyawa, ina fatar hakan zai daure Allah ya kara hada kanku, su ma na yi magana da su, kuma zan sake yi sai na hadaku gaba daya na yi muku nasiha, and idan za a fita da ita waje tare za mu da kai, ko da sauran ba su samu damar zuwa ba”

“In Shaa Allah”

Ameer ya fada sannan ya juya ya fice daga falon.
[8/4, 9:57 PM] My S Line: 71

Misalin 11:30am Abiey da Ameer, Maleek da Mahmood har ma Namra da Ummi suka raka Waira gurin karbar shahadar shiga musulunci, Imam din ya gabatar musu da duk wasu abubuwa da suka kamata, ya fara da yi ma Waira shimfida yadda zata kara fahimtar addinin kuma ta natsu da shi, kana ya tambaye ta ko wane yayi mata dole ko kuma ya tsorata ya saka take son shiga addinin musulunci ta amsa da aa. Kanta a rufe da hijabin dake kara bayyana kyauta wato black hijab sai doguwar rigar abaya. Ya fada mata dokoki da sharudan karbar kalmar shahada ta ce ta aminta, zata daina bautar kowa sai Allah kuma zata bi duk wata doka da Allah ya kafa. Bayan ta gama sauraren dokikin ta amince ta gabatar masa da tambayarta.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.