Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 18 of 227

Tassss Daddy ya wanke masa fuska da mari mai kyau, har sai da Ameer ya hade hakoransa na sama da kasa ya dantse ya yarfar da fuska gefe ya rufe ido. Kamin ya bude idanuwansa sun hada wani karamin yaki da ya haifar da sauyawar launin kalar idonsa daga fari fes zuwa ja.

“For What Dad?”

Ya tambaya wasu jijiyoyin bacin rai da takaici na bayyana a goshinsa, a take Daddy ya sake marinsa a barin da ya mare shi dazun yana masa wani mugun kallo irin na fadan Uba da ďa, wannan karon Ameer be rufe idon ba, sai dai ya sake yarfar da fuskar ya kalli kasa, da wani irin tashin hankali Momy ta hade yawun bakinta, idon kanwarsa Humy kamar zai fito tsabar mamakin Daddy ya mari Ameer har sau biyu a lokaci daya. Ameer ya dago yana yi ma mahaifinsa wani kallo da be taba yi masa irinsa ba, kallo ne mai kama da harara irin na Ƴaƴan da suka gagari iyayensu, a take Daddy ya sake marinsa, cikin karfin hali Ameer ya sake dagowa nan ma Daddy ya sake sauke masa wani lafiyayyen marin, Momy na ganin hakan ta shiga tsakiyarsu ta tura Ameer baya tana kallon Daddy da tsananin mamaki, Humy kan tuni hawaye na wanke mata fuska domin ba Momy kadai ba ita kanta ta tsorata da halin da ta ga yayanta da mahaifinta a yau.

“Haba Alhaji me yake faruwa da kai yau? Ameer kake mari har haka?”

Daddy ya nuna Ameer cikin zafin zuciya naman fuskarsa na rawa kamar zai fado.

“Kudi da gata suka saka ka zama haka ko? Ka taka wani wanda ka ga dama ka mari wanda kake so, ka wulakanta kowa ka kade mutanen da ba su maka komai ba, ka kori ma'aikatan kamfani na akan karamin dalili, sannan na ce kayi ka tsallake layin da na shata maka ka yi tafiyarka inda ranka yake so, kuma na kira ka a waya ka kasa dagawa? And i slap you, you ask me for what? Sai na koya maka darasi, daga yau babu kai babu kamfanina, babu kai babu kudina, babu kai babu motocina, babu kai babu duk wani abun da kasan nawa ne, ko kuma zaka saka sunana ka samu, ka tattara duk abin da ka san nawa ne ka dawo min da abu na”

“Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un, Ameer ne fa”

Momy ta furta cikin tashin hankali da tsananin mamakin furucin Daddy. Daddy ya kalleta.

“Ameer Ubana ne? Ni na haife shi ba shi ya haife ni ba, idan kudin da nake sakar masa yake sakawa yana wannan halin daga yau na daina...”

Kamin Daddy ya kai aya Ameer ya tari numfashinsa.

“And Daddy kana tunanin ba zan iya rayuwa idan babu arzikinka a tare da ni ba? I had my own money too ina kudin da zasu isheni na gina kaina da rayuwa ta”

Ya karashe maganar cikin zafin rai gafen fuskarsa na dama na kara bayyana shatin marin da Daddy yayi masa, kasancewarsa farin mutun da jikinsa baya daukar wahala.

“Duk wani abu da kake takamar naka ne, ka samu ne a karkashina domin a kamfanina ka yi aiki, kamin kamfanina abinci da ruwana da suturata ka saka har kai a inda kake yanzu, nuna min naira biyar da ka samu ta karkashin wani wanda ba ni ba, idan har kana son ka burge ni, kuma ka nuna min ka isa ko kudin da yake account dinka karka yi amfani da shi, and already ma fadawa Bello duk wani abun da yake da sunana akai na ka, ya dakatar da shi”

Daddy ya fada cikin kakkausan lafazi. Ameer yayi wani shu'umin murmushi ya girgiza kai, takawa yayi a hankali ya karasa kusa da kujerar da Daddy yake tsaye ya aje masa keys din motar dake hannunsa ya kalleshi ba tare da ya sake cewa komai ba ya juya ya fice fuuuu kamar walkiya. Momy ya bi bayansa da gudu tana rikosa.

“Baka da hankali ne Ameer wannan fa mahaifinka ne, be kamata ka yi masa haka ba, domin kai kake da laifi, ka koma ka bashi hakuri Ameer karka yarda ka yi fushi da mahaifinka, karka yarda shaidan ya shiga tsakaninku...”

Juyowa Ameer yayi ya kalleta.

“Da hadin kanki aka yi komai, ke kika shirya masa duk abun da yayi karki zo kina min wani wasan, gida ne zan tafi na bar muku abun ku”

Ya juya ya cigaba da tafiyarsa, sai kuma ya juyo ya dawo cikin falon har lokacin Daddy na tsaye a inda ya bar shi, Momy kuma ta biyo bayansa suka dawo falon tare, Upstairs ya nufa ya shiga dakinsa tsayawa yayi ya karewa dakin kallo, sannan ya shiga boutique dinsa dake dakin, tulin kayan da suka kawata dakin ya bi da kallo be ji zai iya daukar ko daya ba saboda ya same su ne duk ta hanyar mahaifinsa, kuma shi a yanzu ya shirya nuna masa he can live without him, gurin da ya saba aje sarewar ta busa ya nufa ya bude gurin ya dauki box din sarewar gaba daya domin ita ba da kudin mahaifinsa ya same ta ba.
    Fitowarsa ta fi shigarsa tashin hankaki, domin ya fito a yanayin da kallo daya zaka masa ka san fitar da zai yi ba ta dawowa ce ba.

“Ameer... Ameer... Ameer...”

Momy na kwala masa kira amman ko amsawa be yi ba balle har ya juyo ya saurareta, haka ya saka kai ya fice ko gefen da Daddy yake be sake kallo ba.

“Be kamata ka yi masa haka ba, na san abun da yayi maka be kyauta ba, amman ka dubi girman Allah ka yafe masa, tafiya zai yi baka san inda zai je ba, baka san wane hali zai fada ba”

Momy ta kai har kasa tana kuka tana rokon Daddy da take kyautata zaton ya fita daga hayyacinsa, domin ko mafarki bata yi zaton zai iya yi ma gudan jininsa da yake ji da shi haka ba balle a zahiri, idan kuma hakan ya faru a zahiri to ba a banza komai ya afku ba.

“Idan kika sake yi min wata magana akan Ameer ke ma zan shata miki layi, kar wanda ya sake furta min sunansa a gidana....”

Ba shiri Humy ta rufe baki, domin bata taba ganin mahaifinta a fushi irin wannan ba, duk kuwa da kasancewar ta san abun da Ameer yayi be kyau ba, sai dai ba ta yi tsammanin akwai wani abu da Ameer zai aikata Daddy yayi masa irin wannan hukuncin ba, ba ita kadai ba sauran yan'uwanta ma idan suka ji ba karamin kaduwa za su yi ba.

WAIRA POV.

Sai da ya gama nada ganyen yayi masa kwaliya da fulawa sannan ya dauka ya dora mata akai kamar crown. Murmushi ta yi, irin murmushin da ta dade ba tayi ba.

“Kin yi kyau”

Ya fada yana kallon yadda kwayar idonta ke yawo.

“Ya min kyau?”

“Kin masa kyau”

Ya amsa mata yana gyara mata domin ita ta yi ma Crown din kyau ba shi yayi mata ba, a take ta kara fadada murmushinta ta daga kai tana kallon sama sai ya saka hannunsa ya tare mata hasken ranar yadda zata ga saman da kyau. Hannayenta ta saka ta ture hannunsa ta juya baya baya tana kyalkyalar dariya kamar ba ita ce take ta faman zaman cikin kunci ba kwana biyu da suka gabata. Tsaye yayi yana kallonta tana tafiyar baya har ta jingina jikin icen turare sai ta daga kanta sama ta kalli icen. Juyawa ta yi zata hau icen sai dai babu wani rame da zata yi matakala ta hau sama. Juyowa ta yi ta Kalli Eid sai ta ga babu shi a gurin a take ta fara waige waige, hankalinta be bata yana kan icen ba har sai da kunnuwanta suka yi arba da sautin busar sarewar da take matukar so da kauna, daga ita har shi suna jin dadin busar balle kuma mutanen garin. Lumshe ido ta yi ta bude tana murmushi mai bayyana hakoranta da dauďa ta yi ma katutu saboda rashin wankewa. Rawar da ta saba yi idan yana mata busar ta soma yi tana juyawa a take zuciyarta ta cika da nishadi da farinciki, kamar yadda ta Eid ma take a lokacin da yake busar yana kallonta daga can saman dogon icen da yake zaune kai ka rantse da Allah dominsu kadai gurin da duk wani abun da ya wakana a lokacin sakamakon yanayin da busar da kuma nishadin dake tare da su. Rawa ta yi har sai da ta gaji sannan ta mika masa hannu sama ya sauko ya kama hannunta.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.