Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 209 of 227

Yayi shiru tare da jan dogon numfashi ya sauke.

“Amman akwai abun da likitocin da suka duba ta a can suka fada mana, wanda ni da Maleek muka bar maganar a tsakaninmu muka yi shiru da bakinki saboda kar a tashi hankalinku musamman ma Ameer da take yawan magana, kana cikin ranta sosai Ameer”

Ameer da idonsa ya cika da hawaye har suka fara zuba yana kallon Abiey ya ce.

“Idan ma mutuwa ta yi ka fada min ban isa na hana Allah ikonsa ba, ni ma ban isa na tare mutuwa ta ba balle na tarewa wani”

“Bata mutu ba, jiya ma ai ka yi waya da ita da ta mutu ai da ba zaka gan ni a nan ba, amman dai likitocin sun tabbatar mana cewar Mahaifiyarka ba zata wuce wata biyar a duniya ba, domin tana 1 percent a yanzu, kuma last checking din da suka mata ciwon ya taba lungs spinal and liver dinta, infection din yayi mata over bata wuni bata yi tarin jini ba, she's feeling very weak ga yawan bachi numfashinta ma ya canja loss of bladder and bowel and unconsciousness...”

Namra ta fashe da kuka sosai jikinta har rawa yake, Ameer kuma ya rumtse idonsa sosai yana jin duniyar gaba daya ta juye masa, ina ma Abiey be fada masa haka ba, sai a yanzu ya gane dalilin da ya saka a duk lokacin da yayi unkurin zuwa sai ya dakatar da shi da cewar ya jira har su dawo, Mahmood ya saka hannu biyu ya rufe fuskarsa yana hawaye shi kam daman ya dade da katsewa tun a lokacin da ya ga gashin kanta na cirewa. Maleek ma hawaye ne ke masa zuba amman hakan be hana shi kwantar da kan Namra a kafadarsa ba yana jijjigata alamar rarrashi.

“Idan na rasa Ummi na shiga uku na rasa yar'uwa yanzu kuma zan rasa uwa wayyo”

Ameer ya dago ya kalleta hawaye na masa zuba kamar ba gobe.

“Ba ke kika shiga uku ba, ni na shiga uku domin ni na rasa kowa, na gane cewar ita ce mahaifiyata a kuraren lokaci a kuraren lokaci, komai ya canja min abubuwan da ban zata sun faru da ni ta hanyar da ban yi tsammani ba, you guys are lucky kun rayu da ita tun tashinku har girma, tun kuna jarirai har kuka girma kun san in and out na ta, ta kula da ku tarbiyarta da kulawarta ce kuke kai, kun yi babbar sa'a ni ban samu wannan ba, a yanzu da ya kamata na rabe ta mu san juna ta nuna min kauna na nuna mata kuma mutuwa na shirin yanke alaka...!”

“Haka take yawan fada, cewar ita kadai ta rage maka kuma zata tafi ta barka”

Abiey ya fada sai kallon Ameer yake cike da tausayinsa.

“Ina tunanin zan yi duk abun da ya kamata na bar kasar nan gobe, daman kullum ina son tafiya sai ka ce na jira sai ka dawo da na san abun da zaka dawo ka fada min kenan da ban jiraka ba”

Cewar Ameer yana jin zuciyarsa kamar zata fado saboda bakinciki.

“Ba tafiyar ce mai muhimmanci ma, cika mata burinta na son ganin aurenku ne mai himmanci, shi ne dalilin tara ku a nan da na yi, daga ke Namra har Maleek balle kuma Ameer har kai Mahmood dan Allah idan akwai wadanda kuke so ku gabatar mana da su ayi abun da ya kamata cikin lokaci, farincikin nan da take bukata ku saka mata shi, Ameer idan har zaka tafi gurinta to kaje mata da wannan albishir din na gabatar mata da aurenka cikin kankanen lokaci, Namra ke kuma ki yi magana da Shuraim ki fada masa gaskiya idan ya shirya ina son aurar da ki kasa da wata biyu, daman na san shi ni kawai yake jiran na ba shi umarni, toh ki fada masa ya turo da magabantansa”

Abiey ya saka yatsunsa ya tare hawayensa ya jefar, ya maida dubansa gurin Maleek da Mahmood.

“Maleek na san babu yarinyar da kake so a yanzu ba, amman please try ka samu yarinyar da ta kwanta maka a rai kuma ka ji ka natsu da ita ba ko da kadan ne, yar gidan mutunci Mahmood kai ma haka inda hali, Ameer na san ba shi da matsala zan yi magana da Nuwaira matukar ta amsa tana sonsa za ayi komai cikin sauki, ina son hade aurenku ne if possible, kuma ina fatar zan samu goyon baya da hadin kanku”

Duk suka yi shiru sai Maleek ne kawai ya iya magana.

“In Shaa Allah Abiey, Ummi ba zata mutu a yanzu ba, babu wanda ya san mutuwar wani sai Allah kuma sau da dama akan samu irin haka amman sai ka ga Allah ya arawa mutum rayuwa ya rayu fiye da yadda ake tsammani, kuma da yardar Allah Ummi har yayanmu sai ta gani”

“Haka ne, amman kai ma likita ne kasan duk abun da yake nan, so try your best please make her happy”

“I will”

Ameer ya mike tsaye ba tare da yace komai ba ya fice daga falon. Kai tsaye gurin motarsa ya nufa, sai da ya shiga sai kuma ya ji ba zai iya tukin ba. Sai kawai ya kifa kansa a ya rufe ido, wayarsa ya dauka sai kuma ya tuna ba shi da hotonta ko daya a wayarsa, wanda take ita kadai ma balle kuma ace wanda suka dauka tare. Fasa shiga Gallary yayi sai yayi dialing number Daddy, wayar na daf da katsewa Daddy yayi picking.

“Assalamu Alaikum”

“Daddy kana da gida?”

“Aa ina Villa akwai meeting din da muka fito yanzu tare da vice president me ya faru?”

“Daddy i need to see you”

“Daman gida zan je daga nan, kana ina kai?”

“Gidan Ummi”

“Ka same ni gida yanzu nan”

“Okay”

Yana aje wayar ya kunna motar ya fice daga gidan, tafiyar minti arba'in yayi ta cikin minti ashirin da biyar saboda gudun da yayi. A haka din ma sai da yayi jiran one hour a harabar gidan domin kasa shiga ciki yayi, gaba daya duniyar ta fice masa a rai ji yake kamar ya mutu ya mutu. Sai da ya ga motar Daddy ta kunno kai cikin gidan sannan ya bude motarsa ya fito yana kallon motar har Direban Daddy yayi parking ya budewa Daddy, Ameer be tsaya jiran Daddy ta iso inda yake ba ya nufe shi da sauri ya rumgume shi yana hawaye.

“You're my only love Daddy, kai kadai ka rage min a yanzu a duniya, i have one no one now”

“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un”

Shi ne kawai abun da Daddy yake fada a tunaninsa Ummi ta rasu ne, domin kullum sai ya tambayi lafiyarta a gurin Ameer yace masa jikin da sauki wani lokacin ma ya kan ce yanzu ya gama waya da ita, amman yau ya zo masa a haka ko da yake tun bayan tafiyar Ummi yanayin Ameer ya canja damuwa ta yi masa yawa na halin da Nuwaira take masa, ga kuma Ummin da bata kusa sai ya zama zuwa gidan Ummi baya masa dadi, idan kuma be je ba sai ya ji ba shi da natsuwa saboda ruhinsa yana can tare da Nuwaira, hakan ya saka shi tarewa a gidan kakarsa wato Hajiya, domin Humairah tana debe masa kewa sosai matukar yana tare daita bata barinsa yayi missing wani abu, ko kuma ya shiga damuwa.
[8/17, 10:15 PM] 🦋-🦋: 81

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.