Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 166 of 227

“Kamar ya? Ana karbar busa? Ya za'ayi bayan kuma ka koya min”

“Toh zamu gani dai, yanzu ka dawo nan da zama ne?”

“Daman a nan nake, karatu ya kai ni Europe”

“Hakan na da kyau, ina maka fatan nasara”

Eid ya mika masa hannu suka gaisa. Ameer ya saka hannunsa aljihu yana lalaben wayarsa.

“Let me get my phone mu yi pic na nunawa Waira dan garinsu”

“It since like Waira dai budurwarka ce”

Ameer yayi murmushi ya duka cikin motarsa ya dauko wayarsa.

“She's the love of my life, ina sonta sosai gaskiya kuma so na aure”

Eid ya dafa kafadarsa yana murmushi.

“Ka yi sa'a kai ne, sai dai duk da haka zan fada maka ka yi hankali, ba aure daga garemu kuma ba ma aure daga wasu, idan ma ita Waira din ta yaudareka da zancen zata aureka to zata wahalar da kai”

“ta fada min komai, amman duk da haka ina son aurenta na shirya bada komai akanta, ina son yarinyar nan Eid fiye da tunaninka”

“Wani kuma ya rigaka sonta, tun tana karama yake kiwon abarsa har ta kai ga girma”

“Waye kenan? Ka ce baka santa ba? Ita ma kuma bata fada min tana soyayya da wani ba”

“Kawai na ayyana hakan ne a raina, kasan mafi akasiri mata masu kyau haka ake musu, kuma na san tun da ka ce kana sonta tana da kyau”

“Tana da kyau sosai gaskiya, irin kyau nan mai daukar hankali”

Eid ya dauke hannunsa ya matsa gefensa sosai Ameer yayi selfie din sannan ya sake daukarsa shi kadai, sannan suka yi sallama Ameer ya shiga motarsa da zumudin zai tafi ya nunawa Waira dan garinsu. Eid kuma ya nufi cikin asibitin yana yi yana waigen Ameer...

WAIRA POV.

A hankali ta fara bude idonta tana ganin dishe-dishe kamar wadda ta dade a sume, ta maida idon ta rufe ta sake budewa still the same thing, ta dago hannunta ta murda idon ta sake budewa wannan karon da dan sauki tana iya kallo da shi saidai ba kallo irin na mai gani normal ba, haka dai ta daure ta tashi zaune ta kai hannu ta dafa kanta ta shafa goshinta ya rufe idon na wasu mintuna sannan ta sake budewa tana kokarin tuna abun da ya faru sai ta kasa, ita dai abun da ta sani Ummi ta fada mata Malamimta na kiranta after ta fito ta ga malamin ya bata baya, bata sake sanin me ya faru ba, sai a yanzu da ta ganta a kasa kwance. Mikewa ta yi tsaye tana jin wani abu mai kamar jiri yana dibanta tana daga kafar daker tana takawa idonta na wanyewa a hankali har suka koma daidai, sai dai jirin be daina daukarta ba har ta tura kofar falon ta shiga. Bakin kofar falon ta tsaya tana kallon cikin falon kamar wata bakuwa sannan ta cira kafa ta taka a hankali zuwa kitchen, hannu ta mika zata dauki cup har ta riko cup din ya subuce a hannunta ya fadi kasa ya fashe, ta sake mika hannu ta janyo wani shi ma ya sake faduwa sai ta rike sink din da kyau jin tana rawa kamar zata fadi.

“Are you okay”

So take ta juyo ta kalli mai mata magana amman ta kasa. Maleek ya karasa cikin kitchen din ya tsaya daidai ita yana kallonta ba abun ya taba ta ya san haramcin yin haka sai dai yadda take ta juya ido ya nuna kamar bata cikin hayyacinta. A maimakon ya dauko wani kofin zuba mata ruwa ta sha sai ya kunna tab ya tara hannunsa ya ciko shi da ruwa ya kai mata saitin bakinta, sainta fara sha da sauri kamar wadda ta kwana bakwai bata ga ruwa ba, ya sake tara mata hannunsa ta sake sha, haka yayi mata har sau hudu sannan ta zauna a kasa gurin tana sauke numfashi jirin na sakinta kamar daman can ruwan ne maganin jiri.

“Me ya same ki?”

“Haka nan kawai nake ganin jiri”

“Okay maybe ruwan jikinki ne yayi kasa, tashi ki koma falo zan duba ki”

Ta mike tsaye tana fadin

“Lafiyata kalau maybe ina son zuwa gida ne”

Da mamaki Maleek ya kalleta.

“Gida kuma? Wane gida?”

“Garin mu inda iyalina suke, ina son na koma garinmu”

“Ssboda me? Bayan kin ce baki son zuwa kuma kina tsoron karki je su kasheki?”

“A da ne, yanzu duk wannan ya kau, bana bukatar ko'ina sai garinmu”

“Ummi ta matsa miki sai kin tafi gida ne?”

“Aa kawai dai ina son na tafi gida ne”

“Saboda muna fada da Ameer ne?”

“Aa kawai dai ina son na koma garinmu ne, lokaci yayi da ya kamata mu yi bakwana”

Fada take hawaye na sauko mata muryar na karkarwa, ita dai har a ranta ta san bata son tafiyar, sai dai tana jin ana kiranta an cire mata duk wata natsuwa da zata samu a zama garin da ba na su ba. Ji take kamar akwai wani aiki da ya kamata ta tafi ta karasa a garinsu. Maleek ya ji wani iri a kamar wanda aka cewa mutuwa zata yi ta bar shi duk inda jindadi da walwala suke a zuciyarsa sai ya neme su ya rasa.

“Kin ga zauna”

Ya kai kasa tun kamin ita din da ya bawa umarni ta zauna, damuwar bijiro da maganar tana son zuwa gida da ta yi ya saka shi manta a kitchen suke ya mike kafafuwansa ba tare da fargaba ko tsoron wani ya shigo ba. Ganin haka ya saka ita zauna a kasa tana kallon wani bangare na kitchen din zuciyarta cike da abubuwa marasa dadi.

“I know baki son tashin hankali you're too young for that, amman ba ina rigima da Ameer ba ne saboda wani abu, sai dai ina kokarin baki kariya, tsoro nake kar ya lalata rayuwarki kamar yadda ya lalata rayuwar sauran mata, ciki har da kanwata, yayi sanadiyar mutuwarta, har a bada ba zan manta ba, mutumen da tausayin da imani suka fice a zuciyarsa saboda son rai, yayi wasa da zuciya da rayuwa har sai da muka rasa ta”

Waira ta juyo ta kalleshi.

“Ba irin wannan soyayyar Ameer yake min ba, baka gane ba, shi yana sona ne kamar yadda nake son sa nake son Ya Nimra da Mahmood, yana son yayi min kirki ne”

“Aa ke ce dai baki gane ba, amman so yake miki irin wanda yake yi ma Nimra, domin ya fadawa Ummi cewa yana sonki, sai dai ke ya ce Aurenki zai yi ba kamar ita ba”

Ta girgiza kai ko bata san miye soyayya ba ta san minene aure wata igiya dake hada mutum biyu suke a karkashin inuwa daya.

“Aa ba aure ba, ni bana son aure bana son Ameer da aure”

“Why? Ko da ace ke ba zai cutar da ke ba? But ban yarda da hakan ba, na yi magana Ummi ta ga laifina, dazun ya fito yana fada mana magana son ransa saboda Namra ta yi magana Ummi ta mareta ni ma na yi magana ta mareni, tun da nake a rayuwata Ummi bata taba dukana ba tun ina karami har girma sai a yanzu, and all because of you”

Kallonsa take tana jin wani abu na rashin jindadi a sakamakon fada mata da yayi Ummi ta mare shi. Ita ma zata iya shaidar cewar Ummi bata taba maaa wani hukunci mai karfi irin wannan ba.
Ta bude baki zata bashi amsa Mahmood ya shigo kitchen, tsaye yayi yana kallonsu with full of surprise domin be taba ganin Maleek a kitchen din zaune ba ko da kuwa ace Ummi ce a ciki tana girki, amman sai gashi ya ganshi zaune kuma a kasa tare da Waira ita ma Waira tana zaune kasa.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.