Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 176 of 227

Nuwaira ta karasa kusa da Abiey ta tara hannu biyu ta karbi prayer mat din.

“Na gode”

Ta shafa carpet din dake cikin wani jacket mai kyau kamar ba prayer mat. Ameer ya tashi ya fita, Namra kuma ta shiga dakinta sai gata ta fito da katon akwaiti ta sauko da shi.

“Ban san me zan baki ba, kuma na san kayana ba su miki, so shiyasa na zabi baki tufafin da ban danka ba gasu na hada miki guri daya a akwaiti, akwai turarukan jiki da na fesawa, kuma akwai mayuka da sabulai masu kyau”

“Na gode”

Nuwaira ta yi mata godiya tana kallon madaidaicin akwatin. Kamin ta juyo ta kalli Ameer da ya mika mata box, ta karba da hannu biyu ta bude sai ta yi arba da kur'ane mai kyau. Ta bude ido ta risina kasa ta saka hannu biyu ta ciro kur'anen ta sumbanceshi sannan ta kalli Ameer idonta na cika da hawaye.

“Na gode”

Ta sakar mata murmushinsa mai matukar tsada ta warware wata yar karamar sarka ya daura mata a hannu a yayin da take rike da kur'anen, abun hannuna ne mai kyau fari mai kamar azurfa.

“Welcome to the peace”

“Thank you, duk wannan saboda kai ne Ameer”

Abiey ya mike tsaye yana fadin.

“Ameer ka yi abun a yaba, ka kyauta kuma na jidadin haka Allah ya baka lada, ya saka maka da alheri, ina fatar a yanzu ba za a sake samun matsala ko tsabanin tsakaninka da yan'uwanka ba, Allah ya hada kanku”

“Ameen”

Ya amsa yana kallon Nuwaira da ta aje kur'anen tana ta taba abun hannun da ya saka mata cikin farinciki da jindadi.

“Yayi kyau”

“Do you like it?”

Tambayarta yake tana kallonta kamar daga shi sai ita ne a falon, gaba daya ta dauke masa hankali baya ganin kowa. Ta daga alamar yes she like it kamin ta dago ta kalleshi wannan karon hakoranta a waje yake, can kuma ta juya ta kalli Mahmood da ya mika mata chocolate da carbin hannunaa yar maroko, wato counter.

“Ga wannan zaki iya yin tasbihi da ita ko salati, zata kirga miko ko adadin guda nawa kike son yi, kuma ga chocolate kowa ya baki komai ban san me zan baki ba”

“Thank you”

Ta karba ta dora saman jikinta sannan ta kalli Maleek, shi kam be roko mata komai ba domin ba sa ran su ma za su mata kyauta ba, idan ma zai bata be san wace kyautar zai bata ba. Hakan kuma ba karamin dadi yayi ma Ameer ba daman shi so yake ya zama shi kadai ne yake burge Nuwaira baya son abokin takara.

“Maybe next time ni ban riko miki komai ba”

Ta yi murmushi ta maida hankalinta gurin abun hannun da Ameer ya daura mata, ita dai tana kaunar ayi mata kyauta wani abun da ya danganci sarka ko abun hannu.

“Ameer kai ka katse min sarkar da Sulem ya ba ni ka tuna?”

“Gashi nan ai na baki wani”

Ta yi dariya ta mike tsaye ta rufe kur'anen ta dauka ta rumgume.

“Na gode All”

Ta nufi stairs duk suka bita da kallo, Ummi na ji kamar tace mata kar ta tafi.

“Har a yanzu da ta musulumta tafiya zata ti Ummi?”

Namra ta tambaya. Sai Abiey ya amsa mata.

“Tafiyar zata fi zaman, ko ba komai zamu san yan'uwanta kuma tafiyarta ba yana nufin mu barta a can shikenan ba, no zamu bibiyeta ko dan sanin halin da take ciki, shiyasa na ce ba zata tafi ita kadai ba sai tare da jami'an tsaro, kuma Maleek zai rakata kamar yadda Ameer ya bukata, zuwa gobe zamu shirya komai jibi sai ta tafi”

“Haka ne, Allah yasan hakan ne alheri a gareta da mu gaba daya”

Addu'ar da Mahmood yayi sai duk suka amsa da ameen. Duk a cikin kyautukan da suka mata babu wanda ta fi so kamar abun hannun da Ameer ya daura mata, da kuma alkur'anen da ya bata, domin ta dade tana sha'awar kur'ane yawan sauraren da take idan Maleek na karantawa da kuma abubuwan da Ameer yake fada mata sai yace akwai a ciki kur'ane sai dai bata san yadda zata yi ta karanta ba. Sai dai ta zuba masa ido ta yi ta kallo tana shafawa, Prayer mat din da Abiey ya bata kuma sai ta taimaka mata sosai gurin yin ibadarta yadda ya dace tana fadar duk abun da nau'urar dakw ciki take fada, kana kuma ta bi yadda take nunawa. A kowa ce Sallah. Abiey yayi magana da Cp dake Abuja ya fada musu tafiyar da Nuwaira zata yi har ma da dansa Maleek da zai rakata, sai aka basu police biyu da za su raka su, bayan sun zo har gida sun yi mata tambayoyi sai ta fadi iya inda zata iya ganewa a kofar garinsu, daga inda ta fito zuwa gurin da ta hadu da Ameer, domin nan kadai gurin da ta sani, sauran abubuwan da suka faru bata iya labarta ko daya, kasancewar bata cikin hayyacinta aka kawo ta asibiti, daga Katsina zuwa Abuja ma bata san komai akai ba domin ko da aka iso tana bachi. Police biyu aka basu daga Abuja bayan an sanar musu wasu police biyu za su tare su daga Katsina tare da wanda ya san hanyar garin har zuwa inda Nuwaira zata gane.

Tun cikin dare Ummi ta shiryawa Nuwaira komai nata, ta zaunar da ita ta yi mata nasiha ta karfafa mata guiwar cigaba da rike addininta konda kuwa danginta za su nuna basa son addinin nata. Namra na tsaye jikin kofar dakin rumgume da hannayenta tana kallon Nuwaira dake ta rutsar kuka kamar an mata mota, shigowar Ameer ne ya saka Namra ta hanye daga jikin kofar ta karasa cikin dakin kusa da Ummi ta tsaya daga tsaye yayin da Ummi take zaune Nuwaira na jikinta sai kuka take, bata son rabuwa da Ummi kuma bata san me zata je ta tararda a garin ba, zancen sarautar yana nan ko kuma kasheta za'ayi? Ya za su karbeta idan suka ji ta canja addini da al'ada? Yana daga cikin abubuwan da suke matukar daga mata hankali.

“Ummi Daddy ya ce na zo da ita, yana son su yi bankwana”

Maganar Ameer yake yana kallon sahibarsa yadda take kuka abun ba dadi yake masa ba, shi ma tafiyarta domin kawai ta zame masa dole ne amman baya son rabuwa da ita ko na minti daya, idan kuma ya tuna da Maleek zata tafi sai ya ji hankalinsa ya tashi domin ganin yake kamar shakuwa ce zata kara shiga tsakaninsu. Nuwaira ta dago daga jikin Ummi ta kalleshi da jajayen idonta, hakan ya bashi karfin guiwar karasowa ya risina inda take zaune yana kallon fuskarta.

“Daddy na yake son ganinki, na fada masa gobe zaki tafi shi ne ya ce na zo da ke yanzu”

Ta mike tsaye sai ya ja baya domin bata dama ta taka, bandaki ta shiga ta wanke fuskarta sannan ta fito ta dauki daya daga cikin hijab din da Ummi ta bata ta saka daya, sannan ta kalli Ummi alamar tana neman izinin fita, Ummi ta daga mata kai

“Tafi”

Ta juya ta wuce gaba Ameer ya bita baya, Namra da Ummi suka bi Ameer da kallo ganin ya zama kamar wani jela.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.