Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 108 of 227
“I promise you ba zan jefa kaina a halin da hankalinku zai tashi ba, i will control my temper, i will take care of myself”
“Thank you, please pick up your phone call your dad ka yi magana da shi”
“Does he know kin fada min gaskiya?”
“No kawai na kira wayarsa a saboda na kiraka baka daga ba, sai ya fada min shi ma ya kira baka dauka ba kuma na san ya damu”
“I already reach home bye”
Ya yanke kiran ya jingina jikin motarsa, this is the first time da ya taba tsayawa haka a gate din gidansu peacefully ya danna horn yana jiran a bude masa. Yaja motar kamar marar lafiya ya shiga yana ta kallon bangaren da mahaifinsa yake. Calmly ya faka motar ya bude ya fito ya bar wayarsa da takardar da Zahra da bashi tare da hoton ya nufi Garden. Tun da yake a rayuwarsa be tana kunna fonfon Garden yayi alwala na sai yau, saboda yana matukar kyamar gurin, kasancewar ma'aikatan gidan suna yawan zuwa gurin diban ruwa idan babu a fanfon masallaci. Damuwa ta mantar da shi dokokinsa na ware kansa da yake a masallaci yana sallah a one place ba tare da hada kafada da sauran mamu ba, sai gashi a sahun gaba, wani direban Daddy yayi ikama, mai bawa fulawowayin gidan ruwa yaja Sallah, kamin su sallame mamaki ya cika kowa. Ya sallame kamar yadda ake sallame ko wace sallah magarib, ya karanta addu'o'in sallah as usual ya daga hannunsa zai yi ma mahaifiyarsa da be taba manta ta mutu ba addu'ar samun rahma a kabarinta, sai ya tuna she's alive and healthy, hawaye suka zubo masa, saurin rumtse ido yayi ya hade yawu, ya mike tsaye sannan ya bude idon ya fice daga masallacin. Fitowarsa ta yi daidai da shigowar Motar Daddy, saboda kauna irin ta uba da ďa sai Daddy ya kasa tuka motar ya wuce ďansa sai sauke gilashin motar yayi yana tukin daidai tafiyar Ameer da ya ki yarda ya kalleshi, but murmushi yake saboda ya boyewa Daddy damuwar da ta bayyana kanta a fuskarsa.
“Yau na yi latti ka riga ni samun jam'i”
“Mu ma yanzu muka gama sallah”
Yanayin yadda ya amsa masa da kuma muryarsa da kallonshi da Ameer ya kasa yi ya kuma damuwar da ya gani a fuskar dansa, ya saka yayi saurin isa inda yake aje mota ya faka, domin shi yake tuka kansa da alama fitar ba mai nisa ba ce, domin jallabiyar dake jikinsa ama ta nuna haka. Kamin Ameer ya iso Daddy ya fito motar yana kallonsa. Sai Ameer ya kasa karasawa inda yake ya yanki hanya ya shige bangaren Mommy. Daddy na ganin haka ya ciro wayarsa dake pocket ya kira Hajiya Jamila. Kamar tana jiran kiransa domin ringing daya ta fara ta yi picking.
“Kin kira ni dazun, kina tambaya ta Ameer na fada mikin nima na kira shi be daga ba, and now yarona ya dawo gida, baya son kallon idona, na ga damuwa da ban taba ganin irinta ba a fuskar ďana, ya kasa karasowa kusa da ni ya shige bangaren Mommy, fada min me kike fada masa?”
Hajiya Jamila dake sanye da hijabi tana zaune gaban TV ta yi shiru for a seconds sannan ta ce.
“Gaskiya na fada masa, saboda ya bukaci na fada masa, kuma ya yi min ikirarin cewar idan na masa karya zai tsane ni, ba kuma zai sake yarda da ni ba, ba zan iya rusa wannan alakar dake tsakanina da Ameer ba, domin na fika sonsa, na san komai daren dadewa gaskiya zata bayyana”
“Da gaske kike yi? Ba duk gargadi da na yi miki?”
“Me yasa baka gargadi Zahra ba? Sai ni? Kana tunanin har yanzu kana da iko da ni? Ko kana tunanin zan manta irin butulcin da ka yi min bayan duk abin da na aikata saboda ka samu farinciki mu jidadin rayuwar aure na aikata? Amman duk baka duba wannan ba, a tsame ni a gidanka, ka raba ni da ďan da nake kallo a matsayin nawa, ďanta ruwan nonona ya taba zauna cikinsa, ďa daya tilo da na taba rumguma a hannuna a matsayin jaririna, ďan da duniya take kallo a matsayin ni na haife shi, kana tunanin duk zan manta da wannan? Ai kaima ka cancanci ka ji dacin da na ji”
“Idan har zaki iya fadawa Ameer gaskiya, to ba son gaskiya kike masa ba, kuma a yanzu na gode Allah da ya raba ni da ke tun wuri, kuma fada masa gaskiya ba zai canja komai ba, Ameer is still my son, babu wanda ya isa ya kwace hakan daga hannuna, har ita mai ikirarin uwarsa, na yi ma mijinta gargadi saboda ya ja mata kunne, idan kuma ba su ba, na san yadda zan yi da su all, and from today babu ke babu Ameer”
Ya yanke kiran ya nufi bangarensa yana takawa da karfi, kana ganinsa kasan ransa a bace yake. Ameer sai da ya kwatanta Daddy ya shige cikin sannan ya shiga bathroom dinsa ya wanke fuskarsa ya fito rike da towel yana goge fuskar. Boutique dinsa ya shiga ya tsaya a dakin yana kallon yadda Daddy ya zuba masa tufafin sakawa kamar shi ya fi kowa gata a duniya.
*Littafin WANI GARI na kudi ne biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660 ki huta karanta na hakki*
Juyawa yayi kadan ya kalli kansa a katon madubin dake nuna har talkamin kafarsa. Zafin yana kirjinsa da idanuwansa, kansa yake kallo amman a badini gobensa yake hangowa, this is the most painful truth he has ever know gaskiya mai mugun daci da dafi a zuciyarsa. Hoton fuskar mahaifinsa dake jikin moton da Ummi ta ba shi yana ta dawo masa a ido yana ganin kansa a matsayin mahaifinsa. Ya jefar da tawul din a tsakar dakin ya fito kamshi na tsara shi ta ko'ina the women he thought is his step mom tana sakawa a gyara masa dakin a saka masa kamshi kamar yadda yake so saboda tasan abun da yake so kenan, kuma Daddy ya fada mata zaman lafiyarta ta yi ďansa abun da yake so.
Ya fito waje ya sauko falon ba tare da ya bar kowa ya ga fuskarsa ba, one of his fav Sis tana masa magana ya ki kulata ya fice daga falon. Cikin motarsa ya koma ya zauna ya dauko takardar yarjejeniyar ya sake karantawa countless times ya dauki hoton Deen ya kura masa ido, sai a yanzu ya lura sam baya kama da Daddy ta ko'ina, but how come be taba lura da hakan ba? Bude motar yayi ya fice rike da takardun bayan ya dauki wayarsa ya nufi bangaren Daddyn feel dizziness.
NAMRA POV.
Ta yi murmushi tana daidaita tsayuwarta.
“Mai jiki da sauki sosai”
“Maa Shaa Allah, Allah ya kara mata lafiya, ke fa ya kike?”
Shuraim ya tambaya a dayan bangaren.
“Ina nan kalau, saboda kana kusa ni, yaushe zaka sake shigowa kasan dai ba zaka wuce ba tare da mun sake ganin juna ba ko?”
“Zan zo hakan, ko dan ma yarinyar nan Waira, saboda na kasa manta yadda na barta a gidanku, tana ta kuka ta shiga damuwa, kanwarki ma na so na zo an dubata, amman ina tsoron yanayin da yan'uwanki ko iyayenki za su kalleni”
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.