Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 222 of 227

“Allah ya miki albarka, kuma ya sanya albarka a dararen da muka yi tarayya”

“Ameen Allah ya dawo min da kai lafiya mijina”

“Ameen i love you so much”

Ya sake sumbantarta sannan ya nufi motarsa ya shiga tana daga masa hannu har ya fice. A airport ya samesu har da Nuwaira da ba ita za a je ba, saboda ta likewa Ummi ji take kamar ta shige cikin jikinta a tafi ta ita. Ummi ta fara fita motar Abiey na rike da ita Namra na gafenta sanye da bakin gilashin da ya rufe idonta da kusan rabin fuskarsa. Mahmood daman tuni yayi gaba, Ameer ma da ya iso daga baya tuni ya wuce. Ummi da Abiey da Namra kawai aka bar baya, Nuwaira na ganin Ummi ta fara tafiya sai ya bude motar ta zagayo ta rumgumeta tana kuka.

“Ina sonki Ummi Allah ya baki lafiya, dan Allah ki dawo da wuri kinji?”

“In sha Allah kin yi ta min addu'a kinji?”

Ta daga kai, Ummi ta kalli Maleek.

“Zo ka yi sallama da matarka”

Maleek ya matso yaja Nuwaira sai ta koma gurinsa ta rumgume shi tana kuka, Ummi kuma ta juya suka cigaba da tafiyar. Maleek ya bude mota ya sakata cikin shi ma ya shiga.

“Ya isa haka yi shiru mana Ummi zata dawo In Shaa Allah”

Ta daga kai sai dai zuciyarta ta karaya sosai. Janta yayi jikinss ya rumgume ya sumbanci saman kanta dake cikin hijabi.

“I love you, na manta ban fada miki ba jiya mun yi magana da Ameer Humairah zata dawo ta zauna tare da ke kamin mu dawo”

“A gidanka?”

“A gidanki dai a gidanki ne ba nawa ba, kin ga kin hanani abun da na yi ta roko gashi zan tafi, wai ni kin ma taba yin period wai?”

“Minene period?”

“Measuration haila”

Ta girgiza kai.

“Aa ni ban taba yi ba, minene ma hailam toh”

“Jinin al'ada da mata suke yi duk wata, ta gabansu”

“Ni dai ina yin fitsari”

“Na san ai kina fitsari, ke wai yaushe zaki yi wayo?”

A take ta bata fuska daman kukan da take be gama tafiya ba.

“Toh Ummi ta baka amanata dai fada zaka min?”

Be ce mata komai ba ya jata jinkinsa ya rumgume.

“That's why nake kara sonki ni kadai zan iya da fitinarki, waya nan na aje akan gadonki idan na isa zan kira sai mu yi waya”

“Toh i love you”

Ta fada a shagwabe kamar mai shirin yin kuka, sai da ya sumbance ta ya saka hannayensa a hijabinta ya yi yawo da su inda yake har inda take hana shi tabawa wannan karon yayi sa'a bata hana ba, sannan ya zare ya bude motar ya fita.

“I Love you more Allah ya tsare min ke da mutumci”

Yana rufe motar ta ce me zata yi ba kuka ba, a take ta kifa kai ta fara kuka na kewar mijinta da kuma Ummi.
[8/23, 11:36 AM] 🦋-🦋: 86

Zaman Humairah a gidan Nuwaira ya taimaka mata sosai ta bangaren kara kwarewa a kana girki, da kuma sanin yadda zata kula da gidanta. Tun a washe garin ranar da Humairah ta je gidan Nuwaira ta tambaye minene Haila, kuma ita tana nan, a nan fa Humairah ta yi mata bayani dala dala cikin har da yar fahimtarta na lokutan da ake iya daukar ciki bayan gama Haila da kuma wahalar da wasu suke sha gurin ciwon mara duk wata. Hunairah ta sha mamaki sosai jin cewar Nuwaira bata taba yi ba, ta kam ji labarin ance wasu matan baza yi gaba daya, wasu kuma sai sun dade suke farawa wata kila Nuwaira tana daya daga cikinsu har take ce mata ta yi dace domin ance macen da ke dadewa ba ta yi haila ba, sadakinta dabam yake. Wasu mazan kuma basa son wadda bata yi domin wasu kan ce bata haihuwa ita da wadda bata da nono a kirji, sai dai ana samu ko da ba a haila a haihu domin haihuwa na Allah ne.

Ranar da Humairah ta cika sati a gidan tana nunawa Nuwaira yadda ake bude gmail account har a bude account a YouTube domin ta rika kallon karatunka malamai da kuma cigaba da koyon addininta. Humairah take zolayarta wai kila ma ta samu rabo.

“Rabo kamar ya?”

“Ciki mana”

Nuwaira ta wara ido ta shafa cikinta.

“Da gaske? Ya aka yi kika gane?”

“Yoh ni ba zolayarki na ke ba, kuma na ga kin yi fresh ne yau ai”

“Yanzu kenan akwai da a cikina? To kuma ba kin ce wadda bata haila bata haihuwa ba?”

“Ba lallai ne haka ya kasance ba, ana samu amman few kawai dai anfi samun saurin daukar ciki ne immediately after period da zarar miji da mata sun yi mu'amalar aure”

“Kamar ya?”

“Sorry ke ba bahaushiya ba ce to s** nake nufi”

Tana jin haka sai ta gane abun da Maleek yake ta kokarin ta fahimta kenan ta kasa yarda.

“Da gaske ne sai an yi haka ake samun ciki?”

“Eh mana toh a ruwa ake sha?”

“Ni ba zan yarda ba, bana so wannan abun ba shi da kyau”

Humarah ta fara da mamaki kamin ta bushe da dariya.

“Ban gane ba”

“Kawai bana so, ni ba zan yarda, Ya Maleek ma yayi haka ban yarda ba ai, har da fushi yake fa, ni a garin ma ba a haka”

Dariya sosai Humairah ta saka kamin ta gane akwai aiki babba a gabanta na wayar da kan Nuwaira ta wannan bangaren, domin duk mutumen da yayi rayuwa a guri na dabam ba tare da mutanen da za su nuna masa daidai da akasin haka ba dole ya samu kansa a cikin duhun kai, saboda haka bata ga laifin Nuwaira ba, kuma ta yabawa Maleek, tana ganin ta in Ameer zai iya wannan juriyar. Tun daga ranar Humairah bata da labari da Nuwaira sai na yadda zata fahimci hakokin da Maleek yake da su akanta kasancewarsa mijinta. Wannan ya haifar da shakuwa da kusanci a tsakaninsu sosai kuma ya hanasu kewar mazanjensu kamar yadda suka yi tsammani musamman ma Nuwaira da abun ya so hade mata biyu na Ummu da Maleek, gashi shekarunta da tunaninta ba kamar na Humairah da ace bata da wanda zai yi guiding dinta da ta wahala sosai a gidan. A kowane dare Ameer sai yayi waya da matarsa haka ma da dare, idanbe kira ba ita zata kira, kullum safiya sai ta gaisa da Ummi ta yi mata da jiki, da farko kam jikin nata yayi tsanani sosai hankalin iyalanta ya tashi matuka kamin sauki ya fara samuwa su kansu likitocin sai da suka yi mamaki, domin ikon Allah kadai ke iya tsallakar da mai irin ciwonta da ya kai stage dinta, mace da aka bawa kwanakin mutuwa kuma aka cire mata rai daga rayuwa sai gata tana hira da yaranta har da dariya. All zaman da ta yi asibitin na tsawon wata daya yaranta Maleek da Ameer suna tare da ita, Namra ce kawai ta koma gida after ta yi week a garin, farincikin gurin Abiey har ba a magana domin bashi da tashin hankali da tsoro kamar ciwon matarsa, gashi yanzu yana ganin samun saukinta ta hanyar da be zata ba, ya san ba komai ba ne sai addu'a da kuma karin tsayen rayuwar dake da sauran shan ruwa a gaba. Ciwonta is still there amman yayi kasa, date din da suka saka mata na mutuwa ya ce bata mutum ba sai ma karin samun sauki da ta yi. Aman jinin da ta fara yi da canji fata sai suka dauke mata. Nuwaira ma ta yi mamaki a lokacin da take video call da ita tana tambayar yaushe zata dawo.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.