Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 197 of 227

Cikin tsananin mamaki Nuwaira ta kalli Eid da har lokacin Maleek yake harara, sannan ta kalli Maleek da be san abun da take fada ba balle kuma abun da Sarkin yake tanbayarsa.

“Me kuke tattaunawa?”

“Wani abu mai ban mamaki Ya Maleek”

“Ku tambaye shi, me yake bukata daga garemu? Idan rakiya yayi toh zai iya komawa mun gode da zuwansa, amman ba zamu zauna da butulu irinki ba, idan muka yi kora ba ma bukatar dawowarta a cikin danginmu, a da mun yanke shawarar kasheki, sai dai Eid ya bauta miki ya jure duk wata kalar azabar mu saboda mu barki ki rayu, ta karkashin kasa mun yi ta aika miki da mutuwa har a daren jiya, abun mamaki kin aje al'adarmu da addininmu saboda kin ga na wadanda suka fi mu karfi. Tabbas yaro baka shigo garin mu ba sai da ka shirya, domin wani be taba gwada karya mana dokoki haka ya kwashe lafiya ba, ba mu tana tsarrafa tsafi irin wanda muka yi a daren jiya ba, amman komai ya kasa samunka a kusa da dakin ma aljannunmu ba su kusanta ba, a tare da kai mun ga aljanna mai irin tsafinka mun saka wadanda suka fita karfi da iko sub rabata da kai a tunaninmu ita take baka kariya, da muka sake aika tsafi sai ya dawo mana, tun farkon shigowar muke ta jefarka amman jifar ta kasa isa a inda kake, madubin tsafinmu ya kasa ganin fuskarka, jama'ar da ake turawa su kiraka kana saka musu fargaba da tsoro, a yanzu ba ma jayya da kai mu dai ba ma shiga gonar kowa kuma ba ma son a shiga gonar mu, Eid ya fada min tun jiya ka dage sai ka ga Sarki zaka tafi, fadi bukatarka Sarki zai sallame ka ka yi tafiyarka”

Sarkin ne da kansa yake fada Eid na fassara masa dan dolensa, mamaki da jindadi da kauna ya hana Nuwaira cewa komai sai kallon Maleek dake cike da burgewa.

“Alhamdulillah, hakika duk wanda ya dogara ga Allah shi kadai Allah ya isar masa, ni bana tsafi van tana tsafi ba, kuma ban taba sanin yadda ake yinsa ba kuma bana fatar yinsa, ni dai na san ina bautar Allah ba tare da shirka ba, sannan ina karanta ayoyi da addu'o'in kariya, a jiya ma na kwana ina karanta suratul Bakara, kuma duk wanda yake karanta iya da ayatul kursiyu Allah ya turo mala'ikunsa su yi gadin Mutum ne, a inda mala'ika yake kuma aljani be isa ya raba gurin ba, muka karanta ta a gidanmu shiyasa kuka aika tsafinku be isa a garemu, domin idan aka karanta sau daya a wata tana tsare gida ta hana duk wani abu mai cutarwa rabar gidan har wani wata, saboda wannan ni ba tsafi nake ba da za ku surfafa bincike da za ku fahimci wannan addini ne ba tsafi ba, kuma ina fatar wata rana za su aje na mu addinin da al'adar ku karbi cigaban da duniya ta zo da shi haka ma ku rumgumi musulunci ku watsar da tsafinku”

Cikin alfaharin da jindadi Maleek yake fada ana fassarawa Sarkin da yarensa, har sai da ya kai karshe sannan Eid ya ce.

“Ba mu bukaci ka tallata mana addininka ko al'adarka ba, ka bar mu da na mu, kai ma ka rike naka, Sarki yana tambayar dalilin ganinsa da kake son yi, kuma ina ganin ka samu abun da kake bukata zaka iya tafiya”

“Aa ban fadi bukatata ba tukuna, dan haka ba zan bar garin ba sai na isar da abun da ya kawo ni”

Eid yaja numfashi da karfi da bakinciki sannan ya fadawa Sarki abun da Maleek ya fada.

“Tuk rid jaur bhakar suuf hutk garfha ifftuk galink galink ket”

Eid ya juya ya fassarawa Maleek.

“Ya fadi bukatarsa ba ma son zamansa a cikin garinmu”

“Ina neman auren yarku Nuwaira ne, saboda a yanzu irin addini take yi, ta saba da irin al'adata da kuma dangina, ina tunanin bata da bukatar zama a cikin garin nan, domin ba zata canja addini ba ba zata sake komawa addininku ba, kuma ba zata karfi kujerar tsafin da kuke son bata ba, idan har kuka yarda kuka ba ni aurenta zan dauke ta mu bar garin nan da ita yau din nan ba sai gobe ba, kuma ba za su sake ganinmu ba, ina tunani bata da amfani a gareku a yanzu saboda ta karya dokokinku kuma kun yafe ta kamar yadda ka fada”

Eid ya mike tsaye ya bar kujerar da yake zaune ya nufo inda Maleek yake cikin zafin nama, kamin ya karasa Sarkin ya daka masa tsawa.

“Karka kuskura kai kanka ga halaka, kana ganin wannan matashin ka san sai da ya shirya sannan ya shigo garin nan, neman yake a taba shi ya janyo mana fitina, fassara min me yake da bukata”

Sai da Eid yayi da gaske ya yaki zuciyarsa sannan ya iya fadawa Sarki abun da Maleek yake da bukata, daga baya ya jadadda masa da cewar ba za su aminta da haka ba, domin wannan ya zama cin fuska, kuma saboda ta karya dokokinsu har sun yi fushi da ita sun yafe ta ba shi yake nufin a barta ta aure wani bare ba. Sarki ya daga masa hannu.

“Yanke hukunci ba a hannunka yake ba Eid karka zafafa, kuma kar bacin rai ko soyayya ta saka ka manta da ka'idodi da dokikin garin nan, idan muka yafe mutum muna nufin cire hannayenmu daga duk wani lamari nasa, ko da kuwa zai mutu ne, kuma ba zamu tarbe shi ba ko da zai bukaci dawowa a garemu, ba kuma zai aura daga garemu ba.
Kaka ya taba fada min cewar kamin a haife ni, wasu mutane biyu sun taba karya mana doka, ya saka aka koresu daga garin nan, har yanzu babu ruwanmu da iyalansu, ta farko daga cikin gari take, lokacin da dadin tsafi yayi mata yawa sai ta zurfafa ta dauki maita, mu kuma ba mu yarda da maita ba, duk wani tsafi bayan wanda muka gada gurin iyayenmu ba mu yarda da shi ba, sanadin hakan muka kora Iya ta bi duniya, har yau babu ruwanmu da zuri'arta, bayan ita kuma Wasim ɗa daga masarautar nan, soyayya ta dibeshi kamar yadda take son dibarka a yanzu, ya karya mana dokoki ya shigo mana da bare, kuma ya fitar da ita ba tare da izinin kakanmu ba, daga karshe ya zabi addininsu da al'adarsa ya watsar da ta mu, hakan ya saka shi ma muka yafe shi, shi ma babu ruwanmu da shi da zuri'arsa, dan haka karka yi kuskure biyewa son zuciya ta kai ka ta baro”

“Duk wata azabtarwa da wahala da na jurewa sha a gurinku, tsawon lokacin da Waira ta dauka bata kusa, na jure ne saboda ina sonta ban taba fadawa kowa wannan maganar ba amman zan fade ta a cikin fadar nan, na san kowa ya lura da hakan, na raine ta tun tana karama har ta fara wayo, rana daya kuma sai wani ya dauke min ita?”

Wani daga cikin manyan masarauta da suke gurin ya mike tsaye ya isa gurin da Eid yake tsaye ya dafa shi.

“Kwantar da hankalinka Jarumi na, akwai mata da yawa a cikin garinmu da suke sonka, akwai matan da suka fi Waira kyau da komai ciki da wajen masarautar nan, ka rufe idonka daga ganin Waira ka bude idonka a garesu cikin kankanen lokaci za a gama da su, karka yarda zuciya ta deba ka gujewa umarnin masarautar nan, domin wannan matashin ba zai yarda ya barka maka Waira ba, ko da kuwa ka yarda ka koma cikin kalar tsafinsa ne, idan kuma muka hana masa ita zai iya gwada jayayya da mu”

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.