Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 121 of 227
“Na tafi can?”
Ummi ta yi murmushi ta shafa kanta, sai idonta ya cika da hawaye tana tunawa da Nimra.
“Aa zauna a nan, amman dai kar wani yayi miki wani abu ki ce an miki ba daidai ba, nan gurin cin abinci ne ba gurin karatu ba”
Da kai Waira ta amsa mata ta cigaba abun da take har sai da ta ga Ummi ta bar falon ta koma kitchen saboda shigowar Hanne. Sannan ta tashi da kamar sanda ta nufi upstairs ta hau, bangaren da dakinta yake ta nufa kamar zata shiga sai kuma ta wuce dakinta ta tsaya bakin kofar dakin Maleek, har yanzu zuciyarta da kwadayin son zuwa gurin Ameer dan haka take jin kamar idan ta yi ma Maleek magiya zai yarda ya kaita. A hankali ta murda kofar dakin ta bude ta leka, sai ta hango shi zaune kan kujera yana fuskanta windows din dakinsa dake bude, bata san abun da yake ba domin kansa a kasa yake yana ta rare karatun Al'qur'ane, baya ta yi kadan ta yadda ba zai hango ta ta tsaya rike da kofar tana sauraren yadda muryarsa take da dadin gurin karatun, yadda yake jan aya ya direta ya dauki wata ya tafibda tunaninta, zakin muryarsa da kuma dadin abun da yake karantawarta ya saka ta tsayuwa jikin kofar har ta kai zaune ta tsanu tana jin ayayoyin da bata san akan me suke magana ba, wani yare ne mai dadin sauraro da saukar da natsuwa,ba wannan ne karon karfo da ta ji karatun a gidan ba, sai dai bata taba maida hankali ta saurara da natsuwa ba irin yau, kuma wani be tana karatu da murya mai zaki ba irin ta Maleek, wannan ne karon farko da taba jin Maleek yana karatun, a yanzu kam ta tabbatar wannan yaren ya fi nata da na su Ummi da kuma wanda aka koya mata wato turanci dadi nesa ba kusa ba. Shi yake karatun ita tsigar jikinta yake tashi ji take bata taba jin wani abu mai dadi saurarowa irin wannan!
Dan juyowa yayi kadan sai ya lura da kofar dakin dake bude kadan, ga kuma inuwar mutum a zaune, be tabbatar ba amman zuciyarsa ta raya masa cewar Waira, domin ita kadai zata yi masa haka, Namra ya san idan tana bukatar wani abu zata iya masa magana, balle ma dakinsa ba gurin shigowarta ba ne tun a lokacin baya hakan ya saka sai suka dauke kafarsu daga dakinsa gaba daya, Ummi ma dake shigowa ba zata masa labe ba. Yana kawai a karshe aya, ya rufe qur'ane ta aje ya tashi ya nufi kofar ya bude tana ganinsa sai ta mike tsaye da sauri ta daga kai tana kallonsa ta manta da hawaye a idonta har sai da ta ga yana kallon fuskarta.
“Cry???”
Ta saka hannu ta sauri ta share.
“Abun da kake yi ne?”
Ta fada a shagwabe, sai ya tsaya tunani domin be san wani abu da yake ba.
“Oh karatu?”
Ya tambaya tunawa da yayi. Sai ta daga kai masa.
“Shi me yasa baka koya min ba?”
“Shi ak karatu ne, wani bangare ne na ibadar mu, ke kuma ba Musulma ba ce”
“Ke ma ba kuna da ibadar ku ba?”
“Yes amman wannan karatun yana da dadi, na ji wani iri karatun akwai dadi”
He's not in the mood if not da sai yayi mata murmushi ko kwararran bayani, sai dai shi ma yana cikin bacin rai na abun da Ameer yayi da kuma bakinciki rashin kanwarsa Nimra, wannan ne silar karatun al'qur'anen da yake da yamman nan domin samun walwala.
“Why are you here?”
Bata san tana da wayon iya roko ba sai a lokacin, kamar wata almajira haka ta zube kasa ta hade hannayenta ta daga kai, daman sai da daga kai kam tana tsaye ma ta daga kai ta kalleshi balle ta zube kasa. Marairaice murya ta yi ta fara masa magiya.
“Please Ya Maleek i know you hate me, but please ka kai ni gurin Ameer, ina son magana da shi, please”
Da hannu yayi mata nuni da ta tashi ta fice domin ya lura bacin rai kawai take son kara masa. Sululu a tashi ta juya ta fara tafiya tana yi tana waigensa shi kuma yana tsaye bakin kofar yana kallonta har sai ta sauka. Dinning ta dawo ta zauna tana kuka domin jin busar sarewar da ta ji Ameer yana yi tana son ta sake jin irinsa kuma tana son ta yi masa tambayoyi akai idan ma bata masa tambaya ba zata so rumgumarsa ta san komai. Tana tsaka da matsar kwalla mai goge mata uniform ya danna door bell din kofar, sai ta gwada yin karanbanin budewa domin bata taba mata gwada budewa wani kofa ba, ko da yi knocked din kofar sai dai ta yi ta kallo ko ta fadawa wani an taba kofa a zo a bude amman ita ba zata bude ba. Sai dai yau yadda ta ga Ummi na yi idan zata bude kofar haka ta yi har ta bude.
“Hajiya Waira yau ke ce da bude kofa?”
Cewar Haruna yana rike da uniform dinta da ya goge hannunsa. Kallonsa kawai take kamar wata marar wayo bata ce masa komai ba, sai yayi murmushi ya mike mata kayan.
“Gashi an goge, kuma malaminki ya iso tun dazun yana jiranki”
Da zumudi ta karbi kayan bata ko iya kaisu dakinta ba ta aje su akan kujera ta nufi dinning ta dauki jakarta da kayan karatunta ta fice da sauri. Kamin ta isa inda yake har da hadawa da gudu, sai dai yanayin yadda ta yi arba da fuskarsa ya katse duk wani hanzarinta. Zaunawa tai tana kallon yanayinsa da alama dai kam yau ransa a bace yake matuka.
“Good Evening”
Ta fada tana kallonsa sai ya amsa mata ba tare da ya kalleta ba, a ka'ida idan zai mata darasi na gaba sai ya yi mata tambayoyi akan darasin da aka yi na baya, sai dai be yi mata tambaya ko daya ba ya cigaba da dora mata daga inda ya tsaya a kwana ukun da suka wuce. Sakancewarta mai fahimta ta maida hankali sosai akan darasin har aka yi aka gama. Yana kokarin maida kayan da yayi mata karatu da su a jakarsa ta kalleshi.
“Wani ya bata maka rai yau ko Uncle”
Ba tare da ya kalleta ba ya amsa mata.
“Baki marmarin gidanku ne? Baki kewar garinki da mutanenki ne? Akwai abun da yake burgeki a nan?”
Ta sauke kai kasa tana taba littafin dake gabanta.
“Ina yi, amman....”
Ta kasa karasawa bata son ta fada masa cewar tsoron komawa take. Sai kawai ta saka hannu ta share hawayen da suka cika idonta.
“Abubuwa da yawa suna burge ni a nan”
Ta dago ta kalleshi.
“Kamar rayuwarsu, yadda suke mu'amala ababen hawansu, yadda uwa take kula da yayanta, yadda suke rayuwa a gidan nan, yarensu, da kuma yadda zuciyarsu take da son mutane da nuna kauna ga kowa, ni ba jininsu ba, ba yar garin ba amman Ummi ta nuna min kulawa da soyayya, kamar a garinmu idan ba jininmu basa son kowa basa barin kowa ya zauna, basa maraba da kowa, basa yarda su koyawa kowa yarensu”
Ya tsayar da abun da yake ya kalleta.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.