Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 115 of 227

“Saboda makiyanka suna cikin gidan daka saba kwana?”

“No Daddy no har abada, kawai dai ina jin gidan kamar ya matse ne, ina jin wani yanayi marar dadi idan na tunkari gidan”

“Shiyasa na ce ka bar abun nan ya zauna a sirri, domin har yanzu baka mallaki hankalin da zaka iya controlling kanka da zuciyarka, me zai saka ma na yarda a gidanka kake? Kuma idan a gidan kake waya san iya abun da zai biyo baya? Zaka iya illata kanka ko ka illata wani, ko kuma a zo a yi maka wani abun”

“I can controlling myself, Daddy ni ba karamin yaro ba ne zan iya kula da kaina, sanin gaskiya ba zai kara min komai ba sai kwarin guiwa da sanin waye ni, bani da halin wulakanta kowa a yanzu, mutanen da nake ganin kamar na fi, wata kila sun fi ni komai, i need to know su waye familyn mahaifina, waye shi, wata kila ni din ba dan kowa ba ne, na ci mutuncin mutane da dama, saboda ina jin cewar na fi su, ashe ba haka ba ne”

“Ko a yanzu ka fisu Ameer, fada maka gaskiya ba zai canja matsayinka da duniya take kallonka da shi ba, ba kuma zai saka na tashi daga mahaifinka ba, babu abin da zai canja, sai dai idan butulce min zaka yi, ina son zan samu Zahra mu tattauna wannan maganar a barta ta zauna a sirri, kuma har yanzu Ameer shi kadai ne ďa namiji da Mr Bashir ya taba haihuwa, babu wanda zai fika gata da jindadin rayuwa i promise you this”

“Mahaifin Maleek ya fada min, saboda rashin kudin aiki aka siyar da cikina, kuma bayan siyar da cikin Ammy ta fada min Zahra ta kyauta da ni a gareka, wata kila saboda tsoron talauci ne ko Daddy? Akwai abun da ya fi wannan zafi? Kana ganin zan iya aje wannan abun na manta da shi?”

“Ameer ka dawo gida ka kwana, bana son ka je ko'ina”

Daddy na fadar hakan ya yanke kiran be tsaya jiran abin da Ameer din zai fada ba, domin ya fahimci Ameer din yana son jan maganar ta yi tsawo kuma ba lallai ya fahimci abun da yake kokarin lurar da shi a yanzu ba. Aje wayarsa ta yi daidai da sauwa hawaye a babban mutum kamar Mr Bashir ba tare da ya kalli Mommy dake gabansa ba ya ce.

“Jamila ta lalata min duk wani abu da shirya, ko da yake ba laifinta ba ne ita kadai har da Zahra, yanzu sun kirkiri tazara tsakanina da wanda na fi kauna a duniyar nan, kuma sun yi nasara shiyasa bahaushe yace tsintacciyar mage bata mage, da na san wannan ranar zata zo da ban karbi wannan kyautar da Zahra ta yi min ba tun farko”

Cikin yanayi mai ban tausayi Mommy take kallon jagoranta nata idon na kwarar da kwalla ta ce.

“Ka yi hakuri, haka Allah yake ikonsa idan ya zo, da ace ya so da dauke Ameer zai yi gaba daya ya mutu, ba ku san abun da zai faru gaba ba, dan Allah ku bar jayayyarsa, masu iya magana sukan ce ba a jayyyar ďa da miji, idan aka yi jayayyarsu tafi suke su bar masu jayayyar”

Mommy bata taba sanin cewar ba shi ya haifi Ameer ba sai a yanzu da komai ya lalace. shakuwarsu da yadda kaunar Ameer take a zuciyar mijinta take tunawa sai tausayinsa ya kamata. Tun da ya aureta be taba zancen mahaifiyar Ameer da ita ba idan ma ta dauko masa sai yace mata baya son maganar a dole take kawar da zancen domin ita macece mai matukar son farincikin mijinta yana ďaya daga cikin dalilin da ya saka take nunawa Ameer kauna, domin ta lura yana matukar kaunar Ameer ya kuma tabbatar mata da hakan tun kamin ya aureta.

“Baka taba kuskuren aikata wani abu da zai nuna Ameer ba ďanka ba ne, ko da wasa baka son bacin ran Ameer, Wallahi a rayuwata ban ga wani uba da ya nunawa ďansa gata fiye da yadda ka nunawa Ameer ba, lallai duniya zata girgiza idan labarin nan ya fita”

Tana fada tana kuka, ita ma tausayin Ameer din take jin cewar be sani ba sai a yanzu, kara ma Daddy ya san da sirri amman ya boye saboda farinciki ďansa, amman Ameer fa? Dare daya da wuni aka ruguza masa komai.

“Wata kila da Jamila bata aikata abun da ta aikata tun farko ba, da ba mu jefa yaron nan da kanmu a matsala kamar haka ba, ina tsoron kar ya shiga wani hali”

“Jamila ai dole ta fada masa gaskiya, saboda ta bata alakarku, na yi imani ba zata tado maganar kai tsaye ta fada ba, amman idan har ya bukata zata fada masa domin tana kallonka a matsayin wani wanda ya samu farinciki da kyautar ďa silarta amman ya kasa zama da ita, ya ki yarda ta bawa wannan yaron kulawa a karkashinsa, kai ma baka yi mata adalci ba, domin saboda kai ta aikata haka sai gashi kuma ka rabu da ita.... ”

Mommy na aje ayar zancen Daddy ya rufe da fada, domin ji yake a yanzu ba shi makiyiya a rayuwarsa kamar Zahra da Jamila, ba ma kamar Jamilar da ita ce silar komai.

“Toh zama zan yi da ita? Bayan ta yaudare ni? Ta jefa a matsala ta aikata kuskure da addinin musulunci ma be yarda da shi ba, sannan yanzu ki kalli idona ki ce wai na kyale ta? Haukace ne ni da zan zauna da ita? Ko kuma neman haihuwa hauka ne? An isa ayi ma Allah wayo ne? Yanzu da ya tashi ba ni yayan ba ya ba ni ba? Taya za zauna da macen da bata da tawallaki da imani a zuciyarta? Idan har zata iya aikata hakan me kike tunanin gaba? Da ace ban gane gaskiya ba haka zamu yi ta zama ina kallonta a matar kirki? Ashe ke ma dai baki da hankali, ina ganinki mai ilmin ashe na banza ne”

“Allah ya huci zuciyarka, ban ce ka zauna da ita ba, kawai ina fadar abun da na fahimta ne”

“Fahimtar banza fahimtar wofi, mai daki ai shi ya san inda yake masa yoyo, karki fada min maganar banza, ina neman abun da zai zame min mafita ni da ďana sai kuma ki fara fada min wata maganar banza akan Jamila Malama tashi ki fice daga daki”

“Ka yi hakuri dan Allah... ”

“Ki tashi ki fice na ce”

Ta mike tsaye cike da nadamar maganar da ta yi ta fice daga dakin ta bar shi sai huci yake, abun da ba halinsa ba domin mawuyacin abu ne ta ga bacin rai a fuskarsa idan ma ransa ya bace yakan yi kokarin boye abun ya barshi a ransa.

AMEER POV.

Ji yake kamar shi kadai ya rage a duniyar nan he's feeling so lonely. Wani irin tarin bakinciki da damuwa ne a cikin ransa, ya dade a cikin motar kwance idonsa a rufe sannan ya bude motar ya fito ya shiga ciki, sai da ya fara bude fridge ya dauki gorar ruwa ya sha sannan ya dawo falonsa ya zauna yana sauke ajiyar zuciya. Be yi bachi ba kuma be tashi daga falon ba har kusan 11pm, tunani yake wani abun yana zuwa masa baibaiwa wani a daidai, wani tunanin kuma idan ya fadada sai ya ji kamar ya fashe da kuka. Sha daya na dare da yan mintuna kiran Abdull ya shigo wayarsa, yana ganin sunan mai kiran gabansa ya fadi zuciyarsa ta raya masa cewar Maleek ya labarta abokansa abun da yake faruwa shiyasa Abdull ya kira shi by this time. Amsa kiran yayi ya saka wayar a speaker yana tunanin kalar amsar da zai bawa Abdull idan ya tambaye shi.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.