Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 134 of 227

“Jiki Alhamdulillah ďan nan, Allah yayi albarka kana ta fama da dawainiya”

Humaira ta mike tsaye ta bashi kujera, sai dai ta san ba zai zauna ba, domin ba gwada zama a dakin ba duk zuwan da yake.

“Kullum zai kin kin ba ni kujera, kuma kin san ba zama nake ba”

Ta yi murmushi.

“Ina jin ba dadi ne ace ina zaune kana tsaye”

“Kuma kullum sai na tararda ke a nan ke kike jinyarta bayan ga mahaifiyarki, ba kasafai nake tararda ita, Allah yass dai kina zuwa aiki”

“Duk lokacin da zaka zo kana sa'a da ina nan ne shiyasa, aiki kuma na daina zuwa ai tun a wacan lokacin”

Ya daga mata kai.

“You got lucky na canja if da yanzu na koreki”

Dariya Fiyya ta yi kamar yadda Humaira ma ta yi dariyar.

“Baka bukatar ka koreni ai, ni na kore kaina?”

“Why?”

Ta daga kafadunta.

“Kawai dai”

Be sace cewa komai ba, ya kalli agogon hannunsa.

“Kuna bukatar wani abu?”

“Aa bama bukatar komai a yanzu”

Shigowar da Dr yayi ne ya katse hanzarinsa daga yi musu sallama ya fice. Likitan dake cikin shiga ta kayan likitoci ya iso gurin ya mikawa Ameer hannu suka gaisa.

“An fada maka sakona”

Ameer ya kalli Humaira wadda ta dago tana kallon Likitan.

“Yanzu nake kokarin yi masa bayani”

Likitan yayi murmushi.

“Kin manta kenan?”

“Aa na tuna yanzu da na ganka”

Ta fuskanci Ameer dake jiran abun da zata fada masa.

“Yace gobe za a kwance daurin da aka yi mata, a duba, idan yayi haka ake so, idan kuma be yi ba sai an sake wani”

Tana fadar idonta na cika da kwalla.

“Sarkin kuka daga magana sai hawaye, haka jiya kika min fa”

Likitan ya fada yana kallonta.

“Bana son tashin hankali, ba mu da yawa a dangi kusa, bana son na sake rasa kowa”

“Ba saki rasata ba, aiki ne kawai kuma ni ba cinye ta zan yi ba, I'm not zombie”

Ta yi murmushi tana share hawayen idonta.

“Ni ban ce ba”

“Da dai yafi”

Duk abun da ake Ameer be ce uffan ba, sai kallon tsohuwar dake cin ayarba hankali kwace yake kamar ba ita ake fadar za a sakewa aiki ba.

“Ita hankalinta a kwance ma yake naki ne a tashe”

Likitan ya fada yana kallon Humairah

“Toh abun da Allah ya kawo ba sai hakuri ba, gwagwarmaya wace kala ce ba mu gani ba?”

Ameer yayi murmushi yana kallonta, karfin halinta da imani ya burge shi.

“Allah ya kara lafiya”

Ya fada sannan yayi ma Fiyya alama da su tafi da ido, Fiyya ta yi musu sallama suka fice. Likitan ya juya ya kalli Ameer har sai da ya fice sannan ya maida dubansa gurin Humairah.

“Am ya sunanki ma?”

“Humairah..”

“Haka ashe na rike sunan”

Ta yi murmushi tare da sauke kai kasa, sai ya dauki file din da ya shigo dashi bayan ya gama duba Tsohuwar ya fice. Zaunawa Humairah ta yi tana fadin.

“Yau Mama bata zo da wuri ba, gashi ina son na shiga makaranta kar na yi latti”

“Ki zuba min abinci da aka kawo sai ki tafi, ai zata zo wata kila ta tsaya wanke tsumman da tafi da su jiya ne”

“Maybe”

Ta dauki plate din ta bude coolar jalof din shimkafa ce da aka yi mata ado da doya ta sha kayan kamshi da vegetables ga kuma mai har yayi yawa. Rabin plate ta zuba mata ta dora mata a saman gadon ta matsa mata da ruwa kusa.

“Ba zaki ci abincin ba?”

“Sai na dawo zan ci”

“Toh Allah ya kiyaye hanya, yau ba su bada kudin da suka saba fadawa ba”

“Yau da gobe ai sai Allah Hajiya, wata kila sun fara gajiya ne ko kuma sun manta”

“Ba dai gajiya ba, sai dai ko mantuwa amman dan dan abun da suke ba mu ai be taka kara ya karya ba a dukiyarsu. Ni ba dan ba a son kaddara ba ai da na ce kara da aka yi haka, dubi ki ga kullum sai an kawo abinci, ga kudin nan, kuma sun dauke duk wata hidima ta asibitin nan, gaskiya suna da kirki, ko da can ke ce da masifar ki kike ganin kamar ba shi da kirki, kullum fa sai ya zo, mamansa ma kullum tana hanya”

“Hmmm Hajiya, ke dai kin ganshi kawai amman da can ba haka yake ba, yanzu ne ya canja”

“Ke ma ai na san halinki fitina ta miki yawa”

Ta yi dariya ta nufi gefen gadon Hajiya ta dauki jakarta ta goya, sannan ta yi mata sallama ta fice, tana tafiya harabar asibitin ta ji an kira sunanta.

“Humairah”

Ta dan juyo kadan sai ta yi arba da Likitan dazun, murmushi.

“Doctor”

“Na'am fita zaki yi?”

“Eh makaranta zan je”

“Wace makaranta? Ina kike karatu”

Ya jera da ita suna tafiya.

“Sky King University”

“Ah makarantar manyan mutane kenan, wane course?”

“Microbiology”

“Wow, ke babba ce”

“Kune manya ai”

“Kika ce ba, muje na sauke ki”

“No akwai inda zan biya kamin na wuce”

“Karki damu duk zan iya sama direbanki, kin ga wata rana zan yi alfahari na ce na taba daukar Humairah yar Microbiology a motata, zan ce ta yi min alfama ta shiga motata”

Murmushi ta sake yi ta girgiza kai.

“Bana son zolaya, Likita za'ayi ma alfama?”

“Eh mana ke baki san babba ce ba?”

Bata son jan zancen da tsawo dan haka ta yi shiru bata sake cewa komai ba har suka isa gurin motae yar yayi mai matukar kyau, kana ganinta kasan sabuwar mota ce, sai da ya saka key sannan ta bude front seat ya shiga ta zauna.

AMEER POV.

A Area 2 ya sauke Fiyya gidan wata kawarta da zata yi birthday, sannan yayi driving kansa zuwa gida, tun a harabar gidan yake kallon bakuwar motar da ke fake a compound din. Domin ba ta yi kama da motocin gidansu ba, yanayin yadda akai parking din ma ya fahimtar da ba direbobin gidansu ba ne. Yana wasa da key hannunsa ya shiga falon, sai ya samu Mummy da Ummi zaune, Daddynsa yana kan dayar kujerar fuskarsa dauke da murmushi. Ummi na ganinsa ta mike tsaye kamar karamin ma'aikaci ya ga boss dinsa.

“Ameer ka dawo”

Daddy ya fada, sai ya nufi inda Daddy yake ya zauna yana yi ma Ummi kallon tsanaki, ta yi rama sosai farinta ya wuce na ainahin fatarta wani fari ne mai sheƙar da fata, fatan idonta ta yi fari kana kallonta ka san lafiya bata isheta ba.

“Baka gaishe da Mamanka ba, tun fitarku take nan tana jiranka”

Mummy ta fada tana murmushi, still be ce komai ba, sai kallonta kawai yake. Hakan ya saka Ummi jin wani iri sai ta ji kamar ta tsargu, domin ganin take komai ta yi ma Ameer a yanzu ba zata burge shi ba.

“Na zo ne kawai na ganka, Daddyka ya fada min abin da ya faru, ina addu'a Allah ya tsare gaba, kuma idan ka ba ni dama ina son ni ma naje na dubata for the sake of you”

Ta karasa maganar muryarta na rawa kamar mai tsoron abun da zai fito daga bakinsa. Ya dauke kai sannan ya mike tsaye.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.