Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 21 of 227

Ya mika masa dayan wayar dake aje a cikin motar.

“Akwai Sim a ciki, zaka iya kira da ita take care of yourself”

Kallon wayar kawai yayi isa da takama ta hana shi mika kallo ya karba, ko ba komai dai wayar ta masa karama domin baya rika kananan wayoyi, iPhone 14 ce while wayar dake dayan hannunta is iPhone 14pro max duka wayoyin yana jin ba ajinsa ba ne, ko ba komai shi baya son abun da kowa zai rika yayi, ya fi son nasa ya zama dabam ace kalilan ke da abun hakan kan banbanta da sauran mutane.

“1742 is my ATM Password, wayar kuma ba password”

Ganin ba zai karba ba ya saka ta aje wayar a muhalinta dake cikin motar, ta sake bude jakarta ta dauko dollars ta aje a gurin.

“Ko da bukatar cash ta kama ka”

Ta bude motar zata fita.

“Miyasa kike min duk wannan?”

“Because I care for you, i don't want why i don't how, kawai ina jin na damu da kai, don't hurt yourself please”

Wannan karon ta yi sa'a ya daga mata kai, sannan ta sake dubansa ta fice daga motar ta rufe masa kofar, tsaye ta yi har sai da ta daina hango shi sannan ta shigo cikin gidan da masu gadi suka dade da bude mata gate.

WAIRA POV.

Har cikin dakinta Eid ya kawota, a nan wani babin nishadi ya sake bude sabon shafi, sai dai wannan karon hira yake mata irin na wanda ya saba mata lokaci zuwa lokaci, na wasu mutanen da suka banbanta da su ta bangaren abinci, al'ada da kuma addini da ma rayuwar kacokam.

“Ai akwai zafi sosai”

Ta fada a lokacin da yake mata bayanin yadda matansu suke rufe jiki, domin ita duka tufafinta guntaye ne, rigar da zata iya kiranta da doguwar riga bata rufe mata kafafuwa ba, da kadan ta wuce quiwarta, wani lokacin kuma zata saka riga da skirt na fata ko na saki irin na mutane da da ake yi da kaďa rigar iya cibiya skirt din iya guiwa ko ya wuce kadan, ba al'adarta bace saka talkami komai zafin rana da ake, komau hadarin guri haka take shiga da kafafuwanta babu ruwanta da saka talkami balle kuma wanke kafar.
Ta mika hannu beran dake lalen kwanon da take cin abinci ya hau hannunta ta saka shi a tsakankanin kafafuwanta tana shafa shi.

“Akwai wanda na san idan ya shigo dakin nan sai ya mutu ko ya suma saboda tsananin tsabtarsa”

Ta juya ta kalli dakinta da yake ya mutse, ita kam sam bata ga wani abun kyama ko Allah wadai a dakin ba, ita dai yadda take rayuwarta a haka tana jin dadin rayuwarta sosai.

“At takfr hur verrr gulta jaget”

_Yayi tsabtarka?_

“Ya fi ni sau dubu”

Ya fada yana kallonta, sai ta ya mutsa fuska domin Eid ma ganinsa take mai tsananin tsabta da idan zai ci abu sai ya wanke ga wanka a kullum idan kuma aka ce akwai wanda ya fi shi ai abun be burge ba.

“Bana son irin wadanan mutanen sam, amman fatar jikinsa ba irin wannan bace ko? Saboda tsabta”

Yayi murmushi mai sauti, ya kama hannunta ya dora saman goshinsa ya yana kallon kyakkyawar fuskarta dake dauke da datti, so yake kawai ta ga yadda suka yi rayuwa da mutumen na dan lokaci kadan domin ya san tana da wannan tsafin da idan ta dafa kan mutum tana iya ganin da jin abun da ya faru a rayuwarsa ta baya. Runtse ido ta yi sai ta fara arba da karar wani abu mai da bata taba jin irinsa ba, karar ta girmin kunnuwanta, hayaniyar da take ji ta yi yawa, dishe dishe ta fara ganin wani abu bata taba gani ba yana gudu wasu kalar na binsa a baya karar karfe da karfe suna gaduwa kamar za su tashi kwakwalwarta, da sauri ta dauke hannunta ta bude ido domin karar da take ji ta girmi kunnuwanta.

“Kara sosai”

“Abun da nake baki labari kenan Mota, ita suke hawa a madadin dabobin mu”

“Outar.... ota...”

Ta maimaita tana mamakin wace irin rayuwa ce wannan. A gurinta ya wuni har dare sannan ya kunna mata wutar tsafi ta haska mata dakin na adadin awawanin da zai yi kamin ya kwanta a daidai lokacin da wutar zata mutu.
*⚜️ ...WANI GARI... ⚜️*

_Na Khadeeja Candy_

9️⃣

Kai ta daga sama ta kalli Namra dake tsaye tana kallon duk abun da yake wakana a kasan murmushi kawai ta yi ta maida kanta kasa ta cigaba tafiyar ta har ta shigo cikin gidan, sai da ta duba ko'ina bata ga Ummi ba sannan ta hau sama ta duba dakin Ummi nan ma bata ciki, sai ta zagaya ta inda yar'uwarta take tsaye tana kallon harabar gidan, tun kamin ta karasa kusa da ita ta ce.

“Ummi bata dawo ba?”

“Suna can gurin case din”

“Kirana fa ta yi wai na dawo gida, ta ji abun da na yi miki”

“Na fada mata komai ai, akan wani banzan saurayi zaki wulakanta ni”

Duk maganar da suke Namra bata juyo ta kalleta ba, ita kuma bata fasa murmushi da mamakin halin yar'uwarta ba.

“Kyakkyawa ne ko ba haka ba? Yana da masifar kyau Namra baki gani ba”

“Kyaun ne matsalarki?”

“Yana da kwarjini, yana da natsuwa yana jin kanshi, samarin dake jin kan su ba su cika kula mata ba, domin gani suke kowace mace ba tsararsu ba ce”

Magana take tana murmushi domin ji take kamar yana a gabanta tsaye tana kallonsa. Namra ta juyo ta kalleta.

“Ke wai tsaya ba dai shi kika bawa motarki ba?”

“Mota kawai kika gani? Ke baki ga alamar zan iya ba shi rayuwata ba ma?”

“Love is stupid....”

Ta fada tana jan tsaki, tsabar haushi ma ya saka ta bar mata gurin, Nimra ta yi murmushi domin ita kadai ta san abun da take ji a game da Ameer.
Bata sauko ba sai da ta hango Shigowar iyayenta tare da Yayanta Maleek da kuma Mahmood, kamin ya zagayo ta sauko har sun shigo cikin falon.

“Ummi an kama shi?”

Shi ne abun da ta fara tambaya, Hajiya Zahra ta yaye mayafinta ta zauna saman kujerar da ba a isa a saka a gidan wani karamin mai arziki ba tana fadin.

“Abban ku be bari na shiga ciki ba, a mota suka bar ni ban san ya aka yi ba, sai fada yake min wai miyasa na bi su”

Nimra na kallon Abiey ya dankaro mata harara.

“Daga yau kar mu sake fita akan wani issues irin wannan ki dauki mahaifiyarki ku bi bayanmu”

Nimra ta marairaice fuska try to act innocent.

“Ba laifina ba ne fa, ita ta ce sai mun kaita saboda hankalinta ba zai kwanta idan tana gidan nan ba”

“Na fada miki dai, this should be the last, kuma an rufe case din nan daga yau kar na sake jin maganar mun yi solving da mahaifinsa”

Ummi ta kalleshi da sauri tare da mikewa tsaye Nimra da yar'uwarta ma haka, Mahmood da Maleek da suka san abun da ya faru ne kawai ba su yi mamaki ba, ba ma kamar Maleek da hakan yayi masa dadi.

“Saboda me? Shiyasa ka hana na shiga? Yaron ya fi karfin a hukunta shi ne? Taya mutum zai nemi kashe min yaro kuma kace kun sulhunta Ba sulhu nake so ba, hukunta shi nake son ayi idan ya saba yi ana kyaleshi to yanzu ya kai karshe”

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.