Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 2 of 227

MALEEK POV.

A fusace ya nufo downstairs, kamin ya karasa saukowa Ummi dake zaune a cushion kusa da mijinta ta yi saurin sakin hannun mutumen da a kullum ita Amarya ce a gurinsa ta mike tsaye tana kallon ďanta, daman can ta san za a rina hakan ya saka take son ta tari fushinta tun kamin ya isar mata da sakon dake bakinsa.

“Ka yi hakuri ni na saka ta shiga ta share maka ďakin”

Cak ya tsaya ya jimke hannunsa da karfi yana tauna hakora.

“Amman miyasa zata shiga tana kamshin turaren mata? Not just perfume har lips stick ta shafa min a mirror, and you all know how i hate duk wani abu da ya shafi mace miyasa zata min haka?”

“Zan mata magana, amman Maleek ka rika sassautawa...”

Bata kai aya ba Abiey ya tari numfashinta yana mikewa tsaye.

“Alright Son je waje ka sha iska, zan saka a gyara maka dakin, kuma ka bar ni da kanenka nan i will deal with them”

Sai a lokacin ya sauke numfashi ya kalli mahaifinsa

“Thank You Abiey”

Ya fada sannan ya juya ya fice, Ummi ta bishi da kallo cike da damuwa ajiyar zuciya ta sauke sannan ta juyo ta kalli Mijinta.

“Be kamata kana karfafa masa guiwa ba, wannan abun ya ishe ni haka I'm sick and tired of this”

Cikin kuka ta karashe maganar, Abiey ya kara masowa kusa da matarsa Zahra da bayan son damuwarta ma balle abun da zai saka ta zubar da hawaye ya rumgume ta.

“Ya isa Hayatie, kowa da yadda Allah yake halittarsa shi haka Allah yayi shi baya son mata a rayuwarsa ko wani abun da ya shafi mata”

“Ko dai asiri aka masa? Ni ban taba ganin mutum irin Maleek ba, ko kuma dai aljana ta aure shi?”

Sai kuma ta yi shiru, irin shirun dake karantar da mijinta wannan ciwon ya dade a kirjinta yana cinta.

“Ko kuma alhaki ne yake bibiyata?”

Ta yi masa tambayar da ba shi da amsarta, balle kuma ita da abun ya kullewa kai

“Ba ko daya, Zahra ya kamata ki gane kowa da yadda Allah yake halittarsa, ki daina saka komai a ranki, wata rana zai daina, kuma dai ki jawa yayanki kunne su daina taba min yaro”

Abiey ya fada yana kokarin kwantar da hankalin matarsa, dagowa ta yi daga jikinsa ta share hawayenta tana jin zafin halin da danta yake ciki.
Maleek na daya daga cikin irin mutanen da duniya take kafa tarihi da irinsu daidaiku a cikin mutane, domin ba kasafai kake jin mutumen da yake barin tahiri irin na shi ba, Maleek yana da wata bakar dabi'a da Allah ya halicce shi da ita ta tsanar mata, ko sunansu baya son ji sai dole, ya taso da wannan bakar dabi'ar ne tun yana yaro karami har zuwa girmansa, wannan ya saka ya yanke duk wata alaka da abun da zai hada shi da mace, ya'ala turaren mata ne ko wani abu na kayan kwalliyarsu, ko da hanya ce ta hada shi da mace idan akwai wata zai canja saboda kar su hadu, sai dai hakan be saka ya tsira daga gurin kanensa mata ba da suka mai da shi abun tsokana duk kuwa da tsoronsa da suke.
Sai dai ta inda abun ya zo masa da sauki be tsani mahaifiyarsa kamar yadda ya tsani kanensa ba, hakan kuma ba yana nufin ya zauna da ita su yi hira ko ya ci abinci da ita a teburi daya, idan yana neman shawara ko yana cikin wata damuwa mahaifinsa Abiey ne kadai zai iya zama da shi ya fada masa damuwarsa, sai kuma kanensa namiji.

Idan ka yi arba da Maleek yana wasa da dariya da sake fuska yana tare da abokansa ko yan'uwansa maza ne ko kuma mahaifinsa Abiey.
Yana daya daga cikin dalilin da ya saka baya son shiga yanar gizo, domin baya son cin karo da mata, wannan ya zame masa kamar wata cuta mai cutar da shi har ga Allah yana cutuwa sosai har ma ya cutar da wasu, wato mahaifiyarsa da kuma kanensa mata, wani abun da zai baka mamaki shi ne yadda mata suke rushing dinsa, domin saurayi ne da ya iya wanka da sanya turare mai jan hankali, ga kuma kyau da cikar kalama da zati irin na jaruman maza.
Babu daren da ba ya addu'ar Allah ya yaye masa wannan damuwar da mahaifiyarsa take kallonta a matsayin cuta, ya san ko ba a yanzu ba, wata kila a nan gaba abun zai fi cutar da shi fiye da yanzu, sometimes ya kan zauna yayi tunani dalilin da zai saka ya tsani mata sai ya rasa, and no matter how zai kwatanta sausauta kyamar abun a zuciyarsa da zarar yayi arba da mace ko ya ji muryarta sai tsanar ta mamaye zuciyarsa.
Kamin ya kawo yanzu ya sha wahala rayuwa sosai, domin ta ko'ina yana haduwa da makiyan nasa har zuwa lokacin da iyayensa suka fahimci damuwarsa suka fara sama masa mafita. Ko kadan hakan be taba dagawa Mahaifinsa Abiey hankali ba, domin a gurinsa ba wani abu ba ne dan ka tashi ka ji ba ka sha'awar wani abu ko kuma wani abun baya burgeka a ganinsa halittace, sai dai ta gurin Hajiya Zahra wato Ummi abun ba haka yake ba, domin ďanta baya iya zama da ita yayi hira balle ya fada mata damuwarsa, baya zauna a gurin daya da yan'uwansa mata, babu ruwansa da mace komai kyau da kwalliyarta, hakan ya saka take jin kamar ďanta ba daidai yake da sauran yaya ba, domin ta sani Maleek yana cutuwa da halin da yake ciki kamar yadda ya taba fada.

AMEER POV.

Jikinsa ne ya bashi ana kallonsa, hakan ya saka shi juyowa, sai yayi arba da Momy dake tsaye bayansa rumgume da hannayenta tana kallonsa fuskarta dauke da murmushi. Shi ma murmushi yayi ya sauke sarewar da yake busawa ya mike tsaye gaba daya.

“Momy”

“Na'am ďana tun dazun nake tsaye nan”

“Why”

“Ameer, bana son na katse maka busar sarewar da kake yi ne, domin ni ma yana min dadi”

Yayi murmushi ya shafa kansa, shi kansa da yake busar tana masa dadi balle kuma masu saurare.

“Ban san inda ka koyo wannan busar ba amman tabbas wanda ya koya maka kwararre ne sosai, domin tana shiga har cikin zuciya”

Wannan karon dariyar shakiyanci yayi wanda ta bayyana fararen hakoransa, sannan ya wuce gaba ya fara takawa, Momy ta bi bayansa tana fadin.

“Daddynka yana falo yana jiranka, na fada masa kana nan Garden kana hutawa ya bukaci a katse maka hutarwa a kiraka”

Ya juyo ya kalleta yana tafiya baya baya.

“Hmmm an kai masa karata kenan”

“Ka yi laifi ne?”

Ya juya ya cigaba da tafiyar ba tare da ya ce mata komai ba.
Ya rigata isa kofar falon hakan ya saka shi bude kofar ya jefa kafarsa a ciki yana wani lumshe ido saboda kamshi dake tashi a katon falon mai kama da wata karamar hadaddiyar daular Larabawa. A gurin da aka tanada domin aje talkami ya aje talkaminsa ya saka na shiga falon sannan ya karasa ciki. Kai tsaye Upstairs ya nufa yana wani taku kamar ba zai mutu a saka shi a ciki kasa ba, kamar an masa dole haka ya bude kofar dakinsa a hankali ya shiga, ko wace kusurwa da bango na dakin kamshi yake, kamshin turare da babu hanci da zai tantance iya kalolin da aka hada ya bada wannan kamshin mai dadin shaka, ko'ina na dakin tass yake an gogeshi sai kyalli yake irin kyalli da ko yawunka suka zuba saka iya dangwala yatsa ka laso abunka saboda yadda aka gyara gurin kai ka rantse da Allah ba a takashi ma, cikin wata tafiyar izza da girman kai ya tura kofar wani karamin dakin canja tufafi wato Closet mai yanayi da karamin Boutique.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.