Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 102 of 227

Abiey ya dafe kansa ya runtse ido yana jin duniyar na juya mishi. Can ya dago yayi ma Mahmood alamar ya fita da hannu.

AMEER POV.

Barin gidan yayi gaba daya bayan ya fito bangaren mahaifinsa, tunani kala kala akan maganar karshe da ya tarar Daddy na yi a waya, be gamsu da abun da ya ji yana fada ba. Ta dayan bangaren kuma zuciyarsa na ta son ya tattauna akan kalaman Ummi. Tuki yake yana tunanin kiran Hajiya Jamila duk kuwa da mahaifinsa ya ce kar ya kirata, but he need to ask her few questions, wata kila ita da Ummi sun san juna if not Ummi ba zata ambaci sunanta ba. Be ankara ba ya ji an bugu bayan motarsa da karfi a lokacin da ya karyo kwana, a take ya faka burki, daman mai nema a duhu balle an haska masa, da dai shi ya bugu motar wani ba zai tsaya ba, amman tun da tasa motar aka daka dole zai duba. A fusace ya bude motar ya fito wanda hakan yayi daidai da fitowar Jabir a tasa motar dake bayan ta Ameer.

“Sorry please amman kai ne mai laifi domin baka duba ba kawai ka hau babban titi”

“Oh Really saboda titin na Ubanka ne? Ni da motata zaka fada min ban duba titi ba? Baka tukin hankali ka yi shaye shayenka sannan ka fada min maganar banza....”

“Amman dai daga ganinka baka da tarbiya, daga magana sai ka fara zagin mutane...”

Jabir ya mayar masa a fusace yana nunashi. Ameer zai yi magana idonsa ya sauka akan Waira dake zaune gaban motar ta runtse ido sosai ta dafe kunnuwanta tun a lokacin da motarsu ta bugu da Ameer. Wannan ne karo na biyu da ya sake ganin kyakkyawar fuskarta a garin Abuja, at first ba zai manta ba a school bus ne, sai kuma a nan sai dai ya kasa tuna a inda ya fara ganinta, wata kila kuma kyauta ne yake rudarsa har yake ganin kamar ya santa. Kamar an masa allurar kwantar da tarzoma haka ya rasa duk wani kuzari da zafin zuciyar daya fito da shi da zimmar yin fada da wanda ya bugar masa mota. Yadda yake kallon Waira ya saka Jabir juya ya kalleta ya juyo ya kalleshi sai suka hada ido, Ameer be sake ce masa komai ba ya juya ya nufi motarsa ya shiga. Da kamar mamaki Jabir ya koma ya shiga motarsa yana rufe gambun sai Waira ta kara firgita ta kamkame kanta jikinta ya fara rawa.

“Hey ba fa hatsari muka yi ba bude idonki”

Ta girgiza kai alamat ba zata bude ba, har Jabir yayi baya yaja motar suka wuce bata bude idon ba.

“Gida nake so”

Ta fada tana son yin kuka, daman can bata gama wankewa daga tsoron mota ba, gashi kuma yanzu sun bugu motar wani.

“Babu abun da zai sake faruwa fa, kuskure ne kawai aka samu, shi ya shigo gurin da karfi be duba ba”

“Aa ina son gida gurin Ummi please”

“Shikenan bude idon to”

Ta girgiza kai gani take kamar hatsarin za su sake yi.

“Idan baki bude idon ba ba zan maida ke gida ba, that's the rule”

Ta bude idon kadan ta kalli titi sai ta yi saurin maida idon ta rufe, bata bude ba har sai da ta ji ya faka, a kokarinta na tantance inda take ya saka ta bude idon, wani katon shopping mall ne da ya ji ado tun a waje.

“Zauna a nan ina zuwa”

Ya bude motar ya fita, this time around hankali kwance take kallon gaban mall din. Be dade ba ya fito rike da leda, side dinta ya bude ya dora mata ledar saman jiki. Kamin ya zagaya ya shiga motar har ta bude ledar few abubuwa ne a ciki, chocolate, biscuits, sai wani katon milk candy dake cikin gwangwani mai kyalli kamar an watsa masa zinari.

“Na ki ne you can eat, dan dana na ji akwai dadi”

Ba ko wane kalar abu take ci ba, dan haka bata taba komai ba sai chocolate shi ma saboda rubutun chocolate ne a jiki, tasan ba irin wanda ta saba ci ba, sai dai a yadda ta fahimta ko wane chocolate yana da dadi sai dai dandanonsu ya babanta. Bakinta ta saka a take hakoranta dake da kaifi suka yanke mata ledar sai ta yaye ledar daga sama ta fara ci a hankali.

“Akwai dadi?”

Ta daga masa kai, bata san rowa ba dan haka ta gutsura rabi ta mika masa. Yayi murmushi yana girgiza mata kai

“Sha abun ki ni bana shan kayan zaki”

Ta rike da dayan hannunta idan ta ci na hannu dama sai ta ci da hagu, shi dai be ce mata komai ba har suka isa gida kamar yadda ta bukata, ba tare da ya je inda yayi niya ba.
[6/24, 4:36 PM] My S Line: 42

A gurin ya tsaya yana kallon motar su Jabir har ya ja suka wuce, sannan ya faka tasa gefen titin. Daman fitowa kawai yayi daga gidan ba dan yana da gurin zuwa ba. Sosai ya zurfafa a tunani yana son gano inda ya san Waira ko ya taba ganinta amman ya kasa, kallon da yayi mata a mota ma yanzu ya ki ya fita idonsa, sai da yayi da gaske sannan ya iya focusing akan abun da ya kamata ace shi ne a gabansa ba tunanin kyaun wata yarinyar da bata san da zamansa ba, kuma karamar yarinyar kanwar kanwarsa ba ma babbar mace ba. Ac motar ya kara sannan ya dauki wayarsa dake aje a inda ya saba aje ya yi dialing number Ammynsa. Kiran farko bata daga ba haka ma na biyu da na uku sai da yayi mata na hudu sannan ta daga.

“Ameer my son how are you?”

“I'm good Ammy”

Ya kai hannu ya rage ac jin kamar baya bukatarshi kuma.

“Ammy wani abu nake son na tambayeki, i don't want you to lie to me, kin san na yarda da ke, karki rushe wanann amince da ke tsakaninmu, kuma karki dubi Daddy ko ni ki fada min abun da ba gaskiya ba please..”

“Mene ne haka zaka tambaye ni Ameer?”

“Daddy ya kira ki?”

Ta yi jim kamar mai son ya canja mata tambaya.

“Eh ya kirani”

“I know na tambaya ne saboda na tabbatar zaki fada min gaskiya ko akasin haka, seriously bana son ki fada min abun da ba gaskiya, idan kika min haka zai yi wuya mu sake shiri da ke, you know how much i love you ko? Kin san ke na kallo kamar uwata right”

“Ni din ma uwarka ce Ameer, tambaye ni duk abin da kake so na maka alkawarin zan fada maka gaskiya”

“Akwai wata mata da na hadu da ita dazun, ta fada min maganar ban da da maganarta ba sai dai kuma sunanki da ta ambata ta ce na aje na tambaye ki idan kina raye ya saka na ji kamar akwai kamshin gaskiya a ciki....”

Sai da ya fara bata labarin abun da ya faru tsakaninsa da Maleek duk kuwa da ya san Daddy ya fada mata komai, sannan ya dora da abun da ya shiga tsakaninsa da Nimra zuwa yau da Ummi ta fada masa wannan maganar.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.