Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 79 of 227

Wata uwar harara Ameer ya watsa mata, ba dan yana a yanayin da baya son biye mata ba, da sai ya gaura mata mari a gurin ko ta shiga hankalinta, domin ya kura bata tsoronsa sam kuma bata kunyar fada masa magana, sai dai baya a cikin yanayin da zai biye mata su siyar da hali a gurin, dan haka ya dauke idonsa yana kai zuciyarsa nesa ya tattara hankalinsa ya maida gurin Nimra. Ganin hakan ya saka Humaira ta juya rike da gorar ruwanta ta koma a iyakar gaskiyarta take neman Allah y isarwa yarinyar da zuciyarta ke raya mata Ameer cutar da ita yayi, ko da yake ta ďayan bangaren tana ganin kamar har da laifinta taya za'ace duk wakar nan da take mata idan suka zo gurin bata dauki haske ta gane Ameer yaudararta zai yi ba, saboda yawan taba ta yake ta kyale shi yana shiga jikinta gashi yanzu har ta kai yayi mata duka kuma ya dauko sun ta zo gurin babu ko mayafi a jikinta babu talkami.

Ameer na ganin kiran number da ya kira ta Ummi dazun ya fahimci sun iso gurin, sai ya yanke kiran ya aika mata da sako daidai inda zata tsaya ta jira shi. Sannan ya kalleta ya ce.

“Tashi mu tafi”

Gudun kar ya rikata su fita tare mahaifiyarta ta gani ranta ya bace sai ya nemi Humaira ta rika masa ita suka fito yana gaba Nimra dake dafe da Humaira tana bayansa, sai da suka iso gurin motarsa da yayi parking sannan Ummi ta bude motar da facing din ta su ta fito tana kallonsa kamanin da ta gani a fuskarsa da jikinsa sun matukar daga mata hankali zuciyarta sai rawa, ita kadai take masa kallon tausayi da kauna, Abiey da Maleek kuma suna matsa kallon tsana daga cikin motar kamin su bude su fito. Nimra na ganin iyayenta sai hankalinta ya tashi ta fashe da kuka.

“Ameer kaika kira su?”

Ya juyo ya kalleta.

“Ba zan iya bari ki aikata kuskure nan ba Nimra”

“Ba kai ka fada min zaka iya mutuwa a kaina ba?”

“Hakan baya nufin na cutar da ke a yanzu, ba ki san abun da yake kasa ba”

“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un ”

Ta fada tana runtse ido. Maleek da Abiey suka iso gurin da suke tsaye Ummi kuma ta kasa karaso sao kallon Ameer take. Abiey ya kai hannu ya fisgo Nimra daga hannun Humaira ya tsinka mata mari sai da wutar kanta ta yi daukewar wucin gadi. Sannan ya kalli Ameer cikin bakar fuska ya ce.

“Babu kai babu jinina, babu kai babu zuri'ata, babu kai babu iyalina...”

Ya juya ya nufi motarsa yana jan hannun Nimra da karfi, ita kuma da yake bata da kunya sai kiran sunan Ameer take, har mutane suka fara lura da abun da ke faruwa. Allah ne kadai ya tsare Ameer be fadawa Abiey bakar magana ba, domin babu mai fada masa magana marar dadi be rama ba, sai dai tausayin Nimra da son nema mata sassauci ya saka be furta ma Abiey komai ba, sai kallon Ummi dake tsaye tana hawaye yayi daga inda yake yake fadar.

“Wata kila kin taba yin so a lokacin da kike da kurciya, ban sani ba ko kin san yadda yake da zafi da rikita zuciya, CIWON SO yana da wahala da dimauta mai yinsa, mutum kan fita hayyacinsa ya aikata abun da be dace ba, dan Allah ki dubi Nimra da idon rahma, wanda be taba so ba idan ya samu ba zai fita ďakin son da sauki ba, karki bari mijinki ya cutarta da ita dan Allah. Bata watsar da tarbiyar da kuka mata ba, duk abun da ya faru ba laifinta ba ne laifina ne...”

Each and every words da ya furtawa Ummi sai ta ji kamar magana yake jefa mata, gaba daya duniyar ta juye mata upside down. Maleek ya tabe baki yana kallon Ameer da tsarki.

“Nice one Ameer kai kake furtawa Ummi wannan maganar saboda da baka da kunya kuma baka da mutumci?”

Ameer ya matsa kusa da Maleek yana furzar masa da numfashi da karfi tare da saka hannayensa aljihu yana kallon cikin idonsa.

“Saboda bana da uwa a raye ba shi yake nufin van san darajar uwa ba, kai kuma baka san miye soyayya ba, baka san CIWON SO ba, saboda haka be kamata ka tsoma rubabben bakinka ba, baka san komai akan masoya ba dan haka karka sake karanbanin shiga a abun da ka zahilta, zan raga maka ne kawai saboda Uwa...”

Ameer ya daga hannunsa ya nuna Ummi dake tsaye, suna kallon kallo akuya kallon kura shi da Maleek. Maleek yayi kamar ya fada masa magana sai kuma wata zuciyar ta hana shi ya juya yana huci da jin ďacin maganar da Ameer ya fada masa ya nufi motarsu.

“Wayyo Allah zuciyata...”

Ummi ta fada tana kai hannu ta dafe zuciyarta, Maleek ya rikata da sauri ya saka a back seat inda Nimra take zaune ya rufe motar sannan ya bude front seat ya shiga domin Abiey ne yake tuka motar. Daga Humaira har Ameer tsaye suka yi suna kallon motar har ta fice daga gurin sannan Humaira ta cire hannayenta biyu da suke dafe a fuskarta tun a lokacin da Abiey ya mari Nimra ta ji kamar ita aka mara ta dafe kumatunta bata dauke ba sai da suka wuce. Sannan ta kalli Ameer tana hawaye ta ce.

“Baka kyauta ba, kalli yadda ka saka ƴa da uwa kuka saboda selfishness dinka, ka san yadda uwa take ji idan aka lalata tarbiyar ƴarta? Wallahi kana da hakki da yawa akanka”

Ya juya zata koma ciki, ya saka hannunsa ya rika dantsen hannunta ya fisgota ya dawo da ita daf da shi har tana iya iya jiyo numfashinsa ya kalli cikin kwayar idonta ita ma ta kalli tasa...

©Khadeeja Candy
©®Copyright
2023
[6/17, 10:49 PM] My S Line: 𝐖𝐀𝐍𝐈 𝐆𝐀𝐑𝐈

33

Sun dauki tsawon lokaci a haka ya kasa ce mata komai.

“It hurt...”

Ta fada slowly, sai ya kalli hannun nata ya sake.

“Ban yafe ba”

Ta fada da muryar da zai iya ji bayan ta wuce shi, yawu kawai ya hade ya nufi motarsa, ya bude ya shiga sai a lokacin ya kalli wayar Nimra dake hannunsa, samun kasan yayi da rashin sukunin abun da ya aikata, ya daga kujerar ta daya kwantar a dazun yana kallon gurin kamar tana nan, kamin ya kwantar da tashi kujerar ya kwanta a gurin gaba daya ya rasa ta inda zai dafa ya wanke Nimra, halin da ya jefata a yanzu ya matukar daga masa hankali, yana kwance cikin motar har la'asar sannan yaja motar ya fita daga gurin ya faka a gurin wani masallaci dake bakin hanya yayi sallah la'asar nesa da mamu.

*** *** ***

Har suka isa gida Nimra bata daina kuka ba, Abiey na faka motar ya fita ya nufi gurin masu gadi yayi musu gargadin cewar kar wanda ya kuskura ya bar Nimra ta sake fita daga gidan. Sannan ya dawo ya bude gefen da Nimra take ya fito da ita ya jefar a kasa kamar wanda be san inda ta fito ba, Ummi ta juyo da sauri ta kalleta sai dai bata da kuzarin da zata iso gurin domin zuciyarta a rike take. Abiey ya sake rika hannunta ya nufi cikin gidan da ita kamin ya isa falon Namra da Mahmood sun fito Waira ma tana bayansu, sai kowa ya kasa bawa Abiey hakuri ganin yadda fuskarsa take a hade kamar bakin hadari, tun da suke a rayuwarsu Abiey be taba saka hannu ya dakesu ba kuma ba taba yardar wani ya taba masa yara ba domin yana matukar kaunar yayansa, sai dai a yau shi da kansa yake yi ma Nimra hukunci. Sama ya hau da ita ta saka ta cikin dakinta ya janyo kofar da karfi.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.