Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 154 of 227

“Son”

“Abiey akwai matsala”

“Kamar ta me?”

“Wai Ameer yau ya fadawa Ummi yana son ya auri Waira imagine?”

“What? Bayan duk abun da yayi? Ita kanta yarinyar ya manta yadda ya barta a wulakance yanzu an dauke an gyarata ta yi kyau shi ne zai ce zai aureta”

Maleek ya tashi zaune da kyau yana jin yadda Daddy ya tabo masa inda yake masa kaikaiyi.

“Yauwa Abiey dadina da kai kana da sauri fahimta, ni abun ya bani mamaki kuma ya ba ji tsoro jikina shaking kawai yake gaba daya tunanina ya jagule bana son na ga abun da zai cutar da yarinyar nan ko kadan, amman Ummi bata ganewa sai fadar take wai ba yadda nake tunani ba ne, gaba daya na rikice Wallahi na ma rasa kalar tunanin da zan yi, amman gaskiya ba zan jure ganin Ameer tare da Waira ba innocent soul like her”

Daga dayan bangaren Abiey yayi murmushi domin yana iya fahimtar abun da ke zuciyar dansa ba tare da shi dan ya sani ba, Abiey ya dade da karantar abun da ke zuciyar Maleek ba dan shi Maleek din ya fahimci zuciyarsa ba.

“Idan kuma mahaifiyarka da gaske take fa? Ameer ba zai cutar da Waira ba? Kuma idan muka yi bincika muka tabbatar da haka zaka yarda mu aura masa ita?”

Kamar an kashe mutu haka Maleek yayi shiru a wayar ko numfashinsa ba aji Abiey kuma yana testing dinsa ne domin gane ko daidai a ma'aunin da ya dora ďansa Maleek. Rasa yayi me zai ce idan yace ko a haka be be dace da aurenta miye hujjarsa? Saboda ya wulakanta ta could be enough? Idan kuma babu hujja zai iya yiyu ace ya tsani Ameer din ne.

“Abiey yarinyar nan bata dace da aure a yanzu ba, ni da zaka dauki shawara kuma ka amince ka saka Ummi ta amince zan fitar da ita waje ta yi karatu mai kyau kamin ta dawo ta yi hankali ta san kanta then by that time tana da yancin zabar abokin rayuwa, amman a yanzu ko ba Ameer ba ni bana son ganin kowa a tare da ita, ita fa bata san wa take so ba, kalli yadda ta rika waken tana son Shuraim a baya sai ka dauka saurayinta ne, idan wani ya samu irin haka ai sai iya amfani da weakness dinta ya cutar da ita, bayan duk abubuwan da ta yi going through”

“Maleek”

Abiey ya kira sunansa a natse.

“Na'am”

“Umminka ta san ka kira ni?”

“Okay don't tell her, karka ma nuna mata mun yi waya, maganar Ameer da Waira kuma ka barta a hannuna Waira tana karkashin iko na ne a yanzu, that's mean nine jagoranta a yanzu, and na manta ma ban fada maka ba, tun kwana baya na saka a bincika min garinsu ko za a samu danginta”

“Okay”

Maleek ya fada sannan ya sauke wayar yana dan jin sassauci a ransa, dazun kan jin yake kamar ya cire zuciyar daga kirjinsa ya jefar tsabar bakinciki da rudani.

AMEER POV.

After yayi dropping Humairah ya nufi gurin friends dinsa he spends time with them sai bayan Sallah Isha'i ya nufi gidan Daddy. A al'adar da ya daukarwa kansa a yanzu yana shiga gidan fuska a not like can baya da yake musu yadda yake so. Teema ce kadai a falon

MALEEK POV. 

Da sassarfa ya sauko kana ganinsa kasan sauri yake yi, domin kilif din rigarsa ma yanzu yake kokarin sakawa, sanye yake da sky blue shadda kansa babu hula sai dai royal shoes ne a kafarsa dark blue da suka karawa shaddar kyau.

“Yadda ka sha wankan nan kyauta ace zance zaka je, ina matukar son na ga aurenku”

Cewar Ummi tana tauna yayan itatuwa dake gabanta zube a plate. Maleek yayi murmushi not knowing what to say domin shi dai be san ranar da tunanin aure zai zo masa har yayi yunkurin yi, kawai dai yana fatar wata rana shi ma ya zama kamar ko wane namiji ko dan cika burin mahaifiyarsa.

“Ameer dai ya kama haya”

Maleek ya dan tabe baki.

“Good for him”

Ummi ta yi murmushi tana kallon agogon da Maleek ya ciro aljihunsa ta ce.

“And abun farincikin, kasan wa yake son ya aura Waira”

He don't know how when da agogon da yake kokarin daurawa ya subuce daga hannunsa ya fadi kasa, glass din dake jikin fuskar agogon ya fashe ya kalli Ummi da sauro jikinsa na shocking fuskarsa na nuna tsananin mamaki da kiyayya da abun da yake na farinciki ne a gurin Ummi.

“What Wai... Ra... How....? That can't be possible, yanzu kin fahimci abun da nake fada miki ko? Yana da wani manufa akan yarinyar nan, rayuwarta yake son lalatawa kamar yadda yayi ma Nimra, daman opportunity kawai yake nema”

Ummi ta aje grapes din hannunta ta mike tsaye.

“No ba yadda kake tunani ba ne, wannan karon da gaske yake, na ga hakan a cikin idonsa, kuma aurenta yace zai yi, ita ma kuma na san tana sonsa, domin shakuwarsu da yadda suke kula junansu ya isa ya fahimtar da duk wani mai ido haka”

He don't want to argue with her because he don't has that energy now, jikinsa rawa yake kamar yadda zuciyarsa ma take ra rawa gaba daya tunaninsa ya rikice kuma ba zai iya fadar dalili ba, kawai dai shi dai ya san baya son Ameer ya kusanci Waira balle kuma aure ya hada su. Kamar wadda aka daurewa baki haka yayi shiru ya nufi kofar fita falon, Ummi dake ta kafa masa hujjoji ta bishi da kallo ganin kamar hankalinsa baya gurinta, kamin ya shiga motarsa har gumi mai zafi ya jika shaddar jikinsa ya shiga ya zauna ba tare da ya tashi motar ba, duk wani hanzari da yake na fita daga gidan zuwa gurin da yake ta uzuri sai ya kau hausawa suka ce sawun giwa ya take na rakumi. Ya kusan minti talatin a cikin motar zaune kamar ruwa sannan ya rufe motar ya saka key din ya tashi motar. Tukin kawai yake ya manta inda zai je, titin ya bi ya kai karshensa ya dawo ya sake kaiwa karshen ya sake dawowa haka yayi ta wuce gidansu yana zagayo kamar wanda aka yi ma sihiri. Can kuma ya faka motarsa kusa da gidansu ya ciro wayarsa ya kira Abiey domin shi kadai ne mutumen da yake jin zai iya fadawa wannan maganar au tattauna kuma ya fahimce shi. Ringing biyu kamin ta yi na uku Abiey ya daga.

“Son”

“Abiey akwai matsala”

“Kamar ta me?”

“Wai Ameer yau ya fadawa Ummi yana son ya auri Waira imagine?”

“What? Bayan duk abun da yayi? Ita kanta yarinyar ya manta yadda ya barta a wulakance yanzu an dauke an gyarata ta yi kyau shi ne zai ce zai aureta”

Maleek ya tashi zaune da kyau yana jin yadda Daddy ya tabo masa inda yake masa kaikaiyi.

“Yauwa Abiey dadina da kai kana da sauri fahimta, ni abun ya bani mamaki kuma ya ba ji tsoro jikina shaking kawai yake gaba daya tunanina ya jagule bana son na ga abun da zai cutar da yarinyar nan ko kadan, amman Ummi bata ganewa sai fadar take wai ba yadda nake tunani ba ne, gaba daya na rikice Wallahi na ma rasa kalar tunanin da zan yi, amman gaskiya ba zan jure ganin Ameer tare da Waira ba innocent soul like her”

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.