Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 65 of 227

A nan ma sai da Ameer ya dan saurari wakar, Nimra kam duk zuwan da suke bata taba kula da abun da Humaira take ba... Sai da suka nufo hanyar fita daga gurin sannan ta janye hannunta daga rikon da yayi mata ta gyara zaman mask din dake fuskarta, shi ya fara shiga sannan ta bude ya shiga yayi motar key, a hankali yake tuka motar har suka isa gidansa ya danna horn mai gadi ya bude masa ya shiga da motar, a da can idan ta shigo gidan tsoro take ji saboda bata saba ba, sai ta rika ganin kamar wani zai ganta, gashi daman bata saba zuwa dakin saurayi ba, yanzu kuwa Ameer ya bude mata ido, domin basa da gurin hira sai a nan kadai saboda bata son yan gidansu su san tana soyayya da Ameer, bata shiryawa hakan a yanzu ba, kuma bata san ranar da zata shirya ba, domin a kullum tana fargabar barinsa yaje gidansu da sunan hira, ta toshe duk wata hanya da za a gane cewar da shi take mu'amala tun daga kan hotunansa har zuwa chat din da suke da kiran waya.

“Sai yaushe?”

“Wani lokacin kuma”

“Karki dauki lokaci kin san bana son nisa dake, ni far har tsoro nake Allah yasa ba breaking heart dina zaki yi ba, saboda kin ki yarda yan gidanku su san ni”

“Ba zan taba iya breaking heart dinka ba Ameer kasani, kawai ina tsoron abun da zai biyo baya ne, ina matukar tsoron Mahaifina kara ma Ummi tana da fahimta da hakuri, amman Abiey idan ransa ya bace baya yi da sauki”

“Baki shiryawa fuskartar ko wane kalar kalubale akaina ba kika bari na fada sonki? Mi na yi ma iyayenki ne suka tsane ni? Just because of abun da ya faru tsakanin da Maleek ni fa na dade da watsar wannan abun, soyayya ba haramun bace kuma aure ba zamu yi ba wai muna soyayyar ba ne dan mu rabu, da kin san yadda Daddy yake matsa min lamba akan maganar aure da kin tausaya min”

“Ni ma ai matsa min ake yi, kawai na kasa fitowa na fada musu cewar kai bake so ne, na kuma kasa bawa kowa kofar da zai furta min so ko ya nuna min haka, saboda gudun kar a cilasta ni na fitar da wani ba kai ba, ina matukar sonka Ameer, na jefawa maza da yawa dutse saboda da kai, kamin na hadu da kai idan maza sun taya ni bana amsawa balle na siyar, bayan haduwa ta kai ma kamar ammin turaren farinjini haka maza bina da nuna soyayyar a gareni, amman na saka amsar kowa, idona be ganin kowa zai kai Ameer, bana jin muryar wani namijin na jidadi sai kai, sunan kowa baya min dadi sai kai, kullum mafarkina da burina yadda zan yi rayuwa da kai ne, na karya dokakin gidanmu, na gurbata tarbiyata saboda kai Ameer, yanzu kuma ina shirin fuskarta wani babban kalubalen saboda kai, Allah yasa wata rana karka juya min baya, karki min irin abun da wasu mazan suke yi na butulcewa matarsu, idan na rasa ka zan shiga mawuyacin hali, ina matukar sonka Ameer...”

Tana maganar hawaye na sauko mata, gaba daya sai jikinsa yayi sanyi zuciyarsa ta yi wani iri, a sirrance ya sauke ajiyar zuciya, ya matsar da fuskarsa kusa da tata ya tsatsa bakinta, sai ta lumshe ido hawayen na cigaba da yi mata zuba....

“Ya kamata ki tafi kar a sake kiranki, i love you”

Ta bude ido ta share hawayen tana kallonsa, sannan ta bude motarsa ta fita ta nufi tata motar ta shiga, ta murza key ta yi reverse tare da horn Mai Gadinsa ya bude mata ta fice. Ta madubin motar yana hangota har ta fice sannan ya kwantar da kujerarsa baya ya jingina ya lumshe ido yana busar da iskar bakinsa...

©Khadeeja Candy
©®Copyright
2023
[6/17, 10:49 PM] My S Line: 27

Hanne ta kawo ma Dr Zainab abincinta a daki, yaranta kuma suka ci nasu abinci a falo bayan sun yi sallah. Maleek ne kawai ya fito da abincinsa a waje ya zauna ya ci a balcony da ya gama kuma sai ya zauna a gurin be tashi ya cigaba da latsa wayar da yake. Sai da yamma list Ummi ta hada Waira tea ta kuma saka Hanne ta soya mata dankali, sai ta fito ta zauna a Balcony nesa da inda Maleek yake zaune tana sipping tea da Biscuit, irish din da aka soya mata ma bata taba shi ba, idonta harabar gidan kawai take kallo da motocin da aka faka, har yanzu tana mamakin yadda rayuwarsu mutanen gidan take duk girman gidan ace su kadai suke rayuwa a ciki, ga kawata ko'ina da aka yi kamar ba za a mutu ba, har gobe tana tsoron hawa mota sai dai tsoronta ya ragu ba kamar da ba. Jin an zauna kusa da ita ya saka ta juyo a hankali sai ta yi arba ďaya daga cikin bakin da suka zo dazun, murmushi yayi mata ita kuma ta maida kanta kasa ba tare da tace masa komai ba. Ya kai hannunsa ya dauki biscuit ďaya ya fara ci.

“Waya saka miki zobe a wuya?”

Ta kalli zoben.

“Sulem...”

“Sulem.... Waye kuma Sulem.... Saurayinki ne?”

Ta yi shiru, sai ya kara matsowa kusa da ita.

“Na sanki ni na tsince ki a lokacin da aka jefar da ke kin tuna”

Ta kalleshi da kyau.

“Yes karki min karya kin san dai na sanki ko? Fada min ina iyayenki suke, na sani ma domin yayanki abokina ne kuma na ga suna nemanki, amman ina son na sake sani ne”

Ba zata iya fadar wanda ya dauko a lokacin da hankalinta ya gushe ba, sai dai ta san kamin ta suma mutumen da ta gani ko kadan be yi kama da wannan ba. Hakan ya saka ta mika hannunta ta taba hannunsa be san manufar ta yi hakan ba shiyasa be hana ta taba hannun nashi ba, sai ma kallon hannun da yayi. Gardamar da suka yi da Mahmood ta gani har yayi ikirarin cewar shi ya san yadda zai yi ta fada masa inda iyayenta suke, bayan Mahmood ya labarta masa cewar har yau bata taba cewa komai akan iyayenta ba.

Be ankaro ba ya ji ya bushe da dariya sosai har tana tintsirawara, shi ma murmushi yayi yana kallon yadda dariyarta take da burgewa. Maleek ma sai da ya dago ya kalleta ya dauke kai ya cigaba da latsa wayar da yake.

“What...”

Jabir ya tambaya yana kallon kansa da mamaki domin ban san abun da take yi ma dariya ba, Waira kam plan dinsa take dariya da yadda ya sha alwashin sai ya mata wayo ta fada masa komai. Kofar falon aka bude Ummi ta leko tare da Mahmood da Nimra har da Hanne suna kallon ikon Allah.

“Jabir me ka fada mata take dariya haka?”

Ya dan karkato ya kallesu.

“Nothing bata dariya ne?”

“Tun da take a gidan nan bata taba dariya ta kyalkyata ba”

Ya juyo ya kalleta a yanzu kuma murmushi take wanda ya bayyana hakoranta. Ummi ta yi murmushi cike da jindadin ganin farincikin Waira.

“Well done Jabir daga zuwanka ka saka min ƴa dariya”

Yayi dariya shi ma ba tare da sanin abun da Waira take yi ma dariya ba, shi dai ya san tambayar kawai yayi after that be fada mata wani abun dariya ba. Ummi ta juya ta koma ciki tare da Hanne suna ta mamaki, Nimra kuma ta kashe masa ido irin na zolaya.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.