Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 25 of 227

“Ummi ta cika daukar komai da girma, ko karamin abu ne sai ta dauka ta saka a ranta”

Maleek ya fada, duk a tunaninsu saboda abun da ya faru ne take kuka ban da Abiey da ya san dalilin kukanta.

“Ku fita waje bari na yi magana da ita”

Fita suka yi daga dakin cikin damuwa, ko a tsakaninsu wani ya shiga damuwa damuwa suke da Matsalarsa balle kuma uwa kamar Ummi. Sai da suka fice sannan ya zauna kusa da ita ta kalleta da duba na tsanaki  da natsuwa ya ce.

“Wannan kukan duk na minene? Na fada miki an yi solving matsalar nan komai ya wuce, kuma na miki alkawari iri haka ba zai sake faruwa ba”

Sai a lokacin ta samu damar dago kai ta kalleshi da jajayen idanuwanta.

“Abiey ka san yaron nan?”

“Ni ban taba ganinsa ba”

“Amman kasan mahaifinsa?”

“Aa na dai yi magana da step mother dinsa”

Ta hade kuka daker.

“Mahmood.... Mood.... Ya ce dan Mr Bashir ne kuma yan Kano ne”

“Eh haka ne, mun yi magana da ita kuma ta tabbatar mana cewar ba zai sake ba”

Ta kai hannu ta dauki wayarta ta bude ta nuna masa hoton Ameer, karba yayi ya duba.

“Oh shi ne wannan yaron kamar mai natsuwa, Allah ya shirya na fadawa Maleek kar na sake ganinsu tare”

“Ranka ya dade Ameer ne, Ameer..... Ameer...”

“Wane Ameer kuma?”

Gangan yayi mata haka saboda ya kawar mata da tunanin da take.

“Dana Ameer...”

Wani irin deep breath Abiey yayi taking sannan ya ce.

“Kina da wani ďa bayan Maleek da Mahood?”

Hajiya Zahra ta kalleshi da duba na irin wanda yake son yayi wasa da hankalinta ya juya tunaninta.

“Ameer ďana na farko da na fara haihuwa, ďan da na haifa da Deen, ka kalli fuskarsa sunansa da sunan mahaifinsa”

Wani irin kallo Abiey yake mata mai kama da harara zuciyarsa ta hau bugawa da mugun karfi.

“Wata kila ba ki gane ba ne”

“Na gane shi Ameer ne Wallahi, ta ya zan auri ubansa na haife, na kwana da shi a raina na tashi da shi har yau tunanin Ameer be bar raina ba kuma ka fada min cewar ban gane ba, wannan ďana ne Abiey jinina ne, ka daina canja min tunani Abiey mu ba yara ba ne”

Mikewa yayi tsaye ya daka mata tsawa da sai da ta zabura.

“Kin gane shi saboda har yanzu kina rike da shi da ubansa a ranki, na dade da sanin cewar Mr Bashir yana garin nan tare da Iyakinsa sai dai ban san akwai alaka tsakanin ďansa da Maleek ba, da ban bari abun ya kawo haka ba, ni da ke mun dade da rufe babin Deen da duk wani abu da ya shafe shi, ďa dai kin riga kin siyar yana da rayuwarsa da iyayensa a yanzu, yana da dangi da yan'uwa, ba san ki ba be san da labarinki ba, so this should be the last time da zaki sake yin maganar Ameer a gidan nan, kar son zuciya ya saka ki rusa rayuwarsa da ta wanda kika bawa, karki ruguza farincikin Mr Bashir da shi kanshi Ameer din, and mafi muhimmanci yarana ba su san da wannan maganar ba, ba su san ma kin taba auren wani kamin ni ba, karki kawo mana wani bakon al'amari a gida, na fi son yayana fiye da kowa karki tashi hankalin yayana...!”

Yana kaiwa nan ya kabe rigarsa ya fice daga dakin a fusace har yana sakin kofar da karfi.  Kalaman da yayi mata a yanzu sun kara tabbatar mata da cewar Ameer din ta ne, sai dai ya shata mata layin da bata isa ta tsallaka ba, kamar yadda ta yi ma kanta kataga tsakaninta da shi da bata isa ta rusata a yanzu ba. Ba tayi mamakin kalaman mijinta ba domin ta san ba shi da makiyi kamar Deen, hakan ya saka a duk lokacin da ta nuna damuwa akan Ameer sai ransa ya bace ya ce saboda yana ďan Deen ne, a kullum ikirarinsa bata son Maleek saboda jininsa ne sai Ameer da yake ďan makiyinsa.

‘Gaskiya ne, Ameer ba ďana ba ne a yanzu, ďan wasu ne, yana da family da iyaye yana da rayuwarsa ta dabam’

Da zuciyarta take magana tana kokarin ganin ta kawar da tunaninsa a ranta ta cire shi daga zuciyarta, ko ba komai yanzu dai ta san yana a guri mai kyau kamar yadda take buri, ta san Mr Bashir ya ba shi gata da kulawa kamar yadda yayi mata alkawari tun da har ya hana police su kama shi saboda abun da ya aikatawa ďanta Maleek, ya girma a yanzu ya zama babban Saurayi rayuwar baya ba ita ce a yanzu ba, ya kamata ta manta da komai. Hakan ya saka ta tashi ta shiga bandaki ta wanke fuskarta ta fito ta zauna bakin gadonta dafe da zuciyarta, har yanzu bata daina jin wannan mashin da ya tsoki kahon zuciyarta ba, a yanzu kam ta yarda ta rasa Ameer har a bada, sai dai idan ta tuna bata bashi kulawa yadda ya kamata ba, sai ta ji wani iri a ranta, ga cutarwa da ta yi ma iyayen Deen na raba su da ďan Deen tilo da zai iya zame musu sanyin ido.

“Hakki ba zai bar ni ba, na cutar da yaron nan na cutar da kananinsa na cutar da kaina, miyasa ban yarda na karbi hukunci tun a wacan lokacin ba?”

Ta fashe da kuka sosai tana tsananin nadamar abun da ta aikata, ina ma ace da halin gyara da ta gyara komai a yanzu, yanzu ta kara tabbatar da hakkin ne yake bibiyarta shiyasa Maleek baya kaunar matsowa kusa da ita, kuma baya son ko muryar mata ya ji, ita kuma ta kasa manta abun da ta aikata hakan ya hana ta farinciki. Mikewa ta yi tsaye ta dauki wayarta ta yi clearly din searching din da Namra ta yi mata na Ameer, a kokarin na engaged din kanta da wani abu ya saka ya canja tufafin jikinta zuwa wasu marar nauyi ta sauko falo, Mahmood kawai ta samu zaune yana lasa wayarsa, dagowa yayi yana kallonta har lokacin idonta be cire kumburi ba.

“Abiey yace mana Bachi kike”

“Yanzu na farka”

Ta fada tana kokarin ta yi murmushi amman ta kasa, haka ta wuce Kitchen suna da masu aiki, sai dai ta sabawa kanta ita take girkawa mijinta abun da zai ci da kanta, hakan ya saka ta fara shirye shiryen girka masa abin da ya fi kauna saboda ta san ransa ya bace, sai dai me tana kai hannu ta bude fridge sai ta fashe da kuka.

AMEER POV.

Be isa Katsina ba sai 11pm na dare sai da ya fara tsara dajikan garin ya fara tunanin me ma zai kawo shi garin? Miyasa ya zo nan?

“To ina zan je idan ba nan ba?”

Ta tambayi kansa domin ya san barin kasar a yanzu ba abu ne mai sauki a gare shi ba, idan ma ya bar kasar duk inda zai je zai samu kansa cikin bacin rai ne da damuwa. Ya cika bakinsa da iska ya busar tare da kai hannu ya dauki wayar Nimra da sakonta na uku ya shigo domin jin lafiyarsa tsoron kiransa take kar ransa ya kara baci wata kila be huce ba har yanzu.
Kai tsaye ya aika mata da kira ringing daya ta daga kamar daman can jiran kiransa ake, sai dai yayi mamakin jin wata muryar wacce ta girmi ta Nimra ta daga wayar tare da sallama, da gangan yaki amsa sallamar domin ya san ba Nimra ba ce, kuma shi tun da ba wanda yake son waya da ita ce ta daga ba be ga amfanin yin magana ba, sai kawai ya kashe wayar. After like 3 minutes Nimra ta kira shi sai ya daga ya saka ta a speaker.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.