Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 131 of 227
“Wai haka aka ce ku yi a makaranta? Kina wahalar da wannan zomon ace sai an dora shi kan takardar sannan a zana waya ce ku zana zomo”
Waira ta kalleta with her cute laugh ta ce.
“Babu wanda ya ce na yi Ummi, kawai ina son na zana ne”
“Kin sa miyasa mai lessons dinki be zo ba yau?”
“Aa be ce komai ba da zai tafi”
“Ko maybe ba shi da lafiya ne?”
Waira ta bude baki zata yi magana kenan aka murda kofar falon, Ummi ta juyo ta kalli kofar Maleek kuma ya dago kansa ya kalli kofar, Waira ta maida dubanta a inda suke kallo. Ameer ne ya shigo cikin shiga ta kananan kaya sai kamshi yake kamar sabon ango, hannunsa rike da school bag din Waira. Mamakin zuwansa ya hana Ummi amsa sallamar da yayi, Maleek kam daman shi ba zai amsa masa ba, balle kuma Namra da sai a lokacin ta dago ta kalleshi. Waira ta washe hakora kamar bakauye ya zo birni, Hanne ce kawai ta amsa masa sallama domin bata wayance shi da kyau ba. Maleek ma mamakin zuwansa yake duk kuwa da yana kallon dalilinsa na zuwa wato jakar Waira dake rike a hannunsa, sai dai abun da ya fi daure masa kai shi ne yadda Ameer yake kokarin kula Waira yarinyar da ko a mafarki aka ce masa Ameer zai yi haka ba zai yarda ba.
“Ba a maraba da zuwana ne?”
Ya fada ganin yadda kowa yayi tsaye yana kallonsa kamar sun samu tv. Sai a lokacin Ummi ta dawo hayyacinta tunaninta ya dawo jikinta.
“Of course you're welcome, kai da gidan mahaifiyarka Ameer”
Ta fada idonta na cika da hawaye even though ta san ba zuwansa ne ya kawo ta amman a haka murna take ďanta ya shigo gidanta, sallamar da yayi kawai ta isa ta saka ta fahimtar da lalama ya shigo gidan nan.
“Please dan Allah ka zauna”
Kujerar da ta nuna masa dabam kujerar da ya zauna dabam, ta nuna masa dayar kujerar dake kusa da inda Waira ta dora jakarta, shi kuma sai ya zauna a kujerar da ke kusa da Waira. Da sauri Waira ta saki abun da take ta tashi tsaye ta zauna kusa da shi kamar zata shige jikinsa.
“Jakata ka kawo?”
Ya daga mata kai try to smile, kallonta kawai yake kana gani kasan ta gama dauke masa hankali, domin ko kadan be lura da sauran mutanen da suke falon ba, balle har ya san da zamansu.
After two weeks later...
Yana tafe Fiyya na bayansa rike da basket din da Mummy ta zuba masa kulolin abincin da za a kawo asibitin. Shi ya fara tura kofar ya shiga ya rike mata kofar ta shiga sannan ya rufe. Fiyya ce ta fara karasawa gurin gadon ta aje musu abincin tana yi ma Tsohuwar ya jiki tare da isar musu da gaisuwar Mummy, domin ita bayan kwana biyu take zuwa ta duba su, kanensa kuma time time idan zai so ko direba zai kawo abinci, Ameer kan kullum idan zai je aiki ko ya dawo sai ya shigo asibitin duba tsohuwar, domin jin yake kamar nauyinta a yanzu yana kansa.
“Ya jikin?”
Ya tambaya yana kallon Tsohuwar dake rike da ayaba tana ci.
“Jiki Alhamdulillah ďan nan, Allah yayi albarka kana ta fama da dawainiya”
Humaira ta mike tsaye ta bashi kujera, sai dai ta san ba zai zauna ba, domin ba gwada zama a dakin ba duk zuwan da yake.
“Kullum zai kin kin ba ni kujera, kuma kin san ba zama nake ba”
Ta yi murmushi.
“Ina jin ba dadi ne ace ina zaune kana tsaye”
“Kuma kullum sai na tararda ke a nan ke kike jinyarta bayan ga mahaifiyarki, ba kasafai nake tararda ita, Allah yass dai kina zuwa aiki”
“Duk lokacin da zaka zo kana sa'a da ina nan ne shiyasa, aiki kuma na daina zuwa ai tun a wacan lokacin”
Ya daga mata kai.
“You got lucky na canja if da yanzu na koreki”
Dariya Fiyya ta yi kamar yadda Humaira ma ta yi dariyar.
“Baka bukatar ka koreni ai, ni na kore kaina?”
“Why?”
Ta daga kafadunta.
“Kawai dai”
Be sace cewa komai ba, ya kalli agogon hannunsa.
“Kuna bukatar wani abu?”
“Aa bama bukatar komai a yanzu”
Shigowar da Dr yayi ne ya katse hanzarinsa daga yi musu sallama ya fice. Likitan dake cikin shiga ta kayan likitoci ya iso gurin ya mikawa Ameer hannu suka gaisa.
“An fada maka sakona”
Ameer ya kalli Humaira wadda ta dago tana kallon Likitan.
“Yanzu nake kokarin yi masa bayani”
Likitan yayi murmushi.
“Kin manta kenan?”
“Aa na tuna yanzu da na ganka”
Ta fuskanci Ameer dake jiran abun da zata fada masa.
“Yace gobe za a kwance daurin da aka yi mata, a duba, idan yayi haka ake so, idan kuma be yi ba sai an sake wani”
Tana fadar idonta na cika da kwalla.
“Sarkin kuka daga magana sai hawaye, haka jiya kika min fa”
Likitan ya fada yana kallonta.
“Bana son tashin hankali, ba mu da yawa a dangi kusa, bana son na sake rasa kowa”
“Ba saki rasata ba, aiki ne kawai kuma ni ba cinye ta zan yi ba, I'm not zombie”
Ta yi murmushi tana share hawayen idonta.
“Ni ban ce ba”
“Da dai yafi”
Duk abun da ake Ameer be ce uffan ba, sai kallon tsohuwar dake cin ayarba hankali kwace yake kamar ba ita ake fadar za a sakewa aiki ba.
“Ita hankalinta a kwance ma yake naki ne a tashe”
Likitan ya fada yana kallon Humairah
“Toh abun da Allah ya kawo ba sai hakuri ba, gwagwarmaya wace kala ce ba mu gani ba?”
Ameer yayi murmushi yana kallonta, karfin halinta da imani ya burge shi.
“Allah ya kara lafiya”
Ya fada sannan yayi ma Fiyya alama da su tafi da ido, Fiyya ta yi musu sallama suka fice. Likitan ya juya ya kalli Ameer har sai da ya fice sannan ya maida dubansa gurin Humairah.
“Am ya sunanki ma?”
“Humairah..”
“Haka ashe na rike sunan”
Ta yi murmushi tare da sauke kai kasa, sai ya dauki file din da ya shigo dashi bayan ya gama duba Tsohuwar ya fice. Zaunawa Humairah ta yi tana fadin.
“Yau Mama bata zo da wuri ba, gashi ina son na shiga makaranta kar na yi latti”
“Ki zuba min abinci da aka kawo sai ki tafi, ai zata zo wata kila ta tsaya wanke tsumman da tafi da su jiya ne”
“Maybe”
Ta dauki plate din ta bude coolar jalof din shimkafa ce da aka yi mata ado da doya ta sha kayan kamshi da vegetables ga kuma mai har yayi yawa. Rabin plate ta zuba mata ta dora mata a saman gadon ta matsa mata da ruwa kusa.
“Ba zaki ci abincin ba?”
“Sai na dawo zan ci”
“Toh Allah ya kiyaye hanya, yau ba su bada kudin da suka saba fadawa ba”
“Yau da gobe ai sai Allah Hajiya, wata kila sun fara gajiya ne ko kuma sun manta”
“Ba dai gajiya ba, sai dai ko mantuwa amman dan dan abun da suke ba mu ai be taka kara ya karya ba a dukiyarsu. Ni ba dan ba a son kaddara ba ai da na ce kara da aka yi haka, dubi ki ga kullum sai an kawo abinci, ga kudin nan, kuma sun dauke duk wata hidima ta asibitin nan, gaskiya suna da kirki, ko da can ke ce da masifar ki kike ganin kamar ba shi da kirki, kullum fa sai ya zo, mamansa ma kullum tana hanya”
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.