Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 34 of 227
“Motar ta ce kawai, amman abun da kuke zargi ba ita ta aikata ba, ni ma kuma ba da ganganci na aikata hakan ba, daga ita har ni zamu zo station yanzu nan, amman zaku ba mu police daya da zamu tafi tareda shi a motar gida”
Su sansu sun san inda suka shigo, hakan ya saka ba su masa musun abun da ya bukata ba suka amince, sai ya juyo ya dawo cikin falon ya kalli Nimra ya ce.
“Tafi ki dauko mayafinki, kuma duk tambayar da za ayi miki ki ce ni na karbi motarki”
Ta daga masa kai sannan ta tashi da sauri ta shiga ciki, fitowarta ya zama aiki domin gani take kamar idan taje ba zata dawo ba, na tsoron yan sanda take ba domin a masu gadin gidansu ma akwai police fushin mahaifinta take tsoro kar ya sa a yanke mata hukunci mai tsauri. Maleek ne yaja motar dayan police din yana front seat Nimra kuma na baya. Aka bar Ummi daga ita sai mai aikinta da ta gagara komai sai kallon ikon Allah take, da can bata san miya faru ba amman a yanzu ta fara fahimta akwai matsala a gidan. Wani dishe-dishe Ummi ta fara gani yana jin jikinta babu karfi ko'ina ya dauki ziza kamar jijiyarta ta yi majirya ga kanta dake sarawa, dafa kan ta yi tana wani tangadi kamar wanda ta sha kayan maye, Mahmood na ganin haka yayi saurin karaso ya riketa ya zaunar da ita mai aikinta ma ta karoso kusa da ita tana mata sannu, bata iya amsawa domin bata jin wani kuzari na magana ma balle motsi, sai dai hankalinta be gushe ba, wani kalar yanayi take ji a jikinta wanda ya banbanta da wanda ta saba ji, a duk lokacin da kalar rashin lafiyar ta ziyarceta.
“Mahmood kai ni daki zan kwanta”
Ya mike tsaye da taimakon mai aikinsu suka haura da ita sama suka kwantar da ita kan gadonta, Mahmood ya lullubeta da blanket sannan ya kashe Ac dakin ya fito ransa a jagule. Lumshe ido ta yiba dan bachi ba sai dan ta samu sa'ida, tana jin yawunta ya kafe sosai har ya haddasa mata bushewar baki,
AMEER POV.
Yana tsaka da wanke idonsa fuskar Waira ta yi masa gizo, be san lokacin da ya bude idon haka da kumfa ba, a take yaji ya shige masa a idon, a nan yaji wani sabon amai na taso masa yana ta jin kyankyami a jikinsa, tun da yake a rayuwar be taba wanka tara at the same time ba sai yau, ba wanka iya na sabulu ba har da na tsarki sai da yayi ba kuma dan yayi komai ba, sai dan ganin Waira da yayi da tabata da carpet din yake ji ba kamar ma har da wankan tsarki yana bukata saboda kazantar ta yi jawa wata kila idan be yi wankan tsarki ba zai iya jawa kansa matsala aki karbar sallah shi.
Ya san yadda Hajiya Jamila take sakawa a tsabtace komai na dakinsa amman hakan be kwantar masa da hankali ya taba tawul din dake aje a bathroom din ba, haka ya fito ya nufi gurin da tufafinsa suke aje ya dauko sabbi fil ya saka sannan ya shafama jikinsa mai ya saka turare, talkami ya saka ya sauko fito daga dakinsa zuwa falon Hajiya Jamila tea ta fara tarbonsa da shi sannan ta zuba masa soyayyaen nama domin ya san yadda yake son naman da aka soya suya mai kyau, doya ta sarrafa masa da miyar kabeji wanda ta ji kaza, tun kan ta kawo masa abincin kamshi ya cika hancinsa. Lafiya lafiya ya fara cin abincin kamin ya tuna da kazantar Waira sai gashi ya tashi da sauri ya nufi bathroom din Hajiya Jamila cikin tashin hankali ta bi bayansa tana tambayar ko abincin ne be masa dadi ba ko kuma wani abun ya gani a ciki. Haka ta tsaya a bayansa tana kallonsa har ya gama aman ta kunna fanfo ta tara masa ruwa ya wanke bakinsa.
“Wani abu ka gani a cikin abincin ne?”
“No inda na tafi ne na ga wata kazanta da ban taba gani a rayuwata ba”
“Ina kaje Ameer?”
“Wani daji ne, a KT”
Bedroom suka dawo, ya zauna ya labarta Hajiya Jamila duk abun da ya faru ciki har da motar da Nimra ta bashi and da reason din da yake ganin ya saka ta ba shi motar. A yanayin yadda ya bata labarin ta gama fahimtar bashi da gaskiya domin shi ya fara tsokanar abokin nasa amman tsoron bacin ransa ya saka ta kasa nuna masa sai tausarshi take kar ya aikata abun da zai zame masa matsala.
“Da ka yi hakuri ka kyaleshi Ameer idan ma ya ci amanarka zai gani a nan gaba, zalinci ba shi da kyau idan ka zalinci mutum komai ta dade sai hakkinsa ya fita, ka saka masa ido kana zaune hakkinka zai ita matukar ya zalince ka Allah ba zai bar shi ba”
“Ni ko ba a taba ni ba, kin san zan taba balle kuma an taba ni, bana bari ga Allah”
Ya amsa mata kai tsaye, numfashi ta sauke a hankali ta mike tsaye.
“A dauko maka wani abincin?”
“Na koshi, a sama min flight din da zai tafi Abuja anjima zan kwanta yanzu idan babu kuma zan je da mota”
“Ba zaka kwana a nan ba?”
“No ina son na je na duba jikin Daddy hankalina ba zai kwanta ba sai na ganshi”
Hajiya Jamila ta shafa kansa, sannan ta fice cike da damuwar da ita kadai ta santa. Kwanta yayi saman lafiyayyen gadon abun ka da wanda ya marmarin bachi nan da nan bachin yayi gaba da shi.
Mafarkinsa gaba daya akan yarinyar da tunaninta ke saka shi tashin zuciya da mai ne, ba mafarkin abun da ya faru a dajin yake ba, mafarki yake akan wata yarinyar da aka tsabtace ta sha ido da kwalliya, kamshi ta ko'ina ta ratso taron jama'ar da ake gabatar da Event din da be san na minene ba, ta iso gare shi, sai ya risina kamar mai jiran isowarta ta saddan kansa kasa alamar girmamawa a gareta ita kuma ta cire wani zare a hannunta ta daura masa a wuya ta yi mashi murmushi, sannan ta juya ta fice daga taron a zuwa wani dakin dake da icen tuffa ga kuma wani itacen na dogon yaro (Dalbejiya or Bedi) a tsaye. Can kuma mafarkinsa ya sake daukarsa zuwa gidansu Nimra, kuka ya hango tana yi tana fadar shi yayi kisa ba ita ba, hakan ya sake haddasa fada a tsakaninsa da mahaifinsa har ya sake korarsa a karo na biyu...! Firgigit ya farko daga bachin na rana ya yarfar da hannu ya shafe wuyansa, tsabar kyamar Waira da yake ko a mafarki ya ga ta taba shi kazanta yake ji, Even though ya san mafarki ne amman hakan be hana shi sake yin wani wankan ba, har mamaki yake in wanda haukar mafarki da kwashe kwashe shi miye hadinsa da kazama da har zai kawo masa ita a bachi, ba kawo ta ne kawai matsalar ba daura masa zaren dake hannunta da tayi a wuya shi ne matsalar domin jinsa yake kamar gaske.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.