Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 71 of 227
Bayan kowa ya gama karyawa Ummi ta saka suka kwashe kayan suka kai kitchen, Maleek da Mahmood da Namra suka yi shirin tafiya aiki. Daman Waira tuni ta yi shirya a uniform dinta na makaranta school bus ta wuce da ita ita First fita a gidan sannan Maleek da Mahmood, daga baya Namra ita ma ta fice. Jabir kadai aka bari a gidan sai Umar da Nimra, shi ma be dade ba ya fita tare da Dr Zainab da Umar zuwa gurin wasu yan'uwansu da suke cikin garin Abuja.
Misalin 12pm Ummi na kitchen tana hada ma Waira cake Nimra ta shiga sanye da doguwar rigar material sai black hula dake kanta, jikin kofar kitchen din ta tsaya tana kallon Ummi.
“Ummi me kike yi”
“Cake”
Ta amsa mata ba tare da ta juyo ta kalleta.
“Waira ake yi ma ko? Toh a saka da mu, Ummi ina son zan tafi gurin saloon din nan jiya ban samu ba, amman yau na yi da ita zata gama min da wuri”
Shiru Ummi ta yi kamar ba zata amsa ba, tana ta kallon harabar gidan da take hangowa ta windows din kitchen din sai kuma ta juyo ta kalli Nimra.
“Miyasa ba ayi miki ba a jiya?”
“Akwai jira ne sosai kuma da kika kira ni cewar Mommy ta zo sai na fasa na dawo gida”
Ta daga mata kai.
“A dawo lafiya”
Har ta juya ta fita sai kuma ta juyo ta ce
“Ummi lafiya kike yau kuwa?”
“Me kika gani”
“Na ga kamar kina cikin damuwa yanayin ki ba kamar na kullum ba”
“Daman akan samu hakan ai a gurin ko wace uwa, wata rana farinciki wani lokacin kishiyarsa karki damu tafi inda zaki je Allah ya tsare”
“Ameen”
Ta juya ta fita, tana fita Ummi ta wanke hannunta a tap ta fito Kitchen din da sauri ta haura sama Hijabinta kawai ta dauko ta saka ta ta dauki key motarta ta koma jikin Windows din dakinta tana kallon waje, har sai da ta hango Nimra ta fito sannan ta sauko da sauri kamar zata fadi, a jikin kofar falo ta tsaya sai da Nimra ta shiga mota murza key sannan Ummi ta fito ko da ta shiga tata motar Nimra ta fice daga gidan, masu gadin suka fasa rufe gate din suka budewa Ummi. Ta yi sa'ar hango inda Nimra ta bi saboda titin unguwar mai tsayi ne sosai kamin ka kai karshen road din ka dauki wani tafiya ce mai dan nesa. A hankali Ummi take binta sai dai tana nesa da ita ta yadda Nimra ba zata iya hangota ba, ko kadan bata jindadin abun da take kokarin aikatawa na bibiyar sawun yarta, sai take jin kamar be kamata ta yi hakan ba, sai dai ya zame mata dole ko dan ta wanke zuciyarta daga zargin da take yi na Nimra. Sannu a hankali Nimra ta tuka motar har cikin unguwar da gidan Ameer yake, Ummi na binta sau da kafa har ta hango ta tsaya a bakin gate din wani gida ta danna horn, wani maji karfi ya leko gate din sannan ya koma ciki ya bude mata ta shiga. Ummi ta ji wani abu mai karfi ya tsaya mata a makoshi, zuciyarta ta hau bugawa fiye da kima, yaushe Nimra ta lalace haka? Miyasa zata watsar da tarbiyar gidansu ta dauki wata bakar dabi'a? Tun yaushe take mata karyar fita zuwa wani gurin tana zuwa nan? Gurin wa take zuwa?
“Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un”
Ta furta tana saka hannu ta dafe zuciyarta.
“Allah ka gani na iyawar iyawata, na ba su tarbiya daidai gwargwadon yadda zan iya, Allah ka kama min, na shiga uku ni Zahra, farko Ameer ta shi ta wuce, daga baya Maleek shi ma ya fara samun sauki a yanzu, sai kuma Nimra, bayan ita kuma sai wa”
Ta lumshe ido hawaye na sauko mata, son sanin me take aikatawa kuma da wa take aikatawa ya saka ta share hawayenta ta bude motar ta sauko, ta taka da kafa har zuwa inda gidan yake da tunani kala kala. Ta dade a tsaye sannan ta kai hannu ta kwankwasa gate din gidan, babu jimawa mutunen da ya budewa Nimra ya bude mata.
“Dan Allah tambaya nake ko masu gidan na ciki?”
Ta kalli Ummi sama da kasa, yana ganinta ya san ba irin masu zuwa manyan gidaje roko ko neman wani abu ba ne domin hannunta ma rike yake da key mota.
“Aa baya nan lafiya kike nemansa?”
“Lafiya kalau, na yi magana da shi ne yace na zo na same shi a nan”
“To gaskiya be iso ba, tukuna amman dai yana kan hanya tun da kika ga wannan matar ta zo”
Ummi ta hade yawun bakinta daker.
“Ko zan iya shiga na jira shi a ciki?”
“Aa gaskiya, saboda be yarda na bar kowa ya shiga gidan nan ba”
“Amman yanzu na ga wata ta shiga”
“Eh to ita ya san da zamanta, shi ya bada umarni da zarar ta zo na bude mata ta shiga”
“Amman dan Allah ta dade tana zuwa nan ne?”
“Wannan kuma wani abu ne da be kamata ki ji shi a bakina ba, domin be kamata na fadi wani abun da ya shafi gidan a gurin bakuwar fuska ba, dan Allah ki jira shi ya zo ko kuma ki kira shi”
“Haka ne, na bar wayata a mota bari na dauko na kira shi”
Ta juya ta nufi gurin motarta hawaye masu zafi na sauko mata, tana barin gurin mai gadin ya juya ya koma ciki ya dauki tasa wayar ya kira Ameer ya sanar masa abun da ya faru. Ummi na shiga motar ta dafe saka hannu biyu ta dafe kanta ta fashe da kuka....
AMEER POV.
“Oh Really”
“Kasan ai ba zan iya ce maka No ba, amman dai ka yi sauri domin ba zan dade ba, kasan dole na tafi gurin saloon din kar karyar ta yi yawa”
Yayi wani shegen murmushi yana lila da kujerar office din.
“Alright gani nan zuwa”
Ya aje wayar ya mike tsaye ya dauki keys dinsa ya fice daga Office din, sa sassafar ya sauko ya fito waje da tafiyarsa irin ta zarumai da basa jin wahalar komai kamar yadda basa da nauyin kowa akansu. Motarsa ya shiga ya murza key ya fita daga Kamfanin tana tuki a hankali, ransa be bace ba sai da ya kai gurin traffic, wani guntun tsaki yaja ya danna horn da karfi yana jin kamar ace zai iya taka motocin dake gabansa ya wuce, traffic na ďaya daga cikin abun da ya tsana a hanya. Ta cikin bakin gilashin motarsa ya hango wata kyakkyawar yarinya take cikin School Bus, tana sanye da uniform ta rumgume jakarta ta Teddy kana ganinta kasan a tsorace take, ta yi parking din gashin kanta baya, fara ce sol bw tabbatar da hakan ba sai da ya sauke gilashin motarsa yana kallonta, ji yayi kamar ya santa ko kuma ya taba ganin wata mai kama da ita a wani gurin sai dai ba zai iya tunawa ba.
“Amman yarinyar nan kina da masifar kyau”
Ya fada yana shafa kansa kallonta yake sosai, ita kam bata ma san yana yi ba domin hankalinta yana gurin motocin dake gaban bus dinsu, sai da aka saki green light sannan yaja motarsa zuwa hanyar gidansa yana waigen School Bus din da ta ďauki wata hanyar dabam. Wayarsa ta yi ringing ya dago wayar ya duba.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.