Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 175 of 227
“Akwai tsafi a jikina, ta yadda nake iya gane abun da ya faru da mutum a rayuwarsa ta baya, kuma zan iya wasu abubuwan na siddabaru idan ina so, amman ban taba yi ba, kuma ba zan iya fitar da tsafin ta hanya mai sauki ba, har sai na fasa jiki”
“Dole ne ki rabu da tsafin, ko da kuwa hakan na nufin tsare wani bangare na jikinki ne, a nawa ganin tsafi kaucewa Allah ne, a haka nake ganin be dace kina tare da shi ba, saboda haka nake shawararta ki idan har da gaske zaki yi addinin Allah kuma zaki karbe shi da zuciya daya ne, to ya kamata ki watsar da duk wani abu da zai kaiki ga shirka”
Ta daga masa kai. Sannan ya gabatar mata da kalmar shahada tana maimaitawa.
“Ashahadu Allah La'ilaha illallah”
“Ashahadu Allah La'ilaha illallah”
“Wa'ashadu ana Muhammadan rasullullah”
“Wa'ashadu ana Muhammadan rasullullah”
“Na shaida babu abun bautawa da gaskiya sai Allah, kuma na shaida Annabi Muhammad Manzon Allah ne”
Ta nanata haka hawaye na sauko mata, Ummi ma hawaye take matan dake hidima dake sallamacin ma kallonta suke with emotional.
“A yanzu kin zama musulma, kin dawo jaririya kamar a yau mahaifiyarki ta haife ki, baki da zunubi ko daya, kuma kin zama yar'uwarmu muma mun zama yan'uwanki zumuncin da ya fi na jini karfi, Allah ya tabbatar da ke a cikin addinin musulunci”
Waira ta fashe da kuka tana jinta a wani irin yanayi na aminci da gamsuwa da natsuwar da bata taba kasancewa ba. Namra ta rumgume ta tana hawaye, Ameer ya ji kaunarta ta kara cika masa zuciya, Maleek ya ji ta cika ta ko'ina a yanzu bata da bukatar kari.
“Maa Shaa Allah, barka da zuwa addinin Allah addinin amincin da kyautatawa, yanzu kin zama yata baki da banbanci da Namra ko Maleek a gurina”
Abiey ya fada yana kallonta cike da burgewa.
“Ya sunanki?”
Imam din ya tambaya. Sai ta amsa masa tana kuka.
“Waira”
“Waira suna ne mai kyau, sai dai asalin sunan Nuwaira ne ba Waira zalla ba, saboda haka zamu iya kiranki da Nuwaira, ko kina sha'awar a canja miki sunan ne?”
Ta girgiza kai alamar aa, ta juyo ya rumgume Ummi.
“Allah ya miki albarka ya tsare rayuwarki da imaninki Nuwaira”
Duk suka amsa da Ameen. Matan da Iman din ya gayyato suka gabatar da Nuwaira yadda zata yi ibada, wanka tsarkin da zata yi na shiga addinin musulunci, da kuma dokokin da suka wajaba a kanta, suka tambayeta ko akwai wata matsala da take fuska ta musallin ko abinci ko kuma wata baraza ta amsa da cewar babu ko daya. Sai da aka fara tada Sallah azahar sannan Mahmood ya dawo da su Ummi gida, Ameer da Maleek suka yi sallah a masallacin tare da Abiey.
Ummi ce ta jagoranci Nuwaira gurin nuna mata yadda zata yi wankan tsarkin, bayan ta nuna mata a waya yadda zata yi a waya sai da ta tabbatar ta iya sannan ta fita ta bata guri, Nuwaira ta yi wanka da kanta ta fito tana daure da tawul ta rufe kanta da wani. Ummi dake zaune gafen gadonta tana jiranta ta mike tsaye ta mika mata sabuwar rigar abayar da zata sauko mata har kasa.
“Wannan kyauta ce daga gareni, farkon zuwana makka na siyo rigar nan amman ban taba sakawa ba, da na aje har sai idan daya daga cikin yayana za su yi aure na ba su saboda tsadar rigar, sai dai musuluntar da kika yi a yau, ya saka kin zama ďaya daga cikin yayana, zan iya miki komai fiye da yadda zan yi musu ma”
Nuwaira ta tara hannu ta karba tana kallon Ummi dake hawaye tare da murmushi.
“Na gode, ina ma ace zan iya saka miki da duk abun da kika yi min? Hakika ke uwa ce ta gari, kin cancanci ko wane irin Award na girmamawa da karanci”
“Idan kin shirya ki fito waje yan'uwanki suna kasa suna jiranki”
Ta gyada kai sannan ta karbi rigar ta aje saman gadon. Ummin ta juya ta fice daga dakin, Hannu Nuwaira ta kai ta taba rigar yadda ta sha stone tana kyali ga yadin sai walwalniya yake yana daukar ido, kana kallon rigar kasan an zuba guri gurin siyenta. Ta dade tana kallon rigar sannan ta mike tsaye ta cire tawul dinta ta dauki rigar ta zura, daman can bata mu'alama da birejiya dan haka bata damu da neman inda take ba balle ta saka. Tana zura rigar ta dauki mayafin abayar ta rufe kanta sai ta taka gurin madubi ta kalli kanta. Dan murmushi ganin yadda dark green din abayar ta yi mata masifar kyau kai kace sarauniyar Abuja ce, tsayin rigar 58 ne ita kuma tana saka 54 ne haka ya saka rigar ta yi mata fadi da tsayi, sai dai ko kadan hakan be rage komai daga kyaunta ba. Ta saka hannu ta rike rigar tana takawa a hankali har ta isa gurin kofar ta bude ta fita, tana fara saukowa stiars idon kowa ya dawo kanta, Ameer be san lokacin da ya mike tsaye yana kallonta kamin murmushinsa ya fara yi mata marhabun da saukowa. Maleek ya kalleshi ya kalli Abiey sannan shi da Mahmood suka kalli juna, Ummi ma kallonsa ta yi kamin ta dauke ido ta kalli Nuwaira. Tsaye ta fara yi a lokacin da ta sauko har sai da Namra ta mike tsaye ta isa gurinta ta riko hannunta.
“Zo na nuna miki wani abu little Sis”
Gurin wata Laptop dake aje kan kujera Namra ta nufa da ita, suna isa ta saki hannunta ta bude laptop din ta shiga whatsapp din ta kunna video call, few seconds Shuraim yayi picking fuskarsa da murmushi, Nuwaira na ganinsa ta durkusa a gaban laptop din tana kallonsa da murmushi a fuskarta.
“Sulem...”
“Baby girl Welcome to World Of Islam, na yi matukar farinciki na jidadi a lokacin da na Namra takw fada min hukuncin da kika yanke, na yi bakinciki da bana kusa da ke, da yanzu da ni za a samu wannan ladar, amman a haka ma ina farinciki yanzu kin kallama komai duk wani abu da ake so a mace a yanzu kin hada shi”
“I miss you”
Ta fada hawaye na sauko mata.
“I miss you too baby girl, idan zan zo zan kawo miki tsaraba mai yawa kuma mai ban mamaki”
“Maybe ba zaka same ni ba, zan tafi gida gobe”
Shuraim ya dan yi jimm for some seconds sannan ya kalli Namra dake gafenta.
“Why? Akwai matsala ne Namra?”
“No ita dai take ra'ayin zuwa”
“Ina fatar ba za su cutar da ke ba”
“Nima ina fatar haka”
“Zan tare a Katsina, sai na ganki i miss you so much”
“Ina da labari da yawa da zan baka”
“Ni ma ina da labarai da yawa Baby girl ”
Ta taba hancinta ta kai hannunta ta taba jikin computer sai yayi dariya shi a ya taba hancinsa ya taba computer.
“See you”
Namra ta rufe computer, Nuwaira ta juya ta kalli Namra tana murmushi.
“Nuwaira ga wannan na san zai taimaka miki gurin Sallah saboda yanzu kika fara, yana magana kuma yana fadar duk wani tasbihi da ya kamata ki yi a cikin Sallah”
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.