Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 136 of 227

“Welcome”

A take dadin muryarta da shaukin ganinta ya wanzar da murmushi a fuskarsa.

“Thank you”

Ya amsa yana kallon yadda ta bude masa hakoranta ita kawai muryar yace zai zauna a gidan take. Ya kalli kanta.

“Ke miyasa baki son ďankwali? Baki rufe kanki? Kin ga gidan nan akwai maza da yawa kuma za a iya cewa yayi kyau ko ki burge wani”

“Su waye mutane?”

Ya wara ido yana kalle-kalle sannan ya kalli abun da ya fi daukar masa hankali a fuskarta wato idonsa.

“Masu aiki aljannu, ranar ma da wani saurayi na ganki a mota ga kuma Maleek da Mahmood”

Ya karasa yana rage murya kamar baya son a aji.

“Ni bana son komai a kaina, a garinmu ba a rufe kai, bana son rufe kai na”

“Mu kuma a nan ana rufewa ai, kin ga ko hulace ya kamata ae kina sakawa, idan a garenku ba ayi a nan ai ana yi, ko baki san kin girma ba? You're not that small child”

“Na sani, ni kawai bana son rufe kai ne”

“Sai idan zaki yi Sallah kawai kike rufewa?”

“Ni bana sallah ai”

Ya matso kusa da ita da mamaki.

“Ba ki sallah kamar yaya? Baki ga mutanen gidan suna sallah ba?”

“Na gani?”

“Uhmm?”

Ta motsa kafada.

“Bana yin irin addinku”

“Ohh too bad, Babe you missed alot, akwai wani irin natsuwa, da imani da kusanci da aminci da rahma da tsaro a cikin ganawa da Ubangiji, shiyasa bana yarda ko da raka'a daya na rasa balle kuma jam'i, kin bar dadi yarinya”

“Bana son na bar addinina, ko malamin dake mana lessons ya ce kar na kuskure na sake aikata laifi biyu kar na bar addinina”

“Christian ne?”

“Aa irin addininku yake”

“Kuma yake son hana ki, yana son karki kwashi rahma da lada ne kawai, ke baki ga yadda Ummi take yi ba? Be burgeki ba?”

“Ya burge ni, amman dai bana son na bar addinina”

“No one will force you, sai dai na miki alkawari matukar ina gidan nan sai rayuwarki ta haskaka zuciyarki ta bude ki karbi gaskiya”

Zancen zama a gidan da yayi ya tuna mata da abun da Ummi ta fada mata, cikin zumudi ta ce.

“Ummi tace zaka zauna a nan da gaske ne? Wai na raka ka zaka dauko kayanka?”

“Yes for, for her. Happy?”

Ta yi tsalle.

“Yes, can I hug you?”

“Da can da kike rumgumata izini kike nema?”

“Toh ai Ya Maleek ne ya ce ba kyau, wai harame ne”

Ta fada a shagwabe tana dan turo baki gaba, kalmar Haram ta kira da Harame domin haka kalmar ta zauna a kanta. Ya sakarwa fuskarta ido babu ko kyaftawa.

“Ke ai yanzu baki san banbancin Haram da Halal ba, hukuncin be hau kanki ba”

Ya rage tsawo tare da mika bakinsa ya sumbanci karan hancinta, yana dagowa motar Maleek na kunno kai cikin gidan, sai da ya kalli motar sannan ya sake maida bakinss ya sumbanci saman fatar idonta dake rufe tun a lokacin da ta ji numfashinsa na kokarin kwaurawa da nata. Jin karar motar ya saka ta bude idon da sauri ta juyo tana kallon motar dake fake saitinsu sai dai nesa da su, hakan kuma be hana ta yi ido hudu da Maleek ba, da ya kasa fitowa motar sai kallonsu yake, yaƙin duniya na uku na shirin haduwa a kirjinsa, yan sojojin zuciyarsa sai kawo makamai suke, jinin dake circulating a a jikinsa yana jefo masa da bomabamai.
[7/17, 6:22 PM] My S Line: 55

Ameer ya kai hannu ya juyo da fuskarta ta fuskance shi, sai ya sakar mata murmushi.

“Waya baki wannan zoben?”

Ya kai hannunsa ya taba zoben wuyanta, ta sauke kai ta kalli zoben.

“Sulem”

“Wane Sulem?”

Bata amsa masa ba ta juya ta kalli Maleek da ya bude mota ya fito idonsa na kansu. Ameer ya sake kai hannu ya juyo da fuskarta.

“Hey kalleni a nan karki sake juyawa, Sulem dan'uwanki ne?”

Ta girgiza kai tsoro na bayyana a fuskarta. Sai ya saka hannu biyu ya tsinka sarkar ba tare da tsayawa ya ji waye Sulem din a gurinta ba.

“Kai waya ce ka tsinka ina so fa”

“Zan siya miki wani, bana son ganinki da abun kowa sai nawa”

Tana mika hannu ta karba sai yayi baya da hannu yana murmushi, kamin ya juyo ya kalli Maleek dake magana yana aje numfashi da karfi.

“What a shame kamar kai? Yaushe ka gama da Nimra kuma ace cikin gidansu kana kokarin yi ma wata? Na yi zaton abubuwan da suka faru sun koya maka darasi, ashe kara maka kawai suka yi”

A take murmushin da fuskarta Ameer ya gushe, Waira ta koya bayan Ameer ta boya ganin Maleek ya tsaya daf inda take tsaye, sai tunaninta ya bata cewar dukanta zai yi.

“Ban zo dan yi rigima da wani ba, ban kira sunan wani ba, dan haka bana gayyatarka a rayuwata, ni ba yaro ba ne kamar kai, ina magana da Waira ne kawai, kuma ina tunanin babu alakata tsakanin Waira da Nimra, dan haka zanen kaddarar kowa ma dabam ne”

“Hakane. Shiyasa ya zama abun dariya da mamaki idan aka ganka da wata, watan ma yarinyar da ka yi ikirarin baka sani ba, baka tsoron hakki zai bibiye rayuwarka? Kissing her ka taba ta ba abun kunya ba ne a gurinka Maleek”

“Ita fa bata san banbancin halal da haram ba, a addininta komai daidai ne? Me kake kokarin karewa game da ita? Kai da na san babu ruwanka da rayuwar mata amman har kake iya magana saboda na taba ta? Miye damuwarka da haka? Ko dai kai ma ka fara rai ne? Na yi tunanin mataccen ne kai ai”

Ameer ya fada sannan ya kama Waira ya dawo da ita gabansa ya rike hannunta.

“Ni da kai muna da alaka da Nimra Ummi ta fada min, amman wannan ajiyata ce, ka daina shiga tsakanin bawa da Ubangidansa”

Yana fadar hakan ya nufi inda ya faka motar Ummi. Maleek ya hade yawu da karfi ya danne numfashinsa da duk wani bacin rai dake kokuwar barin zuciyarsa ya fito fili. Jin kamar ba zai iya jurewa ba ya saka shi juyowa ya kalli Waira dake kokarin shiga motar.

“Waira wuce ki shiga cikin gidan”

Kamar daman can umarnin take jira sai ta a juyo da sauri ta kalleshe ganin babu wasa a fuskarsa ya saka ta bar jikin motar da sauri ta nufi main door din gidan tana gadawa da gudu.

“Aa nonono karka tsallake layi Maleek, ba kamata haka na faruwa tsakaninmu ba, ya kamata ka zama mai tunani mana”

“Matukar ina raye ba zan bari ka lalata rayuwar yarinyar nan ba, tana a gidanmu under my father control”

“To zamu gani idan ka fini gata a gidan...!”

Ameer ya fada sannan ya rufe motar da karfi, ya rufawa Waira baya. Yana shiga cikin falon Waira na sauko da gudu daga stairs tana kuka, bata son fadan da suke akanta, gashi ta shiga ta yi ma Ummi complain bata same ta a dakinta ba.

“Me ya faru?”

Ameer ya tambaya yana jin wani irin tashin hankali a kallon hawayenta da yake. Tsoron zuwa bangaren Abiey take domin bata taba gwadawa ba, ganin kamar basa lasar miya a kwano daya ya saka bata sha'awar bin Ummi a duk lokacin da ta shiga bangaren. Hakan ya sakata ta zauna a saman kujera nesa da inda Ameer yake tsaye

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.