Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 214 of 227
“You're such a wonderful Sister, thank you sai na dawo”
Ya juya ya fice daga dakin, sosai tausayinsa ya kama Namra. Ta juya ta kalli Nuwaira dake kuka.
“Ina ma ban dawo ba, na bata ran mutane a nan na saka wasu a damuwa Ummi ma ba zata ji dadin haka ba, me yasa zan zaba a tsakanin yan'uwa?”
Namra ta aje system din hannunta ta nufi inda Nuwaira take tsaye ta rumgumeta.
“Baki da laifi ke ma, Ameer ba shi da laifi haka ma Maleek, so baya duba kusanci ko tazara, haka baya duba alaka da yan'uwanta baya duba arziki da talauci, na tabbatar da ace Ya Maleek ne ya rasa ki zai iya rasa ransa ma”
Nuwaira ta dago ta kalleta.
“Ya Maleek din?”
“Kwarai Nuwaira yana sonki fiye da yadda kike tunani, sai dai yana da wani irin kawaici da karfin hali, yana da halin girma da kokarin na danna abun da yake ji a ransa”
“Amman be taba fada min yana so ba”
“Yana duba alakarki da Ameer ne, amman a yanzu komai ya zo karshe dole ne kowa ya karbi kaddarasa kuma ya yarda da gaskiya”
Nuwaira ta maida kanta a kirjin Namra ta kwantar tana tunanin Maleek din. Gaba da rikicewa Maleek yayi a lokacin da Ameer ya sauko kasa, sai ya dan juya baya yana taba kayan dake dinning din, kunyar kallon Ameer yake kuma yana jin kamar be kyautawa Ameer din ba. Ameer na ganin haka ya isa gurinsa ya saka hannu biyu ya dafa shi yana murmushi.
“You got lucky, babu wanda ya fada min amman a yanzu na fahimci kai ta ce tana so kenan”
Maleek ya juyo ya kalleshi cikin karfin hali, zai yi magana Ameer ya tari numfashinsa.
“Please don't say anything, Wallahi ban ga laifinka ba, yarinyar nan ta cancanceka, kuma kai sadaukarwa ka yi da zuciya daya, sai Allah ya saka maka, na san zaka rike amana fiye da ni kuma ina mai tabbatar maka hakan ba zai taba alakarmu ba blood is thicker than water”
Maleek ya rugume shi yana jin babu dadi, if ba dan neman ya faranta ran Nuwairar ba da shi ma zai iya hakura da ita, domin ba ya jin zai iya samun farinciki ga bakinciki dan'uwansa. Ameer ya sake shi suka yi sallama sannan ya fice. Gidan Hajiya ya nufo a falo ya same ta bayan ya gama yi mata sallama ta sanar masa Humairah tana dakinta fever ya rufeta, cikin sauri ya shiga dakin sai ya same ta kwance a kan gadonta idonta a rufe ta lulluba da blanket. Gefen gadon ya zauna ya kira sunansa sai ta bude idonta a hankali.
“Me ya same ki?”
Hawaye ne ya sauko idonta.
“Ina ta tunanin abun da zan maka na dauke damuwar nan dake tare da kai a yanzu Ameer, gashi gobe zaka tafi zan yi kewarka sosai”
Yayi murmushi.
“Ki yi min addu'a kawai kuma tafiya ai zamu yi waya, zamu yi video call ma”
Ta tashi zaune.
“Zan je na yi magana da Nuwaira kamin ka dawo maybe ni zata fahimce ni”
“No na rufe babinta a yanzu Humairah, ba mu iya cilasta wasu su so mu, ya kamata mu koyi haka? Ba ma iya juya zuciyar wani garemu”
“Haka ne, da zamu iya da mun juyo da zuciyar wasu izuwa garemu, dole ne mu karbi kaddara”
“Yeah, kuma daman can kin yi min baki idan an rasa mai so na ba zai na dawo ki san yadda zaki yi da ni ba”
Cikin zolaya yayi mata maganar amman a take ta ji an zare mata duk wani ciwo da take ji, sai ta sauko da kafafuwanta ta sauke idonta kasa tana murmushi. Shi kuma ya mike tsaye yayi mata sallama ya fice daga dakin. A cikin mota ya zauna yayi ta kukansa kamin ya isa gidan Daddy domin duk wani abu da yake yana jurewa ne kawai saboda ya sabawa kansa amman deep down ya san yana cikin damuwa. A dare kasa kwana yayi ya raya dare da nafila yana rokon Allah ya cire masa son Nuwaira a ransa gana daya domin yanzu ya fahimci ba kaddarasa ba ce. Bayan sallah asuba ya samu kwantawa bachi minti talatin ya tashi ya shirya domin jirgi da zai bi da wuri zai tashi. 8 daidai Mommy ta shigo dakin ta dora masa da nata kalar nasihar ta karfafa masa guiwa har ma ta dora da cewar.
“Ni dai daman can saboda babu damar zaba maka mata ne, amman Daddynka Humairah ya ci burin ka aura, mun tattauna da shi ya nuna min haka tun a baya ma saboda yana ganin kamar zaku dace kuma hakan zai faranta ran Hajiya, ya gyara alakarta da Ummi, sai dai nuna masa kana son Nuwaira a ya saka dole ya aje maganarta a gefe, kuma tun da har ka ga Allah be baka ita ba to ba alheri ba ce a gareka, sai ka gode Allah kuma ka roki Allah ya baka mace ta gari”
“In Shaa Allah Mommy na gode, daman Humairah ce yarinyar da Daddy ya so ya gabatar min a matsayin matar aure?”
“Ita ce”
Yayi shiru be sake cewa komai ba har ta fice daga daki.
Memorial Sloan Kettering Cancer Center United Kingdom. Misalin karfe 10 na dare jirginsu ya sauka a airport, zakuwa da son ganin Ummi ya hana shi sauka a gidan Daddy dake garin, kai tsaye ya dauki taxi zuwa asibiti, daki daki ya bi dokinsu sannan suka ba shi damar shiga dakin da Ummi take. Cikin fargaba da tunanin halin da zai tararda da mahaifiyarsa ga kuma tausayinta da ya cika masa zuciya ya shiga dakin. Slowly ya isa inda gadonta yake. Kusan dakin cike yake da na'urori kala kala na kula da ita, tana kwance a wani kasaitacen gadon asibiti sai bachi take, fatar jikinta ta yi haske sosai kamar ba nata ba, ga bakinta ya canja wani yanayi mai kamar tsufa ya bayyana a fuskarta. Zaunawa yayi a kujerar dake kusa da gadon ya kai hannunsa ya rika hannunta dake sanye da wata karamar na'ura yana kallonta, hawaye ne kawai ke zuba a idonsa kamin ya fashe da kuka marar sauti ya kifa kansa a gadon yana jin kamar ya mutu ya huta.
[8/19, 2:12 PM] 🦋-🦋: 83
Ummi bata farka ba sai kusan asuba domin ta dade bata samu bachi mai dadi irin na yau ba. Har lokacin kuma Ameer yana tare da ita yana jiran farkawar nata. At first rufe idonta ta yi bayan ta kalleshi a zatonta mafarki take, ta bude ido ganinsa ya saka ta sake rufewa wannan karon kuma sai ta yi tunanin gizo idonta suke mata. Har sai da ta ji hannunsa a fuskarta kamin ya kwanto ya dora kansa a saman kanta. Da sauri ta bude ido ta karkata kan tana kallonsa sai ya kirkiri murmushin karfin hali ya ce.
“Ssnnu Ummi”
“Ba mafarki nake ba?”
“Zahiri ne, ban Fada miki zan zo ba shiyasa kika ganin kamar bs gaske ba ne”
Ta gwada yunkurin tashi zaune saman babu kuzari.
“Ameer how are you”
“I'm fine Ummi ys jikinki”
“Alhamdulillah ina ta ibada kai kadai ka zo”
“Yeah kina son ganin wani ne?”
Ta yi shiru bata ce masa komai ba, sai kallonsa take irin kallon nan na kauna da take jin kamar ta bude zuciyarta ta saka shi, dayan hannunta ta kai ta taba fuskarsa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.